Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 86
Da sauri Goggo Dada ta karɓi Zaitoon ɗin.
Ummi kuwa Zaid ta karɓa.
Dariya sukayi baki ɗayansu jin Aunty Amarya da tace.
“Ikon Allah wannan anyi raguwar mace, ga Yadda duk fuskantar tayi jazir”.
Mamy ce tace.
"ina Mahmoud ɗin.”
Nasir ya bata amsa da.
“Ya tafi”.
Dr Nasir ɗin ne ya amsa sallamar da Salim yayi tare da masa iso.
Kana suka gaisa daga bisani dai suka tafi cikin gamsuwa da samun sauƙin Zaitoon ɗin.
Daga nan kai tsaye gidan Amina suka wuce daga bakin ƙofar suke jigo Muryar Mahmoud dake faɗa kamar zai daki Amina dake bashi haƙuri.
“Haƙuri ko? To tabbas wata ran maciji zata sa mata a wuya, yarinyar nanfa ba hankaline da itaba.
Wlh Allah kenan ranar juma'a zan karɓe yarannan a hannunta”.
Ido ta zuba mishi dan ta fahimci a fusace yake.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
"Yau naji daɗi na, Ummi da Goggo Dada a gidana”.
Cike da farin ciki tai musu iso tare da shigawa kitchen jim kaɗan ta fito.
Da tray plate biyune a kai ɗaya cike yake da fruits ɗaya kuma pepper chicken ne mai zafi wanda Mahmoud tayiwa.
Sai kuma ta koma ciki ta kawo musu drinks.
Da sauri Goggo Dada tace.
“Ke zoki zauna mu gaisa, mu a ƙoshe muke”.
Fuska ta kwaɓe tace.
“Dan Allah Goggo Dada kar kuyi min haka, kuci kusa min al'barka”.
Ummi tace.
"Ai al'barka dai kullum cikin sa muku ita muke”.
Amina tace.
“A'a Ummi ai na yau daban nake sonsa, dan Allah kuci kusha fruits ɗin”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Kuma kawai sai mu buɗe ciki muci abinci a gidan surki”.
Da sauri tace.
“To ba matsala zan haɗa muku shi ku tafi dashi”.
Mahmoud ta ɗan kalla tare da cewa.
“Kaima kaƙi kaci”.
Da sauri Goggo tace.
“Kuma ko breakfast baiba ya fita”.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
“Ummi zan karɓe yarannan fa”.
Kai ta jinjina mishi alamar to.
Ganin haka ne ya miƙe tsaye tare da juwa ya nufi waje.
“In ka fita kace Salim ya shigo”.
Kai kawai ya gyaɗa ya fita.
Ido suka zuba wa set ɗin akwatuna kala biyu, da Salim da Hafiz da ya zo da nufin gayawa Mom ɗinsa abinda ke faruwa.
A tare suka shigo dasu akwatunan .
Da sauri sauri Amina ta rinƙa buɗesu ɗaya bayan ɗaya.
“Hmmm kai masha Allah kaya kam sunyi kyau, kuma nasan Fariyda zataji da ɗinsu ko ba komai zamu sata farin ciki.
Duk da dai nasan dole mutuwar Yah Amin sabo zata zame mana ranar da zata fita takaban”.
Ido Ummi ta lumshe.
“Kada dai kuje kuyi ta koke-koke, Abu mafi kyau addu'a zamuyi ta yiwa Aminullah, in taga kunje da ɗan sakin rai itama abin zai zo mata da sauƙi.
Goggo Dada ma zataje ita da Mama.
Naji kuma Samira ma da Jidda da Abida matar Ahmad zasuje sai matar Barrister da maƙociyarmu Hajia Adama.
Tana mai lumshe idanun da son maida hawayenta tace.
“In sha Allah Ummi bazamuyi ta mishi kuka ba, addu'a zamuyi ta mishi”.
Salim da Hafiz dake shan fruits ɗin dasu Ummi suka ƙi sha ne Salim yace.
Goggo Dada muma zamu iya zuwa ne?”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“A'a kam maza kam basa zuwa mata dai yan uwa da abokan arziki za'a haɗu da ɗan ihsani dan kyatatawa da samawa zuciyar mai fita takaban farin ciki”.
