Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 65 of 86

Mumbai tsaki mai sawo yaja tare da kwaffa.
Da sauri ta juyo tana mai jijjiga Zaitoon dake bayanta dan zafin garin ya hanata bacci tunda Fariyda ta kashe Ac.
"Wai meyasa baki da hankali ne?”.
Tana jijjiga Zaid tace.
"Akan me zakace bani da hankali akan bola ka ganni ne”.
Yana kunna AC saboda zazzafan zafin daya turnuƙeshi tunda zazzaɓin ya sauƙa yace.
“In banda hauka me yasa zaki kashe mana AC”. A kufule tace.
“Dawanauce ni, ai da ban kashe AC ba da ka sanƙare da sany”. Sai kuma tayi shiru tare da ja da baya, sabida ganin mugun kallon da yake mata.
“Tabbas zan zubda haƙoranki kab a Indian, in baki daina min gautsin baki da rashin kunya ba, ina mgna kinayi ni sa'an kine”. Ƙasa tayi da kanta ba tare da ta kuma cewa komai ba sai ɗan moi-moi da take yi da bakinta.
Shi kuwa Mahmoud komawa yayin yakwanta tare lumshewa idonsa.

A hankali ta kwantar da Zaitoon ɗin kana ta koma kan 3 seatter ta kwanta.
Wuraren ƙarfe tara dai-dai ya farka daga baccin da ya maida bayan sallan asuba.

Zaune take bisa dukkan alamun tayi wanka tayiwa su Zaid dan sun canza kaya sai ƙamshi da suke mai daɗin shaƙa, ta gefen ido ya kalli bowl ɗin data basu Cerelac, yana sauƙa kan gadon yace.
"Da wanne ruwan kika dama musu Cerelac ɗin”. Ya tambaya cikin tsareta da ido, jin ya kuma tambayarta ne yasa ta miƙe tsaye tare da cewa.
Kitchen nasu na kira na gayawa”.
Numfashi mai sanyi ya fesar dan da fari yayi zaton dana bathroom ta dama musu.
Plate ɗin dake kan Tray da ɗan cup ɗin tea dake gefe ya kalla alamun tamayi breakfast.
Hanyar fita ya nuna mata tare da cewa.
“Fice min daga ɗaki”. Cikin takaici da ƙosawa da rashin mutuncinsa tace. “ina zanje”.
Card ɗin dake kan mirror ya harara tare da cewa.
"In kinga dama ki fire sama, in bai mikiba ki nitse cikin ƙasa, waye damu dake ma a duniyar bare yayi ƙuncin batanki”.
Juyowa tayi ta fuskanceshi cikin dakiya tace.
"Ba inda zani”.
Ta ƙare maganar da zama kan kujerar tana jawo wayarta ta buɗe data.
Tana buɗewa kiran Ummi na shiga.
Barka da safiya Ummi.
Jin haka ne yasa ya dakata, ya juyawa ya ɗan shafa kan su Zaid dake tsaye a gabansa
Bathroom ya shige.

Nigeria.
“Eh tace da sauƙi, wai har ya fara masifa”. Ummi ta faɗawa Abba dake zaune bisa sallaya, Goggo Dada ne tace.
"Bata san masifar ma tafi yawa ba in baida lfy, da kowa ma faɗa yakeyi bare kuma ita”.
Ummi tace.
"Zan kirashi ai tace ya shiga wanka”.

Sa'ad ne ya zubawa hoton Fariyda daya ɗauketa a Arrival, wanda fuskar Mahmoud ta ɗan bayyana kaɗan a can bayanta.
Hoton ya saka a status tare dayin ɗan guntun rubutu.
"Mafarin Family". Sai kuma ya ɗanyi murmushi tare da lumshe idanunsa kamanin fuskantar da surarta yake dawo mishi tamkar tana gabansa.
“Yah Allah ka mallaka min Fariyda a matsayin matar aurena abar biyan buƙatar jiki da zuciyata”.
Da sauri ya kalli saƙon Sara yar ƙanwar Mamanshi dake Kano da tayi screenshot na hoton tare dasa alamun tambaya kan fuskar Mahmoud.
“Ka sanshi ne?”. Ganin bai bata amsa bane yasa tayi saurin kiransa, yana ɗagawa tace.
"Please Sa'ad wannan na gefen, ka sanshi ne? A ina kuka haɗu?”.
Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.
"Flight ɗinmu ɗaya Form Abuja to Mumbai, tare mukayi transit a Ethiopia, ya kika ganta ta haɗuko tayi ko?”. Da sauri tace.
"Yah Salam tayi sosai ma, amman ni ba a kanta nake magna ba ka sanshi ne, sunansa Mahmoud ko?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
"Eh sunansa Mahmoud brother ɗin My princess ne. Harma yace an bani ita”.
Da sauri tace.
"Alhamdulillah ya Allah na gode maka, tunda muka bar kano muka dawo Katsina ban ƙara ganin Mahmoud ba Sa'ad shinefa Cousmate ɗina da nake ce muku. Papi”.
Da sauri yace.
"Haba dai shine”.
Please dan Allah ka amshi number ƙanwar tasace.
Sa'ad yace.
"Eh amman ina ta kira layin baya shiga”. Please turo min tace da sauri.

