Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 83 of 86

Wuraren ƙarfe tara da rabi na dare ya fito bathroom, idonsa a runtse yake tafiya saboda tsananin ciwon kan da rashin bacci ya jaza mishi, a hankali ya buɗe idonsa yana ɗan kallon gefen gadon, durƙushe take a tsakiyar gadon hannunta duka biyu na kan mararta. Da sauri ya kuma rufe idansa da sarawar da kansa keyi. Parlour ya wuce.
Kimtsawa yayi cikin pajamas farare ƙal, turaren baccinsa mai Ni'imtaccen ƙamshin ya fasa a duk wani sashin jikinsa.
Gaban 3 seatter da su Zaid ke kwance a kai ya sunkuya ya É—ago Zaitoon bedroom É—in ya nufa.
Yana shiga yayi saurin rufe idonsa dan har yanzu bata kashe wutan É—akinba, a hankali ya kwantar da Zaitoon É—in kana ya juyo ya É—auko Zaid, yana fita daga É—akin murya cike da bacci da ciwon kai da gajiya yace.
“Ke ki kula dasu dan yau zanyi bacci, ko sun farka karki tasheni ki bar baccin jarabar nan ki kularmin da yara”. Jin shiru bata ce ko ƙala bane yasa ya ɗan kalli gefen gadon.
Durƙushe take har yanzu a yadda ya barta ɗazu har lau hannunta na bisa mararta, sai kai take jujjuyawa cikin yanayi mai tafe da azabar ciwon da mararta keyi.
Baki ya taɓe tare da juyawa ya fice.
A hankali ya sauƙe gajiyeyyen numfashi mai tafe da nannauyan bacci da zafin ciwon kai, lokacin da ya zauna bisa 3 seatter ɗin,
ni'imtaccen numfashi mai haɗe da salama yake sauƙewa wanda ya haɗe da sanyin AC da sanyin dare da ni'imtaccen ƙamshin jikinsa dana parlour ya bada sukunin jin baccin ya kashe dukkan kuzarin jikinsa, tafin hannunsa ya ɗaga a hankali ya yi Azkarul Naum, ya shafa dukkan jikinsa, kwanciya yayi bisa gefen dama tare da fara karanta suratul mulk a hankali yake motsa lips ɗinshi.
Cikin baccin da ya fizgeshi ba tare da ya kai karshen surar ba, ya buÉ—e lumsassun idanunsa da suka sauya launi, saboda jin sautin kuka daga cikin bedroom É—in, idon ya maida ya lumshe ya jawo duvet É—in ya rufe har kansa.
Tsaki mai sanyi yaja ya juyawa gafen hagu, ya zaro ɗan pillow ya ɗaurasa kan kunnunwansa wai ko zai samu ya hanasa jiyo sautin sheshheƙanta. Amman ina sabida sautin ƙara ƙarfi yakeyi. Cikin tattaro dukkan ragowar ƙarfin jikinsa ya yunƙura ya tashi zaune, yana dafa jikin hannun kujerar ya samu ya miƙe tsaye saboda mutawar da jikinsa yayi, ido a lumshewa ya nufi bedroom ɗin.
A hankali ya ƙara matsowa gaban gado, yana ƙara ware manyan idanunsa da suke buge da mayen baccin da bai samu yayi na kwanaki huɗu ba cikin narkekkiyar muryar yace.
“Ke lfy meke damu ki?”. Yayi magnar da ɗan sunkuyowa saboda ganin yadda jikinta yake wani irin tsuma ga zufa da take tsatstsafo mata tako wanne sashin jikinta, har lau a durƙushe take damƙe da mararta da hannu duka biyu sai kai take jujjuyawa tana sassayan sheshheƙan kuka mai cike da rauni, juyawa yayi ya zari remote ɗin Ac, gudun AC ya ƙara har zuwa 18. sai kuma ya dawo bakin gadon ya zuba mata ido cikin mmki ya kuma cewa.
“Ke meke damunki?”. Murya da jiki na rawa tace.
“Marata wayyo Allah marata zata daddage”. A hankali ya sunkuyo kanta sosai dan son jin abinda take faɗa.
“Wayyo Allah Mamy na Marata zata daddage”.
Ido ya zuba mata cikin yaƙi da baccin da yake son yardashi a wurin yace.
“Mara kuma?”. Kai ta gyaɗa mishi tana yarfa hannunta ɗaya, ɗaya kuma na damƙe da marar lips da murya na rawa tace.
“Marata! marata!! Marata!! Zan mutu”. Ganin yadda gaba ɗaya jikinta ke rawa da sheshheƙan da takene ya sashi fara jero mota tambaya.
"Dama yana miki ciwone”.
Da sauri ta jujjuya mishi kai alamar a'a.
“Kuma ba period bane!”. Ya faɗa a ransa saboda tunawa da lokacin da tace masa tana son pad, a ƙalla ma bata wuce kwana shida da fara salla ba.
Numfashi mai nauyi ya sauƙe gami da taɓe baki ido cike da bacci ya juya ya fita parlour, wayarsa ya ɗauka tare da ɗan yin rubutu kaɗan, kana ya zauna kan 1 seatter yasa hannunsa duka biyu ya damƙe kansa dake masa barazanar rabewa biyu.
