Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 61 of 86

Ita kuwa Fariyda bakin gadon da ya ajiyesu ta zauna tare da jawo Zaitoon da Zaid É—in jikinta sabida sanyin AC da aka banka, wanda ya taimaka wurin kashe mata jiki sako mata bacci.
Bobo dake cikin jakarta ta fidda ta basu da sauri suka amsa tare da fara sha.
Hand lounge É—in nata ta, buÉ—e tare da zaro rigunan baccinsu da hula sucks sai blanket nasu da pampers É—insu.
A karo na uku ta kuma kallon corridorn har lau bai fitoba, sai dai taji motsinsa cikin corridorn É—in.
A hankali ta juyo kanta ganin Zaid ya nufi can.
Wani irin ƙamshi yake bazawa tare da sheƙi da ƙyallin jiki dana saje, da alamu wanka ya fesa mai rai da lafiya, wasu tattausan kayan baccine masu masifar kyau farare ƙal ya saka.
Hannunsa riƙe da wayoyi uku sai system nashi.
Ido ta zuba wa É—aya wayar dan ta gane na Yah Amin ne wanda yake juya Business nasu a ciki.

Da sauri ta É—auki Zaid É—in tare da amsar goran bobon ta wurga cikin duzbin É—in dake bakin corridorn,
Sai kuma ta É—auki Zaitoon É—in ma da hannu É—aya.
A corridorn ta cire musu kayan da pampers É—in da basu wani yi fitsarin kirki bama.
Bathroom ta shiga tare da watsa musu wanka, kana ta fito fasu bakin gadon ta zauna tana naÉ—esu cikin towel É—in, Zaid ta fara shafawa mai kana ta shirsa tasa mishi komai.
Da sauri ya nufi wurin Mahmoud dake zaune kan gadon ya jingina bayansa da kan gadon system nashi na kan sawun wasiccin dake miƙe, da saurin ya kalli Zaid da ya isa inda yake yana dariya.
Baki ta taɓe tana mai kimtsa Zaitoon tunani take tunda Allah yasa ta sanshi bata taɓa ganin yayi murmushi ba a rayuwarsa, ko ya su Zaitoon suke gane fara'arsa har suke iya masa dariya.
Ido ta zuba Zaitoon ɗin da taga tuni tayi bacci tun kafin ta ƙarisa sa mata scoks ɗin.
Gyara mata kwanciya tayi tare da rufeta ta miƙe ta nufi corridorn ɗin wanka tayi ta kimtsasu cikin wata tattausar Turkish gawn mai masifar taushi wacce take haɗe da ɗan ƙaramin hijjab turaren da itama kanta bata taɓa gajia da ni'imar ƙamshinsa ba ta fesa.
Sannan ta fito sallayar da ta gani a ninke a gefen 2 seatter É—in dake gefen su ta É—auka ta shimfiÉ—a.
Salla ta kabbarta magrib da ishah da bacci yasa batayi ba.

A yatsine yake kallonta ganin wai batayi sallaba.
Saboda bacci ne ko sakarci ko bata san ana salla a cikin jirgi bane oho.
Gyara zamansa yayi yana tallabe Zaid da yake manne a gefenshi na dama yaci gaba da danna system nashi.
Bayan ta idar tsaye take gabanshi tare da zuba mishi ido cike da takaici.
"Wai a haka zai nuna mata ta cika baccin asara”.
Tsaki taja tare da shafa cikinta da yake É—akale saboda yunwa.
A hankali ta matso kusa dasu sabuda ganin yadda Zaid ya takure a jikinsa sai tsuma jikinsa keyi, ga system nashi da yayi gefe ƙiris ya rage ya faɗi, baki ta taɓe tare da sunkuyowa dan ɗaukan Zaid ɗin.
Dai-dai lokacin kuma ya........

