Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 29 of 86

Jin anyi kiran sallane.
Yasa Malam ya kalli Sadik tare da cewa.
Medasu ciki lokacin salla yayi.
Mahmoud shiga akayi alwala mu tafi masallaci”.
Ya ƙare maganar da nuna masa toilet ɗin dake parlour nasa, alwalan sukayi kana suka tafi masallacin dake can ƙofar gidan nasu.

A cikin gida kuwa, cikin mamaki Amina ke kallon Fariyda data cire ɗan ƙaramin hijab ɗin dan zatasa babba dan yin salla.
Cikin sanyin murya tace.
“Innalillahi Fariyda baki da lfy ne”.
Adda Nana da ɗazu tazone tace.
“Lfyarta ƙalawa sai dai zuciyar ce ba daɗi, bata son cin abinci ko kaɗan daga tea fa sa Custard shine abincinta ga yadda ta rame.”
Mimi maman Salma dake shigowa ne tace.
“Ai ina gayawa Mamy ta dagewa Fariyda da ci, dan ba'a son mai takaba ta rame. Anfi son tayi kumari tayi kyan gani.”
Kai kawai ta jinjina musu kana ta kabbarta sallah.

Ita kuwa Amina zama ta gyara tunda tayi nata sallan.
Adda Nana ce ta jere masu abinci a gabansu.
“Bimillah Amina”. Tace “Aa bari Fariyda ta idar muci tare”.
Cikin jin daɗi Adda Nana tace ai kuwa wata ƙil ta samu taci”.

Koda ta idar matsin Amina yasa ta ɗan ci abincin daga bisani sukayi sallama suka tafi.

“Eh gidan Maman Hafiz naje, sai kuma na samu zataje duba Zaid ba lfy shiyasa muka tafi tare.”
Ya ƙare maganar yana kallon Abba da ke kishingide bisa tum-tum.
“Eh haka dai jiya ai naje”.
Goggo Dada ce tace.
“In sha Allah muma in anyi magrib Hafiz zai kaimu”.
Ummi da take haɗawa Abba abincinsa ne tace.
“Ni wlh komawar Fariyda da yaran nan, fin ƙarfina kawai akayi da anan aka barta sai ta fita takabarta sun ƙara wayo sun ƙara saninmu suna wadatuwa da baby food ɗinsu kawai da sai a yayasu a bar mana su”.
Cikin jin sanyi a rai Mahmoud ɗin yace.
“In sha Allah yanzuma an kusa yayesu Ummi”.
Abba dai shiru kawai yayi ya zuba musu ido.

Washe gari da safe a hankali ya iso cikin parlour cikin shigar malam baushe riga da wando na 7 star Wanda yasha ɗinkin riga da wanda da yar babbar rigar sama irin ta matasa wacce ke buɗe sai yar masaƙalin igiya a tsakiya.
Kasancewarsa Royal Blue ne yayi masifar ƙara bayyana hasken farar fatarsa, sai hular dara daya kafa a kansa wanda yake kalan zaren aikin yar saman nasa ne sky blue da ɗan baƙi.
Takalmin shi half cover shoe sky blue color masu kyau da ƙyalli.
Ido Ummi ta zuba mishi tare da cewa.
“Allah mai iko yau ka zama Aminullah sak da sak da kayi irin shigarsa inama ace zaka dawo da yin komai naka irin nasa”.
Ido ya rumtse a hankali kana ya buɗesu tare da zama gefen ta.
Ganin yadda take murmushi ne yasashi jin sanyi a ransa.
Goggo Dada ne ta fito kitchen riƙe da Tray breakfast nasa a gabanshi ta ajiye.
Sai kuma tace.
“Masha Allah babana kaga yadda ka zama Aminullah a fili, kawai dai murmushinsa ne babu kan fuskarka”.
Ɗan guntun murmushin gefen baki yayi tare da kure duk malajin fara'arsa ya ɗan sake fuskarsa.
Murmushi mai sauti Ummi tayi tare da cewa.
“Haƙurin kuma fa”.
Yana ajiye woyoyinsa yace.
“Hmmmmm”.
Yar dariya Goggo Dada tayi tare da cewa.
“Wannan ne kam har abada da wuya Mahmoud yayi haƙuri irin na Aminullah dan kowa da irin zuciyarsa.
Kai ya jinjina mata alamar yess haka bazai yiwuba kan.”
Plate ɗin Irish ɗin da egg Ummi ta miƙa masa, cikin sanyi ya kauda kansa tare da cewa
“Ummi tea ya isa”.
Cikin damuwa tace.
“So kake yunwa ta kada kai ka samu cikin wani yanayin ne Mahmoud”. Ta ƙare maganar ido na cika da ƙwalla.
Ganin hakane yasa ya buɗe plate ɗin tare da sakura kaɗan, meda plate din yayi ya rufe, ya ɗauki cup ɗaya ya fara ɗan shan tea ɗin yana sauraron Maman Samira dake cewa.
“Ikon Allah ashe dama kuna kama da Aminullah har haka shigarkuce ke banbantaku”.

