Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 34 of 86
Ranar jumma'a da hantsi
Amina, Samira, Jidda, Goggo Dada, Abida matar Yah Ahmad da matar Barrister Hajia Adama.
A tare suka isa gidansu Fariyda.
A parlour Aunty Amarya akayi musu iso.
Kana Hafiz da Sadik suka shigo da kayayyakin da suka kawowa Fariyda na fitar takaban kai tsaye Side ɗin Mamy suka kaisu.
Goggo Dada ce ta shafa kan Fariyda dake durƙushe gaban tace.
“Barka da fita lfy ƴata. Allah Ubangijin talikai ya jiƙan Aminullah mukuma Allah ya bamu ladan haƙuri.
Allah ya raya yaransa yasa sun zame masa al'wadussaliha Allah ya bar mana zumuncinmu”.
Kusan duk a tare suka amsa da Amin ya Allah.
Sai kuma suka kalli Amina da muryarta ta fara ɗan rawa.
A hankali Abida tace.
“Kiyi haƙuri Goggo Amina kada kiyi masa kuka, in sha Allah Aminullah ya huta”.
Kai ta gyaɗa tare da gyara zama a hankali tace.
“Muyi masa addu'a.”
Da sauri su Mamy, Aunty Jamila, Goggo Abu, Saddiqa dake ajiye musu drinks and snacks duk suka zauna tare da buɗe tafukan hannunsu.
“Amin yah Allah”.
Suka haɗa baki domin yadda sautin muryar Amina ke amsa amo da rawa da jerawa Aminullah ɗin addu'o'in neman gafarar Allah.”
Sit wurin sai muryarta sai in an isa muhalit shahid na cewa Amin su amsa da yaƙini”.
Ita kam Fariyda yadda Muryar Amina dake rungume da Zaid yake rawa hakama tata muryar take, rashin ya dawo mata sabo.
Sai dai kuma a hankali suka fara jin sanyi a zukatansu sabida falalar ambaton Allah da suke yi.
Ameeeeeeeen Ya rabbil alamin.
Suka amsa tare da shafawa.
Cikin mutuntaka Aunty Amarya tace.
“Bismillah kusha ruwa”.
Goggo Abu ne ta kalli Goggo Dada tare da cewa.
“Goggon Aminullah wannan hidima ta kaya ai tayi yawa”.
Cikin sanyi tace.
“Ai duk abinda muka yiwa Fariyda ta cancanci fiye da haka.
Ummimsu ma tace in gaidaku”.
Mamy tace.
“Muna amsawa an gode da hidima Allah ya bar zumunci da qauna”.
Amin suka amsa.
Aunty Jamila ne ta miƙawa Amina bottle water bayan ta balle marfin sabida jin yadda take ta ajiyan zuciya.
Amsa tayi tasha.
Sai kuma ta miƙawa Fariyda ma.
Itama amsa tayi ta sha tare da cewa.
“Goggo Dada nayi kewarku.”
Da sauri ta sunkuyar da kanta dan jin hawaye zai cika mata ido.
Hafiza ce ta miƙe da sauri tare da cewa.
“Eh ina ciki, to gani nan zuwa”.
Ta faɗa tare da katse wayar tata.
“Mom Uncle Mahmoud ne, yace in je in sameshi a waje”.
Kai kawai ta gyaɗa mata.
Samira ne fa rarrafo ta matso kusa da Fariyda hannunta ta kama tare da cewa.
“Our Aunty muma muna kewarku, ba randa gari zai waye dare yayi da bamuyi mgnarki keda sun Zaid ba, gidan ba daɗi ko kaɗan yanzu, duk farin cikinmu a tauye yake.
In mun tuna rayuwar mu ta baya a dole muke zubda ƙwalla, ko yaushe parlour Ummi cike da rahma, amman yanzu ko zama a parlour ba'a cikayi ba”.
ido ta fara jujjuyawa don hana hawayenta zuba.
Sai kuma kai ta kife kanta bisa guiwowin Goggo Dada.
Da sauri ta fara shafa kanta tana faɗin.
“Karkiyi kuka Fariyda in sha Allah zamuyi farin ciki”.
Shigowar Hafiza dake cewa.
“Ehyeh ashe yaune twins zasu cika one year”.
Da sauri Saddiqa tace.
“eyeh wannan uban Cake ɗin duk na birthday dinsu ne.
Dan Allah muyi haƙuri yanzu mu taya my twins murna.
Kuci abinci muyi salla sai muzo mu yanka cake din ko”.
Dai-dai lokacin kuma.
Baba Malam, Uncle Sani baban Salma da Uncle Muhd Baban Zainba ne ƙannen Baba Malam.
Bapp Lawan Abba da kuma Barrister.
Zaune suke a parlour Malam.
Abba ne ya miƙawa Uncle Sani wasu takardu tare da cewa.
“Gashi wannan tumin gadon Fariyda ne, don tun bayan rasuwar Aminullah nasa an ware duk mallakinsa duk da dai dukiyatace suke juyawa. Haka bai hanasu mallakar halal ɗinsu ba domin kowa da albashinsa duk wata.
Duk da bazai gajeni ba tunda ya rigani kwanta dama.
Amman yana da mallakinsa.
Gashi wannan na Fariyda ne.” kai yake jinjina masa cike da gamsuwa
Sai kuma ya ɗauko wasu files ɗin ya kuma miƙa yace.
“Wannan kuma na yaranta ne Zaid da Zaitoon bayan an tattara komai nasa Malam ne yayi rabiyar gadon yadda musulinci ya tsara”.
Da sauri Uncle Sani da Malam da suka haɗa baki sukace.
“A'a na Fariyda dai zamu danƙashi gareta amman yara kam bar nasu hannun Mahmoud”.
Da sauri Uncle Muhd ya dakatar da Abba daya buɗi baki da nufin yin magana.
“Kayi haƙuri Alhaji Umar karkace komai.”
Bappa Lawan da Barrister ne sukace hakan ma ai shi yafi dacewa.
Gyara zama sukayi baki ɗayansu tare da fara amsa addu'o'i da Malam ke yiwa Aminullah ɗin.
Bayan sun shafane duk suka miƙe tsaye saboda jin an fara huɗubar sallan jumma'a a matsallacin ƙofar gidan Malam ɗin da sauri duk suka mike suka tafi.
Bayan an idar da sallan jumma'a ne.
Akayi sanarwan akwai ɗaurin aure.
Wanda hakan yasa mafi akasarin mutane suka koma suka zauna.
Wani irin Zabura Salim yayi tare da zaro idonsa baki ɗaya ya juyo ya kalli Dr Nasir wanda shima yayi masifar kaɗuwa da jin tabbatuwar ɗaurin Auren.
Mahmoud Umar Al'umma da Fariyda Ibrahim Santuraki akan sadaki 200k cib lakadan ba ajalanba .......
*Anzo wurin yanzu ne mafa muka fara kutsawa cikin labarin, to ta yaya Mahmoud zai yi aure? Menene dalilin da yasa ake ta nanata bai taɓa iya aureba a rayuwarsa? Ta yaya kuma akayi aurensa da Fariyda? Me Muhajid zai aikata? Ko ya Salma zatayi. Wane mataki Jidda zataɗauka? WANNE IRIN ZAMA ne za'ayi a gidan Ummi? Tabbas akwai show musamman da za'a buga a gaba parlour Ummi zai haɗa tarzoma Ya Mahmoud zai yi ? Me zaice? Yaya Fariyda zatayi*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 13
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma sdw, da dai sauran abubudann ban lissafa Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.