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 27
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Ya buÉ—e idonsa tare da saurin sa hannunsa na dama ya kama Zaid na hagun kuma ya kama System nashi idonsa kuma na kanta.
Da sauri ta janye daga sunkuyon da tayi a kansu.
Tsaki ya É—an ja tare da meda idonsa ya lumshe.
A hankali ta sauƙe ajiyan zuciya tana mai ƙara zuba musu ido, tabbas yau ta yarda Zaid da Mahmoud yake masifar kama, bata taɓa yardaba sai yau da suke jere a gabanta da kaya iri ɗaya zama iri ɗaya.
Askin gashin kansu ta zubawa ido ga mamakinta ko askinsu iri É—aya ne salon kwanciyar gashinsu.
“Mitsss”. Ya kuma jan tsaki tare da buɗe idonsa da launisu yayi masifar sata bugun zuciya wanda hakan yasata yin ƙasa da kanta.
“Yunwa nakeji”. Ta faɗa a hankali.
Idonsa ya kuma lumshewa kamar bai jitaba.
“Yunwa nakeji, tun safe fa ban kuma cin komai ba”.
Har lau bai kulataba. Jiki na rawan yuwar dake zaƙular ƴaƴan hanjinta cikin ɗaga murya kaɗan tace.
“Yunwa nakeji”.
A kufule ya miƙe zaune tare da zuba mata tsawa da narkekkiyar muryarsa Yace.
“Cinyeni tunda ke mayyace zo ki cini”.
A yunwace tace.
“Ai da inacin mutane da na dade da cinyeku”.
Da sauri yace.
“Yanzu ma ai kin fara tunda kin cinye min ɗan uwana, nima ɗin dan nafi ƙarfinki ne da tuni kin cinyeni, su Ummi kuwa ai bazasu ciyu a wurinki ba”.
Da sauri ta ɗago kanta da idanta da tuni ya fara zubda ƙwallan zafin furucinsa na cewa ita ta cinye Yah Amin, kenan shi da gaske mayyar da ya taɓa ce mata hakan yake nufi ne”.
Murya na rawa tace.
"Allah ya sani, ni ba mayya bace, Yah Amin kuma Allah ya sani ba abinda nayi masa, kuma ko zanci kowa a duniya kai kam bazan cikaba, da in cika ai gwara in mutu da yunwa in ma ya zama kaine abincin ƙarshe da zai ceci rayuwata”.
Yana mai nunata da yatsa yace.
“Ɓace min daga nan”.
Da sauri tace.
"Yunwa nake ji, tun safe banci komai ba”.
Miƙewa zaune yayi.
“To acici wa kika ga yaci wani abu bayan wanda mukaci a gida”.
Tace.
“Ku wa kuke feeding”.
Yana tsareta da ido yace. “Kada kiyi musu ƙarya tunda muka fito in banda bobo da kika yi ta ɗura musu sai Cerelac da aka basu, saboda tsabar muguwar zuciya suma kashe sun kike sonyi da yunwa”.
Hawaye ne suka fara zirya a fuskantar wani na korar wani.
A hankali ya miƙe tsaye tare da ɗaukar Zaid kana ya juya ya nufi kofar fita.
Da sauri ta É—auki Zaitoon ta mara masa baya.

A hankali ta tsaya a Danning hall É—in hotel É—in da komai na wurin su free ne a garesu duk yana cikin transit É—ina su.
Cike hall É—in yake da matafiyan.
Gefen da aka jera abincin da suke nan kala daban-daban ta nufa bayan taga shi ya zauna bisa kujerar table É—in da ba kowa akai, kan table É—in ya ajiye Zaid kusa da Zaitoon data ajiye dan duk sun buÉ—e idonsu.

ÆŠibi da kankane ba faÉ—a, hakan yayi mata daÉ—i sosai.
Snacks tai ta sinta kalan da tafi so, kana ta É—an haÉ—a da Tandoori chicken. Sai kuma mulkishakes.
Gegenshi tazo ta zauna tare da yin Bismillah ta fara ci.
Miƙewa yayi ya nufi wurin.
Ta hangoshi plate ya É—auka, tsaki taja tare da hararansa.
“Shegen iyayi su wannan ɗin kasan waɗanda suka dafane da zaka ci”.
Sai kuma tayi shiru ganin fruit ya tsitstsinta suma iya waÉ—anda ba ayanka ba, kamar su Apple, Grapes, strawberry, cherry, pear, ido ta zuba mishi ganin yadda ya tsaya ya dage yana wanke su bayan a tun tuni a killace suke, ikon Allah sai kallo.
Inda ya tashi ya dawo ya zauna saboda rashin wani wurin zaman a kusa.
Fruits É—in ya fara sha tare da bawa su Zaid É—inma.
A hankali tace.
“Da bance a fito a ci bafa”.
Da sauri tayi ƙasa da kanta saboda ganin ya juyo kanta alamun yajita
Ido ya zuba wa plates and bowls da ta bari akan tray nata ganin duk ƙanƙantar abincin data ɗan tsatstsakuro ɗin ko rabinsu bata cinyeba, kuma wai ta tashi ta barsu.
Fruits É—in ta É—iba iya ababen da take so.
Babanan da ta jido ya kalla da gefen ido sai su Apple da blueberries.
Bananan ta fa ci tana lumshe ido.
A ranshi yace.
“Biri da abincinsa an haɗu”.
Banana uku tacin cikin shida data É—auke sai rabin Apple sai blueberry É—in.
ÆŠan chips É—in dake gefen plate É—in ta tasa fork ya soko tare da kaiwa Zaid da kai ya jujjua alamun iya bobon nan da ya sha ya ishesa.
Wayarsa ya kalla ganin ƙarfe ɗaya har ta gotane yasa ya miƙe tare da nufar hanyar komawa sama
Da sauri tabi bayansa, suna shiga ya rage hasken wutan É—akin tare da haurawa saman gadonsa rungume da yaran duka biyu itama kwanciyar tayi tare da kunna hasken wayarta ta ajiye gefenta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.