Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 26 of 86

Washe gari da safe.
Abba ne zaune a parlour yayinda duk ahlin nasa suke zaune a ƙasa harda Mamyn Fariyda.

Cikin rawan murya Ummi da suka gama sauraron jawabin Abba na yadda sukayi da Baba Malam.
Ido na zubda ƙwalla tace. “Allah sarki mutuwa, ta rabaka da matacce ta kuma rabaka da rayayye, ko ya zaman gidan nan zai zame mana ba Aminullah. Ba Fariyda, Ba Zaid da Zaitoon, to wani farin ciki ne kuma ya rage mana a gidan”.
Sai kuma ta kalli Goggo Dada data jawo Fariyda ta rungume tare da faɗin.
“Fariyda muna sonki ki zauna damu, bama son kiyi nesa damu, jinki muke cikin jini da tsokar zuƙatanmu”.
Tunda akayi rasuwar sai yau kwalla ta zubo mata murya na rawa tace.
“Nima ina sonku Goggo Dada, bana son rabuwa daku, amman zan haukace in ina gidan nan, bazan iya zama a cikinsa ba Yah Amin ba, ji nake tunanina yana hautsinewa kamar zanyi hauka, in naga Ummi na kuka ji nake zuciyata zata fashe, in su Zaitoon suna kuka raina gasuwa yake ji nake kamar in dora hannu a kai inyi ta ihu”.
Sai kuma duk suka kalli Amina data kife kanta jikin kujerar da Abbansu ke kai ta saki kuka tana faɗin.
“Aunty Fariyda yanzu mun rasaki kenan”.

Kai ta fara jujjuya mata tare da cewa.
“Maman Hafiz bamu rabubq, in sha Allah muna tare”.
Hafiza ce ta fashe da kukan da yasa su Zaitoon ma kuka.
Nanfa duk suka kacame da kuka har Abba yau saida ya zubda ƙwalla.
Ita kuwa Fariyda kamar abin iska sai gata ta kuma sume wa.

Suman tane yasasu yin shiru tare da yayyafa mata ruwa.

Shi kuwa Mahmoud duk abinda akeyi rungume su Zaitoon kawai yana jin tamkar ya maidasu cikinsa.

Nasiha mai ratsa jiki Abba yayi musu da tunasar dasu ladan dake cikin haƙuri da mahimmancin yiwa mamaci addu'a.
Hakan ne yasa suka ɗan nitsu.

Haka dai Samira da Raihana suka Tattarawa Fariyda duk kayan yaranta, sai kuma nata da suka kimtsesu a akwatuna, huɗu na yaran kuma akwati uku da baby drawer ɗinsu.
Duk Dr Nasir ya maidasu gida.
Sai dare yazo ɗaukarta da mahafiyarsu.

A hankali ta durƙusa gaban Abba da Ummi da Goggo Dada.
“To Abba zan tafi, Ummi ku yafe min Goggo Dada in akwai abinda na taɓa yi muku cikin rashin sani ko ajizanci na ɗan adam.
Ni baku taɓa jimin komai ba, koma kunmin na yafewa kowa.”.
Sai kuma ta kamo hannun Amina da Samira tana zubda ƙwalla tace.
“Ku yafe min”.

Hannu Abba ya ɗaura a tsakiyar kanta tare da cewa.
“Ba komai Fariyda Allah yayi miki al'barka” ya raya mana yaranki, ki kula da takabarki wanda Allah ya ɗaura miki tashi kuje”.
Ya ƙare maganar yana kallon yadda duk su Ummi mutuwar ta dawo musu sabuwa.

A hankali Mamy ta miƙa wa Mahmoud hannu tare da cewa.
“Kawosu”.
Ido ya ɗago ya zuba mata ba tare da ya bata yaranba,
Sai kuma ya kalli Dr Nasir Cikin murya mafi rauni da karaya Mahmoud yace.
“Mamy gasu Amana ne a garemu baki ɗaya, gasu a hannunki keda Dr Nasir na danƙasu da Baba Malam.
Na bada su da sharaɗin duk randa aka yayesu zanzo in amshesu.
mamy a kular min dasu domin sune madadin ɗan uwana”.
Kuka mai karfine ya kwabcewa Fariyda wanda yasa ta nufi waje da sauri.
Da sauri Goggo Dada ta mara mata baya.
Shi kuwa Mahmoud Mamy ya bawa Zaitoon kana ya bawa Dr Nasir Zaid”.
Daga nan suka fita suka tafi tare da rakiyar Ummi da Abba Hafiza da Samira da Amina kam tuni kuka yasata shiɗewa dib ganin hakane yasa Matar Barrister da Abida mayar Yah Ahmad da Maman Jidda sukayi kanta....

