Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 67 of 86
Gaban Fariyda ta tsaya cikin sanyi ta kalli Fariyda sai kuma ta matso kusa da ita kib da kib a hankali tace.
“Kinyi sa'ar samun mijin da nake burin samu a rayuwataâ€.
Wani irin matsiyacin kallo Fariyda tayi mata ba tare da tace mata komai ba, numfashi mai nauyi ta fesar tana lumshe idonta ta shaƙi ni'imtaccen ƙamshin jikin Fariyda sai kuma ta buɗe idanta tare da kamo hannun Fariyda cikin hausarta ta yar bawa tace.
"Irinshi basu da yawa a cikin mazan wannan duniyar da muke, ko a duniyar mafarkima ban taÉ“a samun namijinin duniya kamar Papi ba, ki godewa Allah da ni'imar da yayi miki na mallakarsa ta hanyar aure har kuka haifi yara, nasan kin san abinda nake nufi tunda kina rayuwa dashi a gado É—aya, yana manna kanki a faffaÉ—an Æ™afaÉ—arsa mai ni'imar Æ™amshi da yelwa, duk da na daÉ—e ban ganshiba ban mance da Æ™arfin jarumtarsa ba, shi na fara sani É—a namiji a duniya shima ni ya fara sani, rashinsa lfyarsa yasa na rasa shi, sanadin rasa shi yasani bin maza iri daban daban a duniya wlh har yau ban ji namiji kamar Papi baâ€.
Wani irin kallon ƙyama da takaicin bayyana laifin da alfahari da yin alfasha da Idaya keyi yasa Fariyda take kallonta a wulaƙance. Ita kuwa Idaya idonta dake cike da hawaye ta rumtse tare da buɗesu murya a karye taci gaba da cewa.
“Shima ni ya fara sanin Æ´a mace a duniya sai Æ™awata Sara. Wata Æ™il shi dagani da ita bai kuma sanin wata É—iya maceba sai ke tunda muna tsaka da cin ribar lafiyar Æ™uruciyarmu boko haram sukayi sanadin watsa mana alaÆ™a, badan wannan ba Wlh da duk yadda zanyi sai nayi Papi ya aureni.â€
Ƙara kama hannun Fariyda data tsura mata ido tayi tare da matsota cikin sanyi tace.
"Duk da nayi aure, kuma na zaÉ“i É—aya daga cikin mazan da nake ga zasu cike min gurÉ“in Papin wlh har yau ban kuma jin daÉ—in wani namijiba a duniya kamar Papi ba, shi na mijine mai zarra da riÆ™o É—aya zai sa duk wata ya mace samun nitsuwa na wata guda shi na mijine da iya kalaman bakinsa ma zai É—auke miki duk wani bege da iya kiss É—aya Mahmoud zai sa kiji duk duniya babu kamarsa da runguma É—aya zakiji bazaki Æ™ara kallon wani na miji ba a duniya sai shi koda yake ai duk abinda zan faÉ—a miki a yanzu kin fini sani a kansaâ€.
Tsaki Fariyda taja tare da cewa.
“Sake min hannu, kije ki fara tsarkake tsakinki da Allah ki daina tutiya da zina da mararin abokin aikata alfashan naki duk da kina da aure ni ba matarsa baceâ€.
Tana kai wa nan ta raɓa gefenta ta wuce.
Mahmoud kuwa kiran da Sa'ad keyi masa ba sahirtawa ya amsa. Mgnar suka É—anyi kana ya katse kiran tare da zura wayar a aljihunsa lokacin da ya shiga cikin jirgin.
Ticket É—inta ta É—an duba lokacin da ta shiga cikin jirgin.
Da sauri ta kauda kanta daga kanshi kan kujerar su Zaitoon ta zauna ya zamana su suna kan nata tsakanin shi da ita kenan.
Juyo kanta tayi ta kalleshi.
Ta gefen ido yake kallon yadda ta
Taɓe baki tare da suke fuska cikin jin ƙyama tayi masa wani irin kallon kyamar aikinsa da karuwarsa ta gama faɗa mata, da ƙarfi ta.........
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Book 2, page 31
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Tunda ta shigo ta zauna, ta watsa mishi kallon da ya yake ta son fahimtar me ya ƙunsa bata kuma sake kallon komai ba dan idonda ta lumshe, bata kuma buɗe idon ta ba har jirginsu ya ɗaga yayi ta keta hazo Form Mumbai 2 Ahmedabad.
