Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 53 of 86
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗine 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo Evidence ɗin ki ta nan 09097853276 mutane Niger 1000cfa +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 22
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
https://arewapen.com/u/garkuwa
*Ku biyoni Arewapen kusha karatu ba ɓata lokaci*
Kai Ummi ta juyo tare da watsa mishi kallon dake nuna fushinta, sai kuma suka kalli Fariyda data miƙe tsaye ta juya ta bar parlour fuska cike da takaici.
Shi kuwa gefen Goggo Dada ya zauna tare da cewa.
"Dan Allah ayiwa yaran nan wanka a canza musu kayaâ€.
Cikin takaici Ummi tace.
“Uwar me kayan jikin nasu yayi, duk iyayinka dai ba fin Fariyda tsabta kayiba, Æ™a'idarta kullum kafin tayi sallan asuba takewa yaranta wanka ta canza musu pampers ta sa musu kayansu ko yaushe ka jisu suna Æ™amshi.â€
Yana ɗan kwaɓe fuska yace.
“To Ummi ai tunda kuma sunyi bacci kusan na awa uku sun farka ai ya kamata a Æ™ara musu wankaâ€. Da sauri Goggo Dada tace.
"Wlh itama dama haka takeyi suna farkawa kuma ko abinci bata basu sai ta Æ™ara musu wanka, ai wlh ko kasuwar maÆ™iya aka dasa rayuwar Fariyda an san yarinyace mai masifar tsabta da gayu.â€
Miƙe yayi tare da cewa.
“To ni me za'a dafa minâ€.
Cikin fusata Ummi tace.
“Wallahi tallahi daga yau sai ka nemi mai maka girki, tunda ni da Goggo Dada ba bayinka bane da zamuyi ta hidima da É—awayyina da kai tun kana yaro har yanzuma daka girma bazamu hutaba. Wlh tallahi in dai bazakaci girkin matarkaba in kaga dama ka zauna yunwa ta kasheka, yaro sai iyayi da tsurfa kayi ta juyani kamar wani ubana, inda yarinya ta zauna tayi maka girkin da ko maÆ™iyinta zai gani ya yaba kuma kowa yasan Fariyda da iya girki amman da yake kai ba'ayi maka gwaninta kai ta kushetaâ€.
Daga nan ta juya ta nufi bedroom É—inta, da sauri ta tsaya ganin zai fara É—abi'artasa da yatsa ta nunashi tare da cewa.
“Wallahi tallahi in ka bini sai naci mutuncinka, in kana son zaman lafiya dani Mahmoud kaci abin cin nan in kuma É“acin raina kakeso to kaje kai da Allahâ€.
Da ƙarfi ya rufe idanunsa tare da cewa.
“ Innalillahi wa inna'ilaihi rajiunâ€. Bata ma tsaya taji me zai É—aura akai ba.
Da sauri ya juyo wurin Goggo Dada, da sauri ta tsuƙe fuska dan ta lura ƙiyayyar Mahmoud akan Fariyda ya wuce zatonsu ɗaukar su Zaid tayi tare da cewa.
“Bari inje in musu wankanâ€.
Da sauri yace.
"Goggo Dada me Ummi take nufiâ€. Tana tafiya tace.
"Tana nufin in bakaci abincin da matarka ta dafa makaba Allah ya isa bata yafe maba, ta barka da Allahâ€.
Da sauri yasa yatsunsa ya toshe kunnensa ya juyawa ya nufi Dinnin area É—in.
Ita kuwa Fariyda tana hawa upstairs kai tsaye dakinta ta wuce cike da baƙin ciki.
“Aikin banza aikin wofi, ni da nasan ya dawoma ai ko ance inyi girkin zan cewa Ummi ko nayi ba ci zaiba.
Mara mutunci wanda baisan darajar É—an adam ba, wai jogogole shirme, a haka dai duk gidan girkina sukeci, wai ni ce mai jogogole girki kai wannan Allah yayi mai tsinennen baÆ™ar magna, ai wlh ko danshi ya kamata in cekiyar makarantar koyar da baÆ™ar mgna da karin magna habaici da shaguÉ“e nima inya inyi ta yaÉ“a masa har sai sun kasheshi kowama ya huta mitsssssssâ€.
Taja wani dogon saki tare da shigewa bathroom.
Wanka tayi ta fito har lau tana zageshi a ranta.
