Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 86

Cikin kulawa da so na gskya Baba Malam ke kallon Yah Amin dake durƙushe gabansa yayinda Zaid da Zaitoon ke jujjuyawa a jikinsa.
Murmushi mai cike da Dattaku yayi tare da cewa.
“Zaid fa ba inda ya bar Mahmoud duk kamanninsa ya kwaso”.
Da sauri Yah Amin yace.
“Sosai ma kuwa, har halinsa”.
Cikin yin ƙasa da murya Fariyda tace.
“Allah ya tsareni ɗana yayi halin wancan yaron”.
Murmushi Yah Amin ɗin yayi tare da cewa.
“Malam ni zan wuce Office”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Allah ya taimaka Aminullah ka gaida Abbanku duk dama shi tun jiya yazo. Mahmoud kuwa kace masa tunda shi bazai zo ya gaidani ba ni zanzo in gaidasa har gida”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“A'a Malam in sha Allah zai zo”.
Daga nan ya fice tare da rakiyar Fariyda.

Parlour Mamynta ta wuce, daga rakiyar tasa.
Cikin mamaki take kallon Zainab ƙawarta yar ƙanin Baba Malam da kuma Salma itama yar ƙanin Baba Malam ɗin da kuma Amira ƙanwarta da suka haɗa uba, sai ƙanwarta Raihana sai Humaira yar ɗan autansu Baba Malam ɗin wanda duk kansu ɗaya.
Zaune suke cike da shaƙuwar ƙawance yan uwantaka suna ganin ta duk suka miƙe a tare suka rungumeta.
Sai Salma da hankalinta da nitsuwarta kab ke kan wayar ta.
Gefen Salman ta zauna tare da sauƙe numfashi dan ƙarɓamata Zaitoon da Zaid dake hannunta.
Da Zainab da Amira sukayi.
Raihana da suke ciki ɗaya, wacce shekara ɗaya rak take bawa Raihana yasa komansu ɗaya, kitchen ta nufa tare da faɗin Aunty Fariy me zan kawo Miki?”.
Tana sauƙe numfashi tace.
“No a ƙoshe nake, ina Mamy da Aunty duk na jisu shiru.”
Amira dake shafa kan Zaitoon ne tace.
“Sun tafi gidan Bappa Ya'u ne duba Aunty Mimi da jiki, amman fa sun kusa dawowa”.

Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Ke nan saɓani mukayi dan ta can na fara zuwa kafin nan”.
Ta ƙare maganar tana kallon Salma da mahaifiyarta ce Aunty Mimi.
Sai kuma ta juyo ta kalli su Raihana cikin alamun tambaya tace.
“Wai dan Allah me take gani haka a wayar ta toshe kunne duka biyu da Bluetooth”.
Murmushi Zainab tayi tare da cewa.
“Leƙa ki gani”.
Kai ta ɗan karkata tare da leka fuskar wayar Salman.
“Mitssss! Taja wani irin dogon tsaki tare da fizge wayar ta fita daga videos Mahmoud ɗin da Salma take kallo tamkar wacce ke kallon farin wata.
Wani irin harara ta watsawa Salma data taso a fusace ganin Fariyda ne kuma yasata lumshe idanunta cike da shaƙuwa ta ɗan rungumeta sai kuma ta amshi Zaid dake kananan kuka.
“Ke kinji dadinki, Allah ya baki ɗa mai kama da Mahmoud”.
Cikin sauri tace.
“A'a ni kam ɗana da ubansa yake kama ba wani can banza ba”.
Da sauri suka kalli hanyar shigowa jin Muryar babbar yayarsu tana faɗin.
"ai kuwa Zaid dai da Mahmoud yake kama, duk da Aminullah ɗinma suna kama da Mahmoud ɗin”.
Ta ƙare maganar tana zama gefen Salman ya zama sun sata a tsakiya, numfashi mai sanyi Salma ta fesar cikin bunƙasar sirrin zuciyarta tace.
“Ni dai Allah ya sani duk duniya babu namijin dake min kyau kamar Mahmoud yana da kyan da na kasa ganin kyan ko wani ɗa namiji sai shi, da ace Allah zai bani miji kamarsa da na gama samun dukkan burina domin nasan matarsa ta more”.
Da sauri Aunty Nanan tace.
“Meyasa kamarsa kice shi kawai mana ƙanwata”.
Murmushin jin daɗi Salma tayi tare da cewa.
“Yesss our Adda Nana Allah ya amsa”.
Cikin fesar da numfashi Fariyda tace.
“Allah ya rufa miki asiri Salma mema zakiyi da wannan yaron uban faɗin rai da girman kai ga rashin kunya ai matarsa ta kaɗe dan azabtuwa zatayi”. Sai kuma ta kalli Amira tare da cewa.
“Jiya Aunty Saddiqa tace min yau zaki koma,”. Tana gyara zamanta tace.
“Sai gobe zan tafi ni wlh bana son gidan Aunty Saddiqa nafi jin dadin zama nan kano a gidanmu cikin yan uwa can Adamawa muna nan kamar marasa dangi”.
Da sauri Salma tace. “Ai kuwa Aunty Saddiqa nada jama'a Wlh ni kuma son Adamawa nake har raina, dan ni da Abuja gwara min can”. Humaira tace wlh kuwa.