A hankali ta buÉ—e idon ta jin ana faÉ—in.
“ladies and gentlemen welcome to Ahmedabad the Manchester City of India the world Heritage city.â€
Gyara zamanta tayi tana ɗan sauƙe numfashi mai cike da jin kyama mai tada zuciya da tsananin zafin tsanarsa daya yake ta ƙara ninkuwa da hauhawa a zuciyarta.
Bayan jinrgin ya dai-daita sauƙansa ne tasa hannunta ɗauki hand lounge ɗin ta juyawa ta fita. Travelling box ɗinsa ya ɗauka ya ɗaura Zaid a kai ya ɗauki Zaitoon a kafaɗa. A Arrival ta ɗauki babban akwatin nata da taimakon ma aikatan wurin.
Ƙarfe takwas dai-dai suka bar cikin Sardar Vallabhbhai Patel international airport Ahmedabad. Numfashi mai sarƙafe da tarin gajiya da bacci ta fesar, dan yunwa kam babu shi abincin da taci a cikin flight ɗin ita da yaran duk ya wadatar musu a dinner.
Ido ta zubawa birnin Ahmedabad É—in tana mamakin tsari da girma da kyan garin, ko shi yafi Abuja ta ko wacce siga da sashi, to ta yaya ma ake cewa India kamar Nigeria ce? ai sam babu ko haÉ—ima. A hankali ta É—an kuma juya gefen damanta tana kallon tsarin gine-ginen da manyan benaye na alfarma ga ci gaba hanya tako wani sashi iya bakin titunan su abin kallone.
Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kafin suka haura kan Ashram Road tafiyar 13 minute sukayi suka isa kan wani tamfatsetsen hotel mai masifar kyaun fasali da zubi ciki suka shiga, sunayin parking Mahmoud ɗin ya fita, kai tsaye Reception ya wuce, jim kaɗan ya dawo fuskarnan a matuƙar tsuke. Da hannu yayiwa driver da shima jikin motarsa yake da tambarin hotol ɗin da shima hotel ɗin yake da tambarin Om family care hospital wanda ke nuni da hotel ɗin da taxi ɗin duk na mamallakin Asbitin Om family care hospital ɗin da suka kawo Zaid ne.
Numfashi mai nauyi ya fesar ya zauna bisa kujerar parlour wanda yake tamkar na wani fada ne, da yatsa ya nuna driver hanyar fita, dan da kudin driver da na hotel din da na duk abincin da zasuci da wankin kayansu da zirga-zirga duk inda zasuje da jinyar Zaid duk sai an gama in zasu tafine zasu buga mishi kuÉ—in.
Driver na fita ya miƙe yajawo akwatinsa yan abubuwan buƙatarsa ya ɗauka ya nufi bedroom ɗin. Ita kuwa Fariyda tunda suka shiga bata zauna ba, bata kuma ce ko ƙala ba, bayan kwantar da su Zaitoon da tayi kan 2 seatter.
A haka ya sameta a tsaye kamar an dasata.
Ko inda take bai kuma kallaba, ƙamshin turarensa ne ya tabbatar mata ya dawo, haka yasa ta juyawa ta kalli ta inda yake ganin ya sunkuya ya ɗauki Zaid ya juya ya nufi bedroom dashi, wani irin kallon mai cike da tsana ƙyama ta kuma danna mishi tare da jan wani irin dogon tsaki wanda yasa ya ɗan kalleta ta gefen ido, lokacin da ya sunkuyo ɗaukar Zaitoon.
Kaita bedroom yayi ya kwantar kana ya dawo parlour. Ranshi cike da takaicin tsarin asbitin da suka sa hotel É—in suka bashi room and Parlour madadin su bashi daki É—aÉ—É—aya, numfashi ya fesar cike da kudurin canza É—aki zuwa gobe dan, gajiyar da yake ciki da ciwon kan da ya diro masane ya sa bai tsaya wannan hidimar ba.
A hankali ta juya ta nufi bedroom bayan ta kuma jan dogon tsakin da yafi na ɗazu, ganin yadda su Zaid ɗin suke sauƙe numfashi a hankali alamun suna jin daɗin baccin ne da tunawa ta musu wanka cikin flight da taje canza musu pampers yasa ta sauke numfashi jin sanyin ba sai ta ƙara musu wankaba.
A hankali ta shiga bathroom ɗin ya Salam shi ta furta haɗe da sauƙe numfashi ta kuma shaƙar numfashi da sauri sabida ni'imtaccen ƙamshin sabulansa da kuma na turaren wankansa.
