Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 23 of 86

Suna nan a gidan har sai wuraren ƙarfe goma.
Suka tattara ita da Mimi da Aunty Amarya.
Da Aunty Rakiya matar bappansu ƙarami.

A hankali suka fito harabar gidan.
Hango rumfar ba mutane da yawa alamun duk sun tattafi ne yasa suka nufi can dan samun gaida Abba da Mahmoud.

Su ɗin kuwa suka Samu Abba, Bappa Lawan, Mahmoud, Sulaiman, Salim, da Hafiz sai Kabir Manager Kebbi.
Sai kuma Yah Ahmad dake tsaye riƙe da hannun ɗansa Ayman da alamun yanzu yake shirin tafiya.
Bayan sun gaida Abba da Bappa Lawan ne.
Salma ta kalli Mahmoud kallo ɗaya daya tsinka mata ruwan hawayenta cikin sanyi tace.
“Yah Mahmoud ya haƙuri.”
Ganin ya gyaɗa mata kai ba tare da ya amsa bane yasa taci gaba da cewa.
“Allah Ubangijin talikai ya jiƙansa da rahama yasa ya huta”.
A saman lips ɗinshi ya amsa da Amin a hankali kamar yadda ya fara tun jiya. Cikin sharce hawaye Raihana tace.
“Allah ya jiƙansa yayi masa gafara”.
Haka ya rinƙa amsa musu da Amin akan Labbansa.
Daga nan dai Dr Nasir da Yah Kamal dake jiransu a mota suka tafi.

Haka dai rayuwa tai ta tafiya zuciya cike da ƙunci yau ne akayi sadakan bakwai.
Bayan an watse, sai iya su na jiki- jiki kawai
Gyara zama Baba Malam yayi tare da kallon Abba da cikin sanyi ya ƙara yi masa ta'aziya tare da jeron addu'o'i masu yawa ga mamacin sannan ya kalli Abban cikin sanyi yace. “To yau kam zamu tafi da Fariyda da yaranta, tunda anyi bakwai”.
Cikin wani irin yanayi mai rauni Abba yace.
“Meyasa bazata zauna a ɗakinta ba tayi takaba a wurin mu”.
Kai Baba Malam ya jinjina tare da cewa.
“Banƙi ta taka ba, Amman ita uwar tata da wuya ta iya zama har tayi takaba a nan, ko nima inaga lokacin da tsawo, sannan ita kuma Fariyda kaga yanayin da take ciki, ko abinci bata ci sai uwar ta matsa mata, sannan bata da isashen lfy, kaga in mun koma da ita Nasir zai kula da ita sosai”.
Kai Abba ya jinjina cikin sanyi yace.
“To ai ga Dada zata zauna da ita”.
Cikin yin ƙasa da kai Dr Nasir yace.
“Afwan Abba zan iya magna?”.
Kai Abba ya gyaɗa masa alamar eh.
Gyara zama yayi tare da cewa.
“Abba kayi haƙuri Amman zaman Fariyda a nan ba sauƙi a zuciyarta.
Dan ko part ɗin ta bata sake shigaba tunda akayi rasuwar nan, jiya tana kuka tace min ita bata son zama a gidan duk inda ta juya idonta tuna mata Aminullah yakeyi”.
Cikin sanyi Bappa Lawan yace. "Lallai haka Jidda take gaya min jiya da muna komawa, inaga a barta su tafi tare kawai”.
Cikin sanyi Mahmoud da sai yau ya buɗi baki yayi magana da ficecciyar murya yace.
“Amman banda su Zaitoon da Zaid ko?”.
Cikin sanyi Abba yace.
“To Mahmoud ta ya zamu rabasu da uwarsu da abincinsu.”
Murya a harɗe yace.
“To muɗin kuma fa sai mu rasa Abbansu kuma suma mu rasa su, ni bani da matsala da tafiyar ta sune dai bazan iya rayuwa ba suba”.
Cikin tausasawa Baba Malam ya dafa kafaɗarsa tare da cewa.
“Kayi haƙuri Mamuda ai da nan da gidana duk ɗaya ne, duk sanda kakeso zakaje ka gansu, bazamu rabasu da uwar bane dan tana shayar dasu.
Da zaran an yayesu duk yadda kakeso haka za'ayi dasu a matsayinka na uba a garesu”.
A hankali ya maida bakinsa da ya buɗe da nufin yin magana ya rufe, sabida ɗaga masa hannu da Abba yayi tare da cewa.
“Ba komai Allah ya raya mana su bisa imani, amman kayi haƙuri Malam Ibrahim ka bari sai gobe azo a ɗaukesu”.
Cikin mutuntaka Baba Malam yace.
“Allah ya kai mu bisa rai da lfy”.
Da Amin suka amsa baki ɗayansu.

