Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 17 of 86
“Ba wani ciwo Fariyda am kawai inaga ya gaji babansane baya son sanyi”.
Cewar Goggo Dada,
“Haka shima Yah Amin din yake faɗa”.
Fariyda ta faɗa tare da zama gefen Zaid ɗin.
Washe gari da safe.
Salma ce da Raihana da Zainab da Humaira
Zaune suke a tsakiyar parlour Fariyda cikin sanyi Salman tace.
“Ke ina kekkyawan gidan nan?”.
Zainab dakeyiwa Zaitoon kitso ne ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Ai dama ni na sani Bama Fariyda kike son ganiba shi da kike mayatar kuma ba ganinsa zakiyi ba”.
Hararar Fariyda tayi tare da cewa.
“To ita me zan kalla a tare da ita, mu tashi tare mu girma tare, tana mace ina mace ta ya zan zo dan kallonta, faɗi ki ƙara yarana nazo gani da bappansu”.
Baki Fariyda ta ɗan taɓe tace.
“Baya ƙasar ma, naji dai Yah Amin na cewa, ko wanne lakaci za'a iya ganinsa”.
Humaira dake kallon Fariyda tamkar ta samu Tv ne ta ɗan sauƙe numfashi lokacin da Fariyda taja hannun Raihana tace.
Zo muje ki fara aikin nan, tunda kunce kwaɗayi ne daku, bazan muku aikiba, ku shiga kitchen kuyi duk abinda kukeso, yanzu Yah Amin ya tafi office bari inje in gyara masa side nasa sannan inzo mu zauna”.
A parlour kuma cikin yin ƙasa da murya Humaira tace.
“Kai Salma Allah yayi halitta a wurin Fariyda, kyau kamar ita tayi kanta”.
Da sauri duk suka kalli Fariyda dake cewa.
“Yah Salam Humaira kiyi istigfari, ai in nice zanyi kaina wata ƙil da saboda munin halittar da zanyi in kin ganni sai kin suma.
Babu ɗa'a wa Ubangiji talikai akan kalmar nan ta kamar wanne shi yayi kansa da mutane suke faɗa, to in ni nayi kaina zanfi Allah da ya halicci raina iya tsarin halittar jikinane.
Ba kyau kada ki ƙara kinji ko ƙawata”.
Cikin gamsuwa suka ce.
“Kuma fa hakane”.
Daga nan ta fice.
Ita kuwa Humaira da ido ta rakata tana kallon dukkan wani takun da take yi cikin shigar riga da wando pallazo Turkish masu masifar taushi red onion collor.
Jalar gashinta dake kwance gefen wuyanta ta kalla tare da jinjina kai sai kuma ta kalli Salma dake cewa.
“Wlh duk da kyan Fariyda.
Bana ganin kyan kamar yadda nake ganin kyan Guy nan”.
ta ƙare mgnar tana nunawa Humaira hoton wani video Mahmoud wanda Hafiz ne yayi masa shi cikin mota yana tuƙi tare da bin baitin wata waƙar wani ɗan Ethiopia musulmi, baima san Hafiz nayi masa video ba.
Kasan cewar tana da number Hafiz da yake shi mai ɗaukar hoto ne kuma suna haɗuwa a nan ɗin har yayi musu hoto, tun a hotunan bikin Fariyda da Yah Amin din suka saba dashi amatsayinsu na ƙawayen amarya, a status nashi ta gani ta dauka.
Kai Humaira ta jinjina tana kallon gashin girar Mahmoud ɗin da manyan idanunsa masu masifar kyau lips ɗinshi da ta kallane yasata cewa.
“Wannan shine namijin duniya, kinaga wasu irin idanun masu manyan sirruka da Allah ya bashi”.
Sai kuma ta maida kallonta kan sajensa dake shimfiɗe da yadda yake motsa lips ɗinshi.
“Yah Salam, ashe ba banzaba Salma kika zauce, kin san da yake ni Abbanmu baya barinmu yin social media wlh ban sanshi sosai ba sai yau, tunda a bikinma ni ban wani ganshi ba”.
Tsuke fuska Salma tayi tare da cewa.
“Kada dai ki zaƙe da yawa”.
Dariya Zainab tayi tare da cewa.
“Yoh ai bata sanshi bane nuna mata shi da kyau.”
Fariyda kuwa tana gama gyaran sida ɗin Aminullah ɗin ta wuce part ɗin Ummi, dan ta gayawa Maman Samira abinda zata girka ta kuma ɗan tayata aiki.
Tana shiga parlour daga bakin ƙofar parlour ta haɗe rai tare da kauda kanta daga kanshi tsaki ta ɗan ja ganin yadda duk suka sashi a tsakiya a hankali tace.
“Shike nan kuma gidan zai zama ba daɗi tunda wannan mara mutuncin ya dawo.
Gefen Ummi ta ɗan rusuna tare da cewa.
"Ummi me za'a dafa muku”.
Da sauri Ummi tace.
“Ba komai ƴata ki huta.
Yanzu Amina ta kirani ashe ita tasan yau Mahmoud zai dawo, tace yau ta hutasheki yanzu Hafiz na hanya,
Je kiji da baƙinki naji kamar sun iso ko inji Samira.”
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“To Ummi a huta lfy”.
