Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 64 of 86

A hankali ta koma ta zauna tana lumshe ido, lokaci É—aya bacci yayi awon gaba da ita, can cikin baccin taji kamar mutane a kanta, da sauri ta buÉ—e ido ganin yes mutanen ne a kanta Flight Attendance É—aya sai nurses biyu, sai wani wanda da alamun Doctor ne.
Da sauri ta juyo ta kalleshi tsuma da karkarwa yake yi, da sambatun da bisa dukkan alamu haka yake in baida lfy.
"Ummeeey kaina, Yah Amin sanyi nakejjyyyyhh”. Sai kuma ya ƙara rarumo blanket ɗin ya ƙara rufe jikinsa har kansa, a hankali Dr ya miƙe tsaye tare da cemusu, su tafi ba komai yanzu zaiyi bacci.
Ai kuwa cikin abinda bai gaza 2 minute ba yayi bacci.
Bayanta ta juya ganin Oum Ansar na bacci dama duk wasu na kusa dasu.
Tafiyarsu ba dadewa flight Attendance suka fara raba musu abinci da abin sha.
Time ta duba ƙarfe tara dai-dai na dare, hakane yasata tambayarsu sun kusa ne.
Kai ta É—an jujjuya ta ce mata saura 4 hours and 22 minutes. Numfashi ta É—an fisar ta fara cin abincin da yafi kala da nasu.

Bayan awa biyu da rabi ya farka jiki a mace, kanshi ya É—an buÉ—e tace.
“Yah Allah Ummeeeyyy”.
Sai ya kuma rufe kan tare dayin wasu sambatun da ba'a iya gane me yake faÉ—a a haka ya kuma bacci.
Bayan awa É—aya ya kuma farkawa blanket É—in ya yaye saboda zufar data fara karyo masa, numfashi ya É—an fesar yana kallon wayarsa.
Alhamdulillah sun kusa, haka ne yasashi gyara zamansa, ita kuwa Fariyda cikin sanyi ta miƙe saboda jin fitsarin da take riƙewa na gab da kubce mata. Lavatory ta nufa.

Shi kuwa Mahmoud da jikinsa ke mace ne, alamun allurar baccin da sukayi masa bai gama sakesa bane yasa ya kuma komawa ya jingina, koda ta fito bata bi ta kanshiba zamanta kawai tayi ta É—auki Zaitoon data farka yogurt ta bata, amsa tayi tasha sosai, ta meda ita kan seat É—in shima Zaid ya farka shima basa tayi yasha yogurt É—in kana ta medasu kan seat É—insu da aka ajiye musu Teddy da yan ababen wasansu da ya É—auke musu hankali.

Numfashi mai sanyi ta sauƙe lokacin da taji ana faɗin.
“Ladies and gentlemen welcome to Mumbai the dream city the financial heartbeat of India.”
Cikin sauri ya buÉ—e idonsa tare da yaye blanket É—in ya gyara zamansa, mitssss yaja tsaki.
Dole sai sun kwana a Mumbai ma dan yanzu karfe É—aya kusan da rabi kenan, kuma jirgin Ahmedabad É—inma sai gobe da yamma zai tashi.

Bayan duk sun fito, anyi komai ne tsaye yake a bakin taxi É—in da hotel É—in Taj mahal tower Mumbai suka turo dan É—aukarsu bayan ya kama musu masauki ta online.
A hankali ta É—ago kanta tana kallonshi ido cikin ido jin yana ce mata.
“Ya baki bawa Sa'ad number kiba, gashi sa mishi”.
Ya ƙare maganar yana miƙa mata wayar Sa'ad ɗin dake gefe yana ta murmushi.
Amsar wayar tayi tasa masa number ta bashi wayarta.
Miƙawa Sa'ad ɗin yayi, da sauri ya karɓa yana faɗin.
“Wanne suna zansa, yana shiga taxi ɗin yaja marfin ya rufe.
"Fariyda”. Ta faɗa tare da gyara zamanta.
Daga nan suka bar wurin yana É—aga musu hannun.

Taj mahal tower Mumbai hotel ne mai masifar kyau da tsaruwa.
Bata gama tabbatar da tsaruwansa ba Saida suka shiga cikin ɗakin, duk da ya miƙa mata card ɗin room ɗinta, tun a reception rashin sanin ta inda ɗakin yakene yasa ta bishi a baya, har ya buɗe ƙofar ya shiga tana biye dashi a baya.
Ido ta zuba mishi ganin yadda yake tafiya kamar baya hayyacinsa.
Cikin mamki ta zuba mishi ido ganin ya faɗa kan gadon cikin rawan jiki ya fara rarumo duvet ɗin, a hankali ta sauƙe su Zaid a gefensa tana ɗan kallonsa saboda yadda yayi sit tamkar ba rai a jikinsa ne yasa tayi saurin j.......

