Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 86
“Yauwa sai ki kawo da inda zaki sawa Aminullah nashi”.
Kai ta gyaɗa tare da juyowa ta kalli Hafiza dake cewa.
“Ai shi nashi a haɗe yake da na Uncle Mahmoud”.
Ita dai Fariyda tuni ta fice daga parlour baki ɗaya.
Acan Dinnin area kuwa tunda ya rumtse idonsa bai buɗesu ba.
So yake ya danne fusatacciyar zuciyarsa saboda ba gani yake ba girmansa bane kula mgnarta Allah ya sani tunda ake faɗin dangin miji na tsanar matar ɗan uwa bai gamsuba sai yanzu da haka ke faruwa a kanshi.
"Na tsani yarinyar nan”
Ya faɗa a hankali.
A parlour kuwa sallama Jidda ne ya maida hankalinsu baki ƙofar.
Da Sauri Samira ta mike tare da rungumeta tana faɗin.
“Ai tun jiya nake zuba idon ganinki shiru”.
Kallonta tayi ba tare da tace komaiba ta ƙarasa gaban.
Ummi da Goggo Dada dake yi mata sannu da zuwa gaidasu tayi.
Sai kuma ta ɗan juyo ta gaida Aunty Amina.
Tare da ɗaukan Zaid da yanzu ya farka daga bacci da yake gefen Babanshi.
Sai kuma ta ɗan kalli Aminullah ɗin cikin girmamawa tace.
“Ina kwana Yah Amin”.
“Yana shafa kan Zaitoon da itama ta buɗe ido yace.
“Lfy lau Jidda Yah Bappa Lawan da Mama”.
Tana gyara zamanta tare da kallon Hafiz da Hafiza cikin sigar harara.
“Allah kuwa yaranan baku da zumunci shi yasa bazan amsa gaisuwarku ba.”
Da sauri Hafiza ta rungumeta tare da cewa.
“Afwan Aunty Jidda”.
Hafiz yace.
“School ne ke hanamu sararawa, duk randa muka gama zakusha ziyara”.
Tureta Hadiza Jidda ta ɗanyi tare da kallon Aminullah tace.
“Yah Amin dama baka tafi bane! Jiya Baba ke tambayan Yah Ahmad yaushe zaka tafi yace.
Jiya da dare zaka tafi”.
“Ban tafi ba tukuna sai ranar juma'a yau ba jirgin Istanbul shiyasa”.
Aunty Amina ce ta kalli yayan nata cikin kulawa tace.
“Yah Amin kaine kuma zaka tafi Istanbul ɗin a wannan lokacin ina Mahmoud ɗin?”.
Dai dai lokacin Fariyda ta shigo cikin jaddada wa Aunty Amina abinda take zargi tace.
“Shi ya isa da shine, yace shi bazai jeba, dole shi zaije ko zai cutu, tunda yana tsoronshi ai shike nan yaje Allah ya tsare shi. Yaro ƙarami yayi ta juyashi kamar shine babba a kansa”.
Ta ƙare maganar tana rufe box ɗin da ta zubawa Abba nasa ta ajiye gefen Ummi Sai kuma ta kalli Aminullah dake cewa.
"Wai ke meyasa bakya fahimta nane”.
Cikin takaicin tasan yanzu zai fara kakkare shegen yaron nan mai masifar ginman kai ne yasa ta miƙe ta nufi Hanyar fita.
Dai-dai lokacin kuma Mahmoud ya fito daga dinnin area ɗin.
Cikin wani irin tsuke fuska da gaza danne fushinsa ya nufe su tare da buɗe murya cikin isa yace.
“Wallahi zan zagi kan uwar mutum in bai daina shiga mgnata ba in yan uwana sunayi”.
Da sauri duk suka juyo suna kallonshi dan banda Hafiza ba wanda yasan yana Dinnin area ɗin.
Ita kuwa Fariyda dai-dai lokacin ta isa bakin ƙofar parlour wani irin juyowa tayi ta kalleshi cikin wata iriyar hararar dake bayyana tsananin tsanarsa da jin haushinsa taja wani dogon tsaki tare da buɗe ƙofar ta fice tana faɗin.
“Ɗan iskan yaro mara mutunci”.
Duk da bai ji taɓa dan tayi ƙasa da murya yadda Ummi bazataji ba, Amman duk sunji tsakin da taja wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta kuma.
Sai kuma duk suka juyo kan Mahmoud ɗin da ya fara zuba faɗa tamkar zai ari baki.
“Na rantse da Allah ka jawa waccar yar iskar yarinyar kunne, Yah Amin wlh Allah kenan zan zubar mata da haƙoranta in bata daina samin baki a lamuran rayuwata ba,
Dan iskanci uwartace ta haifeni da zata lissafa min shelaruna ko ubantane ya cinye min ona year ɗin da take regemin”.
