Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 51 of 86

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo Evidence ɗin ki ta nan 09097853276. Mutanen kasar Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 21
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

https://arewapen.com/u/garkuwa.

Ya matsota tamkar zai rungumeta, da sauri ta ƙara jan baya tare da kauda kanta daga gareshi ganin wani irin kallon zazzafan son da yake mata tamkar zai cinyeta ɗanye, numfashi ta sauƙe tare da nufar bakin ƙofar da Goggo Abu ta ƙaraso ciki.
“Goggo san da zuwa iso ciki”.
Tana ƙarasowa ciki ta sauƙe numfashi hawa upstairs ɗin da tayi tace.
“Yauwa Fariyda na, kai sannu kuna fama da hawa da sauƙan nan”.
Ta dire mgnar tana zubewa kan 2 seatter.
Sai kuma tayi saurin kamo hannun Fariyda data juya tana faɗin.
“Bari in kawo miki ruwa”.
Shi kam Muhajid tamkar zautacecce haka yake kallonta cikin tsananin so da ƙaunarta da yakeji tamkar ya rungumeta, komawa tayi ta zauna gefen Goggo tare da ware gyalan da yake kanta ta yafa a jikinta.
Jin Goggo Abu na cewa.
“Yi zamanki bamu da ƙishi tun ɗazu muna ƙasa wurin surkanki harda kindirmo muka sha, kawai hakin na haurawa saman ne.“
Bayan sun gaisa ne Goggo Abu tace.
“Gidan Aishan Sani mukaje”.
Da sauri tace.
“Kaddai ta haihu ban jiba”. Tana gyara zama tace.
“Eh ta haihu amman tiyata akayi mata, shekaran jiya an cire ya mace”.
Fariyda tace.
“Ya Salam wlh ban jiba, su Mamy basu gaya min ba”. Mujahid ne yace.
“Ai kuwa an faɗa a group ɗin Family, har hoton baby an turo”. Ba tare da ta kalleshi ba tace.
“Kwana biyu da Zaid ba lfy ban cika hawa online ɗin ba”.
Goggo Abu na shafa kan Zaid ɗin da tuni sunyi bacci tace.
“Haka dai Hajara (Aunty Amarya ke gaya min yanzu da muka haɗu a gidan Rashida shiyasa nace Mujahid ya bi ta nan in dubashi da jiki, amman naga da sauƙi gashi har yana bacci a yadda akace yake ihun nan kam”. Tana mai ƙara gyara mayafinta tace.
“Da yake abun tashi yake yi, amman dai Alhamdulillah da sauƙin kam”.
Tace. “Allah ya ƙara sauƙi”.
Amin ta amsa tare da cewa.
“Goggo me zan dafa miki?”. Da sauri Goggo Abu ta miƙe tare da cewa. “Ni kinga tafiyata ma Fariyda am, Allah ya ƙara sauƙi”. Kai ta ɗan langoɓar tace.
“Ayyah Goggo Abu dan Allah mu wuni mana, ki tsaya in dafa miki duk abinda kikeso, bazan ji daɗi kizo wurina kuma ki tafi baki ci komai ba ko ruwa mafa baki sha ba”. Tana kallon Mujahid da ko gezau baiba tace.
“A'a Fariyda ai nasha a wurin surkanki Allah yayi muku al'barka”. Ta ƙare maganar da yiwa Mujahid kallon kai tashi mu tafi mana. Kai ya ɗan juya tare da miƙewa yabi Bayan Fariyda data marawa Goggo Abu baya. Sallama suka yiwa su Ummi kana suka tafi.
Washe gari daddare Mama ce zaune gaban Bappa Lawan dake faɗi mata.
“To Alhamdulillah Salim ya samu yardar iyayen yarinyar da yace yanaso, kuma sun bashi izinin fara zuwa zance, jiya da safe Yaya ya kirani da naje yake shaida min yadda sukayi da Malam”.
Cikin sauƙe numfashi tace. “To Alhamdulillah Allah ya dai-daita tsakaninsu yayi musu zaɓi mafi al'khairi, ya nuna mana lokacin bisa rai da lfy”. Yana gyara zaman glass ɗin idonsa tare da kallon fuskar wayarsa yace.
“Allahumma Amin”. Kai ya ɗago ya zuba mata ido jin maganar da ta shigar.
