Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 46 of 86
Mamy ne ta zuba mata ido cikin tuhuma tace.
“Uwar me ya dawo dake tunda har kin shiga Mota”.
Da sauri Raihana tayi mata bayanin yadda sukayi dashi a mota kamar yadda Fariyda ta gaya mata.
“Innalillahi Fariyda kina da hankali kuwa, kenan fa bada izininsa kika zoba”. Shiru tayi kanta a sunkuye sai carɓin dake hannunta da take ɗan ja.
“To wlh ni baki ɗauka a kainaba, dan ko bakin gate bana fita sai da izinin mahifinku, ke dan fitsara da watsar da tarbiyyar da akayi miki shi ne zaki fita bada izinin mijinki ba, ai dole yace ki jira wanda ya kawoki ya maidake, ai yama yi miki da mutunci, to wlh tallahi daga yau sai yau in kika sake fita koda bakin shagunan ƙofar gidanku ne bada izinin mijinki ba. Allah ya isa ban yafe mikiba”.
Da sauri ta ɗago kanta tare da zubawa Mamy idanun da tuni sun ciko da ƙwalla, cikin tsawa tace.
“Maza tashi yanzu muje ki san me zaki gayawa mahaifinku, tunda ni kin rainani”.
Ido na zubda ƙwalla tace.
"Dan Allah Mamy kiyi haƙuri kar ki gayawa Malam, Mamy kiyiwa Allah ki yafe min kin janye Allah ya isanki a kaina”.
Sunkuyowa tayi ta kamo hannunta tare da miƙar da ita tsaye kana ta fara janta tana faɗin.
“Banyi lalacewar da zaki raina mijinki ni kuma in kasa gayawa mahaifinki ba, inci amanar sa kenan kikeso”.
Da sauri take bin bayan Mamy dan yadda take figarta, magiya takeyi da bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin bazata ƙara yin komaiba saida izininsa a haka suka iso parlourn Mamy dai-dai lokacin Dr Nasir da kullum safiyar duniya yake zuwa gaida mahaifiyar tasu daga gidansa ya shigo.
Ba tare da yasan meke faruwan ba, ya fara taya Fariyda bada haƙuri.
Kwaffa tayi tare da sake hannunta kana ta zauna da sauri ta rusuna gabanta ido na zubda ƙwallan sharaɗin Allah ya isa da Mamy ke yawan ɗaura mata kan wannan mugun yaron.
Ture hannunta Mamy tayi tana yiwa Dr Nasir ɗin bayanin abinda Fariyda tayi.
Cikin tsuke fuska yace.
“Ni wai Fariyda yaushe kika sauya daga Fariyda da muka sani ne”. Cikin faɗa Mamy tace.
"Dama kune baku santaba taurin kan tsiya da raini gareta shiyasa gwara in.gayawa Malam yayiwa tubkar hanci”.
Da Sauri yace.
“Mamy kiyi haƙuri karki faɗawa Malam kinga baida koshin lafiya, yanzu ni da kaina zan maidata, zan kuma bawa Mahmoud ɗin haƙuri”.
Sai kuma ya miƙe tsaye jin Mamy na faɗin.
“To maza tashi ku tafi”.
Da sauri Raihana tace bari in kawo mata wayarta da mayafinta”.
Daga nan ta juya, ita kuwa Mamy hararanta tayi tare da cewa.
“Kada ki yarda ki ƙara zuwa inda nake in dai ba izinin mijinki in kuwa kikayi haka Allah ya isa ko ciwo muke ko muna sharafa ne ban yafe ki fito kizo bada izinin mijinki ba”.
Tana sharce hawayen tace.
“Kiyi haƙuri Mamy ki yafe min”.
Ta ƙare maganar da amsa mayafinta da boronta.
Daga nan tabi bayan yayan nata.
A can gidan kuwa ido Ummi ta zuba wa Goggo Dada dake mata bayanin abinda Mahmoud yace mata, sai kuma ta juyo ta kalli Mahmoud ɗin da ya shigo cikin shirin tafiya office. Zama yayi kusa da kujrear da aka shirya masa breakfast ɗinsa kan Centre table ɗin.
“Ummi ina su Zaid”.
Ya faɗa yana buɗe plate ɗin abincin nasa.
“Samira ta fita dasu”.
Jin an buɗe ƙofa ne yasasu juyawa.
Suna gaba Samira na biye dasu a baya, da sauri suka ƙaraso wurin Mahmoud.
