Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 37 of 86

Aunty Amarya kuwa da Goggo Abu da Goggo Dada Da Mamy da kanta ne a tare suka ƙaraso cikin parlour tare da zama kan tattausan carpert dake shimfiɗe a tsakiyar parlour.
Wani irin sassayan numfashi mai cike da salama da mamaki Aunty Amarya ta saƙe tare da ƙara ware idanunta tana yiwa parlour Mahmoud ɗin wani irin kallon mmki komai dake ciki.
Fari ne ƙal irin mai ɗaukar hankalin nan, sai ɗan ratsin milk collor kaɗan-kaɗan parlour babbane na gasken-gaske irin parlour Nan na alfarma ne da ƙasaita a hankali ta ƙara gyara zama kan carpert ɗin da laushinsa ya zarta zatonta ido ta lumshe tare da shaƙar wani irin ni'imtaccen ƙamshin parlour da sanyin Ac dake busasu tare da cire musu duk wani damuwar zuciya tuni shauƙi mai zaman kansa ya rufe mata zuciya da jiki,
Tsala-tsalan labulayen dake parlour ta tsurawa ido tare da mmkin kyansu da tsuruwarsu, a hankali ta ƙyara zamantan tare da jingunuwa da ɗaya daga jikin hamshaƙan kujeru na alfarma dake bayanta.
“Yah Salam lallai yaron nan Mahmoud duniya ne!!! a tsabta da gayu, komai na cikin parlour special ne, numfashi ta kuma shaƙa tare da lumshe ido dan bata taɓa jin wani ƙamshi a duniya kamar wannan ba.
Tamfatsetsen TV dake kan wani tv stand ɗinsa da yake iri ɗaya da table ɗin dake tsakiyan parlour ta ƙarewa kallo, sai kuma ta maida dubanta kan dinnin area dake ɗauke da dinnin table mai kujeru shida sai fridge dake gefen dama gefen hagu kuma show glass ne, a tsakiyarsu kuma washing hand baby ne, ido ta ƙara tsurawa cikin dinnin area dan ta tsakankanin igiyoyin zirin labulen wurin take ganin komai.
Da sauri ta gyara zamanta saboda jin gyaran muryan da Bana Malam É—in yayi ne yasa ta dawo hayyacinta tare da maida kallonta kansu.

Durƙushe take gaban Malam da sauran Uncles ɗinta da Abba da kuma Bappa Lawan dasu Goggo Abu da Goggo Dada.

