Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 72 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 35
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Baba Malam ya furta a saman lips ɗinshi tare da sauke numfashi ganin kiran ya katse, sai kuma ya maida kallonsa kan wayar Yah Amin da kiran Sa'ad ya kuma shigowa a karo na uku.
Maida bayansa yayi ya jingina jikin kujerar yana kallon su Zaid da Zaitoon da suka miƙe zaune da alamun gajiya da bacci dan idan su da yayi tarwal alamun baccin ya wadacesu, a hankali ya miƙe tsaye ya ɗaukar woyoyin ya sasu a jakar system nashi, sai kuma ya sauƙosu ya sasu a gaba, kana ya juya suka fita dan tsab suke sabida wankan da akayi musune ya sasu bacci ma.
Kai tsaye kitchen ɗin su ya nufa dasu, Custard aka dama masu mai kauri da wadatacciyar madara, da kanshi ya basu har Saida sukayi gyatsa kana ya goge musu bakinsu da tissues zuwa lokacin kuma sun gama watssakewa haka yasa da ƙafarsu suka fito, mai drivernsu ya kira wani kekkyawan Kids garding ya wuce dasu.
Ajiyan zuciya mai tafe da zazzafan zazzaɓi take sauƙewa lokacin da ta fito daga bathroom ɗin da ta ƙara ta'azzara ciwon hannun yau ɗin garin cire rigar jikinta dan yin wanka wanda tayi shi tana kuka tare da rawan jiki saboda tsananin zogin da hannun yake yi mata ga masifar kumbura da yake ta ƙarayi more Especially wurin manna pad a jikin pant da sakashi a jikinta.
Tattausar rigar da ta ciro a Wordrobe kafin ta shiga wankan ta zura a hankali tare da sauƙe numfashi mai tafe da kuka da hawaye duk da rigar mai faɗice ainun ta ɗan fameta wurin ɗaga lafiyyeh hannun yasa ta ɗan jijjiga targaɗeɗɗen, tattausan wonɗo tasa wanda yake iya guiwa, kana ta sake rigar tare da sa ɗan ƙaramin hijjab ɗin.
Tana sharce hawayenta, ganin tuni magrib ta ƙarato yasa ta jingina kanta jikin gadon, tare da rumtse idonta hawaye masu zafi na tsilalowa, murya na rawa ta fara Azkarul masah.
A hankali ya zaro wayarsa daga aljihu, Ummi ke kira picking call ɗin yayi tare da karawa a kunne yana mai gyara riƙon Zaid da yayi bacci a jikinsa.
“Ummi barka da yamma”.
Da sauri tace.
“Barka da dare dai ko?”.
Numfashi ya ɗan ja ya kauda zancen da gaidata, a taƙaice ta amsa tare da faɗin.
“Ina Fariyda”. Fuska ya ɗan kwaɓe kamar yana gabanta yayi ƙasa da kai yace. “Ummi menene hakan”.
Cikin kufula da tsinkewa da lamarin Mahmoud tace. “Baka san Fariyda sunan mutum bane, kenan bare kasan wacece mai sunan, Mahmoud ni zaka maida shashasha ko?”. Cikin sanyi yace.
“Ummi ko jikin Zaid baki tambaya bafa”.
Tana kallon Goggo Dada da take sauraronsu tace.
“Ay ɗiyatace gaba dashi, yau kwana biyu kenan bamuyi mgna da itaba, kuma yanzu Abbanku yake cemin ɗazu bayan sallan isha suna tare da Malam yace yayi ta kiranta da yamma har sau uku bata ɗaukaba kuma har lokacin bata biyo bayan kiranba hankalinsa ya tashi yace ko jikin Zaid ɗin ne ya tashi”.
A taƙaice yace.
“Kuma baki tambayi ya jikin nasa ba”. Cikin ƙosawa tace. “Kai ka isheni da wannan logonin ɗan naka, to ya jikin nasa”.
Yana sauƙe numfashi yace.
“Alhamdulillah da sauƙi gashi nan ma yana bacci”.
Goggo Dada ta ɗan ɗaga murya tace.
“Yaushe ne ma aikin”.
Yana kamo hannun Zaitoon da ta ɗan zame daga jikinsa yace.
“Jibine Goggo Dada”.
Shiru yayi jin Ummi na kuma cewa.
"ina Fariyda bata wayar muyi mgna”.
Cike da takaici yace.
“Tana gida”.
Da sauri Ummi tace.
“To kai kuma kana ina yanzu da yaran kace ga Zaid yana bacci”. Mahmoud yace.
“Na fita da sune na kaisu garding”. Da sauri tace.
“Kuma har yanzu baku koma ba, ka duba time kuwa Mahmoud”.
Kanshi ya sunkuyar yana kallon time ƙarfe 11:23 pm, a daƙile yace.
“Ko 12 batayi bafa Ummi”.
Cikin saurin nazari da fahimtar uwa a kan ɗanta tace.
“To ina wayar Fariyda”.
Yana mi ƙewa tsaye yace.
“Tana gida”. Murya a daƙile tace. “To meyasa bata amsa kiran da akeyi mata, Babanta ya kira bata amsaba batabi bayan kiran ba, nima na kira bata amsaba sannan Abbanku ma da kanshi yace ya kira bata ɗagaba, ina wayarta ta shiga? ina take? Me kayi mata?”. Yana miƙawa mai taxi ɗinsa Zaid yace.
