Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 73 of 86

Cikin tashin hankali gami da gudun saɓawa iyayensa ya rinƙa jujjuya kai gami da cewa.
“Ko jiya da na dawo naga dare yayi ne nasan lokacin kunyi bacci ne, shiyasa ban haɗaku bafa”.
Cikin faÉ—a tace.
"Mahmoud ina Fariyda? me kayi mata? Kodai kasheta kayi ne?”. Da sauri ya miƙe tsaye tare da juyawa.
Dai-dai lokacin Fariyda kuma ta iso wurinsa da nufin tambayarsa wayarta da ta kira iyayenta su kawo mata agaji. Cikin sauri ya juya wayar tare da miƙa mata wayar yana faɗin.
“Innalillahi Ummi kisa kuma? Gata nan da ranta Ummi ta ya zakiyi tunanin zan iya kisan kai”.
Ido Ummin ta zuba wa Fariyda da ganin Ummin yasata sakin raunataccen kuka mai cike da galabaitar da yasa jikinta karkarwa.
“Yah Salam Fariyda me ya sameki? Gaya min me Mahmoud yayi Miki?”. Da sauri Goggo Dada ma ta dawo kusa da Ummin ganin yadda Fariyda ke karkarwa da kukan da sautinsa ke fita a disashe, a tare suka haɗa biki wurin rabkawa Mahmoud ɗin kiran da yasa dole ya dawo gefen Fariyda ya zama duk suna ganin juna.
“Fariyda gaya min me ya sameki”.
Goggo Dada tace.
Ummi kuwa tsare Mahmoud tayi da ido tare da cewa.
“Me kayi mata”.
Sai kuma duk suka zaro ido jin maganar Fariyda dake fitowa a raune murya da jiki na rawa.
“Ummi dukana yayi ya karya min hannuna tun jiya da rana ya ƙwace min wayata”. Kanshi ya sunkuyar ba tare da yace komai ba, Goggo Dada ce ta kirashi cikin muryar da tasa dole ya ɗago kansa ya kalleta.
"Da gaske karyata kayi”.
Gefen Fariyda ya watsawa harara fuska tamkar ba abinda yayi yace.
“No ba karyata nayi ba, wata ƙil dai targaɗene”.
Ya faÉ—a cikin salon rashin nadama bare damuwa.
Numfashi mai nauyi Ummi ta fesar cikin rawan muryar kukan da yasa shi saurin kallonta tace.
“Mahmoud Allah ya”. Da sauri Goggo Dada ta rufe mata bakinta da hannunta na dama.
Shi kuwa Mahmoud wani irin gigitaccen zufar tashin hankalin da tashin yace.
"Dan Allah da Manzonsa Ummi kada ki jamin Allah ya isa wlh yanzu zan ja mata targaɗen ai kin san na iya Baba idi ya koya min”.
Da ƙarfi ta janye bakinta tare da cewa.
"Ni in ja maka Allah ya isa akan me? ita dai daka cutar zance maka Allah ya saka mata, ai in na ja maka Allah ya isa ko na tsine maka sai ka iya kasheta kafin ku dawo tunda a zuciyarka ta bushe duk abinda zakayi na tabbatar mana ka tsaneta ai kanayinsa Allah ya shiryeka zance”.
Da sauri yace.
"Ummi zagina tayi fa, ta kira ƙawarta sunanta zagina shine nace ta bani wayar taƙi tace min na ƙarfine wurin karɓar wayar ne ta targaɗe fa”. A fusace tace.
"Ni ban nemi jin komai ba, ai Ubangijinta yana gani, kawai yanzu ka gyara mata targaɗen”.
A É—akile yace to kana ya katse kiran.
Kan kujerar ya koma ya zauna tare da jawo hannunta mai lafiyar ya dawo da ita gabansa.
Fizgota yayi da ƙarfi ya jata ƙasa.
Kuka ta kuma saki tare da durƙusawa a gabansa.
Hannunsa na dama yasa ya kamo hannunta dake ciwon.
Wani irin tsalle tayi tare da abkawa jikinsa tasa hannunta mai lafiyar ta riƙe hannunsa, kar-kar jikinta keyi rawa tamkar mazari.
Shi kuwa Mahmoud ido ya zuba mata cikin kallon tsana mai cike da fushi.
Sawunsa ya buÉ—a hakan yasa ta zame tsakiyar cinyoyinsa.
