Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 86
Bayan kwana shida.
Jidda ce zaune gefen Mamanta cikin sanyi take magna murya cike da so.
“Mama kinƙi ki gaya min menene dalilin da yasa kuke cewa Yah Mahmoud bazai taɓa yin aureba a rayuwarsa.
Ni da zaku gaya min wlh in dai dan cuta yake da ita wacce zan iya raɓarta in ya aureni naji na amince.
Mama ina fa son Yah Mahmoud, ji nakeyi in dai bashi na auraba ban huce auren irin mijin da nake buri da fatan samu a rayuwa tabaâ€.
Ido Mama ta zuba mata har sai da ta kai ƙarshen mgnar ta sannan ta sauƙe numfashin nazari kana a hankali tace.
“Jidda anya kuwa don Allah kike son Mahmoud? Ko dai kina son sane saboda kyan sura da halitta da Allah yayi masa da arzikin dukiya da Allah ya basu, dan ban taÉ“a jin kin danganta soyayyar taki da wata nagartar halinshi ba, sai dai da kyansa da a'a shine irin mijin da kike so gashi É—an gayu a'a gashi baya tausayin kuÉ—i komanshi mai tsadane matarsa zataji daÉ—iâ€.
Da sauri ta fara girgiza kai tare da cewa.
“Mama in ma dan kyau ne ai kyan Yah Mahmoud ya kai a soshi domin sa, bare ba iya kyau bane. Mama a gabana fa Yah Ahmad yake baki labarin nagartar halinshi da tsananin son Æ´an uwa da yake dashi da yaji kina cemin in ma daina son Mahmoud yaron da baida zumunci kowa bai ishesa kalloba, yoron da baya ko murmushiâ€.
Kin manta abinda Yah Ahmad yayi ta faÉ—a a lokacin da yaji kin faÉ—i hakaâ€.
Da sauri tace.
“Eh banace ba, amman ai shi da kansa cewa yayi duk wata nagarta Mahmoud nada ita amman shi Mutum ne mai murɗeɗɗen hali da ra'ayi gashi da kafiya.
Kuma in kin manta in tuna Miki cewa yayi.
Muddin fa Mahmoud ya tsani Abu ko ya nuna baya sonshi to har gaban abadan baya taɓa sonshi.
Tunda ya nuna ko kallonki baya son yi yace.
To koda ma ace yana cikin maza masu aure a rayuwa bazai taɓa aurenki ba ke da kanki kuma kikace mari ya tsitstsinka miki harda cewa miki mai kan angulu.
Dan haka wlh Jidda ki fida daga idona da batun Mahmoud ki daina addabata da magnar yaron da ina dai aurene sai dai a lahira ke da zumuncin ma da zai samu yakenshi zai yi dake nan fa kika faÉ—a min abinda ya miki ranar da kika je ke ko kallo ma kin ishesa ne dama dai Aminullah kikace ko ba komai shi mutum ne na musamman da kowa zai so, shifa Mahmoud baki san waye bane shi ya miki daÉ—i yaron da hmmmmâ€.
Hawaye na zuba take jujjuya kanta cikin sanyin murya tace.
“Mama dan Allah bani da kyau da ya kamata ace Yah Mahmoud ya soni neâ€.
Kai ta É—an É—ago ta kalli É—iyar tata.
Jidda kekkyawace ta dan ita da Aunty Amina duk kamannin Goggo Dada suka É—auka, kyau na asalin Fulatamare wanda itama Goggo Dada wurin mamarta ta gajin kyaun dan babansu asalin bakano ne na gaske shiyasa in suke amsa sunan kanawa kuma hausawa sai dai da suka haÉ—a irin da Fulatamare a hankali tace.
“Jidda kiso Aminullah mana ko Sulaiman.â€
Cikin rauni tace.
“Yah Amin yaci a soshi fiye ma da Yah Mahmoud amman ina wanda yake da kamar Fariyda zai kalli wata mace a duniya ne, matar Yah Amin fa bata bar wata ƙofa koda dai-dai da bakin allurane da zaiso wata mace ba a duniya, kiga irin kalar ƙirar jikinta da surar da Allah yayi mata kamar balarabiya, ga yadda take kula da iyayensa taso danginsa irin duk son da ɗa zai buƙaci matarsa tayiwa iyayensa da yan uwansa ta iya girki, ga tsabta ga gayu, ni wlh kwarjini take min duk da dai na girmeta Amman wani shayinta nakeji, kai ni bazan ma so Yah Amin ba dan bazan taɓa samun son da nake so ba dan duk abinda nake ji dashi bayan matarsa nake, ni ko kusa da ita bana son zama wlh dan ji nake ina muzanta kyanta da ƙwarjini da iya gayunta yana sa inganni wata Bujahari a kusa da ita ga ɗan jikinta mai kyau. Mama Yah Mahmoud fa na musamman ne, shine irin mazan da duk macen da tasan kanta take fata, Mama irin su Yah Mahmoud fa basu da yawa cikin maza,
Yah Sulaiman kuwa ya cika saiÉ“i da sanyi, ko wacce mace zata iya cewa tana sonsa, Amman kinga Yah Mahmoud in Allah ya bani shi fuskarsa ma bata wasa bace ko ya mace tsoronsa zatajiâ€.