Sadik ne ya kalli Fariyda dake kallon Mamy tare da zubda ƙwalla murya na rawa tace.
“Mamy ba kinjiba, shifa baida imani ko ɗigo a cikin zuciyarsa, kijifa wai in yaye su Zaitoon a shekara ɗaya a hakama ya ƙara da rabani dasu kamar shi ya haifa min su”.
Cikin sanyi Mamy tace.
“To yanzu magnar Sadik ɗin ne zaki kuma sawa a ranki har kiyi kuka? Haba Fariyda ki bar zuciyarki ta huta mana, yara dai kin san nasune kuma bamu da ikon hanasu amsarsu, amman duk da haka nasan Malam bazai bari a yayesu a shekara ɗaya ba ki kwantar da hankali zan mishi mgna”.
Murya a sanyaye tace.
“To kije ki yiwa Malam mgnar”.
Plate ɗin data zubo mata indomie ne da kwai ta tura mata tare da cewa.
“Ki cinye wannan tas ki haɗa da tea ɗin nan in kina son inje in samesa da mgnar”.
Da sauri ta jawo plate ɗin ta fara cin indomei tana haɗawa da tea ɗin.
Ido Mamy ta zuba mata cike da tausayawa tasan dolen dole za'a rabata da yaran nan kam, tunda suma dangin uban yaran ne farin cikinsu.
Tana mai ɗanyi gyatsa tare da Hamdala tace.
“Mamy kiyi haƙuri bazan iya cinye wa ba, amman nayi alƙawarin anjima zan ƙara cin aloƙoi-loƙoi Salma tace zata yi min ta kawo min”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“To shanye tea ɗin”.
A hankali ta fara Sipping tea ɗin har dai ta samu ta shanye.

Tana ajiye cup ɗin Salma da Zainab da Humaira sukayi sallama ɗan murmushi tayi tare da cewa.
“Sai yanzu”.
Mamy suka gaida kafin suka ƙaraso bakin gadon.
“Akwai wani Guy da muka wuce a waje yace ayi mishi sallama da Malam.
To mun bar malam a gidanmu yaje duba Baba da jiki, nace masa baya nan sai cemin yayi ayi masa sallama dake”.
Cikin mmki tace.
“To waye ne?”.

“Eh to gsky dai kamar ɗan uwansu Yah Amin ne dan naga guy ɗin yana kama da Mahmoud sosai, kuma a rasuwar Yah Amin na ganshi ko yaushe suna tare da Mahmoud”.
Humaira ta faɗa, da sauri Salma tace.
“Kai Humaira kallon maita har kin gansa har kinga kamarsa da my Star”.
Zainab ce tace.
“Eh Allah suna kama dan na sanshi tun a auren Fariyda”.
Kai Fariyda ta jinjina tare da cewa.
“Salim ne, ayyah Zainab a shigo dashi”.
Da sauri Salma tace.
“A'a bari ni inje inga kamar da suke cewa, dan ni dai na sani duk mutanen wurin bikinki babu wanda ya kai Mahmoud kyau”.
Ta ƙare maganar tana fita.
A parlour sukayi kiciɓis da Raihana Salim na biye da ita baya.
Rungume juna sukayi da Raihana da yanzu ta dawo daga gidan Adda Nana.
Sai kuma suka saki juna jin Salim gyaran murya.
Murmushi Raihana tayi tare da cewa.
“Bismillah ka isa ciki”.
A fakaice Salma ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Saleem ko?”.
Kai ya ɗan karkata mata tare da ɗan rage girman idonsa kana yace.
“Kefa?”.
Tana ɗan kallon shi tace.
“Salma”.
A hankali yace.
“Masha Allah. Zan iya shigowa”.
Da sauri ta matsa daga bakin ƙofar tare da yin ciki kana tace.
“Bismillah”.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.