Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 58 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*SAƘAR MAKAFI*
Page 25
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Tsamin albasan da warin cabeji da na ƙwai ne suka haɗe wuri ɗaya suka bada wani kalan dummm a hancinsa tare da fara haura masa kai.
Da sauri Raihana ta fara ɗan tattare plate ɗin tana ɗaurawa kan trayn Humaira da Zainab suka haɗa bakin cewa.
"Ina kwana”. Salma da tayi ƙasa da kanta tunda ya shigo ne tayi murmushi dama ai ta tuna bazai amsaba.
Ita kuwa Fariyda idon ta zuba mishi cikin tsoron kada yaci zarafin ƙawayenta aminanta kuma ƴan uwanta.
Fuska ya kuma tsukewa tare da watsa mata kallon da ka gani kasan ganin ƙazamai yake musu, kai tsaye ɗakinsa ya wuce.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da yin Hamdala kana ta kalli Zainab da Raihana da tuni sun tattare komai sun mayar kitchen Zainab na wanke duk abinda suka bata da gyara kitchen kana Raihana kuwa ta gyara parlour tsab ta goge ko ina yayi ƙal window ta buɗe tare da cewa.
“Bari iska ya ɗan ɗauke tsamin kabejin nan, kafin insa turaren wuta”.
Salma tace. “Shiyasa ni sam bana son harka da kabeji yanzu zai ɗuma maka wuri kamar anyi tusa”.
Ta ƙare maganar tare da cewa. “Muje ciki Fariyda in shirya miki kaya, ko kin shirya ne?”.
Raihana tace. "Ba abinda ta shirya ita da tace miki tafiyar bata gabanta”.
Da sauri ta kuma kamo hannunta tace. “Muje in shirya miki”. Tana janye hannunta tace. “Kawai shirya min, Humaira zata wanke min kai na”. Da sauri tace. “An gama bari inje in shirya miki harda nasu Zaid”.
Daga nan ta nufi bedroom ɗinta.
Tana shiga ta fara buɗe Wordrobe ɗin, Side ɗin da akwatun suke ta zuba wa ido, daga bisani ta zaro ɗan madaidaici da zai iya cin kaya mai ɗan dama, sai kuma ta zaro da kit ɗinsa da shima zai ɗauki abu da dama.
Kana gado ta ajiyesu tare da buɗe su.
Sai kuma duk ta fara bin Wordrobe ɗin tana buɗewa tana ɗauko duk abun da ke da mahimci na ado da kwalliya duk babu wani abu da tasan duk mace mai aji da kula da miji zata bukata wanda bata saka mata shiba, kaya kuwa tsarin kanta tasa wanda wasuma Fariyda bata san da suba dan na cikin kayan da aka haɗa mata a fitan takabar tane Sleeping dress kuwa tsarin kanta tasa kusan biyar sai kuma Abaya kwaya shida kacal Atamba da lace ko ɗaya bata saba sai tattausan riguna da wanduna masu zafi.
Collar kayan da ta sawa Fariyda ta rinƙa duba irinsu tana sawa su Zaid komai nasu na buƙata, turaruka ta rinƙa sunsuna ƙamshi tare da zaɓa mata na sawa, sai iya man baki sai kum dasu ribbons na Fariyda dana Zaitoon da mangashi duk ta sama komai.
A ƙalla awa ɗaya da rabi tayi tana haɗa mata kayan kana ta fito tana shaƙar ƙamshi da taji parlour ya ɗauka.
Himilin gashin Fariyda da yake baza wani irin ƙelli da ƙamshi ta kalla yadda Humra ke ta kiciniyar tubƙeshi yana suɓale mata.
“Na gama sa miki komai har hand bag naki duk na shirya miki, har kayan da zaku sa gobe in zaku tafi zaki ganshi kan akwatin da naki da nasu Zaid”.
Fariyda tace.
“Kai nako gode MRS Salim”.
Murmushi tayi tare da cewa. “In sha Allah kuwa”. Zainab dake latsa wayane tace.
“Kin sa mata colors da tafi so ko?”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Na dai sa ko wanne amman nayi nazarin collors ɗin da mijinta yafi sawa na saka, dan aje a asha ƙyalli”.
Fitowarsa ne yasa suyi shiru, ko inda suke bai kallaɓa wucewarsa yayi ya fice tare da jan gajeren tsaki.
Sai bayan isha suka sauƙa parlour Ummi suka shiga sukayi musu Saida safe, motarsu na fita na Amina na shiga, tare da Fariyda suka koma ciki tana faɗin.
