Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 78 of 86
Da sauri ya É—aga Zaid É—in dan kar ya tada Zaitoon.
Bisa kafaÉ—arsa ya É—aurasa tare da fara É—an jijjigashi.
Sai kuma yayi saurin sauƙe tare da kallon yadda ya kuma sakin kuka tare da mummiƙewa ya tsandare.
Parlour ya nufa da sauri yana mai jijjigashi.
Ido ta buÉ—e a hankali ta zuba mishi su, kan one sitter ya zauna ya kifeshi kan cinyarsa yana É—an jijjigasa.
“Kin bashi maganinsa kafin yayi bacci?â€. Ya tambaya ba tare da ya kalleta ba.
“Ina idar da sallan isha na bashiâ€.
Numfashi ya É—an fesar sabida jin ya É—an tsagaita kukan.
A hankali ya É—ago kanshi ya kalleta sabida jin wani irin ajiyan zuciyar da ta sauke mai tafe da sassayan numfashi.
“Yayi bacci ne?â€. Ta tambaye shi cikin yin Æ™asa da murya gudun tadashi daga baccin.
Kauda idonsa yayi daga kanta tare da tsuƙe fuska, sai kuma yayi saurin ɗago shi, saboda yadda Zaid ɗin ya kuma sakin ihu mai haɗe da mimmiƙewa.
Jijigashi ya farayi tare da hura masa iska sabida ganin yadda goshinsa yake tsatstsafo mishi zufa.
Sai kuma ya mike tsaye tare da É—aurashi kan kafaÉ—a, yana jijjigashi, fridge É—in dake gefen dinnin table ya nufa.
Ruwa ya É—auko ya bashi.
Ina sam yaƙi karɓa, time Fariyda ta duba ƙarfe ɗaya harda rabi.
“Mittssss yaro nan bacci zai hanamu yau kumaâ€.
Wani irin mugun kallo ya danna mata tare da cewa.
"Ke bacci nema damuwarki ba matsalarsa ba koâ€. Tana miÆ™ewa tsaye tace bashifa da matsalar komai rikicine kawai na gado ai tun jiya ya fara kananan kukaâ€.
Cikin tsuÆ™e fuska yace. “Gado rikicin gado wa ya gada kenan?â€.
Numfashi ta É—an fesar.
“Wa ake gado kuwa banda dangin uba wata Æ™ilma Æ™anin ubanâ€. Ihun da Zaid É—in ya cilla tare da mimmiÆ™ewa ne yasa tayi saurin isa inda yake, shi kuwa Mahmoud baima bi ta kan furucinta ba, sai jijjigasa yake yi cike da tausayawa.
Hannunta ta ɗaura kanshi tana shafawa, fuskarsa da tayi jazir gami da jiƙewa da zufa dake tsatstsafo mishi ta ko ina ne yasata, sunkuyowa kansa ta fara hura masa iskan bakinta, sai kuma tayi saurin ɗago kanta saboda yadda ya auna wani ƙara da ciccilla ƙafa, cikin ruɗani da son uwa akan ɗanta gami da raunin zuƙatan matantaka ta kalleshi sai kuma ta ƙara matsowa kusa dashi sosai murya cike da rauni tace.
“Ina gafa cikinsa ne ya tashin masa, kaga yadda yake yi da kafafunsaâ€.
Sai kuma duk suka miƙe tsaye daga ɗan zaman da sukayi, da sauri ya miƙa mata shi tare da cewa.
“Kiyi breast feeding É—insaâ€. Da sauri ta Æ™arbesa tare da mannashi kan Æ™irjinta cike da tsoron kar ya gane ta yayesu, sai kuma duk suka kalli Æ™ofar bedroom É—in, da sauri Mahmoud ya nufi ciki saboda jiyo kukan Zaitoon.
A tsaye ya sameta tana jijjigashi tana shafa bayansa, yana ɗan zirga-zirga, Zaitoon dake kafaɗarsa ya gyarawa riƙo ya ɗaukan wuyarsa Dr Imran Patel ya kira. Tsaki ya ja ya miƙa hannun ya karɓi Zaid yana faɗin.
