Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 32 of 86
Cikin sauƙe numfashi Mamy tace.
“Yau dai ba iya Fariyda ne tayi rashin hankali ba, harda mu, yarinya tanata ihu kamar zata mutu mun kasa duba jikinta”.
Aunty Amarya ce ta kalli Salma dake cewa.
“Shimafa kamar ta harbesa”.
Da sauri suka kalli motar dake shigowa.
Salim na parking Ummi da Goggo Dada suka fito.
Ganin sune yasa Mamy yi musu sannu da zuwa tare da juyawa sukayi cikin gida.
Salim ne ya kalli Zainab dake gaidasa.
“Ina Mahmoud ɗin?”.
Ya tambaya ba tare da ya amsa gaisuwarba.
Raihana da fuskarta ke cike da tausayi ne tayi masa bayanin abinda ya faru. Ido ya zaro cikin tsoro yace.
“Kunama kuma ta yaya tazo jikin Zaitoon har kanta kuma”.
Sai kuma ya ɗauko wayarsa ya fara kiran Mahmoud ɗin wayar nata ringing amman ba'a ɗagaba.
Ummi ce ta rinƙa shafa kan Fariyda dake zaune gefenta kanta ta jayo ta manna da guiwarta cikin sanyi tace.
"Ba komai in sha Allah zataji sauƙi, kiyi shiru haka ya isa”.
Aunty Amarya tace.
"Wlh abin da ban tausayi munata zaton ciwon kunne ashe kunama ce take addabar yarinya sai ihu take kamar zata mutu”.
Mamy dake ajiye musu ruwane tace.
“Wlh laifin kaina nake gane”. Da sauri Ummi tace.
“A'a ba laifin kowa, kaddarace daga Allah”.
A can waje kuwa Side ɗin Aunty Amarya su Salma suka wuce.
Nasir ne zaune gefen Mamy da ledan magungunan daya jido.
“Mamy wai me Salim ke gaya min ne”.
Cikin sauke numfashi tace.
“Wlh kuwa ashe kunamace cikin hularta tai ta harbinta”.
Da sauri ya riƙe kansa da hannunsa duka biyu tare da rumtse idanunsa.
Dr Fadil ne ya kalli Mahmoud ɗin dake sauƙe numfashi tare da shafa kan Zaitoon dake ta sauƙe ajiyar zuciya akai-akai.
“In sha Allah ba komai Mahmoud, kaga ta samu bacci ma, yanzu zaku iya tafiya gida, sai da yamma a kawota ayi mata wata allurar.
Yanzu dai a samu bata nono zai taimaka sosai wurin ƙara karya kaifin dafin duk da allurar ta karyashi da zoginma kaɗan-kaɗan ne”.
Da sauri yace.
“No Fadil ba bacci tayi bafa, kawai tayi shirune”.
Yana leƙo fuskantar yace.
“Ai dai kaima kaji dafin ya sauƙa ko?”.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da kallon Zaid dake zaune kan ɗaya kujerar.
“Ai ni harbi biyu ne rak, ita kuwa waya sai adadin harɓi nawa yayi mata”.
Yayi magnar da alamun akwai sanayyai sosai tsakaninsu
Yana gyara zama yace.
“Harbi ukune, yayi mata ai na bincika duk kan nata da jikinta kuma mun gwada jininta naga ƙarfin dafin dake jikinta, ai da alamu ƙarinsa a sama yake sai ya sunkuyar da binɗinsa ne yake iya harbi, da ƙarin a ƙasa yake ne da harbin ba adadi”.
Cikin gamsuwa yace.
“Yess ƙarinsa a sama yake dan shiyasama ya iya harbina da zan kaɗesa”.
Yaƙare magnar tare da
Miƙewa kana ya ɗauki ledan magungunan da Dr Fadil ɗin ya haɗa musu a pharmacy ɗinsu.
Zagayowa Dr Fadil ɗin yayi tare da ɗaukar Zaid ɗin kana yace.
“Muje in kaika gida”.
Mahmoud yace
“No bari kawai ai naga kana da sauran aiki”.
Dr Fadil ne ya kalleshi lokacin da suka isa parking lot ɗin su yace.
“Zaka iya?”.
Shiga yayi ya zauna a driving seat tare da gyara rungumar Zaitoon.
Ɗaya gefen Dr Fadil ɗin ya ajiye Zaid da tuni ya fara wasa da ledan magungunan.
“Allah ya ƙara sauƙi, a yawaita bata nono”.
Amin yace tare da jan motar yabar wurin inda yake ɗan jin zogin harbin kunaman kaɗan-kaɗan.
Irin zut-zut haka yake yi sai ya ɗaɗe kuma ya ƙara yana kuma jin itama Zaitoon tana ɗan yawa zabura.
Sadik ne ya shigo Parlour da sauri yace.
“Mamy sun dawo na buɗewa Yah Mahmoud ɗin parlour Malam yana can Zaitoon ɗin ma kamar bacci takeyi”.
