Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 25 of 86

A can cikin gida kuwa dai-dai lokacin.
Sulaiman da Salim suka shigo a tare.

Gaban Abba dake Al'wala Sulaiman ya dire guiwowinsa yana kuka tamkar mace.

Salim kuwa gaban Mahmoud ya wuce yana zuwa ya rungume shi da ƙarfi tare da fara jujjuya kai gami da faɗin.
“Mahmoud kayi? Mahmoud ka zubda ƙwalla”.
Amman ina kamar ma ba dashi yake yi ba, sai addu'ar da yake mai-mai tawa, kukan da Salim keyine ya sashi fara rawan jiki tare da fara mai-maita.
“Allaahum-maghfir lahu warhamhu, wa 'aafihi, wa'fu 'anhu, wa 'akrim nuzulahu, wa wassi' mudkhalahu, waghsilhu bilmaa'i waththalji walbaradi, wa naqqihi minal-khataayaa kamaa naqqaytath-thawbal-'abyadha minad-danasi, wa 'abdilhu daaran khayran min daarihi, wa 'ahlan khayran min 'ahlihi, wa zawjan khayran min zawjihi, wa 'adkhilhul-jannata, wa. 'a'ithhu min 'athaabil-qabri wa 'athaabin-naar.”.
Jin hakane yasa Salim fara bin bakinsa kana suka tashi domin yin al'wala.

Bayan anyi sallan azahar ne, aka sallaci gawar Aminullah da ya samu hallarta dubban al'ummar Annabi na birnin Kano da kewaye yan uwa da abokan arziƙi
Ƙarfe biyu dai-dai aka kaishi makwancinsa, kansa suka dawo zaman karɓan gaisuwa.
Duk da girma da fadin farfajiyar Saida ya nemi gazawa masu shigowa.

A ranar dai haka aka wuni zuciya cike da ƙuna.

Washe gari da safe
Salma ce zaune bisa kujerar table ɗin dake kitchen kuka takeyi har yanzu cikin sanyi ta kalli Miminta murya na rawa tace. “Mimi shekaran jiya uwar hakafa duk muna tare da Yah Amin, Mimi naji tsoron duniyar nan ba komai bace”.
Cikin rauni Mami tace.
“Salma yi haƙuri kizo ki tayani mu ƙarasa aikin nan in samu in tafi gidan gaisuwar nan.”
Tana mai share ƙwalla tace. “Mimi nima yau kam zanje”.
Ta juye kunun data dama cikin wani babban kula tace.
“Ki bari sai gobe kuje dan su Raihana ma basu jeba dan sune a gida”.
Tana kuka tace.
“To zan tafi wurinsu tunda Yau Aunty bazatajeba.”
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A can gidan kuwa Raihana da Zainab da Humaira ce sukayi zuru-zuru dasu ba kowa a gidan sai su sune sukayi abinci mai yawa da masa da kunu suka bada Sadiq ya kai.

A anan gidan su Ummi kuwa.
Mahmoud dai har yanzu bai cewa kowa komai ba.
Koda gaisuwa aka zo masa da ido yake amsawa ko kai sai addu'o'in neman yafiya da gafarawa da yakeyiwa ɗan uwansa.

Fariyda zaune a ƙasa gaban Ummi da Mamy.
Shigowa Sulaiman ne yasata zuba masa ido tun jiya da suka iso basu shigo gidan ba sai yanzu.
Da suka shigo da manyan kulolin abincin da Abida matar Ahmad ta iso dasu.
suna haɗa ido da Sulaiman sai kawai ta kife kanta dan tuno sun da yake kiranta.
Ta Yah Amin mutukar raba.
Kuka mai sanyi Sulaiman ya fara.
Cikin rawan murya tace.
“Ayyah Sulaiman kaga mutuwar tayi gaggawar rabamu ko”.
Kai ya fara jujjuya mata tare da miƙewa ya fice.
Da sauri Salim ma yabi bayansa, ita kuwa lips ɗinta da suke kumbura sukayi jazir tsabar cizasu da takeyi Cizawan ta kuma yi da ƙarfi.

Yayarta Adda Nana dake gefentane tace.
“Kiyi haƙuri Fariyda in sha Allah Yah Amin yana cikin rahamar Ubangiji kiyi masa addu'a ki dena magana”. Aunty Saddiqa da itama jiya tazo daga Yola.
A hankali ta fara jujjuya kai tare da fara addu'a.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ، وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدْ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَما نَقَّيْتَ الثَّوْبُ الأَبْيَضَ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَاراً خَيْراً مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْراً مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجاً خَيْراً مِنْ زَوْجِهِ، وَأَدْخِلْهُ الْجَنَّةَ، وَأَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ
Domin shi kadai take yi taji sanyi.

Washe gari da yamma ranar sadakan Uku.