Sai kuma ta ɗan kalli Aminullah daya kamo hannunta tare da cewa.
“Ba magna ne Hajia”.
Kai ta ɗan juya tare da cewa.
“Afwan Yah Amin kasan in ina gaban Ummi da Goggo Dada ban ganin kowa sai su”.
Kai ya gyada tare da cewa.
“To ga Abu Zaid ma ya dowa,
Je ki kawo masa Zaitoon tun da ya shigo yake nemanta”.
Hmmmm tace tare da juyawa ta fita.
Shi kuwa Mahmoud Zaid dake jikinsa yake ta shafa bayansa dan ƴan ƙananun kuka-kuka da yakeyi.
Kai ya ɗan ɗago ya kalli Ummi tare da cewa.
“Abba fa”.
Tana miƙo mishi mug ɗin fruit salad tace.
“Yau tun safe ya tafi meeting ɗin suna yan kasuwa”.
Amsar mug ɗin yayi tare da ajesa a gefe.
“Zainab kun gama kitso ne?“.
Fariyda ta tambaya tare da zama gefen Zainab.
“Eh yanzu kuma sauran in mata ƙunshi”.
Kai ta ɗan gyaɗa tare da cewa.
“Yanzu dai yi hakuri dan Allah kaita parlour Ummi”.
Da sauri tace.
“No bari dai in gama mata mana ai zaifi kyau su ganta cas da ita”.
Tana kallon kitson da Zainab ɗin tayiwa Zaitoon ɗin tace.
“Kaita kawai tukun wannan Yaron ne ya dawo shine Yah Amin yace a kaita”.
Da sauri duk suka kalli Salma data mike tsaye cikin farin ciki tace.
“Yah Salam Fariyda ni zan kaita, kai Alhamdulillah, na godewa Allah.”
Murmushi Zainab tayi tare da cewa.
“To gata”.
Aiko jiki na rawa ta amshi Zaitoon dake ta mata murmushi.
Ita kuwa Fariyda Raihana ta kira tare da cewa.
“Zo kuje ku gaida Ummi kar kuyi irin na last time da kukazo saida gari ya waye take cemin lfy baku isa wurinta ba”.
Raihana dake kitchen tace.
“To kizo ki karɓa min tuyan mutane suzo gidanki dan wulaƙanci ki wani barmu da shiga kitchen”.
Miƙewa yayi tana kallon Zainab dake zaune tace.
“Zainab tashi kuje duk ku gaidata, Humaira kuje ko!”.
Sai kuma ta kalli Raihana data fito kitchen tace.
“Ai zaki rama wuyar tane kiyi aure, nasan in munje wata ƙil ko idonki bazamu ganiba”.
Tana dariya tace.
“Ai in ramakon nema ke kika koya min”.
Ta ƙare maganar tana kallon
Salman da tuni tayi gaba.
Raihana da Zainab da Humaira ne a baya.
Gyara mayafinta tayi tare da riƙon da tayiwa Zaitoon.
Kana ta tura ƙofar da sallama a bakinta.
Hafiz dake fuskantar ƙofar parlour ne yace.
“A'a my customers kune yau a gidan namu”.
Murmushi tayi tana ɗan raba idon ta ina zata gashi.
Tace.
“Ai dai kam”.
Ummi dake zaune gefen Hafiz ɗinne tai musu sannu da zuwa tana kallon su.
Sai Goggo Dada dake zubawa Mahmoud fruit yogurt amsar cup ɗin yayi tare da ƙara maida kanshi kan Zaid.
A tsakiyar parlour suka zauna.
Cikin yin ƙasa da kai suka gaidasu.
Hafiz yana musu wasa yauma hoto kukazone.
Humaira ne tace.
“A'a yau dai yaranmu mukazo gani”.
Yah Amin kuwa Raihana ya kalla tare da cewa.
“Ashe kina gari”.
Tana ɗan murmushi tace.
“Tun kan Baba Malam ya dawo ai nazo yanzu kam nama dawo kenan”.
Da sauri yace.
“Au butulci zakiyiwa Hajja Inna kenan ta gama shan wahalar ki yanzu zaki gudo ki bar Taraba ma gaba daya”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Haka suke ai ka manta Hafiz Nan na gama wahalar yayensa, na dage dole a sashi a makaranta anan wai dan duk karya gudu a ƙarshe dai gudu yayi ya nuna min yafi son iyayensa”.
Cikin dariya Goggo Dada tace.
“Yoh dama mana yafi son iyayensa, amman yanzu dai ai kuma ya dawo tunda kullum yana nan jiyane da ya taso makaranta ya wuce gidansu”.
Duk dariya sukayi a parlour har Zaitoon.
Amman shi kamar baya wurin tun kafun su shigo kansa a ƙasa yake kuma har yanzu kanshi a sunkuye yake bai ɗagoba.
Sai shafa kan Zaid da yake yi wanda ya samu yayi bacci.
Cikin hikima Salma ta ɗan juyo ta fuskanceshi, murya cike da mararin magana dashi tace.
“Yah Mahmoud barka da dawowa”.
Shiru yayi kamar bai jitaba.
Kai ta kuma lanƙwasawa cikin lumshe ido tace.
“Barka da rana”.
Har lau ko gezau.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.