Tattausar rigar Turkeysh zip gwan tasa mai É—an faÉ—i tare taushi tayi cib-cib da É—an jikinta gyalensa ta É—aura a kanta ta shafa humrarta.
Tsaki taja tana ɗaukar kayan Zaid da Zaitoon ta fesa musu turare su, dan tasan Goggo Dada zata musu wanka, sauƙa tayi dan kai musu kayan a canza musu na jikinsu.
Tana shiga parlour ta hango Goggo Dada a tsaye a Dinnin area É—in, sunkuye yake kan washing hand baby É—in dake Dannin area É—in amai yakeyi tamkar zai haÉ—a da hanjin cikinsa ya amayar.
“Yah Salam sannu Mahmoud am.â€
Sai kuma ta kalli Ummi da itama yanzu ta fito daga ɗakinta bata ma lura da Fariyda dake durƙushe a tsakiyar parlour tana sawa su Zaid Pampas tare da sauya musu kayaba, cikin takaici tace.
“Wai aman me yake yi ne kamar zai haÉ—a da hanjinsa, duk dan nace dole sai yaci girkin matarsane yasashi wannan aman kenanâ€.
Da sauri ta sake Zaitoon data gama sawa riga tare da meda hankalinta kan Goggo Dada dake cewa.
“Wallahi kuwa tunda kikace baki yafe masa ba in bai ciba, yazo ya zauna ya fara ci, ni na tafi yiwa su Zaitoon wanka ne, na fito na samu yana ci, yana cikin ci kuma kawai naga ya tashi da gudu ya nufi nan ya fara kakarin amaiâ€.
Ta ƙare maganar tana kallon yadda ya haɗa zufa yana wanke fuskarsa da ruwan sai kuma ya miƙe tsaye ya dawo ya zauna kan kujerar Dinnin table ɗin manyan idonshi da sukayi jazir ya lumshe, a fadace Ummi tace.
“Wato dan na saka cin abin cin ne, shine bari kaci kuma ka amayarko? Wato dai ban isa da kai ba kenan Mahmoudâ€.
Da sauri ta miƙe tsaye bayan ta gama canzawa Zaid kaya juyawa tayi ta fita, tashin tane kuma yasa duk suka ganta shiyasa Mahmoud ya rakata da mugun kallon tsana.
Goggo Dada data zuba masa ido suna kallon kallone a ranta tace.
“Wannan faÉ—an fa duk Æ™arawa tsanar tasu zafi yake, na tabbatar yanzu Æ™ara tsanarta zai yi tunda aka sashi cin abincinta a dole harda Allah ya isa in bai ciba gashi yaci kuma ya harar akanta kuwa zai huceâ€.
Sai kuma ta kalleshi jin yana magna cikin muryar dake nuna zafin takaicin da yakeji da kuma tsoron fushin Mahaifiyarsa yace.
“Ummi garlic fa tasa a garlic cikin abincinâ€.
Da sauri Goggo Dada tace.
“Ayyah bata san baka son warinshi baâ€.
Ita kanta Ummi kai ta É—an jujjuya cikin sanyi tace.
“Na manta ban gaya mata kada tasa garlic a ciki ba, ba laifinta bane nawa ne sannuâ€.
Ta faɗa cikin tausayawa dan tasan shi baya son garlic ko kaɗan shiyasa tun yana ƙarami ma ake masa abincinsa da ban saboda baya so, ga kuma ƙarin ƙyanƙyami da yake dashi da zaɓen abinci da yakeyi. Ita kuwa Fariyda bata ma san ya dawoba bare ta gane shi zatayiwa girki dan tasan baya son garlic.
Goggo Dada ne tace.
"Bari in shiga in dafa mako wani abincinâ€.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Bari kawai zan je gidan Maman Hafizâ€.
Daga nan ya juya ya fita.
Ita kuwa Fariyda tunda ta hauro sama, wani irin dariyar jin daÉ—i takeyi tare da cewa.
"Kai amman naji daÉ—i, Allah ya saka min ai, ko ba komai moÆ™ogoro dai yaji hazan kakarin ido msifa yayi jaâ€.
Sai kuma ta nufi ɗakinta tana dariya harda riƙe ciki. a haka ta shiga ɗakinta.
A parlour ya zauna tare da yiwa Amina text message zai zo gidanta.
Tana ganin saƙonsa kuwa ta shiga kitchen dan bata ma san ya dawo ba.