Sai kuma ta tsuke fuska gani da É—an jan tsakin da har ranta take jansa.
Wanka tayi da alwala.
ta fito, hand lounge É—inta data shigo dashi ta fidda wasu tattausan rigan bacci riga da wando masu taushi ta zura, tare da naÉ—e gashinta ta cusa cikin hular kanta.
Kai ta É—an jujjuya hand bag É—inta data bari a Parlour take nema.
Shi kuwa Mahmoud zaune yake bisa 3 seatter ya maida bayansa ya jingina da jikin kujerar, kanshi kuwa ya maidashi baya kan saman kujerar, idanunsa ya lumshe cike da tafasar zuciya, sai TV daya kuna wanda ake boxing sai tiÆ™ar juna Æ™attin keyi ba Æ™auÆ™autawa, lips É—insa duka biyu ya matse da Æ™arfi. A fusace ya buÉ—e idonsa, jin yadda sautin jan tsakinta ya ratsa masa kunne, da sauri ya miÆ™e tsaye gabanta ya tsaya yana watsa mata kallon mai cike da tafasar zuciya a fusace yace. "Uban wa kike jawa tsaki?â€. Tana mai jefa masa kallon da zuwa yanzu ya fara fahimtar kamar na Æ™yamane cikin rashin tsoro tace.
"Duk wanda ya tsargu dashi nakey."
Sai kuma tayi shiru bata ƙarasa ba, ganin irin kallon da ya watsa mata da idanunsa da launinsu yasata jin ɗar ƙirjinsa da yakeyin dama da ƙasa ta kalla sai ta kuma jan tsaki tare da juyawa da sauri ta nufi bedroom ɗin.
Ganin yadda lips ɗinsa keyi alamun zafin zuciyar ya sa mgnar da yake son yi ƙagewa a maƙoshinsa.
Da sauri ta ƙarasa shiga cikin ɗakin, bakin gado ta zauna tana mai jin kyamarsa fa har ranta, mazinaci, ashema ƙazamin gaskene shi yake wannan tsurfa da dokar sabta da zaɓen abinci wanda zai ci, mitsssss ta kuma jan tsaki tare da ɗaga hannunta tayi addu'a ta shafawa yaran sannan tayiwa kanta. Ido ta ɗan jujjuyawa tana kallon tsarin ɗakin da ni'imar ƙamshi da sanyi mai ratsa jikin da yasata kwanciya ba tare da kashe hasken ɗakin da yake mai blue ba.
Da asuba a hankali ta shiga bathroom.
Baki ta taɓe ganin alamun ba'a dade da yin wanka da al'wala aka fitaba, a fili tace.
“Ko kifi zaka dawo ai bazai wanke dauɗar najasar zina da kake aikatawa ba, dan haka wankan na banza ne sai dai ya tsaya a iya ƙyalli da sheƙin fata da isar mutane da fitinennen ƙamshin jarabar nacin shiga hancin mutane.
Da haka tayi wanka da alwala ta fito.
Dogon riga ta zura tare da sa É—an hijab É—in sa ta kabbarta sallah.
Bata tashi kan sallayar ba, sai ƙarfe bakwai dai-dai, ƙimtsawa tayi cikin wasu tattausan riga da siket mai hawa-hawa rigar tayi cib da ɗan kekkyawan jikinta, hula tasa bayan ta taje kanta kitse jelar gashinta sai ta naɗe ta sashi ciki.
Turarukanta ta fesa t meda komai ta ajiye.
Tana kallon Zaitoon data tashi zaune.
Murmushi tayi ganin tana mata dariya, ɗaga tayi tana ɗan jan ƙafar Zaid dake bacci.
Da sauri shima ya miƙe zaune.
Wanka tayi musu kana ta shiryasu, hmmmmm taja numfashi sabida jin yadda ƙamshin jikinsu da nata suka haɗe suka bada sassayan ƙamshi.
Sai kuma ta kalli Zaitoon da take ɗan gyarawa ribbons ɗin kanta da suka ɗan sussuɓale, bobo ta miƙa mata, bayan ta bawa Zaid ɗin ma.
Aiko a take suka zuƙeshi.
