Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 59 of 86

Kusan duk suka fito Compaud É—in, sai kuma suka maida idonsu kan motar Baba Malam dake parking.
Da sauri Abba ya nufi wurinsa tare da bashi hannu yana murmushi yace.
“Kazo sallaman abokan kane”.
Malam É—in na shafa kan Zaid da Zaitoon da suke hannun Mahmoud daya matso dasu yace.
"A'a ni ƴaƴana nazo in sallama in musu addu'a, su waɗannan da basa son kowa sai babansu kawai”.
Murmushi su Ummi sukayi tare da gaidashi.
Fariyda ta ƙara matsoshi tare da rusunawa.
“Malam ina kwana”. Murmushi Abba yayi ganin ya sunkuya ya koma hannun Fariyda ya tada ita tsaye tare da cewa.
"Lfy lau Mamana ya mai jikin”.
Murya a sanyaye tace.
“Da sauƙi”.
Yana shafa kanta yace.
“Allah ya ƙara sauƙi Mamana, Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, yasa ayi aikin a sa'a ku dawo kamar yadda kuka tafi da rakiyar farin cikin samun nasarar aiki, Allah yasa ayi farar jinya ko Mahmoud”.
Duk a tare suka amsa da amin.
Idon Fariyda da ya ciko da hawaye suna gab da zuba ya kalla tare da cewa.
"A wacce mota zaku tafi Airport?”.
Salim ne ya nuna masa motarsa.
Hannunta ya kama tare da zuwa jikin motar baya ya buÉ—e tare da cewa.
“Shiga da addu'a”. Kai ta gyaɗa hawaye na zubowa.
Marfin ya maida tare da cewa.
"Mahmoud shiga ku tafi, Allah yayi muku al'barka ga amanar Mamana kada a barta da yunwa ko cuta, duk da tana da saurin hawaye dan Allah kada a kabar hawayenta su zubo sanadin ciwo ko yunwa, in hawayenta na wani abu da banne na rauninta wannan baka da haƙƙi a kansa”.
Duk da bata jin me yake faɗa amman ta fahimci da Mahmoud yake dan yadda ya fuskanceshi tayi, shi kuwa Mahmoud yayi ƙasa da kansa.
Front seat ya buÉ—e tare da cewa.
"Bismillah shiga”.
Shiga yayi tare da su Zaid sai kuwa ya kalli Abba dake cewa.
"Ka dai ji abinda ya roƙa ko”. Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
Su Ummi kuwa addu'a sukarinƙayi.
Salim na shiga Hafiz ma ya shiga motarsa shi da Samira suka mara musu baya suka nufu Airport.

Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja.
Hafiz ne ya kalli Samira da tabi jirgin da ido tace.
“Ayyah sun tafi”.
Yana É—an murmushi yace.
“Sauƙe kanki wuyanki zaiyi ciwo”.
Salim ne ya ɗan loƙo da kansa daga cikin motarsa yace.
“Kai Hafiz mu tafi ko”.
Da sauri yace. “To kana ya shiga mota itama Samira ta shiga suka tafi”.

Salim yace.
“Eh Baba sun tafi”.
Bappa Lawan yace.
“To Allah ya kaisu lfy, yau zasu wuce India ne?”.
Yana É—an kallon Mamansa data zuba masa ido tana faÉ—in.
"Dama yau ne tafiyar tasu”.
Kai ya gyaÉ—a mata yana kallon Abba yace.
"Eh yau zasu wuce, amman a Ethiopia zasuyi transit”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
"A can zasu kwana kenan tunda tafiya yamma zasuyi”.
Salim na kallon time a wayarsa yace.
"Eh inaga yanzu kam sun kusa tashi ma”.
Mama tace.
"Wato an kasa isar masa da saƙon nan dai har ya tafi”.
Bapp Lawan yace.
"Ki daina gaggawa kafin ya dawo dai in sha Allah zamu gama maganar nan zamu bata matsaya da tsaida lokacin”.
Cikin mamaki Salim yake kallon fuskar mahaifin nasu da ke nuna gskyar abinda yake faÉ—a na tabbatar da auren Mahmoud da Jidda.