“To Ummi ta ya zan sani nida bama tare, kuma na barta da wayarta tare a ɗakin wata ƙil bacci tayi”.
Ya ƙare maganar yana ɗaukan Zaitoon.
Ummu tace. “To yanzu uwar me kakeyi a waje da ka barta ita kaɗai a masauƙin naku ka ɗauke mata yaranta”. Yana shiga motar yace.
“Yanzu zamu tafi gida”. Cikin bada umarni tace.
“Kana isa ka haɗani da ita”. Cikin yin ƙasa da kai yace. “In sha Allah”.
Daga nan Ummi ta katse kiran.
Shi kuwa wayar tasa ya sa a flightmode tare da sauƙe numfashi mai cike da nauyi a ƙirji.
Sit parlour sai hasken wutan da ya samu a kunne gyara tallabe su Zaid ɗin yayi ya nufar bedroom ɗin.
Zaune ya sameta a ƙasa ta kifa kanta da jikin gado ta ɗaura hannunta mai lafiyar a kanta tana wani irin kuka mai raunataccen sauti.
Kan gadon su Zaid ɗin ya nufa, ya kwantar dasu kana yayi musu addu'a gami da rufe musu jiki, sannan ya juya ya koma parlour ba tare da ya kuma kallon inda take ba. Jallabiya ya zura ya dawowa ya shiga bathroom wanka ya fesa, kana ya fito ya nufi parlour har lau tana inda ya sameta, bai kalletaba bata kalleshi ba.
Wasu tattausan riga da wando na bacci yasa tare da murza turarensa mai Ni'imtaccen ƙamshin.
Kan 3 seatter ya zauna yana jawo system nashi woyoyin ya fitar na Fariyda 17 missed calls ya samu 4 na Ummi Baba Malam 3 Abba ɗaya, Adda Nana 2, Aunty Saddiqa 2 sai Raihana 2 Salma 2 Dr Nasir 2.
Lips ɗinshi na ƙasa ya taune tare da jan numfashi mai sanyi ya fesar, sai kuma ya zuba wa missed calls ɗin ido. Wayar Yah Amin ya zaro yana mai kallon kiran Sa'ad har 6, sai kuma na Yah Ahmad ɗaya sai MD ɗin su na Sokoto da ya kira har sau uku sai na MD ɗinsu na Lagos kiransa har 4.
Ji yake tunaninsa na hautsinewa kiran Md ɗin Lagos da na Sokoto ya fara bi saboda ganin 17 minute ago suka kira.
A ƙalla 45 minutes sukayi da MD ɗin Lagos kana ya kira na Sokoto da shi ya fara kira yace ya basa awa ɗaya zai kuma kiransa.
“Dama na gama shigar da duk kayan da muke buƙata ne, da kuma kuɗin da na turawa Accounter duk na haɗa lissafin na tura to banji kace komai ba shi yasa na kira.
Yana gyara zama yace.
“Naga kiran Salim inaga ya tura min tun 4:00 Pm da na fita sai yanzu na dawo shiyasa kaji shiru, zan duba abunda kuke so in muna dashi a ƙasa a stores ɗinmu na kano in sha Allah zuwa kwana biyu sun iso wurinku, in bamu dashi a kano bazamu rasa a Lagos ba”.
Daga haka sukayi sallama.
Washe gari da hantsi, zaune yake a parlon hankalinsa duk na kam system nashi aiki yake yi da dukkan nitsuwarsa, su Zaid kuwa da kanshi yayi musu wanka bayan ya basu breakfast suna wasa sukayi bacci a nan tsakiyar parlour.
Da sauri ya kalli wayarsa dake gefensa wacce bai dade da buɗetaba dan kiran Salim da yayi katsewar da kiran Ummin yayine ya sashi sauƙe numfashi da sauri ya kuma kalli wayar ganin ta kuma kiransa video call, saida kiran ya kusa katsewa yayi picking call ɗin ya ajiye wayar kan system nashi ya fuskanceta, a hankali yayi ƙasa da kanshi sabida ganin yadda ta tsuke fuska a hankali yayi sallama ya ɗaurawa da gaisuwa.
Tunda ta amsa sallamar bata kuma amsa mishi gaisuwarba haka yasa ya ɗago kansa ya kalleta cikin sanyi yace.
“Ummi Barka da safiya”.
Da sauri ya gyara zama jin tana faɗin.
“Kada ka sake gaisheni in har bazaka haɗani da Fariyda ba ko ka maida mata wayarta, kada ka kuma gaisheni in Kuma ka gaisheni Allah ya isa zan ja maka, ka gaya min me kayi mata? Ina take? Meyasa ka kwace mata wayarta? Dan nasan tabbas wayarta bata hannunta tana wurinka nasan kai ka kwace ta.”
Cikin tashin hankali ya fara jujjuya kanshi tamkar yana gabanta ya kasa furta komai sai rawa da lips ɗinshi keyi yana kallonta da idanunsa da suka bayyana tashin hankali da kalamanta suka sashi ciki.
Ita kuwa Fariyda dake cikin ɗakin cikin galabaita da azabtar zogi hannun da yayi tsami ga yunwa dan tun jiya da safe rabonta da abinci, da sauri ta rufe kumburarrun idanunta da fuskarta da tayi jazir da kuka.
A hankali take tafiya tana tallabe da hannun da ɗaya hannun nata ta fito parlour tana rumtse idonta don duhun jiri da take gani.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.