Kan gado ta medasu tare da tattare wurin, gefen da taga labule a zagaye ta leƙa, da sauri ta ƙarasa yaye labulen ta shiga ɗan wurin gadon yarane ɗan madaidaicin, wanda yasha gyara an zagayeshi da kayan wasan yara masu kyau da ɗaukar hankali, da sauri ta jawo Zaitoon ta ɗagota, kan gadon ta ɗaurata, dariyar da tayi ne da ɗan leƙo Zaid tana masa alamun yazone yasa tayi saurin ɗaurasa kan gadon cikin farin ciki suka fara wasa da abubuwan wasan nasu.
Shiru ta É—anyi sai kuma ta É—aura hannunta kan cikinta.
Ƙofar parlour ta kalla jin shiru ba alamun kowa a cikine yasa ta fitowa parlour sit ba sautin komai sai na Ac da yake busa sanyin da yasa taji a take jikinta ya amsa, numfashi ta ja ta lumshe idonta sai kuma ta buɗesu tana karewa parlour kallo, wanda ɗan blue hasken da yake kunne ya ɗan bata damar kallon.
Komai na cikin parlour farine ƙal sai dai yanayin hasken wutan yasa zakaga kamar farine da blue, kujerune manya na alfarma masu faɗi da taushin gaske wanda ko kwana zakayi a kai ba takura, sai tattausan carpert dake malale a tsakiyar parlour daga samansa Centre table ne mai ɗan drawer a ƙasa, sai TV dake kan tv stand, daga can dama dinnin table ne da fridge a gefen.
Wasu irin tsala-tsalan labulayen masu kyan gaske blue sai zanen fari-fari.
A hankali ta fara taka sawunta dan shirun yayi yawan da ya fara bata tsoro, ga yanayin É—akin da yafi kama da dare duk da yanzu takwas ta gota,
Wurin da akwatinta yake ta nufa da sauri ta tsaya dai-dai jikin hannun 3 seatter ta ɗan sunkuyo tana mai ƙara ware idanta dan ganin kamar mutum ke kwance kan kujerar, da sauri ta kuma sunkuyowa dan hasken bai gama barinta ganin ras ba, dai-dai kan fuskarsa ta sunkuyo da tata fuskar gab da gab, da sauri ta tashi tsaye lokacin da taga ya buɗe manyan idanunsa ya zuba mata su cikin nata idon.
Gyara tsayuwarta tayi ganin ya tashi tsaye da yatsa ya nunata, cikin muryar bacci bacci da kuma ɓacin rai yace.
“Wai dan Allah bazaki daina yinin wannan jarabebben kallon tsoffin mayun bane?â€.
Cikin takaicin kiranta mayya da yake tayi ta kafeshi da ido.
Cikin tsaida idonsa cikin nata da yake son ganin iya tsaurin idon nata yace.
“Dolen dole dai sai kin cinyeni kamar yadda kika cinye min É—an uwana hankalinki zai kwantaâ€.
Idonta ta fara jujjuyawa cikin nasa idon, sai kuma tayi saurin yin ƙasa da kanta tare da cewa.
"Koda ace ni mayyace wlh kai dai ko yunwa zata kasheni bazan cika ba, dan ni ba Æ™azama bace bana kuma cin abu mai Æ™azanta bare inci Æ™azantar da tafi komai bani Æ™yama, dan gwara inci mushe da incika kai da jiki duk najasa me abin sha'awa tare da kaiâ€. Tunda ta fara magna ya tsareta da ido wanda hakan yasa tayi Æ™asa da nata, tana magnar kuma jikinta na tsuma dan karfin haline kawai ya sata tsayuwa gabanshi tana jero kalaman da takeji suna fitowa daga can Æ™asan Æ™ahon zuciyarta.
Da sauri ya fizgo hannunta ya dawo da ita gabanshi ganin ta juya zata tafi, A tsoroce ta kalleshi.
Cikin wata iriyar murya da bata taɓa jin makancinsa ba yace.
“Nine najasar!? Nine Æ™azami?Maimaita injiâ€. Ƙasa ta kumayi da kanta, sai kuma tayi saurin ja da baya ta É—ago kanta ta kalleshi jin hautsinennen tsawa daya daka mata.
“Ke wai me idayatu ta gaya miki ne?â€.
Moi-moi tayi da baki ba tare da yaji me tace ba.
Da sauri ta ƙara ja da baya, sai kuma tayi saurin kallon bayanta jin ta isa jikin kujerar dake bayanta.
“Zaki gaya min me Idaya ta gaya miki a Airport ko sai na tsinka miki marin da zai nakasa miki ido, nace me tace miki akai na?â€. Murya a tsorace cikin dakewa tace.
“Fasiƙancin da k...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.