Maida ƙafarsa ta dama yayi kan ta hagu ya harɗeta da ƙarfi, wanda hakan yasa ta ƙara shigewa cikin jinsa kai ta ɗago da sauri jin yasa hannunsa ya kamo hannunta mai lafiyar ya matse tsakanin kafaɗarsa da wuyansa, wani irin gigitaccen numfashi ta farayi wani na korar wani da ƙarfi ta yunƙura da nufin miƙewa tsaye Amman ina ko hannunta da ya matse da habarsa ta kasa janyewa hakan ne yasa ta maida kanta kan ƙirjinsa.
Wani tafasasshen numfashi mai tsawo yaja tare da lumshe idanunsa jin yadda ta dasa mishi gigitaccen cizo kan nimple É—in.....

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 36
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“Ahshhhh!”. yaja numfashi da sauri yana taunen gefen liɓenshi na sama da ƙarfi, yasa hannunsa na dama ya tallabo hannunta na daman dake ciwo, idonsa ya rumtse da ƙarfi dan wani irin ƙara data saki ta fara mutsu-mutsun da ta kasa ƙwace kanta, da sauri ya haɗe tafin hannunta da nashi ya tsarƙafe yatsun hannunta cikin nasa hannun, numfashi mai nauyi yaja dai-dai lokacin da itama taja ajiyan zuciya mai ƙarfi a tare suka fesar da numfashi nasu da ya haɗe wuri ɗaya ya bada ɗumi a kan fuskarta da ta rumtse idon da ƙarfin ta kuma dasa kyawawan haƙoranta kan saitin nimple ɗinsa.
Cikin Sham mata ya damƙe hannun tare da murza yatsunta dake sarƙafe cikin nashi.
Wani irin gigitaccen ƙaran mai bayyana azabar da takeji ta saki tare da sandarewa idanunta data zaro duk suka kafe, idanunsa masu cike da zafin nama ya zubawa fuskantar ya bada ƙaimin jujjuya hannun nata da banƙara yatsunta tare da sunkuyar dasu. A tare duk yatsu biyar ɗin suka bada sautin ƙas-ƙas lokacin daya tanƙwarasu baya, wani ƙas-ƙas ɗin suka bada daya kuma kawosu gaba.
Tun ɗazu data sandare bata kuma koda numfashiba dan cak numfashinta ya tsaya, bisa dukkan alamu sumewa tayi, jujjuya hannun ya farayi cikin gamsuwar dai-daita ƙasusuwan, sai kuma ya koma kan wuyan hannun, riƙewa yayi da ƙarfi tare da mummurzawa kana yaja da ƙarfi.
“Wayyyyyyy! Allah na”. Taja numfashi farfaɗowa da ihu mai ƙarfi haɗe da kiran sunan Allah da lafazin da ya ratsa jinsa, murza hannun ya kumayi wanda hakan yasa jikinta sakin wani irin tsuma da karkarwa tamkar mazari ihu take yi gami da magiya ba tare da ta sake yunƙurin ƙwace kanta ba dan jin riƙon da yayi mata ya kanainayeta baki ɗaya ya naɗeta cikin jikinsa ta yadda bazata iya komai ba sai magiyar cikin rauni da rawan disashesshiyar muryata tace.
“Wahyyyoh Allah na, Wayyo Mamy na Wayyo Baba Malam zan mutu, Ummi zai kasheni wayyoh Goggo Dada. Wayyo Allah na Yah Amin ɗan uwanka zai kasheni”.
Da ƙarfi ya ƙare jan hannun tare da sauƙe numfashi dan jin sauti ƙas!!! Daya bada da ƙarfi.
Wani ƙarƙarwa ta saki tare da cusa kanta cikin kan ƙirjinsa tasa hannunta dake kafaɗarsa ta saƙale wuyansa, bakinta data buɗe ta kife dai-dai kan nimple ɗin shi na gefen dama, wani irin cizo mai tafe da mutuwar da zafi yasa haƙorinta yayi ya hana cizon tasirin da zaiji zafi sosai kamar na farkon da na biyun da har yanzu yakejin yana mishi zogi, numfashi mai masifar tsawo yaja ya sauƙewa kana ya saki hannunta duka biyu, kanshi ya maida ya jingina da jikin kujerar ya rumtse idanunsa yana jin cizon da take yi masa ba ƙaƙƙautawa a nimple ɗinsa yana fama na forkon data dasa mishi idonsa ya rumtse da ƙarfi.
Ita Fariyda tuni duk jikinta ya saki wani irin wahalane bacci yayi mata É—ibar karan mahaukaciya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.