Sai kuma ya ƙaraso tsakiyar parlour a fusace yana nuna Aminullah ɗin da yatsa.
“Me haɗinta dani da kai kawai take da alaƙa, kuma alaƙarku bai kai alaƙar da zata ratsa tsakaninmu ba, shegiya mai kama da parrot kullum sai tacemin Yoro uwartace ta haifeni? Da zata addabi kunnuwana da cewa ni yarone kana tsorona wai so take sai ta farraƙa tsakaninmu ne ko meye?
To bazan je ɗinba in taga dama ta nemo Nasir yayanta yazo yaje tunda sun fini sonk...”
Sai kuma Goggo Dada Aunty Amina dasu Hafiz duk suka muƙe tsaye sabida jin wani irin sautin maruka da Ummi ta fara jera masa hagu da dama.
Da sauri Goggo Dada ta riƙo hannun Ummi tare da zaunar da ita gami da faɗin.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun”.
Hafiza da Samira kuwa da sauri suka nufi ɗakin Goggo Dada.
Jidda kuwa tunda ta rumtse idonta bata buɗesu ba.
Shi kuwa Mahmoud hannunsa yasa ya dafe kuncinsa na dama tare da yin gis a wurin tamkar an da dashi.
Aminullah kuwa ƙasa yayi da ƙansa tuni idanunsa ke zubda ƙwalla wani na korar wani!
Murya na rawa alamun kuka na gab da kwance masa ya fara magana a hankali yace.
“Shike nan zanje ɗin nifa nace zanje.
Ummi kiyi haƙuri ki yafe min duk ni naja miki wannan ɓacin ran ki gafarceni, ki yafewa ɗan uwana”.
Ya ƙare maganar cikin tsananin sanyin murya
Cikin tafasar zuciya Ummi tace.
"Rufe min baki Aminullah kar inzo in tsistsinka maka mari, haƙuri haukane, kaci gaba da zama lusari namiji agaban matarka, kana barin ƙaninka yana jujjuyaka da kafa maka duk sharaɗi da dokan da yake so sannan ka bishi kamar shine babba a kanka, wlh Allah kenan kana gab da nema wa kanka raini a gaban matarka idan baka zama mai zazzafar zuciya ba.
In Banda haƙurinka da ya fara zama mutuwar zuciya ta yaya za'ayi a gabanka Ƙaninka da kake bawa shekaru bakwai zuwa takwas ya zauna yana zagin matarka harda ikirarin zubda mata haƙori ka kuma sanshi ba mutuncine da shiba in ba'a taka mishi birkiba zai aikata, tunda kaga har ubanta yake zagi Baba Malam wanda yake ko baka auri yarsaba ubane a gareku tunda abokin mahaifinku ne aminensa ne na tun yarinta.
Amman kayi ka sake kanaji kana gani, baka daka min shiba sai ya daina motsi to wallahi Allah kenan daga yau ban amince ka rinƙayiwa Mahmoud sanyiba tunda shi taurin kan rashin mutunci yake ji dashi ka zamar masa wuta, ka hana shi samun damar taɓaka.
Domin in ba ka tsaya ba muma wata rana sai ya zagemu”.
Ta ƙare maganar tana watsawa Mahmoud ɗin harara ganin zai fara ɗabi'artasa
Da sauri tace.
“Kada ka yarda ka matso kusa dani”.
Bai iya ɗaga kanshiba kuma bai fasa zuwa wurinta ba.
Gabanta ya durƙusa tamkar mai zaman tahiya ya riƙo baki mayafin jikinta.
Da sauri ta buge hannunsa cikin tafasar zuciya da bai taɓa ganin mahaifiyar tasu dashi ba, ta buge hannunsa tare da miƙewa tsaye tana nunashi da yatsa gami da faɗin.
“Kada ka yadda ka kuskura kayi ta bina kamar jela, tunda kai kafi ƙarfin bada haƙuri a rayuwarka yaro sai kace mai zuciyar ifirutu”.
Da sauri Aminullah yace.
“Dan Allah Ummi kada ki ƙarasa kiyiwa Allah da Manzonsa kada kiyi masa mugun baki, in kin masa bazan taɓa yafewa kainaba”.
Da sauri ta juya ta nufi kitchen dan so take tasha ruwan sanyi ko zataji sauƙin ƙunar da zuciyarta keyi.
Da sauri ya miƙe dafe da haɓarsa ya fara binta a baya.
Juyowa tayi tare da ƙara yarfa mishi wani marin.
“Ba cewa nayi ka daina bina ba”.
Cikin zubda ƙwalla Amina ta iso gabanta tare da durƙusawa cikin sanyi tace...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.