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 29
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Da sauri taja da baya ido cike da taoro ganin yadda ya fara karkarwa, da sambatun da bata jin me yake faÉ—in.
“Yah salam”. Shine Abinda ta faɗa ta fara ɗaga ƙafarta a hankali ta ƙara matsowa ta side ɗin da yake kwance, rawan da jijinsa keyi na ƙara tsananta.
Cikin tsoron ganin halin da yake ciki ta ɗan sunkuyo kansa sabida jin sautin ƙaran haƙorinsa dake dukan juna yana bada sayi gat-gat, sai kuma ya ƙara sa hannunsa yana rarumar blanket ɗin ya haɗe ya dunƙule wuri ɗaya.
Da sauri ta juya baya AC dake watso musu sanyin ta kashe ta dawowa bakin gadon.
Ta tsaya cike da rashin sanin abinyi, travelling box É—insa dake gefensa ta É—an kalla sai kuma ta kalli ledan maganin dake gefensa wanda magungunan da Dr Air Indian É—in ya haÉ—a masa ne.
A hankali ta ɗan sunkuyo kansa saboda ganin rawan jikin ya ɗan fara sauƙi, sai kuma kame jikinsa da yake yi kamar wanda ke jin suka a cikin ƙasusuwansa.
Ido ta zuba wa fuskarsa da tayi jazir sai jijiyoyin kansa da sukayi ruÉ—u-ruÉ—u.
Da sauri ta ɗan tashi tsaye da ɗan ja da baya, ganin ya buɗe manyan idanunsa dake cike da zafin launin azabebben zazzaɓi daya yake nuƙurƙusan ƙasusuwan jikinsa da bargwa. Idon ya kafe mata cikin nata, murya na rawa yace.
"Ba shakka ke dai kam mayyace”.
Da sauri ta fiddo idonta waje tare da cewa.
“Wlh ni ba mayya bace”.
Da sauri ya ƙara jawo blanket ɗin dan rawan jikin ya kuma tasowa, haƙorin sama na dukan na ƙasa yace. "In ba mayeba waye zai rinƙa yiwa mutum irin kallon nan, kin cinye Yah Amin yanzu kuma nine abin harinki ko”. Da sauri ta watsa mishi kallon Allah shi ƙara kana a fili kuwa tace. "Naga kamar suma kayi ne, shiyasa na leƙa in tabbatar”. A faɗace yace.
“Irin ki tabbatar ko na mutun nan ko, to Allah ya fiki”.
Juyawa tayi ta bar wurin tare da cewa.
“Kai ka sani kayi duk yadda kaga dama, ni dai ko mutuwa zakayi ba abinda zan maka”. Yana ƙara duƙunƙunewa wuri ɗaya yace.
“Dama na nemi taimakon ki ne”.
Nigeria.
Mama tace.
“Ba komai Jidda in sha Allah sai Mahmoud ya aureki, ai Babanku da kansa ya bani satar amsa da yace, muyita addu'a, hakan ya tuna min malam Auta, kuma kinji abin da yace da kunnenki, tsakaninki da Mahmoud akwai rabon yara mata a jere kafin maza, ya kuma fara aiki da bani tabbacin ko ba daɗe ko ba jima sai kin auri Mahmoud cikin farin ciki”.
Murmushi mai cike da jin daÉ—i Jidda tayi kana tace.
"Allah yasa haka Mamana, ranar da Allah ya mallakamin Mahmoud ai shike nan Allah ya sallameni”.
Kanta Mama ta shafa tana kallonta jin tana faÉ—in.
"Wlh in na tuna wai da aka ɗaura auren Mahmoud da Fariyda har suma tayi sai inji tamkar zan haɗiyi zuciya. Mutum ya samu Mahmoud a matsayin miji ya gaza godewa Allah da azumi sai suma hegiya mai idon Zaiba”. Numfashi Mama ta fesar tare da cewa.
"Jidda kenan to ai itama Fariyda duk mijin da ya sameta, ya samu mace iya macen gidan duniya dai ya sameta, duk kyan Mahmoud fa Fariyda ta ɗarashi, Wlh bana gajiya da kallonta, ga nitsuwa ga tsabta da gayu ga iya ado da kwalliya amman duk yanzu kina son samin tsanarta sauƙinma ɗaya ita Mahmoud baya gabanta.”
Shiru tayi tare da zubawa Jidda ido ganin ta saki kuka tare da cewa.
“Mama zaki fasa min zuciya da kalamankin nan, wai Fariyda ce yarki ko Jidda”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kada ki damu ita fa duk wani kyau da duk wani nagarta take dashi kema kina ɗan dai-dai naki, sannan muna da Malam Auta, kuma kada ki manta shima Mahmoud ba sonta yakeba, baya ƙaunar ko ganinta tun zamanta a matsayin matar yayansa, ko part ɗin ta baya shiga.
Kinga ai muna da damar wuce gabanta”.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.