Ƙarfe biyu dai-dai suka baro Dannin area ɗin su dake kusa da kitchen ɗin hotel ɗin, kusan ma duk a haɗe suke.
Magungunansa ya sha, ya kuma ficewa, ita kuwa baccin da bata samu yinsa da dare da safen bane ta maida bayan ta samu su Zaid ma sunyi bacci.
Cikin yanayi na shaƙuwa mai ƙarfi yake video call da mamansa kekkyawar ba fulatanar Gombe.
“Mommy tayi miki ko?”.
Cikin yanayin gamsuwa da nitsuwar Fariyda da kyanta da ta gani a hoton tace.
“Sosai ma kuwa Sa'ad, zuciyata ta gamsu da ita a matsayin surkata. Yar inace me sunanta”.
A hankali yace.
“Sunanta Fariyda, amman dai bansan daga wanne state suke ba, amman dai tafi kama da Fulanin Yola kona Gembu membila, shi ma yayan nata yafi kama da Fulanin Gembu, sai kalan fatarsa da tafi dacewa da na mutanen Ethiopia”.
Tana gyaɗa kai cikin gamsuwa da jin son Fariyda har ranta tace.
“Yess ai dama Fulanin Gembu membila sunfi kama da mutanen Ethiopia fatarsu, gashi kansu, idonsu, duk irin na Ethiopiayawane, inaga yar Gembu ce, kai dai kaci gaba da kiran layin. Dan inaji a jikina in sha Allah yanzu kam ka samu matar aure”.

Cikin sassauta murya yace.
“Sai 5:30 pm flight ɗinmu zai tashi zuwa Ahmedabad Abba”.
Sai kuma ya ɗanyi shiru yana sauraron Abba.
“Me Doctor yace yake damu ka?”.
A hankali yace.
“Typhoid ne yace”. Cikin kulawa Abba ya kuma cewa.
"Tun yaushe robonka da zuwa Likitanka ya duba ka?”.
A hankali kamar maiyin raɗa yace.
"Abba dama 8 Mount ya bani, kuma basu cikaba”.
Da sauri yace.
"Yaushe lokacin zai cika?”.
Ɗan jim yayi a sanyaye yace. "Yanzu dai 43 days ne ya rage”.
Cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
"In sha Allah kafin anyi aikin Zaid kun dawo, nima zanzo wannan karon tare zamuje Cashmir ɗin, dan ina son jin sahihin gskyar lafiyarka dan har yanzu na gaza gane waye mai gsky tsakanin kai da ɗan uwanka Aminullah da ya bar min wasiyyar aura maka matarsa duk da sanin larurar ka, na yarda da haka da wanzar da wasiyarsa ne dan sanin yafi kowa saninka a duniya yafi kowa sanin lfyarka da cutarka. Kai kuma da kaƙi cewa komai na zuba maka idone dan zanje inji gskyar a wurin mafi sanin komai akan larurar ka ai shi Dr Avinash ɗin zai min bayani”.
Tunda ya sunkuyar da kansa bai kuma cewa kowamai ba.
Abba kuwa dama yasan hakan shine amsar da yake basa tun shekaru goma da ya faɗa cikin wannan jarrabawar sai kuma ya ɗaura da cewa.
“A lokuta da dama nakanyi wa kaina tambaya ko, ban cancanci ka gaya min halin da kake ciki bane shiyasa baka gaya min ada da yanzu da ba Aminullah ma, nasan bazaka taɓa yin wannan maganar da mahafiyarka ba kam to amman nifa da nake namijin ɗan uwanka”.
Cikin sanyi ya fara jujjya kansa murya na rawa cike da rauni yace.
“N.......

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 30
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.