A hankali ya miƙe tsaye saboda jin sheshheƙan ta ya ƙara ta'azzara ɗakin ya nufa yana mai jan tsaki, sai kuma ya dawo baya jin ana Knocking ne yasa ya buɗe ƙofar tare da amsa ɗan flacks ɗin lemon tea da ma'aikatan hotel ɗin na gefen kitchen ya miƙo masa, bisa kan Tray ɗauke da ɗan mug wanda shi ma tea ne a ciki mai wani irin kalla.
Amsa yayi ya maida ƙofar ya rufe.
Da sauri ya isa bakin gadon, saboda ganin yadda take ƙarƙarwa duk zufar jikinta kam ta bushe sabida ƙarfin Ac daya ƙaramata, sai azabar ciwon marar da yasa idanunta kafewa. ya zauna bakin gadon yana buɗe mug ɗin, kamota yayi da hannunsa ɗaya ya ɗago kanta, daga sunkuyen da take, da sauri ya haura kan gadon duka sabuda yadda ta saki wani irin gakabaitaccen sheshheƙan da kukansa ya sarƙafe a ƙirjinta.
Mug ɗin ya miƙa mata tare da cewa.
"Sha wannan zai bari”. Jujjuya kai ta farayi tare da komawa zata kife ƙirjinta kan guiwowinta.
Da hannu ɗaya ya ficikota, haka yasa ta dawo baya ta mannu da kan gado. Mug ɗin ya manna mata a baki cikin zaro manyan idanunsa tare da tsuƙe fuska yace.
"Ke buɗe baki kisha, haka kawai zaki hanani bacci, so kike in faɗine in ban samu nayi bacci”.
A hankali ta buɗe bakin nata saboda ganin yadda ya ƙara matsowa tare da sa hannunsa ɗaya ya matse hancinta, da sauri ta fara shan tea ɗin da taji yana dan ceto numfashinta daya toshe mata hanci. Ƙara danna mug ɗin yayi sabuda ganin tana son zame bakinta, Yadda ya danne ɗin ne da riƙe hancita yasa dole kab ta shanye.
Harara ya watsa mata da idanunsa dake lumshewa su kaɗai, mug ɗin ya ajiye bisa Tray da ya ajiye kan bed side drawer dake gefensa, ya yunƙura da niyar tashi, sai kuma ya koma ya zauna ganin yadda jikinta ya fara wani irin gigitaccen karkarwa, idanunta na tafiya sama.
“Ke me haka? Farriyyha! Farriyyha!!”. Shiru ba mgna sai ƙara naɗewa wuri ɗaya ta farayi.
Da sauri ya kamo hannunta, haka yasa ta faɗo jikinsa, kar-kar haka jikinta ke ƙarƙarwa tamkar wacce ke cikin dutsar ƙanƙara, kanshi ya sunkuyar yana leƙa fuskantar dan jin sautin yadda haƙoranta ke dukan juna, kat-kat sai kuma lips ɗinta na sama ta matse da haƙorinta tana tsotsa na ƙasa kuma ta ɗan turoshi duk ya tattare dan sanyi, da sauri ya gyara zamansa bisa gadon saboda jin saura ƙiris ta ture shi ya faɗi ƙasa. Zaman daya gyara ne ya bata damar naɗewa cikin jikinsa, tare da ƙara cuccusa kanta tsakanin kafaɗarsa da wuyansa, hannunta kuwa cikin rigarsa ta cusasu tare da zagaye bayansa tana mai ci gaba da neman ɗumin jikinsa saboda azabebben sanyin da ya hautsine zafin marar tata yasata ficewa hayyacinta. Cusa hannunta cikin rigarsa shi ya bawa zip ɗin rigar daman buɗewa baki ɗaya. Da ƙarfi ya fara ƙoƙarin buɗe gajiyayyun idanunsa da bacci yayi musu mamaya, sai kuma ya medasu ya rumtse saboda sarawar da kansa ya fara da ƙarfi.
Cikin rawan jikinsa da ya fara saboda yadda nata jikin ke rawa yasa hannunsa ya fara tureta cikin tsoron fatar jikinta dake taɓa tasa fatar dan yasan illar da yake samu na ƙaiƙayi da feso ƙanana ƙuraje in fatar wani ya taɓashi da irin azabar da yake sha na ƙaiƙayi da zazzafan zazzaɓi dake rufeshi.
A hankali ya sauƙe hannunsa saboda nauyin bacci da yadda ta ƙara kanainaye wa a jikinsa cikin fitar hayyacin take ƙara ƙanƙameshi.
Cikin gigin bacci da rashin sanin abin yi ya jawo gefe da gefen rigar ya haɗa kan bayanta yaja zip ɗin rigar da ƙarfi har zuwa saman wuyansa ya zama dashi da ita duk suna cikin rigar, numfashi mai ƙarfi ta sauƙe cikin gigicewar yanayi, da ya rufeta ruf da rigarsa ya zama duk suna cikin riga daya, kanta da ya zame zuwa kan ƙirjinsa ma duk yana rufe ruf.
Rawar da jikimta keyi da yadda take ƙwaƙumeshi ne yasashi zame sawunsa tare da jingina bayansa jikin gadon, ya mana kansa da jikin kan gadon tare da jawo duvet ɗin ya rufesu har zuwa kan ƙirjinsa idonsa ya sassauta rumtsewar zuwa lumshe lokacin da yaji ta kuma yi masa wata iriyar rungumar daya sashi......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.