Washe gari da safe.
Abba ne zaune a parlour yayinda duk ahlin nasa suke zaune a ƙasa harda Mamyn Fariyda.

Cikin rawan murya Ummi da suka gama sauraron jawabin Abba na yadda sukayi da Baba Malam.
Ido na zubda ƙwalla tace. “Allah sarki mutuwa, ta rabaka da matacce ta kuma rabaka da rayayye, ko ya zaman gidan nan zai zame mana ba Aminullah. Ba Fariyda, Ba Zaid da Zaitoon, to wani farin ciki ne kuma ya rage mana a gidan”.
Sai kuma ta kalli Goggo Dada data jawo Fariyda ta rungume tare da faɗin.
“Fariyda muna sonki ki zauna damu, bama son kiyi nesa damu, jinki muke cikin jini da tsokar zuƙatanmu”.
Tunda akayi rasuwar sai yau kwalla ta zubo mata murya na rawa tace.
“Nima ina sonku Goggo Dada, bana son rabuwa daku, amman zan haukace in ina gidan nan, bazan iya zama a cikinsa ba Yah Amin ba, ji nake tunanina yana hautsinewa kamar zanyi hauka, in naga Ummi na kuka ji nake zuciyata zata fashe, in su Zaitoon suna kuka raina gasuwa yake ji nake kamar in dora hannu a kai inyi ta ihu”.
Sai kuma duk suka kalli Amina data kife kanta jikin kujerar da Abbansu ke kai ta saki kuka tana faɗin.
“Aunty Fariyda yanzu mun rasaki kenan”.

Kai ta fara jujjuya mata tare da cewa.
“Maman Hafiz bamu rabubq, in sha Allah muna tare”.
Hafiza ce ta fashe da kukan da yasa su Zaitoon ma kuka.
Nanfa duk suka kacame da kuka har Abba yau saida ya zubda ƙwalla.
Ita kuwa Fariyda kamar abin iska sai gata ta kuma sume wa.

Suman tane yasasu yin shiru tare da yayyafa mata ruwa.

Shi kuwa Mahmoud duk abinda akeyi rungume su Zaitoon kawai yana jin tamkar ya maidasu cikinsa.

Nasiha mai ratsa jiki Abba yayi musu da tunasar dasu ladan dake cikin haƙuri da mahimmancin yiwa mamaci addu'a.
Hakan ne yasa suka ɗan nitsu.

Haka dai Samira da Raihana suka Tattarawa Fariyda duk kayan yaranta, sai kuma nata da suka kimtsesu a akwatuna, huɗu na yaran kuma akwati uku da baby drawer ɗinsu.
Duk Dr Nasir ya maidasu gida.
Sai dare yazo ɗaukarta da mahafiyarsu.

A hankali ta durƙusa gaban Abba da Ummi da Goggo Dada.
“To Abba zan tafi, Ummi ku yafe min Goggo Dada in akwai abinda na taɓa yi muku cikin rashin sani ko ajizanci na ɗan adam.
Ni baku taɓa jimin komai ba, koma kunmin na yafewa kowa.”.
Sai kuma ta kamo hannun Amina da Samira tana zubda ƙwalla tace.
“Ku yafe min”.

Hannu Abba ya ɗaura a tsakiyar kanta tare da cewa.
“Ba komai Fariyda Allah yayi miki al'barka” ya raya mana yaranki, ki kula da takabarki wanda Allah ya ɗaura miki tashi kuje”.
Ya ƙare maganar yana kallon yadda duk su Ummi mutuwar ta dawo musu sabuwa.

A hankali Mamy ta miƙa wa Mahmoud hannu tare da cewa.
“Kawosu”.
Ido ya ɗago ya zuba mata ba tare da ya bata yaranba,
Sai kuma ya kalli Dr Nasir Cikin murya mafi rauni da karaya Mahmoud yace.
“Mamy gasu Amana ne a garemu baki ɗaya, gasu a hannunki keda Dr Nasir na danƙasu da Baba Malam.
Na bada su da sharaɗin duk randa aka yayesu zanzo in amshesu.
mamy a kular min dasu domin sune madadin ɗan uwana”.
Kuka mai karfine ya kwabcewa Fariyda wanda yasa ta nufi waje da sauri.
Da sauri Goggo Dada ta mara mata baya.
Shi kuwa Mahmoud Mamy ya bawa Zaitoon kana ya bawa Dr Nasir Zaid”.
Daga nan suka fita suka tafi tare da rakiyar Ummi da Abba Hafiza da Samira da Amina kam tuni kuka yasata shiɗewa dib ganin hakane yasa Matar Barrister da Abida mayar Yah Ahmad da Maman Jidda sukayi kanta....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.