Ɗagasu yayi ya ajiye a gefensa ya zama sun sashi a tsakiya.
Jin ana Knocking ne yasa Samira juyawa, tare da buɗe ƙofar murmushi tayi tare da jan baya ta basu hanya tana faɗin.
“Sannu da zuwa. Oyoyo Aunty Fariyda”.
Sai kuma ta ɗan sha jinin jikinta ganin ba walwala tare da Fariyda.
Ummi na hangosu tace.
“A'a Nasiru kaine a tafe sannu da zuwa, Fariyda kin dawo”.
Murmushi Dr Nasir yayi tare da miƙawa Mahmoud hannu sukayi musabaha.
“Ashe bamu makara ba, munyi sa'a munsameke a gida”.
Fuska ba yabo ba fallasa yace. “Ayyah”. Ita kuwa Fariyda Ummi da Goggo Dada ta gaida, sai kuma ta amsa gaisuwar Samira.
Ita kuwa Samira daga nan ta juya ta fita daga parlour ta koma ƙofarsu.
Bayan sun gaisa ne Ummi ta ƙara tambaya Dr Nasir kufan jikin Malam yana gyara zamansa yace.
“A Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai.”
Sai kuma ya kalli Mahmoud dake ce masa.
“Bismillah”.
Nasir yace.
“Ina azumi”.
Fariyda dake zaune a ƙasa gefen Goggo Dada ya kalla sai kuma ya ɗanyi gyaran murya yace.
“Mahmoud wurinka nazo”. Kai ya ɗan ɗago ya zuba masa ido ba tare da yace komai ba.
“Ga matarka Fariyda na dawo maka da ita, da kuma ƙarin rakiyar bada haƙuri dan Allah kayi haƙuri abisa kuskuren da tayi, na zuwa gida ba tare da izinin ka ba”.
Kanshi ya maida ya sunkuyar ba tare da yace masa ko ƙalaba.
“Dan Allah kayi haƙuri, Mamy tace itama bata san a gida ta kwana ba sai yanzu da safen nan, da zata gayawa Malam ni na roƙeta alfarmar kada ta gaya masa saboda ganin baida lfy, tace in baka haƙuri dan Allah”.
Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalli Dr Nasir ɗin da yake sa'an Yah Amin.
“Ayyah ba komai”. Ya faɗa tare da ɗan juyawa ya kama Zaitoon datake son sauƙa.
Sauƙa tayi tare da nufar Fariyda tana ɗan dariya.
Ƙin kula Zaitoon ɗin tayi cikin takaicin tunda suka shigo basu kulata ba sai yanzu.
Dr Nasir ne ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi kuyi haƙuri wlh bamuji daɗin abinda tai ba”. Da sauri Ummi tace.
“A haba ba komai Nasir karka damu, ai jin ciwon Malam ɗin ne ya ruɗata”.
Kanshi ya ɗan sunkuyar tare da kallon Fariyda dake jujjuya yatsun hannunta da wayarta kanta a sunkuye.
Wayarsa ya zaro tare da fara yi mata ɗan guntun text message ya tura mata.
Yana mai ɗan ɗago kanshi jin Goggo Dada dake cewa.
“Allah ya tsare gaba”.
Da sauri ta juya wayar tata, ganin text ɗin Yah Nasir ne yasata saurin juyowa ta kalleshi harara ya auna mata tare da nuna mata wayarta da ido, da sauri ta buɗe message ɗin.
“Ki ɗago kanki ki bashi haƙuri, ko in kira Mamy da Malam in faɗa musu, kin iya laifi baki iya bada haƙuri ba, nine zan bada miki haƙurin ma kenan”.
Da sauri ta kuma kallonsa, kallon da ya matane yasa ta meda kanta ƙasa cikin sanyi da gudun ɓacin ran Mamy tace.
“Kayi haƙuri”.
Kamar bai ma san da ita a wurinba haka yaci gaba da cin abincinsa don ko inda take bai kallaba.
“Bakaji tana baka haƙuri bane”. Ummi ta faɗa a daƙile.
Kai ya ɗan juyo kana yace.
“Okay”. Time Dr Nasir ya kalla tare da miƙewa yace.
“To Ummi ni bari in wuce kar in makara ina da patients da yawa”.
Miƙewa tsaye Mahmoud yayi tare da basa hannu kana yace.
“To Allah ya kiyaye hanya”.
Amin yace tare da fita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.