Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 55 of 86
A parlour ta samesu yana bawa Zaid maganinsa
Zaitoon na ganinta tayi kanta tana.
“Ammey Ammey”. Goggo Dada tace.
“Kaddai magna zakiyi ki jawa kanki yaye”.
Ummi tace.
“Bakiji ba da Mahmoud ya shigo wai Appiy”.
Da sauri Fariyda tace.
“Dama ai na gaji yayen zamuyi Goggo Dada”.
Goggo Dada tace.
"Haba ai kya bari suyi shekara ɗaya da rabi yanzu dudu shekara daya da wata uku ne garesu fa”.
Ummi tace.
"Bare ma Zaid da ba fly ce ta ishesa ba, nagama basu da yawan tsotso”.
Mahmoud suka kalla dukansu jin yana cewa.
“Wlh kada a kuskura a yaye min yara basu kai yayeba”.
Murmushi Maman Samira tayi tare da wucewa ba tare da tace komai ba.
Ita kuwa Fariyda cikin tsuƙe fuska tace.
“Ai sune basu damuba wata ranama har a kwana a wuni basa kulawa”.
Yana sinkan grapes yace.
“Ba'a basu dai an addabi rayuwarsu da masifar rowa”.
Murmurshi Maman Samira tayi tana mai hasaso wani irin zama da za'ayi a gidan.
Shiru sukayi daga nan ba wanda ya kuma cewa komai sai Ummi ne ta kalli Fariyda tace.
"Sai yaushe ne zaki tafi sunan”.
Tace.
“Na tambaya yaƙi ya kulani”. Da sauri Ummi tace.
“Mahmoud haihuwa fa akayi musu yau suna ka barta taje mana”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“To Ummi ni me ruwana in taga dama ta zagaye duniya dukama mana”.
Daga nan ya fita bai jira ma me Ummin zata ceba.
“Tashi kije ki shirya kije abinki”.
Ai kuwa da sauri ta dire Zaitoon tare da cewa.
“Ummi Ngd matuƙa. Samira Zo muje ki karɓi kayansu Zaid ki canza musu”.
Da sauri Samira tace.
“Aunty sai dai in jiraki a Downstairs, ba'a shiga parlour Yah Mahmoud ai”. Da sauri tace.
“Zo dai”.
Daga nan ta fita ta bawa Samira kayansu sannan ta koma ta shirya cikin wata Gezna mai masifar kyau da tsadar gaske doguwar rigace data sha aiki na gasken-gaske sai ƙyalli da sheƙin maiƙomta take yi. Pink collar ce da akayiwa aiki da zaro golding.
Cib'cib rigar tayi a jikinta tubke gashin kanta tayi ba tare da ta kitse shiba ta bar shi kwance a bayanta ɗaurin asetta ta murza irin mai ɗan karkacewar nan gyalen shantilly golding ta yafa bayan tasa yan kunnen da sarƙa ma gold ɗan gaske sai takalmi da jaka suma golding color turare ta yaryaɗa mai sanyin ƙamshi kana ta fito tana saƙala agogon Apple watch pink collar.
A bakin ƙofar ta ɗan tsaya jin yana cewa.
“In kika sake taka min cikin parlour da takalmin da ba gogesu akeba sai na karya sawun”.
Baki ta murguɗa ta fita tana faɗin.
“Duk sharrinka ko sasu ma ban taɓa yiba”.
Da harara ya rakata.
"Ta nan kam tana gaba gaba ayi wanka a baza turare a karaɗe gari da yawo kamar marshing da ƙafa kamar na sauro”.
Baki ta tura tare da cewa. "Ni dai bana yawo, yawo ai sai karuwa”. Tayi mgnar ta yadda bazai jiba. Sai kuma tayi saurin sauƙa ganin ya juyo dan jin kamar tayi magna.
Tana sauƙa Hafiz na isowa cikin happy tace.
“Barka na muje ka sauƙeni”.
10k Ummi ta bata tace gashi ta kai mata, har ta juya zata fita ta tambaye ta ita kuma me zata kai mata turmin zanin Chiganvy dake da rigar baby girl wacce cikin na Zaitoon da basu buɗe ba ta ɗauka.
Cikin gamsuwa Ummi tace yayi, daga nan suka tafi.
Gidan suna kam ya cika maƙil cika iya cikar bikin masu manyan family.
Tana shiga parlour duk akayi kanta kowa da abinda yake faɗa.
Hafsah ce yar Goggo Abu tace.