Kan 3 seatter ya kwanta tare da kunna tv boxing ya fara kallo yana ɗan taune lip ɗinshi na ƙasa ji yake yi kamar shi yake dukan boxing 🥊 ɗin.
Cikin ɗan baccin da ta fara ne ta fara ɗan jiyo alamun sowa a parlour a hankali ta sauƙo daga kan gadon.
Ɗan gyalen rigar na saƙale a kafaɗarta.
Ta fito daga É—akin, bata hango kowa ba tunda a kwance yake kan kujerar.
A hankali ta nufo tsakiyar parlour tare da ɗan jujjuya kanta tana shaƙar ƙamshi da ya ƙara wadatuwa a parlour.
Gaban TV ta nufa dan har yanzu bata lura da shiba.
Da sauri ta juyo jin yaja wani irin dogon tsaki sabida yadda tazo ta tare gabansa ya zama baya ganin Tv.
Fuska ta tsuƙe tare da juyawa zata koma ciki.
Cikin zafin nama ya miƙe tsaye, da sauri ta juyo, juyowar da yasa ɗan kwalinta sulewa ya faɗi, cikin dakewa da ganin wani irin kallon da yake mata da nufota, sunkuyowa tayi dan ɗaukan ɗan kwalin.
Da ƙarfi ta runtse idonta tare da sakin ƙara mai ɗan sauti sabida jin yadda ya damƙo jelar tattausan gashinta ya fizgota tsaye, da sauri ta kai hannunta kan nashi saboda jin ya ƙara damƙe gashin da fizga dan jin sulɓin gashin na sawa yana zamewa cikin tafin hannunsa.
Watsa mata manyan idanunsa yayi dake cike da masifa da tsanarta a fili yace.
“Kika ce ke shashasha ce ko? To wlh ni zan saitakiâ€.
Hannunta ta fara yarfawa tuni idonta sunyi jazir ga jijiyoyin kanta da suka fara tashi sama cikin murguÉ—a masa baki tace.
“Ka sake niâ€. Yana Æ™ara matsota yace.
“this is a last worning ina sake tafiya kika kuskura kika kawo min ko wanne tarkacen karanutun baÆ™inki a Parlour na, wlh in na dawo sai na É“aɓɓallaki, ba abinda kika iya sai rashin kunya da tsiwa kiyi ta gautsin baki, sai masifar son jiki komai sai an miki kin haukatamin parlour kin maidashi kamar na mahaukata, dan kinsamu al'barkacin darajar Abba kin samu damar hawa side na har ki shiga parlour na, shine zaki rinÆ™a kwaso tarkacen baÆ™inki kina sako min su nan, to wlh daga yau in kika kuma min wannan iskancin zan saÉ“a miki kamanni, in baÆ™in kikeson kawowa ai gacan old part É—inki ki koma can in kinga dama ki kwaso karnukan family É—inkuma ki kawo nan ni ban damuba, amman parlour na dai karki sake gigin kawo min kowa, antafi anbar min warin hammatan gardiâ€.
Ya ƙare maganar da hankaɗa ƙeyarta da faɗin.
“Tv na kuma ba don kallonki na ajiyeba tunda bazaki iya goge masa Æ™uraba, sannan in kika sake buÉ—e min fridge sai na É—uraki a ciki kin daskare kowama ya huta, in kika sake leÆ™a min corridorn É—akina Hmmmm kima Æ™ara gwadawa ki ga abinda zan miki.â€
Tunda ya fara magnar take kallonsa cike da mmki to ko dai akwai CCTV camera ne a parlour nasa dan dai tasan tabbas da wuya ace su Ummi sun gaya masa zuwan Goggo Abu da Yah Mujahid, in ma sun gaya masa ta ina yasan tana kallo a TVnsa tunda suma basu saniba, sannan ta ina yasan ta buÉ—e mai fridge É—insa.
Cikin tsawa yace.
“Bace min daga nan kije kiyita abinda kikafi iyawa wanka da zumbuÉ—a turare dan baki san tsadar kuÉ—in sayansubaâ€.
MurguÉ—a masa baki tayi tare da juyawa tayi ta fita tana faÉ—in.
“Ai bani na kawo kaina nan ba, nima dole aka saniâ€.
Harara ya auna mata duk da baijita ba.
Dinnin area ya wuce tare da wanke hannunsa Admiral ya É—auka a fridge É—insa ya wuce bedroom nasa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.