Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 36 of 86
Ita kuwa Fariyda jin furuncin da mahaifiyarta tayi mata ne yasa, ta kuma rushewa da wani maraitaccen kuka ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Kanta Goggo Dada ta rinƙa shafawa tare da ƙara jawota jikinta.
Amina kuwa hannunta ta riƙo murya na rawa tace.
“Kiyi haƙuri Fariyda kiyiwa iyayenmu biyayya in sha Allah bazaki taɓe ba, duk da na hanga na duba na kasa gano manufarsu na haɗa aurenki da Mahmoud amman nasan dole suna da hujja da dalili mai ƙarfi wanda suka hango, mu kuma ko zamu hau tsani ne bazamu hango abinda suka hango ba, amman nasan tabbas su Abba da Baba Malam sunyi SAƘAR MAKAFI da bazasu fahimci bakin zarensa ba.
Goggo Dada tace.
“In sha Allah babu komai face alkhairi da kwanciyar hankali”.
Saddiqa ta kalli Salma da ta rungumeta ta baya tana wani irin kukan da yasa duk suka zuba mata ido. Sai Raihana, Zainba, Humaira, Fariyda da suka san irin masifeffen son da takeyiwa Mahmoud.
Sai kuma tayi sauri sake Saddiqa ta juya ta fita da sassarfa.
Goggo Abu kuwa wani irin numfashi mai tafe da samu da rashi da kuma tsoron tabbatuwar gaba tsakanin mijinta da ɗan uwanta tace.
“Hukuncin Allah ya wuce gaban wasa, ina nan ina shirin auren Mujahid da Fariyda sati biyu masu zuwa sai kuma gashi abinda Allah ya ƙaddara.
Allah Ubangijin talikai ya baku zaman lafiya yasa hakan shi yafi Zama alkhairi. Allah ya bawa Muhajid kuma haƙuri yasa ya dangana”.
Daga nan ta miƙe ta fita.
Aunty Jamila kuma kafaɗar Fariyda ta dafa tare da cewa.
“Ƴata kiyi haƙuri kukan ya isa haka, ka
Iyiwa iyayenku biyayya in sha Allah bazaki taɓeba, ki duba yaranki ki sani duk abinda akayi dominsu ne”.
Kai ta fara jujjuyawa sai kuma ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Aunty Amarya Aunty Jamila da Saddiqa suka bita a baya.
Zainab kuwa haka kawai ta tsinci kanta da tuntsurewa da dariyar da tasa suka juyo suna kallonta cikin dariyar da take harda riƙe ciki tace.
“Lallay kuwa akwai dirama a wannan haɗi na wuta da aududa za'asha bala'i ko yama zaman zai kaya su Ummi dai Allah ya tsaresu kada su cinnawa gidan wuta”.
Adda Nana ce ta kai mata bugu tare da cewa.
“Bace min daga nan”.
Salma kuwa Kai tsaye dakin Fariyda ta wuce inda ta san Mimy nacan.
Zaune ta samesu duk matan Uncles ɗinsu.
Kowa na mamakin yadda akayi shirin auren.
“Hmmm yoh sun samu gidan masu akwai na gasken gaske ba, dole su liƙewa ƙani ba tunda yaya ya rasu”.
Amarya Uncle Muhd ta faɗa cikin salonsu na hasadar ko wacce tafi son ace ita da ƴaƴanta ne stars a family ɗin.
Mimi ce tayi kwaffa tare da cewa.
“To ayi dai mu gani, yadda akayi abun a munafurcen nan kam da wuya a samu yadda ake so”.
Da sauri ta fara jujjuyawa Salma kai tare da tsuƙe fuska da bata son kowa ya fahimci wani abu.
“Lfy kike kuka Salma”.
Aunty Amarya ta tambaya, da sauri Mimi tace.
“Yoh tunda kikace Fariyda na kuka ai kuwa shike nan su duka uku hankali ya tashi”.
Cikin rawan murya tace.
“Mimi Fariyda fa bata sonshi bata shiri dashi, ko magana baya matafa tunda suke a gidan”.
Mamy da yanzu ta shigone tace.
“Ya isa haka Salma tashi ki tafi wurin yara yan uwa ki, nan ki bar manya suyi nasu salon fatan”.
Ta faɗa da alamun taji mai suke faɗi.
Daga nan ta juya ta fita.
Jin an kira sallan la'asar ne yasa kowa miƙewa dan yin sallan.
Tunda ya idar da sallan la'asar ya sake ɗaukan Kur'anisa yaci gaba da karatu da sauti.
Ji yake yi babu abinda zai yi a duniya ya sai-sai ta masa fusatarsa da zuciyarsa da yakeji tazo mishi har wuya, ya zaɓi yin karatun ne, dan ya iya sarrafa fushinsa da harshensa da hannunsa shiyasa ya rufe kansa a parlour sa tunda ya baro masallacin ƙofar gidansu Fariyda.
Ji yake ako wani lokacin zai iya fara kai hannu a kan duk wanda ya kuskura ya matso inda yake, ji yake yi zai iya zagin duk wanda yazo mishi da abinda su Abba suka aikata a kansa dan nuna isarsu a kansa.
