Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 86

Maida kallonta kan Abban tayi tare da cewa.
“Ya naga kamar dai ka gamsuwa cewa eh shi ɗin ne ya gani, matacce dai baya taɓa zama rayayye fa”.
Numfashi mai tsananin zafi Alhaji Umar Muhammad Hamman *Al'ummah* ya fesar cike da taraddadin ta yaya zai warware saƙar makafin da yayi da kansa, yanzu tabbatar ɗanza yana raye, kuma gashi bibiyar ɗan uwan nasa yake yi taku bayan taku me zai iya kasancewa da shi ɗin da kuma hargitsin da zai fashe musu ta yaya zai warware wannan shaƙar makafin da yayi.

A hankali ya nufi part É—in sa cikin rashin fahimtar yadda za a gano bakin zaren sakar makafin da akayi a ahlin nasu yasa shi jin zufa na keto mishi ta yaya zai fahimtar da iyayen nasu su yarda cewa É—an uwansa na raye bai mutuba, so yake su fahimta domin a fara neman hanyar nemansa da yadda za'ayi a ganesa.
Numfashi mai zafi ya fesar jin kanshi daya fara sarawa ne yasa hannunsa duka biyu ya dafe kanshi tare da runtse manyan idanunsa zuciya cike da hautsinin

SHEKARA Uku baya...
A ƙalla sun kai su biyar.
A parlour zaune suke cikin zaman da ke nuna da tattaunawa suke yi mai mahimmanci.
Shiru saukayi baki ɗayansu hankilin da idanunsu kab na kan babban tv ido suke zubawa sawun wani kekkyawan matashin first class Guy da ake haskawa daga ƙasan kyawawan yatsun sawunsa dake cikin wasu irin takalma samfurin Turkiya Masu masufar kyau da taushin gaske,
inda ake caccanza wasu tsala-tsalan takalma in one minute sai a haska takalmi kusan kala shida ko wanne da colornsa da kuɗinsa, farar fatar matashin da kyan yatsun sawunsa yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙarawa tallan armashi da kyau, sai kuma aka fara nunashi cikin tsala-tsalan kayan matasa maza na alfarma.
Numfashi mai sanyi ɗaya daga cikinsu ya fesar lokacin da aka fara hasko hulunan kan matashin wanda suka hau sukayi ras baƙin gashin kansa mai cike da ƙyalli da sulɓi yana kwance lib ya bawa hulunan damar yin wani irin masifar kyau da ɗaukar hankali a ƙalla an nuna huluna sama da 12 in two minute a kanshi yadda Camera ke jujjuyawa yana haska ƙeyarsa zuwa gefen sajensa da gaban goshinsa yasa duk suka sauƙe numfashi.
Yess ko magaucinsu zaiji yana sha'awar kayyakinsu duba da tsalon advart ɗin nasu da kuma cikar surar halittar matashin da ziryar madarar kyau da haiba Kanada da ciƙar ƙasaita dake bayyana asalin mishkilancinsa yasa su kansu da suke gungun magauta ne a garesu su gaza ɗauke idanunsu daga kallonsa.