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276, mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 14
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Sai Goggo Abu dake gefe riƙe da Zaid sai Aunty Amarya kuma dake riƙe da Zaitoon.
Wacce kallon da takeyi ne bai bari taji gaisuwar da Mahmoud yayi musu a daƙileba.
“Fariyada”.
Malam ya kirata cikin muryar dake nuna ainihin tausayinta a ranshi.
“Fariyda”. ya kuma kiranta murya na rawa ido cike da ƙwalla cikin rauni tace.
“Na'am Baba”.
Cikin sanyi yace.
“Kiyi haƙuri ki yafe min tauye haƙƙinki da nayi ki yafe min”.
Da sauri ta fara jujjuya kanta tare da É—ago idanunta da wahayen ciki ke kwaranyowa wasu na korar wasu murya na rata tace.
“Baba kayi haƙuri na tuba ka yafe min wlh bana son”.
Sai kuma tayi shiru jin Mamynta na faÉ—in.
“Eh ai ya kamata shima ki nuna masa yanzu kin girma bai isa da keba”.
Kai Uncle Sani ya jinjina tare da cewa.
“Au dama abinda yasa kikace zakizo kenan Maman Nasir, to yi haƙuri bayani za'ayi musu yadda zasu fahimcemu ba faɗaba”.
Kwaffa tayi tare da yin ƙasa da kanta.
Shi kuwa Malam cikin natsuwa ya kallesu ita da Mahmoud din kana a hankali ya sa hannunsa ya kamo hannunta kusa dashi ya ƙara jawota cikin sanyi yace.
“Kiyi haƙuri na tauyeki ki yafe min a bisa hanaki damar zaɓawa kanki minji da kikeso da kanki kamar yadda shariya ta baki dama.”
Murya na rawa tace.
“Baba ni na yafe, ba kayi min komai ba, kawaidai Baba Malam bana sonshi, Uncle Muhd kuyi haƙuri ku gayawa baba ya aura min duk wanda yakeso a duniyar nan ni na yarda ko mahaukaci nema inaso yafi min akan shi, kuma ma ga Yah Mujahid ni shi yafi m”.
Shiru tayi tare da kife kanta bisa cinyar Mahaifin nata jin ya manna kanta da cinyarsa.
“Kiyi haƙuri Fariyda na, na sanki ke mai biyayyace, ki kuma sani duk abinda nayisa nayi da shawarar mahaifiyarki da ƙannena kafin in yarjewa Alhaji Umar in bada aurenki ga ɗansa Mahmoud dan aiwatar da wasiyyar ɗansa Aminullah da ya bar masa yana gargarar mutuwa.
Shi ya roƙi mahaifinsa da mu haɗa aurenki da Mahmoud. Ni kuma da ƴan uwana mun amince ne dan goben yaranki, ki sani ko wacce uwa akan ƴaƴanta take jurar ko wanni irin abu, aurenki da Mahmoud shi zai yiwa yaranki katanga da yin agolanci shi zai samawa yaranki nitsuwa da gurbin uba a kusa dasu, sannan da auren Mahmoud ne kawai zaki rayu da yaranki da bakya son rabuwa dasu inuwa ɗaya, dan shi Mahmoud a tsarinsa dama yau Goggonsu Dada zata dawo musu dasu Zaid.”
A hankali tace.
“Malam ni na haƙura a bashi yaran a raba auren na da shi Abba ƙanin Yah Aminnefa”.
Sai kuma tayi shiru jin Uncle Sani yace.
“Haba dai ɗiyata ni ban san ki da gardama da tirjiyaba, kiyiwa Allah da Manzonsa kada ki kuma sake fadin haka”.
Da sauri suka kalli Mamy dake cewa.
“Wallahi Fariyda In dai kika bari zuciyarki ta kaiki ga nemi saki a wurin mijinki to wlh Allah ya isa.”
Da sauri Abba ya fara jujjuya kai kana a hankali yace.
“Maman Nasir jeki kawai mun sallame ki, je wurin aminiyarki Ummi”.
Ya ƙare maganar da alamun raha wa matar abokin nasa kuma aminiyar matarsa.
Kai ta jinjina tare da miƙewa kawai ta fita.
Shi kuwa Mahmoud tunda yayi ƙasa da kanshi bai kuma ɗagowa ya kalli kowaba wani irin tafasa da harzuƙar da yakeji zuciyarsa nayi har ta kaishi da fara ganin iyayen nasa a matsayin waɗanda basu san abinda sukeyi bane yasashi nanata Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun ko zai samu ya iya sarrafa kanshi kar yayi saɓon yiwa iyayensan kalma mara daɗi, tsananin ɓacin ran da bai samu ya huce bane yasa jikinsa tsuma.
Yayinda itama Fariyda jikinta rawa yake yi dan kukan da takeyi da azabebben sanyin AC daya bunkuÉ—a, dan ta fara sabawa da salon Aminullah da baya son sanyi sosai.

Da ido Baba Malam ya raka Mamy tare da jinjina kai dan yasan manufar Mamy nayin haka su in sun tausasa Fariyda ita sai ta zafafawa Fariyda, duk da itama har kuka tayi da yayi mata magnar auren Mahmoud da Fariyda sai dai ganin ransa ya ɓacine da kuma faɗa mata da akayi wasiyyar Aminullah ne yasa tayi shiru tare da bada goyon baya da kuma fatan alkhairi. Amman ita kanta ba son auren takeyi ba.
Sosai kuwa Zafafawar Mamy yasa Fariyda yin shiru bata kuma ko tariba sai sheshheƙan da yaƙi barinta.
“Allah yayi miki al'barka Fariyda kin yafe minko?”.
Kai ta gyaɗa tare da zubda sabbin ƙwalla
“Allah yayi miki al'barka ya raya miki yaranki Fariyda in sha Allah zakiyi farinciki mara adadi a wannan biyayyar da kikayi min akan zaɓi da hukuncin dana yanke a kanki.”
Da Amin suka amsa baki É—ayansu.
Kana Uncles É—inta sukayi mata nasiha mai ratsa jiki da nuna mata mahimmanci auren akan goben yaranta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.