Tureta Mama tayi kana ta fice daga É—akin tana faÉ—in.
“So ko hauka, duk kin zama fitsararriya akan mutumin da in ya gane kina kallonsa ma, É“alla miki haÉ“a zaiyiâ€.
Amina ce zaune riƙe da waya murmushi tayi tare da cewa.
“To ni dai ka hau online kaga rigunan dana tura maka, Yah Mahmoud.â€
Kai Hafiza dake gefenta ta jinjina tare da cewa.
“Mom kice Our Uncle ya saya min gift É—in birthday a canâ€.
ÆŠan hararanta tayi tare da cewa.
“Ke baki da baki neâ€.
Da sauri ta zaro ido cikin tsoronsa da shayinsa da sukeji tace.
“Tab ni É—in bazan iyaba wlh ina tsoronsaâ€.
Ya jita tsarai Amman sai yayi kamar baijiba.
“Na gama komai fa, ni yanzu Egypt zan wuceâ€.
Da sauri tace.
“To ai ta kwana gidan sauƙi in ban samu na Turkish ba sai in samu na Egypt ɗin.
Amman wai ka kusa dawowa ne?â€.
Cikin fara jin bacci yace.
“Yau kwana na goma a Istanbul, kuma Alhamdulillah na gama komai yanzu can Egypt ne ya rage minâ€.
Kai ta jinjina jin alamun yana hamma.
“Zakayi bacci ko.
Sai da safeâ€.
“Hmmmâ€. Yace tare da katse kiran.
Ita kuwa Aunty Amina cikin yin ƙasa da murya tace.
“Wato Yah Amin na, shine ba'a tsoroâ€.
Tana lumshe ido tace.
“Mom shi yana masifar sonmu yana wasa damu harda dariya, amman Uncle Mahmoud wlh ban taÉ“a ganin inda yayi dariyaba, kema fa naga faÉ—a yake miki, har Uncle Amin É—in ma da kamar tsoronshi yake ji.â€
Da sauri tace.
“Baki san waye Mahmoud bane Hafiza, shima yana sonku, kawai dai shi zafi gareshi, mu kuma ta ya zamuji tsoronsa shinefa Æ™aramin muâ€.
Ta ƙare maganar tana murmushi dan zancen Allah wani lokacin kwarjinin Mahmoud ke mata har taji kamar tsoronsa.
Hafiz dake shigowa ne yace.
“Yasin Aunty Fariyda ce kawai bata tsoronsaâ€.
Da sauri Hafiza tace.
“Tab ai kuwa wallahi Aunty Fariyda ma tsoronsa takeji.â€
Sai kuma yayi saurin kallon Mahaifiyar tasu tare da cewa.
“Yauwa ni kam Mom dan Allah meyesa Aunty Fariyda da Uncle Mahmoud basa shiri ne. Rananfa ya bani tsoro, dan wallahi daya sameta a parlour tsab zai maretaâ€.
Kai Amina ta É—an jujjuya tare cewa.
“Hmmm Allah dai ya kyauta, kinga Hafiza, ke mace ce, ki É—au darasi a tsakanin Mahmoud da Fariyda koda Allah yasa kinyi aure, ki san yadda zakiyi magna da kowa na dangin mijinki, gashi dai Fariyda mutumce iya mutum duk da Æ™aracin shekaratun, amman tana da class tasan yadda zata zauna da kowa, amman dole akwai Æ™uruciyar tare da ita shi kuwa Mahmoud kai na hayaÆ™iâ€.
Zama Hafiza ta gyara tare da cewa.
“Mom sharri tayi masa ne?â€.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Mafarin rashin shirinsu, duk da dama tunda akayi auren shi Mahmoud ba wani shiga sabgarta yakeba dan ko mgna baya mata yace wai yaga tana jin kanta ita matar yayansa shiyasa baya kallon ko ta inda take wai kada ta rainashi.
So lokacin amarcinta a kitchen É—in part É—inta take girki, sai Yah Amin ya kira Mahmoud suje can suci abinci.
Su Ummi kuwa ta kai musu nasu.
To ranar sunyi breakfast sun gama a parlour nanta.