Su Salma ne a durƙushe gaban Ummi sunayi mata gaisuwa sai kuma suka kalli Fariyda data zuba musu ido ba magna sai lips ɗinta da take motsa wa tare da jan carɓi.
Ina Salma kam da Zainab sun gaza danne kansu ganin yadda cikin kwana uku Fariyda ta zama tamkar ba itaba saboda ƙuncin zuciya.

Suna nan a gidan har sai wuraren ƙarfe goma.
Suka tattara ita da Mimi da Aunty Amarya.
Da Aunty Rakiya matar bappansu ƙarami.

A hankali suka fito harabar gidan.
Hango rumfar ba mutane da yawa alamun duk sun tattafi ne yasa suka nufi can dan samun gaida Abba da Mahmoud.

Su ɗin kuwa suka Samu Abba, Bappa Lawan, Mahmoud, Sulaiman, Salim, da Hafiz sai Kabir Manager Kebbi.
Sai kuma Yah Ahmad dake tsaye riƙe da hannun ɗansa Ayman da alamun yanzu yake shirin tafiya.
Bayan sun gaida Abba da Bappa Lawan ne.
Salma ta kalli Mahmoud kallo ɗaya daya tsinka mata ruwan hawayenta cikin sanyi tace.
“Yah Mahmoud ya haƙuri.”
Ganin ya gyaɗa mata kai ba tare da ya amsa bane yasa taci gaba da cewa.
“Allah Ubangijin talikai ya jiƙansa da rahama yasa ya huta”.
A saman lips ɗinshi ya amsa da Amin a hankali kamar yadda ya fara tun jiya. Cikin sharce hawaye Raihana tace.
“Allah ya jiƙansa yayi masa gafara”.
Haka ya rinƙa amsa musu da Amin akan Labbansa.
Daga nan dai Dr Nasir da Yah Kamal dake jiransu a mota suka tafi.

Haka dai rayuwa tai ta tafiya zuciya cike da ƙunci yau ne akayi sadakan bakwai.
Bayan an watse, sai iya su na jiki- jiki kawai
Gyara zama Baba Malam yayi tare da kallon Abba da cikin sanyi ya ƙara yi masa ta'aziya tare da jeron addu'o'i masu yawa ga mamacin sannan ya kalli Abban cikin sanyi yace. “To yau kam zamu tafi da Fariyda da yaranta, tunda anyi bakwai”.
Cikin wani irin yanayi mai rauni Abba yace.
“Meyasa bazata zauna a ɗakinta ba tayi takaba a wurin mu”.
Kai Baba Malam ya jinjina tare da cewa.
“Banƙi ta taka ba, Amman ita uwar tata da wuya ta iya zama har tayi takaba a nan, ko nima inaga lokacin da tsawo, sannan ita kuma Fariyda kaga yanayin da take ciki, ko abinci bata ci sai uwar ta matsa mata, sannan bata da isashen lfy, kaga in mun koma da ita Nasir zai kula da ita sosai”.
Kai Abba ya jinjina cikin sanyi yace.
“To ai ga Dada zata zauna da ita”.
Cikin yin ƙasa da kai Dr Nasir yace.
“Afwan Abba zan iya magna?”.
Kai Abba ya gyaɗa masa alamar eh.
Gyara zama yayi tare da cewa.
“Abba kayi haƙuri Amman zaman Fariyda a nan ba sauƙi a zuciyarta.
Dan ko part ɗin ta bata sake shigaba tunda akayi rasuwar nan, jiya tana kuka tace min ita bata son zama a gidan duk inda ta juya idonta tuna mata Aminullah yakeyi”.
Cikin sanyi Bappa Lawan yace. "Lallai haka Jidda take gaya min jiya da muna komawa, inaga a barta su tafi tare kawai”.
Cikin sanyi Mahmoud da sai yau ya buɗi baki yayi magana da ficecciyar murya yace.
“Amman banda su Zaitoon da Zaid ko?”.
Cikin sanyi Abba yace.
“To Mahmoud ta ya zamu rabasu da uwarsu da abincinsu.”
Murya a harɗe yace.
“To muɗin kuma fa sai mu rasa Abbansu kuma suma mu rasa su, ni bani da matsala da tafiyar ta sune dai bazan iya rayuwa ba suba”.
Cikin tausasawa Baba Malam ya dafa kafaɗarsa tare da cewa.
“Kayi haƙuri Mamuda ai da nan da gidana duk ɗaya ne, duk sanda kakeso zakaje ka gansu, bazamu rabasu da uwar bane dan tana shayar dasu.
Da zaran an yayesu duk yadda kakeso haka za'ayi dasu a matsayinka na uba a garesu”.
A hankali ya maida bakinsa da ya buɗe da nufin yin magana ya rufe, sabida ɗaga masa hannu da Abba yayi tare da cewa.
“Ba komai Allah ya raya mana su bisa imani, amman kayi haƙuri Malam Ibrahim ka bari sai gobe azo a ɗaukesu”.
Cikin mutuntaka Baba Malam yace.
“Allah ya kai mu bisa rai da lfy”.
Da Amin suka amsa baki ɗayansu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.