“Saura kuma batun Jidda da Mahmoud shi banji kace komai ba Alaji, ka kuwa san halin da Jidda ke ciki, duk ta susuce ta hanani kwanciyar hankali akan batun Mahmoud sai gashi kuma baka cemin komaiba”. Yana mai sauƙe numfashi yace. “Nine dai nace ki bari duk yadda mukayi da ɗan uwana zan gaya miki, ai sai ki barni ba kiyi ta uzzura min ba. Ni kaina fa zanyi farin ciki da hakan in Allah yasa mun tabbatar da warakar Mahmoud kamar yadda Aminullah ya faɗa, sai ku barni inyi aiki da hankali bada zuciyar gaggawa ba”. Cikin sanyi tace.
“To wai ai naga da zaifi kyau a haɗa aurenta dana Salim lokaci guda”. Yana maida kallonsa kan wayar da kiran Ahmad ya shigo yace.
“Ke dai kiyi ta mata addu'ar zaɓin Allah nima addu'a nakeyi kafin isar da soƙonta wurin Yayana itama kice ta dage da addu'a in al'khairi ne Allah ya tabbatar”.
Cikin yaƙinin kai da kai tace.
“In sha Allah ma al'khairi ne”. Daga nan ta miƙe ta fice, a parlour ta samu Jidda da ƙawarta data kawo mata ziyarar wuni da sauri suka kalli Mama riƙo hannunta tayi tare da ce mata. “Mama Abba ya yarda”. Tana zama gefen ta tace.
“Bai gaya masaba tukun yace mu dage da addu'a kafin isar da saƙon zaifi kuma dole sai an tabbatar da lfyar Mahmoud”.
Tana gyara zama tace.
“Baki cewa Baba harda azumin bakance ma zanyiba”.
Ƙawar Hajara tace”.
“In sha Allah kuma in dai alkhairi ne zaki sameshi in Kuma kinga baki sameshi ba to ba alkhairi bane a gareki”.
Numfashi Mama ta fesar tare da cewa.
“Ki shirya akwai inda zamuje gobe gwara in sawa abin hannnu muje a jawo mana hankalinsa”.
Cikin jin dadi tace.
“Yauwa Mamana sai yanzu nasan kina son cikar burina”. Tana kallon Hajara data zuba mata ido cikin mmki tace.
“Wurin da nisa kam akwai tafiya mai yawa zaki iya?”. Cikin neman biyan buƙatar rai tace.
“Mama ba abinda bazan iya yiba akan Mahmoud ko ina ne zanje”. Fuska cike da mmkin Hajara tace. “Da dai kin dogara da Allah shine mai bada komai Jidda Mama haramun nefa zuwa irin wuraren nan”. Tsuƙe fuska Mama tayi tana miƙewa tsaye tace.
“To Malam Hajara a gaida mutan gida”. Daga nan ya juya ta barsu a parlour.
Bayan kwana huɗu Ummi ne ta kalli Fariyda dake goye da Zaid da jiya ma ciwon cikinsa ya tashi kwana yayi kuka sai yanzu da ya samu ɗan sauƙin.
“Gobe ne sunan Rashida ko”. Tana ɗan jijjigashi tace. “A'a ɗazu mukayi waya da Adda Nana ke cemin an ɗaga sunan sai wani satin kafin nan ta ɗan ƙara samun lfy dan tiyatar nata ya ɗanyi gardama”.
Ummi tace. “Ayya Allah ya bata lfy, to yaushe zakije ki dubata da jiki”. Kai ta ɗan jujjuya tana tunanin kalaman Mamynta da sharaɗin Allah ya isan data kafa mata, sannan ita kuma ji takeyi bazata iya tambayar Mahmoud izinin fitaba, to gashi ma baya ƙasar ma baki ɗaya, ita ko kalar wayarsa ma bata saniba bare number sa. Ta saki tunanin nata jin Goggo Dada na cewa.
“Kiyiwa Mahmoud ɗin mgna ko ta WhatsApp sai kije ki dubata da jikin kafin sunan, naga kuna da ƙoƙarin lokacin da akayi miki Cs ɗin nan ba wacce bata zo ta dubaki da jikiba kafin suna kuma duk sun zo sun cika”. Cikin sanyi tace. “Ai ita da kanta ne tace in bari ba sai naje dubata da jikinba tunda Zaid ba lfy in bari kawai sai suna dai kam tana zuba idon ganina”. Ummi tace.
“Ayyah to Allah ya kaimu lokacin”. Da Amin suka amsa, sai kuma ta ɗan kwance Zaid ɗin tare da miƙawa Ummi shi ganin ƙarfe biyar tayi lokacin kallon film ɗin da take bibiya a Zee world ɗin yayi ne yasa ta zame ta haura sama.
Bisa kujerar ta kwanta bayan ta kunna TV murmushi tayi ganin dai-dai lokacin aka fara.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.