“Da niyata sai da safe zanzo muyi sallama sai kuma Mahmoud ke cemin 7:00 Am jirginku zai tashi, shine nace bari kawai inzo muyi hira”.
Ta ƙare maganar tana zama kusa da Ummi dake cewa Mahmoud.
“Abbanku na kira”.
Miƙewa yayi ya bar wurin.
Ummi ta bishi da kallo tare da cewa.
“Ɗazu naji yana waya da Salim yace sun mai text sun canza lokacin tafiya daga 7:00 Am sun maidashi 2:00 pm.”.
Da sauri tace.
“Kai kada fa kuma su sa suyi missing flight from Abuja to Addis ababa ɗin, dan yace min su kuma huɗu zasu tashi”.
Hafiza dake jan plate ɗin fruits ɗin da Mahmoud ya bari ne tace.
“A'a in sha Allah bazasuyi missing flight ba Mom tunda har ƙarfe huɗu zasu kai, kafin nan ai sun isa”.
Goggo Dada tace.
"In sha Allah kuwa”.
Nan sukayi ta hira har wuraren goma saura kwata Daddyn Hafiz dake wurin Abba tare da Hafiz da Mahmoud suka shiga ya gaida su Ummi kana ya fita yana cewa Amina ta fito su tafi.
Kan Zaid ta shafa tare da cewa.
"Allah ya bada lfy Zaidullah”. Amin su Ummi suka amsa kana ta ɗan rungumi Fariyda tare da cewa.
“To sai kun dawo”.
Daga nan ta fita suka tafi.
Washe gari da rana misalin ƙarfe ɗaya dai-dai tsaye suke a tsakiyar parlour Ummi Abayace a jikinta mai masifar kyau da sulɓi Blue Black mai kyan gaske ta ɗanyi rollin kanta da gyalensa fuskarta ta fito ras gonin kyau more Especially yadda tudun gashinta ya bada armashi.
Zaid da Zaitoon Black blue jeans ne a jikinsu sai green shirt mai taushi na Zaitoon cike da kwalliya. Kanta ya sha kitson da Zainab ta watsa mata gwanin kyau sai ƙamshi suke yi kamar ka ɗauke su ka gudu.
Hafiz da ya gama kai kayansu motar Salim ne ya kalli Ummi dake cewa.
“Kaima zaka jene”. Kai ya gyaɗa mata tare da shafa kan Zaid yace.
"Tun yanzu gidan ya fara zama ba daɗi, ni gidanmu zan koma dama next week Huzaifa zai dawo gidanmu zaifi daɗi, sai sun dawo nima zan dawo”.
Goggo Dada tace.
"Ai kuwa baka isaba kuyi mana watsiyar dila”.
Ummi ta kalli Fariyda da ba wani alamun farin cikin tafiyar tare da ita, tace.
"Kije Abbanku na kira, kije dasu Zaid ɗin”.
Kai ta gyaɗa mata tare da kama hannunsu suka tafi.
Su kuma shiru sukayi parlour sai Samira dake cewa.
“Allah kamar in bisu”.
A gaban Abban ta durƙusa tare da gaidashi yana miƙawa su Zaid hannu ya amsa, sai kuma yayi murmushi ganin sunƙi zuwa wurinsa sun wuce wurin Mahmoud dake gefensa cikin wani tattausan wonɗo mai haɗe da belt ɗinsa, black blue sai tattausar rigar jikinsa mai guntun hannun ita ma irin tasu Zaid.
“Kuje wurin Abbana ko”.
Ya faɗa yana tura su wurin Abba dake cewa.
“Ƴan al'barka masu ƙiuya”.
Salim ne dake gefen Abba yana shan sauran furar Abban ne yace. “Kuma fa Abba ba kiuya ya sukeba, dan in Mahmoud baya wuri zasu amshi kowa, in sun gashi ne dai basa kula kowa sai shi”.
Murmushi Abba yayi tare da shafa kansu yana mai cewa.
"Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy”.
Da Amin su Fariyda suka amsa. Sai kuma ya kalli Fariyda tare da cewa.
“To Fariyda zaku tafi ko”.
Kai ta gyaɗa masa ido na cikowa da hawayen rauni.
“To Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy cikin farin ciki”. A hankali tace.
“Amin ya Allah Abba”.
Mahmoud dake duba time Abban ya kalla tare da cewa.
“Tashi ku tafi kada ku makara.”
Kusan a tare suka miƙe suka nufi parlour Ummi shi kuwa Abba ya fita ta parlour sa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.