Shi yasa ya baro can a take dan gudun kar ya shaƙe Salim da yazo yana ƙara tabbatar masa aurensa aka ɗaura shi da waccar abar.
Wayarsa da take Vibrate a karo na barkatai ne.
Yasa ya rufe Qur'anɗin ganin yazo ƙarshen Suratul Noor.
Fuskar wayar ya ɗan kalla da gefen ido. Salim ya gani, ido ya zuba wa fuskar wayar yanaji imana da Salim ɗin ne gabansa haka tabbas zai iya shaƙesa kiran Salim na katsewa na Sulaiman ya shigo, ya kasa janye idonsa a kai har kiran ya katse sai kuma ga na Yah Ahmad ma ya shigo.
Da sauri ya kife wayar lokacin da kiran wani abokinsa Usman da sukayi karatu dashi a Texas.
Cikin sauti ya fara karanta suratul Kahf kasan cewar yammacin jumma'a ne.
Ummi kuwa ita da Mama da Maman Samira tuni sun gama komai na aiki suna zaune a parlour.
Dawowar su Abba da Bappa Lawan ne yasa Mama da Ummi suka shiga bayan sun gaisane Abba yace.
“Ina ɗan naki ya dawo ne? Dan Salim yace yabar masallacin tun sanda akayi sanarwar ɗaurin auren, yana ta kiransa kuma baya dagawa.”
Nannauyan numfashi Ummi ta fesar tace.
“Ya dawo amman ko nan bai shigoba, ni kuwa ban je wurinsa ba, na bari ne kai da kanka ka sameshi da hukuncinka dan waƙa a bakin mai ita tafi daɗi”.
Ta ƙare maganar da nazarurruka da yawa a ranta, tabbas tasan shi Abba bai san komai akan zaman Mahmoud da Fariyda ba a matsayinta na matar yayansa duk da dai yasan wasu abu amman wasu abun suna ɓoyewa masa saboda Aminullah da yake hanasu faɗa dan kar ayiwa Mahmoud ɗin faɗa.”
Mama ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
“Ay abin dai kam da mamaki, musamman sani abinda ya faru da Mahmoud a baya”.
Fuska cike da annashuwa Bappa Lawan yace.
“Mudai fatanmu Allah ya basu zaman lafiyar da zai tabbatar mana da gskyr warakar kaddamar Mahmoud ɗin”.
A can gidan kuwa Saddiqa da kanta ta shiga ruɗani dan tasan waye Mahmoud a wurin Fariyda irin ƙannan mijin nanne masu masifar tsanar matar ɗan uwa.
Kiran sallan magrib ne yasa tace.
“Kinji magrib tayi kije kiyi alwala kizo kiyi salla, ki gayawa Allah dukkan bukatunki”.
A hankali ta mike ido a kumbure fuska tayi ja saboda kuka tana nufar ƙofar bathroom tace.
“Allah ya kashe sa kowa ma ya huta.”
Da sauri Aunty Amarya tace. “Haba Fariyda yan uwansa fa, na parlour suna salla kin dai san bazasuji daɗi ba”.
Tai magnar a hankali wai dan kada suji.
Bayan sallan isha, cikin kamala Abba yayi musu jagora har sama side ɗin Mahmoud.
Yana gaba shi da Bappa Lawan, saura duk na biye dasu a baya.
Knocking Abba yayi tare da ɗan yin jim na seconds, sai ya kuma ƙara yin Knocking ɗin a karo na uku ba tare da ya sahirta ba.
Ido ya zuba wa ƙofar yanajin tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa tayi waje, jin yadda ake knocking ɗin ba ɗaga ƙafane yasa ya miƙe a fusace, dan a zatonsa Salim ne, a hatsale ya buɗe ƙofar tare da sako kai da hannu da nufin hankaɗa Salim ɗin Sai kuma yayi ƙasa da kansa ganin zugan mutane bakin ƙofar ɗakin nasa.
Ciki ya ɗan koma tare da ƙara buɗa kofar.
“Afwan”. Ya faɗa akan lips ɗinshi da sunkayi jazir dan cizar fushi da yake musu.
Ciki Abba ya kutsa kai tare da cewa.
“Bismillah Mala Ibrahim ku iso Sani Muhd Abu duk ku iso”.
A hankali ya juya ya nufi cikin parlour nasa.
Qur'anɗin dake kan hannun kujerar 3 seatter da yake kai ne ya ɗauke tare da juyawa zai yi dinnin area.
“Dawo kazo ka zauna a nan”.
Abba ya faɗa tare da nuna masa gefen damansa.
Dai-dai lokacin Malam ya zauna gefen Abba tare da ajiye Fariyda a gabansu ta gefen hagunsu, ya zama suna jere ita da Mahmoud ɗin suna fuskantar iyayen nasu.
Uncle Sani da Bappa Lawan ne suka zauna bisa kujerar 2 seatter.
Uncle Muhd kuwa kan 1 seatter.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.