Jidda ce kwance wayarta ne ya kuma ringing a karo na uku.
“Mitsss”. Taja dogon tsaki ganin kiran Yah Sulaiman ne ya kuma shigo mata a karo na uku.
Idonta dake cike da ƙwalla ta kuma lumshewa tare da kife kanta ta saki sassayan kuka.
“Yah Allah ka shiga lamarina. Allah ka sani Yah Mahmoud nakeso. Allah ka cika min burina, kayiwa ɗan uwana Sulaiman da zaɓi mafi alkhairi”.
Kai Mama dake bakin ƙofar ta jujjuya tare da juwa ta koma parlour.
Washe gari da safe.
“Jiya da Zainab tazo, nace mata tazo gobe laraba tayi miki ƙunshi da kitse”.
Raihana ta faɗa tana kallon Fariyda dake rungume da Zaitoon dake cikin wata tattausan over roll Pink collar.
Kanta ta ɗan jijiga tare da cewa.
“Hmmm Raihana kenan, ƙunshi kuma, kamar wacce farin cikine yayi sanadin taron”.
Da sauri Salma da ita a nan ta kwana tace.
“To ai gyaran kuma ba laifi bane ko”.
Idonta daya cika da ƙwalla ta lumshe sai gasu zir.
“Me zanyiwa ƙunshin, fitar takaban mutuwar Yah Amin na, cika watanni huɗu da kwanaki goma da rabuwarsa zanyiwa farin cikin da har zaisa nayi lalle da kitso, ko duba maraicin yarana da zasu tashi marayu basu san daɗin ɗumin jikin mahaifinsu ba”.
Aunty Amarya da shigowarta kenan dan duba Zaitoon da jikine ta zauna gefen Fariyda tare da dafa kafaɗarta.
“Fariyda ai su Zaitoon bazasuyi kukan maraiciba, domin nasan duk wani abunda uba zaiyiwa yayansa abinda ya fisa Mahmoud zai musu.
Naga tsananin soyayyar yaran nan a cikin ƙwayar idanunsa.
Ki ga jiyafa Mahmoud kuka yake yi sir-sir da hawayen da ko a lokacin rasuwar ɗan uwan nasa bai zubdasu ba, dan haka cire maraicin yaranki a matsayin damuwar rayuwarki, dan nasan ko ke bazaki fi Mahmoud kulawa da yaran nan ba”.
Cikin takaici tace.
“Aunty shifa wannan da kike ta yabawa bashi da alƙibla, to nima uwarsu ji yake kamar ya kasheni fa mutumin da ko dariya bayayi ta zai zame musu kamar uba”.
Salma ce ta ɗanyi miƙa tare da cewa.
“Duk abinda yake yi kyau yake yi.
Wlh komai nashi burgeni yake yi.
Allah ka fini sanin me a zuciyata”. Fariyda tace.
“Ni dai wlh bazanyi komai ba”.
Mamy da takejin duk mgnarsu tace.
“To Maman Raihana, ki fito gashi yanzu Hafiz ya kawo cefene himili guda wai cefenen abin sadaka da za'ayi”.
Da sauri tabi bayanta.
Ido suka zubawa Hafiz ɗin dake miƙawa Mami kuɗin da ya kai 100k.
“Gashi Abba yace in akwai abinda bamu saba sai a saya”.
Yaƙare magnar tare da ajiye kuɗin kan hannun kujerar da take kai.
Himilin kayan da ba abin buƙatar da babu a ciki ta kalla tare da cewa.
“To in Banda ma Alaji da hidima, me za'ayi da wannan duka, abinda ba biki bane, iya yan uwane zasu zo”.
Yana ɗan miƙewa tsaye yace.
“Mami Aunty Fariyda fa”.
Sai kuma ya miƙe da sauri ganin Raihana ta fito rike da Zaitoon amsarta yayi tare da cewa.
“Hello my princess ya jiki?”.
Baki ta wangale masa tare da maƙaleshi.