Shi Yah Amin ya riga Mahmoud gamawa sai ya haura sama zai É—auko wasu files da zayi aiki a kai.
Shi kuwa Mahmoud daya gama sai ya ɗaura plate ɗin kan santa table dake tsakiyar parlour, ya kuma gyara zamansa ya kishinƙida bisa kujerar.
Yayi balance da kyau yadda zaiji daÉ—in zaman.
Garin gyara zamansa ne ƙafarsa ta ture plate da cup ɗin da yasha tea suka faɗi ƙasa.
Sautin faɗuwarsu da fashewarsu ya fito da Fariyda daga kitchen inda take ƙoƙarin haɗa lunch.
Da sauri ta ƙaraso tsakiyar parlour tare da zuba mishi ido, yana miƙe tamkar ba abinda ya faru yana kada ƙafa tare da latsa wayarsa.
Ido ta meda kan plate É—inta na musamman wanda suke a tsarinta iya na mijintane.
Ƙugu ta riƙe da hannu ɗaya tare da tsuke fuska.
Tana kuma kallonshi ko a jikinsa, jin motsin ta shigo da innalillahi da tace lokacin da taga plate da cup É—in a watse, Amman ko Side É—in da take bai kallaba cikin haÉ—e rai tace.
"Wai kai wanne irin yarone, baka ganin É“arnar da kayi min ne, ka wani meÆ™e min kan kujera kana kaÉ—a kafa kamar wani sarki bazaka iya buÉ—e baki kai mgna ba.â€
Dai-dai lokacin kuma Yah Amin ya turo ƙofar zai shigo. Amman ita dashi duk basu ganshi ba, basu kuma jishiba dan bai ƙarisa buɗe ƙofarba saboda jin kalaman Fariyda,
Shi kuwa Mahmoud Cikin tsananin tsuke fuska ya taso daga kan kujerar ya miƙe tsaye wani irin mugun kallo Mai cike da masifar bacin rai ya watsa mata murya a faɗace yace.
“Uwarkice ta haifeni a matsayin Æ™aninki da zaki cemin yaroâ€.
Cikin tsiwa tace.
“An faÉ—a É—in in ba yaro ba, yaronma wanda bai mallaki hankalin kansaba, wazai min abinda kayi min, sannan kazo zaka zagar min iyaye dan nayi maka magna, iyayen nawa da kake shirin zagin sune suka saya min kayan kitchen dana É—aki, ba yayanka bane ya saya bare da zaka hakimcemin kan kujera kazo kuma kai ta fasa min kayan kitchen dan mijina ne suka saya ba dan yaran gidan mijiba, masu kama da masu motsin kaiâ€.
Da ƙarfi Aminullah ya rumtse idanunsa ba tare da ya ƙarasoba.
Ganin yadda Mahmoud ɗin yayi kanta haiƙan ƙadaran tare da cewa.
“Ke wallahi zan É“aɓɓallaki in kika sake cemin yaro. dan na fasa plate É—in banza, me iyayen naki suka kawoki dashi da har kikejin zakiyi goriâ€.
Yana mgnar ne tare da nufo kanta gadan-gadan fuskarnan tayi jazir har wani rawa jikinsa keyi.
Da sauri ta juya ta nufi bedroom É—inta tana faÉ—in.
"To ko dai zaka dakeni ne isheshshe shafeffe da mai, sarkin rashin mutunciâ€.
Ta ƙare maganar da sauri ta shige dakinta ta maida ƙofa ta rufe.
Shi kuwa Mahmoud zuciya a hatsale yace.
“Ai da kin tsaya, na nuna miki Æ™aryar rashin kunya kikeyi, banza mai kama da Æ´aÆ´an ruwa sai É—an iskan bakin rashi kunya kamar parrot ai da kin tsaya wallahi yadda na fasa plate É—in haka zan fasa miki bakiâ€.
Dai-dai lokacin Aminullah É—in ya shigo.
Ganin sane yasa ya É—an juyo garesa,
Files ɗin hannun nasa ya miƙa masa tare da nuna baiji yadda sukayi da matar tasa ba.
“Zauna muyi aikinâ€.
Yace masa fuska É—auke da murmushi,
Kai ya jujjuya mishi cikin ɗaga yatsarsa ya nuna saman part ɗin da ƙasan baki ɗaya da kujerun yace.
“Wallahi har abadan bazan Æ™ara shigowa nan ba, tunda ba iya mallakinka kai kaÉ—ai bane, a ciki dan ni zan iya kai hannu in anamin goriâ€.
Daga nan yasa kai ya fice.
Shi ma Aminullah miƙewa yayi ya mara masa baya, sai dai shi sama ya haura.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.