“Ya sha ne?â€. Ya tambaya cikin tausayawa kai ta jijjiga masa tare da cewa. “Ai basa yarda su shaâ€. Tayi magnar dan samawa kanta mafitar tsira da masifarsa in ya gane ta yayesuâ€. Numfashi mai zafi ya fesar yana kuma kiran Dr Imran É—in a karo na uku har lau tana shiga baya É—agawa.
Ita kuwa Fariyda Zaitoon dake ƙoƙarin dauƙo daga kan kujerar ta ɗaga ta rungumeta a kafaɗa.
Wayarta da ta hanga kan Centre table ta ɗauka tana duba lokaci ƙarfe biyu harda rabi, a ƙalla awa ɗaya kenan cib Zaid ke ta kuka ba ƙaƙƙautawa, kukan da yasa idonta cikowa da ruwan hawaye wayar ta zura cikin aljuhun rigar baccin nata.
Da sauri yace.
“Kawo maganin mu Æ™ara masaâ€. Da sauri ta wuce bedroom ta É—auko maganin.
Numfashi suka sauƙe tare da zuba masa ido ganin ya ɗanyi shiru bayan sun bashi mgnin.
ÆŠaukan magungunan tayi ta maidasu kan Dinnin table.
Da sassarfa ta juyo saboda jin yadda Mahmoud ke cewa.
“Innalillahi Zaid! Zaid!!â€.
Sai kuma kawai ya miƙe tsaye ya nufar waje.
Da sauri tabi bayansa rungume da Zaitoon É—in.
Yana isa Reception É—in su ganin yadda Zaid É—in ke sake a hannunsa alamun a sume yakene yasa, su saurin kiran driver Ambulance É—in dake cikin hotel É—in saboda ajular gaggawa.
Yana fitowa driver na isowa sabida kiran da ya samu daga Reception É—in nasu.
Ƙarfe uku dai-dai suka isa Asibitin.
Wanda tuni Dr Imran Patel ɗin yayi waya da Mahmoud ɗin saboda kiran da Mahmoud ya rinƙa jera masa har ya farka.
Haka yasa kafin su isoma tuni an shirya komai.
Suna isa Nurse suka karɓeshi, ɗakin aikin suka nufa dashi yayinda Mahmoud ɗin da Fariyda ke biye dasu a baya, da sauri Dr Zara ta ɗan tsaya gabansu tana basu baki na su ɗan jirasu, isowar Dr Imran Patel ɗin ne yasa Mahmoud sauri isa inda yake da faɗa mishi halin da Zaid ɗin yake ciki. Kai ya jinjina yaca masa, ai dama matakin da suke jira kenan na haɗewar ciwon da tashinsa.
Daga nan dai sukayi ciki.
A hankali ta zauna a kujerar dake wurin hannunta duka biyu tasa ta tallaɓe haɓarta, sai kuma ta ɗan gyara riƙon Zaitoon dake jikinta ta miƙe tsaye gaban Mahmoud ɗin dake ta zirya bakin ƙofar parlour da ɗakin aikin yake can ciki.
Cikin murya mafi ƙololiwar rauni da tashin hankali tace.
“Baya motsi ko? Naga kamar baya numfashi fa?â€. Ta Æ™are maganar tare da kafeshi da idanunta dake cike da hawaye. Lip É—inshi ya matse da Æ™arfi tare da jujjuya mata kai, da sauri tace.
“Baya numfashi ko?â€. Murya a sanyaye da rauni yace.
“No yana numfashiâ€. Ƙara matsoshi tayi ta riÆ™o hannunsa cikin zubda Æ™wallan tace.
“Zai warke?â€. Kai ya rinÆ™a gyaÉ—a mata babu Æ™aƙƙautawa tare da faÉ—in.
“In sha Allah! In sha Allah!! In sha Allah!!! Zai warke zai samu lafiya zai rayu tare damuâ€.
Gaba É—aya jikinsa rawa yake yi, kamar yadda natama rawa yake yi haka ne yasa ta dawo kan kujerar ta zauna, ta kwantar da Zaitoon a gefenta, wayarta ta kuma kalla. 4:00 Am, da sauri ta duba ragowar katin daya rage mata.