“Ikon Allah bana so bana so harda suma da aka ɗaura aure sai kuma kuka jini dib sai murjewa da baza kyau da ƙyalli nakeyi”.
Dariya akayi dan sanin da Fariyda take.
Ita kuwa Fariyda fuska ta yamutsa tare da kallon Salma tace.
“Mu tafi bedroom”.
Tana kallonta tace.
“Gsky fa Hafsah ta faɗa nima naga sai wani ƙyalli kikeyi kin ga yadda kikayi wani irin mashahurin kyau kuwa ga kamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa.
Da alama dai yanzu kam tafiyar ta fara daɗi”.
Cikin ainihin zuciyarta tace.
Cikin magnar zuci tace.
“Ya mutuma mana, har duniya ta tashi ai bazan daina baƙin cikin abinda su Malam sukayi min ba, ko ya sakeni in na tuna dole inji baƙin ciki”.
A fili kuwa.
“Hmmm kawai tace.
Aisha da sukayi kiciɓis da ita bakin ƙofar ne ta rungume Fariyda.
“Ayyah ƴar kekkyawar ƙanwata har na fara cire rai nace wata ƙil ya hanaki ne”.
Kwaffa tayi cikin sanyi tace.
“Ai kam ya hana ɗin dan yana jin kansa Mamy ta samin sharaɗin dole sai da izininsa zan fita in ban tambaya ba bata yafe ba. Nayi ta masa mgna ko kallona baiba, ni kuwa Ummi uwar kirki tace ya barni in zo.
Zainab da Raihana ne suka shigo riƙe da su Zaitoon.
Kan gadon suka zauna can gefe dan akwai wasu a bakin gadon cikin zaƙuwa tace.
“Salma ina jinki”.
Da sauri Zainab tace.
“Wai da gaske baki san suna soyayya da Salim ba cousin ɗin Mahmoud”.
Cikin mamaki tace.
“Salim ɗin dan Allah fa yaushe aka fara kai amman naji daɗi Alhamdulillah dan Salim mutumin kirkine yana da sauƙin kai”.
Murmushi Salma tai tare da cewa.
“Next week ma za'a kawo kuɗin na gani inaso dana sakun rana”.
Nan ta fara bata lbrin yadda lamarin ke tafiya.
Adda Nana dake gefensu ne tace.
“Shike nan amintaka zata ƙara ƙarfi”.
Nan dai aka wuni lugujen leɓe surutu da nishaɗi har dare Fariyda ta kalli Salma tace.
"Bari in kira Hafiz yazo mu tafi, naga Zaid ya fara halin yaro dama ba fara'a bare ga ciwo ga gadon baƙin hali da masifa duk ya kwaso”.
Salma tace.
"No barshi Salim zaizo sai ya sauƙeki kawai”.
Tana gyara zama tace.
"Aiko shike nan”.
Anayin sallan isha yana isowa.
Salma ce a front seat riƙe da Zaitoon Fariyda da Zaid a baya.
Kan Zaitoon ya shafa tare da kallonta yace.
“Kamar su bamu ko”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Nima haka nace”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Fariyda dake jijjiga Zaid yace.
"Madam dai nasan bata da matsala amman Mahmoud ai mutuwa ce kaɗai zata iya rabasa dasu Zaitoon”.
Sai kuma ya ɗanyi ƙasa da murya yace.
"Ke dai ki shirya kawo biyu kamar su a bugun forko”.
Da sauri ta rufe idonta tare da kallon Fariyda da ɗan kukan Zaid yasa bataji ba.
A haka suka isa gida bayan yayi parking ne Fariyda ta fito riƙe da Zaid da bag da lododin abun suna ke ciki.
"Mu isa mana ku gaisa dasu Ummi”.
Tana ɗan murmushi tace.
"To muje”. Ta fito rungume da Zaitoon da tayi bacci, daga nan shima Salim ya fito a tare suka shiga parlour inda suka samu Ummi kaɗai, jinsune yasa Goggo Dada dake kitchen fitowa nan suka gaggaisa sannan Salim ya miƙe yana kallon Salma yace.
“Muje ko”. da sauri ta miƙe tsaye tana yiwa su Ummi Saida safe.
A Compaud suka haɗu da Mahmoud da ya dawo daga wurin Dr Fadil.
“Ina yi”. Salma tace mishi ba tare da ta kalleshi ba.
Salim dake masa alamun ana gaishaka ka amsa ya harara tare da cewa.
“Gobe da safe ka shigo zamuyi mgna”. Daga nan ya wuce.
Itama bata kuma gaidashi ba suka shiga mota suka tafi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.