A tare suka shigo parlour cikin mamaki Ummi ke kallon Aminullah da yake gabansu Mahmoud da Salim na biye dashi a baya.
Files ɗin dake hannunsa ya miƙa Ahmad daya miƙo masa hannun tare da cewa.
“Ka cike su yanzu kuma tare zamu fita.”
Ya ƙare maganar yana rusunawa gaban ƙanin mahaifin nasa tare da gaidasa cikin jin daɗin haɗin kan yaran nasu ya amsa tare dasa masa al'barka sai kuma duk suka kalleshi jin yana cewa Salim.
“Kai da Mahmoud duk zan yi maganinku Salim”.
Da sauri Salim yace.
“Afwan Yah Amin”.
Shi kuwa Mahmoud lip i shi na ƙasa ya ɗan datsi gefenshi cikin miskilar muryasa yace.
“Me mukayi?”.
Yana gyara zamansa yace.
“Ok kai baka ma san me kuka yi ba”.
Sai kuma ya kalli Bappa Lawan cikin alamun gskyar ƙorafin yace.
“Baba kaga shi Mahmoud bai gama abinda yake yiba ya gudo ya dawo bada izinina ba.
Sannan shima Salim sai yanzu kawai na ganshi ban ma san ya dowa baro Adamawa ba.
Yanzu dan Allah waye zai kula lamarinmu na Adamawa yasanfa shine MD ɗinsu”.
Cikin sauri Salim yace.
“Afwan Yah Amin wlh jiya har ƙarfe sha ɗaya na shigo Kano, naji Mahmoud ya dawo ne, shiyasa Yah Amin kusan wata shida kenan fa bamu haɗu da shiba, kuma naji Yah Ahmad na cewa ya kusa tafiya Turkey shi yasa nace bari inzo”.
Ya kare mgnar da iyakar gskyarsa dake nuna tsananin sabonsa da shaƙuwarsa da Mahmoud ɗin.
Kai Yah Ahmad ɗin ya jinina tare da cewa.
“Yanzu kuwa za'a jiku kuna raba hali”.
Cikin sauƙe numfashi Mahmoud yace.
“Shine ya cika shish-shigi”.
Gyaran murya Bappa Lawan ɗin yayi kana ya fara musu jan kunne kan kula da kasuwancinsu.
Yana mai nuna musu irin jajircewar su Aminullah da Ahmad kana da Sulaiman yaron Goggo Dada dake kula Mall dinsu dake Gombe, wanda shima Sulaiman mate ɗin Mahmoud da Salim ne.
Da sauri Salim yace.
“Wlh Allah Baba Sulaiman kam bai fini jarumtaba, yaro yana nan lagwai-lagwai dashi kullum ƙarshen wata ina rigashi haɗa komai nawa na shige da ficen kudi da lissafin kayan da ake buƙata”.
Kusan duk dariya sukayi more Especially Goggo Dada Maman Sulaiman ɗin kenan dan tasan yadda Salim ya faɗa haka ne sai dai shi saiɓin ne kawai yana da maida hankali kan kasuwancin nasu kuma shi ana iya tanƙwarashi saɓanin Salim da Mahmoud shiyasa baizoba duk da yaji sun haɗu Amman da Yah Amin ya hanasa zuwa ya hanu.

Bayan sallan Isha zaune suke main parlour ɗin.
Hira suke yi cikin nishadi.
Ummi da Goggo Dada suna bisa kujera.
Sai Aminullah, Mahmoud, Salim da kuma Samira da yau ɗin ta dawo daga garin iyayenta, cikin nitsuwar samun anci kai baka ce ita yar mai gadin gidan bane da mamanta dake taya Ummi aiki a da, cikin nitsuwa take tattare wurin da sukayi dinner.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.