Abuja zaune suke a saboda in 30 minute za'a fara boarding É—in Ethiopia Airline.
Zaune take rike da hand bag É—inta.
Tunda ya wuce can gefe ya zauna dasu Zaid dake zirga-zirga a gabashi bai kuma É—aga kanshi daga kan yaran Bama bare ya kalli wani abun.
Da sauri ta kalli gabanta jin sautin takalmin Zaitoon.
Sunkuyowa ta ɗanyi tare da kamo hannunta, murmushi tayi irin na yaran dake cikin ƙoshin lfy da farin ciki ɗan ɗaga sawunta tayi tare da manna lips ɗinta kan kumatun Fariyda, murmushi tayi fahimtar wai kiss tayi mata, sai kuma ta juya da gudu ta nufi wurin da Mahmoud ke zaune rungume da Zaid da yayi lip alamun bacci zaiyi hawa tayi kusa dashi ta zauna tare da fara leƙa idon Zaid ɗin wata kekkyawar matace mai matsakacin shekaru da bazata gaza haifar Mahmoud ɗin ba tace.
"Masha Allah twins ne ko?”.
Kai ya gyaÉ—a mata tare da jan Zaitoon ya dawo da ita gefen dama.
“Mamansu ne waccar ko”.
Ta kuma tambayarsa bai kalleta ba, kuma bai ce mata komai ba.
Miƙewa tsaye yayi tare da kallonta jin an fara nemansu, itama matar miƙewa tayi da mafi akasarin mutanen duka, a hankali Fariyda ta miƙe tsaye tare da bin layin fita da ake sanar musu dan zuwa harabar wurin jirgin.
E Passport ɗinsu ake miƙa musu da takardar visa dake ciki, suna amsa tare da fita har suka gama fitowa, Bus ɗin dake bakin wurin suka shiga ɗaya bayan ɗaya.
Inda ita bata ma hangoshiba sai dai tana jiyo muryar Zaitoon nata gwaranci.
A haka suka isa bakin jirgin nasu Ethiopia Airline jirgin babbane na gaske dan yayi ukun wanda suka taho dashi kano to Abuja.
Cikin sanyi ta ɗan tsaya bayan ta fita daga cikin Bus mutanen dake fitowa take ɗan kallo tare da ƙara matsawa gaba kusa da ƙofar jirgin da aka buɗe, da sauri ta ɗan juyo, jin Zaitoon ta riƙo hannun.
Bayansa taɓ'bi riƙe da hannun Zaitoon data riƙota.
A hankali take biye dashi tana duba seat number É—inta na Business class passengers dake jikin ticket É—inta.
Tafiyar mai ɗan tsawo kaɗan sukayi, numfashi mai sanyi ta fesar lokacin da suka shiga side ɗin business class ɗin. tsarin wurin ya banbanta da Economic class nesa ba kusa ba kujerun bibbiyu ne baya ta ɗan ja ganin zai wuce seat ɗin dake jikin window ya zauna bayan yasa jakarsursa a drawer samansa, gyara zamansa yayi tare da manna Zaid a kan ƙirjinsa, Kit ɗinta tasa a duruwar gefen nasa, kana itama ta zauna tare da gyara riƙon Zaitoon da itama ta fara jin baccin.
Seat belt ya saka jin ana musu tuni kan sakawan, itama sawa tayi tare da haÉ—awa da Zaitoon kamar yadda yayi. A hankali ya lumshe idonsa, tare da fara addu'a dan jin yanzu jirgin zai tashi.