Da sauri Mamy tace.
“Alhamdulillah Fariyda tashi kije”.
Da sauri ta miƙe ta nufi part ɗin Malam ɗin.
Ita kuwa Mami dariya tayi jin Ummi na cewa.
“Raguwar kishiya garemu daga cizon kunama sai ihu”.
Da sauri Goggo Dada tace.
“Kada dai ki bari ta jiki kin san yan biyu ne, kar ta turo miki ɗaya, waya sanima ko Zaid ɗin ne ya tura mata shi, tunda an rasa ta inda kunama zai shiga hularta”.
Cikin zare ido Aunty Amarya tace.
“Ai kuwa ba mamaki”.
Dr Nasir yace.
Bari inje in duba my ɓingel”.
A can parlour Malam dake can harabar gida wurin Salim dake mashi bayanin abinda ya faru shi yasa bai shigoba
Tana shiga ya watsa mata wani irin kallo mai tafe da fusata yace.
“Sam baki cancanci zama uwaba.
Kin bar min ƴa kunama zai kashe mana ita.”
Tana ƙoƙarin sunkuyowa ta ɗauki Zaitoon ɗin dake kafaɗarsa tayi masa hararan takaici tace.
“Allah kuma yaga na camcanta ne, kafin ya bani, kuma tunda ba kaine ka haifamin suba, sai ka sarara min”.
Da sauri ta janye hannunta jin wani irin tsaki da yaja tare da cewa.
“Zan ɓalla hannun da bashida amfanin kula da yaran”.
Baki ta murguɗa masa tare da cewa.
“Sai ka ɓalla ai tunda ubanane kai”.
Miƙewa tsaye yayi tare da nunata da yatsa jiki a fusace yace.
“Ina mgna kinayi, wlh kika kuma cewa ƙala zan fasa bakin rashin kunyar yarinya in banda fitsara ba abinda kika iya.”
Da sauri ta ɗan ja da baya tare da tsuƙe fuska.
“Ai wlh na wuce ace min yarinya”.
Cikin zare manyan idanunsa yace.
“Kin wano sake baki kin bar kunama har cikin hularta, a hakane zakice kina da amfani? Ta ina ma ta yaya kunama ta shigar mata hula?”.
Cin faɗa tace.
“Kafa kama kanka y..”
Da sauri ta rufe idanunta tare da kame jikinta ta daura hannunta duka biyu bisa kanta tare da mannewa da jikin bango jin yadda ya watse mata.....
Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin ne 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276. Mutanen Niger 1000cfa ne Hannatou zakuyiwa magna +22790440050
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 12
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Gyaran murya da Malam yayine yasashi.
Damƙe hannunsa daya ware da nifun yarfa mata mari. “A'a Mahmoud kun dawo, ashe wai kunamace ta ritsa muku ƴar taku da harbi”.
Ya ƙare maganar tare da sa hannu ya amshi Zaitoon dake kafaɗarsa.
Kai ya ɗan sunkuyar yana dai-dai ta fusatacciyar zuciyarsa tare da komawa ya zauna gaban Malam da ya zauna yana ɗan jijjiga Zaitoon data fara mutsu-mutsu.
Da sauri Dr Nasir ya ƙaraso ciki tare da cewa.
“Allah sarki my ɓingel”.
Yayi mgnar yana shafa kanta. ya amsheta tare da miƙawa Fariyda yace.
“Kamar yunwa takeji kiyi feeding ɗinta.”
Da sauri ta zauna tare da sauƙe numfashi kana ta sata cikin hijabin jikinta ta rufeta kib, tare da ɗan sunkuyo ta kai mata nanan bakinta, ai kuwa da gudu ta kama tare da fara wani irin tsotson yunwa.
Tana fidda sauti na musamman wanda in shan nannan yayiwa yara daɗi suke fiddashi.
Kai ta ɗago ta kalli Malam dake ce mata.
“Fariyda garin ya kunama ta shiga har cikin hularta”.
Cikin sanyi tace.
Malam inaga a wurin shanya ya shiga hularta, dan naga jiya da Paulina tayi musu wanki naga har kan flowers ta shanya wasu kayan”.
Wani irin mugun kallo ya watsa mata, domin yama mance gaban mahaifinta yace.
“Ji sakaci da rashin kulawa fa, ta yaya za'a ba wata can da bata san zafinsu ba tayi musu wankin, in mutum nada hankali aka shanya kayan yara a kan flowers ai kamata yayi a binciki kayan in and out kafin asa musu, ta yayama za'a shanya musu kaya a ko ina, ina ama abin shanya kayansu da duk igiyoyin gidan”.
Nasir ne yayi murmushi tare da gyarawa Zaid a hannunsa dan shima yayi bacci.
“Ƙaddarace kawai Mahmoud ba sakaci bane”.
Kwafa yayi tare da yin ƙasa da kai ya hausawa sukayi da Malam daga nan ya ajiye ledan magungunan a gaban Malam ɗin tare da sallamar ya fita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.