A ƙalla 7 minute sannan suka sauƙe numfashi a tare dai-dai lokacin da Arewa 24 ta cire tallar Al-ummah ltd babban Company da ya zaga faɗin Nigeria baki ɗaya harma da ƙasashen dake maƙotaka damu na Afirka baki ɗaya.
Kusan a tare duk suka ja wani dogon tsaki.
Sai kuma suka zubawa É—aya daga cikinsu ido jin yana faÉ—in.
“Wannan shegen yaron Mahmoud shine mafi mana illa a cikin kasuwancinmu, duk sun janye dukkan customers ɗin mu baki ɗaya”.
Da sauri wanda ke gefensa yace.
“Ni nafi tsanar Aminullah fiye da wannan Mahmoud ɗin asalima shi yaron burgeni yake yana min kyau ga kwarjini da shiga rai, gashi tamkar Wahaimiya duk abinda yasa kyau yake masa, kuma duk abinda ya tallata musu sai dai suyi other wani kayan”.
Da sauri wanda ke fuskantar sa yace.
“Hmmm ai kuwa Mahmoud shine babban illa a garemu wannan ƙwarjin da kyan da kake faɗan shine babban makaminsu, da kuma banbanta farashinsu da suke yi da namu shine ke durƙusar damu, shin baka lura da cewa tsawon shekaru Company mai findiga suna goga jigida da Al'ummah ba, sai a shekaru huɗub nan da Mahmoud ya gama karatunsa ya dawo Nigeria ya haɗa hannu da ɗan uwan nasa ne duk suka watsar da shi'o'inmu ƙasa warwas, yanzu baka jin sunan ko wanne Company ko supar market da shopping malls duk a ƙasar nan sai nasu”.
Da sauri ya jinjina kai tare da cewa.
“Wannan tabbas haka yake.
Don ni ina bibiyar duk wani shafinsa na social media.
Wallahi idan yayi musu tallan kayan su sukayi posting a shafukansu kai ka rantse da Allah kace harda aljanu ne ke bibiyarsa ba iya bani'adam kaɗai ba.”
Da sauri wanda tunda suka fara magna bai ce ko ƙalaba yace.
“Inda kyan Mahmoud da kwarjinsa ke mana illa kenan.
Yaro kamar ɗan ruwa duk ƙanƙantar motsin da yayi sai ya jaza musu zugar customers na fita hankali ni in na shiga shafinsa kawai comments section nake tafiya ina bibiyar comments ɗinsu ina karanta yadda customers ɗinsu ke yaba sauƙin farashinsu da ingancin kayansu harfa kama sunayen wasu daga cikinmu suke suna tsine mana yanzu ga hulunan nanfa akwai wacce naga sun sa 180k a farashin sarin suka barsa, ni a Mall Dina 200k ne kuɗinsa to dan Allah wa zai je guna ya samu ragin 20k su kuma ribar da sukabi fa ko 10k bata cikaba kaga darar nan da suka watso kanan a dunu dari biyu da tamanin abinda muke saidawa uku yan 1m ɗin kuma banzayen a dubu ɗari tara suka barsa”.
Tsaki na gefensa yaja tare da cewa.
“Gashi yanzu babu wani abinda basa saidawa shin kun kuwa ga Supar market ɗin da ya buɗe a Gombe. Filin ya kai hawa 7 sun cika su maƙil da kaya, hawa na farko kayan adone na mata ba abinda babu, da kayan yara duk wani abu na jarirai zuwa shekara 12 ba abinda babu a wannan wurin, hawa na biyu gadaje da kujeru, na uku kayan electronics ne ba abinda babu, na huɗu kayan masarufi ne maƙil na biyar kayan mazane da shegen yaron nan ke tallata musu gashi duk abinda yasa kyau yake masa na shida kayan amafin gona ne ba irin wanda babu ga sauƙin farashi buhun takinsa fa 40k abinda muke saidawa 50k me zai hana ya rusamu, can sama kuma stores ne wanda ke maƙe da kaya”.
Cikin takaici wanda ya fara magna yace.
“Ga Ubansu da shegen taurin kai ba yadda bamu zauna da shiba yasa subi tsarin mu wannan dattijo ya kafe ƙib yaƙi”.
Da sauri wanda yace ya tsani Aminullah yace.
“Suma yaran duk taurin kan uban suka gado”.
Rai a ɓace wani matashin cikinsu yace.
“Ai wlh babu mai tsinennen taurin kai kamar Mahmoud ai Aminullah shi mutum ne mai sauƙin kai da raunin zuciya, rauninsa kesa baya iya tsawwalawa kayansu tsada.
Amman kaga wannan shegen yaron mai idanu a bushe ƙamas ba wanda fa ya isa ya juyasa in ya kafe ko ubansu sai dai ya bisa a hankali, shi kuwa Aminullah dama duk abinda Mahmoud keso kuma ya tsara shi yake bi, yana yiwa Mahmoud ɗin wani irin so ne mai cike da jinƙai tausayi shaƙuwarsu kuma ko ɗigon ruwa baya gibta tsakiyarsu. Shi yasa duk da tsanar da Mahmoud kewa Matar Aminullah ɗin da tsananin rashin shirinsu sam bai shafi dangantakarsu Aminullah da Mahmoud ɗinba shaƙuwarsu takan girgiza zuciya domin ba ta inda zamu samu mu farraƙasu”.
Da sauri wanda ke kusa dashi yace to ai ga hanyar farraƙasu da cimma burimu na kauda ɗaya daga cikinsu ta wurin matar Aminullah zamu ci nasara tunda ga ɗan uwanta a cikin tawagarmu”.
Ya ƙare maganar yana nuna wani matashin da duk sun girmasa dan shi bazai wuce 35 years ba.
Cikin yaƙini yace.
“Sosoima kuwa ina da dama”.
Cikin yaƙini babban cikinsu yace.
“Mahmoud ne abin harinmu, domin shine Garkuwar kasuwancin nasu muna kauda shi mun karya logon ubansu, yayan kuma kashe Mahmoud ɗin kamar kashe rayuwarsace shima, domin Mahmoud ɗin ne ƙashin bayansa shine garkuwarsa.”.......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.