“Alhamdulillah jiki kam da sauƙi, sosai yanzu Mahmoud ya dawo da ita daga kaita allura”.
Yana ɗan shafa kanta yace.
“So Sorry mata bazamu yafewa kunamar nan ba kam”.
Dariya sukayi tare da gaisawa da Fariyda data fito.
Daga nan ya fice yana faɗin.
“Yauwa kar in manta Mom tace in gaidasu, wai yau tana da baƙi bazata samu zuwa ba sai gobe”.
Mami tace.
“Ba komai jiya fa har kusan 9/35 pm ta bar nan”.
Ranar Alhamis da yamma gab magrib Ƙanwar Mami Aunty Jamila da Hajja inna suka iso Kano daga Taraba.
Rungume Fariyda Aunty Jamila tayi cike da tsananin so kulawa da tausayawa tace.
“Allah sarki yata”.
Raihana kuwa rungume Hajja inna tayi tare da cewa.
“Kakus nayi kewarki”.
Ɗan bugu Mami ta kaimata tare da cewa.
“Na ƙaryane, ni ɗaga min uwa kada ki ɓalla mana ita, ai da ace kinyi kewar tata, da kin koma Gembu daga zuwa kika butulce mata kikaƙi komawa”.
Ɗan sosa wurin tayi tare da cewa.
“Mami ai ban gaji da ganin ku bane”.
Harararta Hajja inna wacce tun da aka yayata take wurinta a Gembu membila acan ta girma.
Dan lokaci Fariyda ma bata wuce goyoba dan shekara ɗaya kacal take bawa Raihana shiyasa komansu ɗaya ko ƙawayensuma ɗaya ne, son da Aunty Amarya ke mata yasa Mami ake kiranta da Maman Raihana.
“Ni barni yanzu in zan tafi da Fariyda na zamu tafi, tunda da gobe zata fita takaba ita kuma ai su Alaji Abbau sun gama mgna da malam ba har sun zoba batun nema wa ɗansu Rabi'u aurentaba in bata koma Taraba dan niba ai ta koma dan mijinta in anyi auren”.
Ta ƙare maganar tare da jawo Fariyda gabanta.
Sai kuma ta fashe da kuka.
“Sannu Fariyda am yarinya ƙarama dake Allah ya ɗaura miki takaba, ko ni kakarki ban san ya akeyin takaba.
Allah ya jiƙan Aminullah.
Cikin sanyi tace.
“Amin yah Allah”.
Mami dake jera musu abinci da abun shane tace.
"Ke Raihana tashi kuje ga Saddiqa da Amina sun iso.
Yar Aunty Amarya ta fari kenan wacce Sadik kebi wacce a Adamawa take aure tana riƙe da yar autarsu Amira.
Aiko da murna ta miƙe sai kuma ta koma da baya ganin Saddiqan data shigo da sauri tana Fariyda! Fariyda!! Da sauri suka rungume juna.
Sai kuma kawai Fariyda ta saki kuka mai sanyi tare da cewa.
“Sannu da zuwa Aunty Saddiqa”.
Hawayen ta fara share mata tare da cewa.
“Yi hakuri Fariyda karki sani kuka nima.
In sha Allah Aminullah yana cikin rahamar Ubangiji.
Ke kuma Allah ya baki miji na gari, ya duba maraicin yaranmu”.
Da Amin suka amsa baki ɗayansu.
Kana Malam da ya shigo har ciki dan maramtar surkar tasane yayi ta musu nasiha daga nan kuma aka ɗan sake gaisawa.
“Ina Adda Nana”.
Saddqa ta tambayi Raihana dake ce mata.
“Wato dai ni baki ganniba to Adda Nana sai gobe zatazo ta tafi dasu Salma da Zainab Aunty Khadija ma can ta wuce suna aikin masa a gidan tane”.
Ranar dai kam sosai Fariyda ta ji damuwar ranta ta ɗan saketa.
Ganinta tsakiyar su Aunty Jamila da maman Khairat matar kawunsu kenan ga kuma Saddiqa.
Ga Goggo Abu da itama ta iso da dare harda Aunty Miemie maman Salma da sauran matan Uncle ɗinsu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.