Ita kuwa seat É—in dake gefensu wanda bisa alamu duk nasu Zaitoon ne dan taga ticket biyu ne a hannun Mahmoud É—in. A hankali ta meda kallonta ka fuskarsa duk da idonsa a rufe yake ba bacci yakeba dan taga yana motsa lips É—inshi, hakan ya tuna mata da tayi addu'a bayan itama ta lumshe nata idon.
Ajiya zuciya mai sanyi ta fesar lokacin da taji sun gama tashi sama sunyiwa garin Abuja rumfa da inuwarsu, tuni kowa ya sake yana sabgar gabansa. Da sauri ta buÉ—e idonta jin ya manna kansa bisa kafaÉ—arta...................

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*SAƘAR MAKAFI*
Page 26
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Ido ta zuba mishi cike da mmkin saurin baccinsa, numfashi mai sanyi ta fesar tare da mishi wani irin kallo mai haɗe da taɓe baki, tare da janye kafaɗarta tana mai lumshe idanunta tare da shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinsa da tuni ya aminta cikin hancinta, da sauri ta kuma buɗe idon saboda jin ya ƙara maida kanshi bisa kafaɗar nata, tare dasa hannunsa ya saƙalo nata hannun, saboda kusancin kujerun da yadda akayi su a manne ya taimawa mishi wurin samun yin sabonsa na rungumar pillow a jikinsa kafin yin bacci, kwayar kyawawan idonta ta juya cikin watsa mishi harara tare da zuba su kan kwayar manyan idanunsa dake lumshe, da sauri ta lumshe nata idon in one second tare da jan numfashintan ta riƙeshi ba tare da ta fesarba, saboda yadda ya buɗe mayatattun idonsa masu cike da baccin da yasa launinsu sauyawa. Da sauri ta kuma buɗe idanun nata jin wata daƙilelliyar muryasa da fitan amonta ya ratsata da sautin ya amsa amo cikin kunnuwanta da kanshi ke manne da haɓarta.
“Ke matsa daga nan”. Rikitattun Idonsa ya kuma juyawa mata tare da cewa.
“Ki matsa daga jikina nace ko sai na watsa miki mari”. Baki ta murguɗa cikin sanyi da cikar hujja tace.
“Nice zan matsa ko kai”. Da sauri ta rufe bakinta dan yar tsawar da yayi amta lokacin guda kuma ya janye jikinsa.
“Zaki matsa ne ko sai nayi booting up dake”. Ya faɗa da ƙarfin hali duk da ya fahimci shine yake muhallinta ba itaba, cikin sanyi ta kuma cewa.
"In dai ba ƙasa zan koma ba, ko seat ɗin su Zaid ina zan matsa kai ne dai zaka matsa”. Da idonsa ya harari spaces ɗin da ya ɗan bayyana tsakaninsu sabida gyara zamansa da yayi akufule yace.
“Da baki matsa ba, ai zaki ga abinda zan tatamiki a saman nan”.
Yar hayaniyar da suke yi ne, da musun yasa ɗaya daga cikin flight Attendance dake kusa dasu ta matso da sauri, da ka ganta kaga cikakkiyar yar kasar Ethiopia, ido ta zuba wa Mahmoud tare da tambayarsa ko suna buƙatar wani abu ne. Fuska ya tsuke dan wani irin kallon mayata da yaga tana mishi, hannunsa ya ɗan ɗaga tare da jujjuya mata yatsa.
Idonta ta maida kan Zaid dake runƙume a ƙirjinsa, sai kuma ta kalli Fariyda dake rungume da Zaitoon ɗan rage tsawonta tai kaɗan tare da tambyarta ko tana buƙatar wani abu.
Tana ɗan kallon Zaitoon da hayaniyarsu tasa ta farka tare da fara mutsu-mutsun, ganin hakane da tunawa da tun safe basu kuma cin komaiba, ne yasa ta ja hand bag ɗinta dake gefe goggonin Cerelac ɗin ta fidda tare da dan bowl spoon ta miƙa mata, tana faɗa mata ta dama musu.
Murmushi tayi tare da ƙara kallon Zaid da shima ya buɗe idon, cikin iya kulawa tace, ta bari bari taje kitchen yanzu zata kawo musu.
Meda gongonin da bowl É—in tayi tare da gyara zamanta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.