A can gidan Baba Malam kuwa tuni Raihana da Salma sun gama shiryawa Fariyda komai nata a bedroom ɗin dake gefen na Mamynta inda nan Raihana take kwana tunda tazo Hajja inna ma nan ta sauƙa inda tayi kwana biyar ta koma Gembu jiya.

Koda suka dawo nan ma sai gidan ya zama salam saboda ba wani farin ciki sosai a cikinsa.

Haka dai rayuwa tai-ta tafiya.
Har yau da akayi kwanaki arba'in cib da rasuwar Aminullah.

Zaune yake a parlour Baba Malam rungume dasu Zaitoon da suke ta maƙale wuyanshi suna zagayesa, sunanta dariya da Balankwace.
Yayinda Hafiz ke ta shigo da kayayyakin da suka yiwa su Zaid shopping.
Ido Baba Malam ya zuba musu ya gaza janye idonsa daga ganin shi da yaran ɗan uwan nashi.
Mamaki yake yadda yaran ke tsananin shiga farin ciki in sun ga Mahmoud ɗin.

Numfashi ya ɗan fesar tare da kallon kayan masarufi da Hafiz ya gama jibgesu.
Kama daga madarar Naan Sugar Custard Cerelac Pampas and tissues omo sabulu set ɗin baby shampoo and conditioner baby oil. Sai kuma cartons ɗin Bobo indomie da pasta sai buhun shinkafa ɗanye da gumi, kana da manyan gongonayen madara, da kuma set ɗin rigunan sanyi na yara kusan kala biyar-biyar.
Cikin sauƙe numfashi Baba Malam ya fara girgiza kai.
“Mahmoud”.
Ya kirasa cikin kulawa cikin girmamawa ya amsa tare da zuba mishi ido. “Duk wannan kayan na menene haka? Hidimar tayi yawa, du-du yaushe ka turo Hafiz ya kawo kaya kamar haka, abin ko wata ɗaya bai cikaba, sannan yanzuma ka kuma libgo kaya haka kada abin ya zama almabazzaranci fa, sannan kuma meyasa zaka rinƙa haɗowa da shinkafa yaranda iya karsu indomie sai abubuwan shansu da suka bawa mahimmanci”.
Cikin yin ƙasa da kanshi yana shafa fuskar Zaitoon yace.
“Baba Malam ai haƙƙin nane in kula da duk wasu buƙatarsu, bana son su buƙaci wani abu su rasa shi yasa”.
Da sauri yace.
“Ai duk abinda suka buƙata zamuyi musu”.
Cikin sanyi yace.
“Bana son kowa yayi musu wani abu dan bana son su tashi su jisu kamar marayu, Malam tunda suna dani ba bukatar kowa ya taimaka musu a rayuwar nan.”
Kai ya gyaɗa mishi cike da raunin da yasa idonsa na cikowa da hawaye.

Hafiz ne ya amshi Zaid dake ƙoƙarin tahowa wurinsa.

Zaman awa ɗaya yayi da yaran da tunda suka dawo baizo ya gansuba sai yau sai dai duk ranar juma'a zaisa Hafiz ya ɗaukosu suzo gida su wuni tare sai dare yake maidasu, bayan sun tafine.
Baba Malam ya kalli Mamyn Fariyda dake mamakin kayan da Mahmoud ɗin ya kuma libgowa.
“Malam da dai an hanshi wannan hidimar tunda ba shi zai rinƙa ciyar da gidan nanba dan su Zaitoon na gidan”.
Kanta ta ɗago ta kalli mijin nata jin shiru bai tanka mata ba.
Idonsa da taga cike da hawaye ne yasa tace.
“Malam to kaima kenan yanzu in Fariyda ta iso ta samu kana ƙwalla ita kuma tayi yaya kenan?”.
Murya cike da kamala yace.
“Wlh ina jin tausayin Aminina mahaifinsu Mahmoud yana bani tausayi ya rasa ɗansa, gashi Mahmoud kuma bashi da damar cike musu gurbin Aminullah.
Wlh da ace Mahmoud zai iya aure da tabbas zan aura masa Raihana taje ta riƙe ƴaƴan yar uwarta, dan nasan Mahmoud bazai taɓa bar mana yaran nan ba, kuma suma iyayen nasa bazasu barin ba, dan yaran ne farin cikinsu”.
Kai ta jinjina cike da tausayawa tace.
“To ya zamuyi haka Allah ya tsara, ni kaina na tuna haka da ace Mahmoud zai yi aure da yaran Fariyda bazasuyi maraiciba Raihana zamu bashi ya aura su riƙe ya'yan tayunsu.”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.