Number Baba Malam ta kira cike da yaƙini yanzu dai idonsa biyu cikin rashin sa'a kiran bai shigaba.
Ido ta lumshe tare da jigina kanta jikin kujerar.
Sai kuma ta ɗago kanta tana fesar da numfashi saboda jin wuyanta yayi tsami dan a ƙalla ta kai 36 minute a haka, ba kuma bacci tayi ba, sai addu'o'in neman lafiya da take tayi a saman lips ɗinta.
Mahmoud kuwa a hankali ya koma bakin ƙofar parlour ya tsaya a karo na barkatai har yanzu shiru basu fito ba, ko motsinsu basu jiba gashi har 5: tayi
Ya ilahi ya mujibadda'awati. Awa biyu kenan cib da shiga da shi har yanzu shiru.
Wayarsa ya zaro aljihu jin kiran Sallah wanda hakan ke masa nuni da lacin sallan asba ta cika cib.
A hankali ya juyo jikin kofar ya manna kanshi jikin glass ɗin ƙofar.
Dai-dai lokacin kuma yaga an buɗe ƙofar ɗan ƙara min gadon da yake kwance a kai tamkar gawa suka nufa shida Fariyda dake rungume da Zaitoon.
“Zaidâ€. Fariyda ta kirashi sai kuma tayi shiru saboda É—aga mata hannun da Dr Imran Patel É—in yayi alamun tayi shiru.
Wani corridor mai girma da yelwar haske da tsabta suka nufa.
Tafiya kaɗan sukayi a ciki suka shiga wani ɗaki mai girman gaske, wanda yake ɗauke da wasu irin na'urori masu tarin yawa masu sarƙafe-sarƙafen woyoyi da madubai. Wanda suke kusa da gadon yara guda ɗaya sai kuma 3 seatter sai drawer mai ɗan girma a can gefe, sai fridge TV dake jere, wani tattausan Centre carpert ne mai masifar kyau a shimfiɗe a tsakiyar ɗakin, sai abubuwan wasan yara dake jere a saman ƙarfen gadon, harda su balum a jere da wasu flowers masu kyau da aka ɗan jere a jikin yar ƙaramar katangar da take bayan gadon sai daga can gefe ɗan corridor ne da ƙofan bathroom a ciki.
A hankali suka maidashi kan gadon dake cikin É—akin kana É—aya daga cikin Nurse É—in ta fita da gadon da suka shigo dashi É—in.
Cikin yin ƙasa da murya Dr ya cewa, Mahmoud su tafi suyi salla ya cewa Fariyda ta shiga tayi alwala tazo tayi salla amman kada tace zata kiransa.
In Kuma tasan Zaitoon zatayi kuka su tafi masauƙinsu kawai akwai masu kula dashi.
Da sauri Mahmoud ya girgiza masa kai alamun a'a suna nan.
Gudun AC ɗaya Dr ya ƙara da cewa kada su rage har sai in su suka rage,
Kai Mahmoud da Fariyda suka jinjina, a hankali ya ɗan ƙara matsowa jikin gadon so yake yajishi rungume dashi, amman ina.
Ganin yadda yake kallonsa ne yasa Dr jan hannunsa suka fita.
Ita kuwa Fariyda kwantar da Zaitoon dake ta bacci tayi bisa 3 seatter, kana ta dawo gaban godon ido ta zuba mishi tana kallon robarobin dake manne kan ƙirjinsa, idon ta maida kan na'urar dake gefe wacce zanen numfashin sa ke nunawa a ciki.
Numfashi mai nauyi taja ta lumshe idonta sai kuma ta fara karanto addu'o'in tana É—an hura iskan bakinta ta kanshi saida tayi kusan 12 minute a kanshi kana, ta shiga tayi alwala.
Cikin sanyi ta fito daga bathroom ɗin tare da jan ƙofar ta rufe a hankali, sai kuma tayi saurin ƙarasawa cikin ɗakin da sauri saboda jin wani irin ƙara da yake fita ta inda Zaid ɗin yake.
Ƙeeeyy! ƙeeeyyy!!! Ido ta zaro ganin yadda cikinsa yake sama da ƙasa har zuwa ƙirjinsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.