Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 52 of 86

Washe gari da safe Salim ne zaune gaban Abba suna shan tea Goggo Dada na gefe ita da Ummi.
“Yau zamu tafi tare Salim inje in kwana biyu kuma a can Goggo Dada ta faɗa. Da sauri Ummi tace. “Dan Allah ayi haƙuri, in kin tafi gidan ba daɗi wlh”.
Dariya sukayi jin Abba na faɗin. “Ina ga dai shima Lawan zan dawo dashi nan kusa damu kawai hankali zaifi kwanciya”. Salim ne ya ɗan gyara zama tare da cewa.
“Allah kuwa Abba haka zaifi daɗi dan muma muna son Goggo Dada a kusa”. Hafiz ne dake shigowa yace.
“A haka ma Uncle Sulaiman ke cewa in yayi aure wai zai ɗauketa”. Ummi tace.
“Shima ɗin ai ba inda zaije a part ɗin da aka gina wa Mahmoud kawai zai zauna, su in sunga dama randa suka gaji da zama a sama nan sa koma part ɗinsu Aminullah”. Salim dai sai murmushi yake tamkar zai haɗiye haƙori nai tunda Abba ya shaida mishi bashi izinin zuwa da bashi Number Salma da aka basa ji yake kamar anma ɗaura auren.

Bayan kwana biyu.
“Ni kam Ummi sai yaushe Uncle Mahmoud zai dawo ne, yaufa watanshi ɗaya cib da tafiya”. Tana gyara ganyen bisashshen yakuwan tace.
“Ni tun jiya ma banyi waya da shiba.” yana ɗan ture Zaitoon dake ta kaiwa Camera sa wawura yace.
“Yau da safe ma kafin in tafi school ya kirani video call yaga su Zaid yace wai Zaid ya rame yayi ta faɗa wai ba'a kula da shiko”.
Goggo Dada tace.
“Na san dai a satin nan kam zai dawo dan bai cika wuce wata ɗaya ba zuwa kwana arba'in”.
I ta kuwa Fariyda tana kitchen.

Washe gari da asuba bayan ta idar da sallan asuba dayin dukkan addu'a da tasbihanta kamar kullum ta fito dan wuce ƙasa wurinsu Ummi.

Da tsari taja ta tsaya a bakin ƙofar bedroom ɗin nata, numfashi ta shaƙa tare da lumshe idonta sabida wani irin ni'imtaccen ƙamshin daya bugi hancinta da sanyin Ac da ya ratsota tamkar anayi mata yayyafin dusar ƙanƙara.
A hankali ta buɗe idonta tare da fara ƙarewa parlour kallo, da mamaki ta ƙarasa fitowa daga ɗakin nata zuwa tsakiyar parlour da yake wani irin sheƙi da ƙyallin gyara da baza ƙamshi, sabbin labulayen da taga an canza an cire na da ɗin ne ya sata kallon Carpert ɗin da shima sabo akasa dashi da labulayen duk kusan fararene sai ɗan rasin ɗigo-ɗigon blue, da sauri ta kalli su kujerun tabbas sune amman kai kace basu bane an gogesu sai ƙyalli suke sai kuma su tv da tv stand da Centre table ɗin suma sai ƙyalli suke, Dinnin area ta juya da mmaki take kallon yadda yake ƙelli daga nesa sai ƙamshi da ko ina yake yi, kitchen ta leƙa shima fes.
Wancan corridor ta leƙa da sauri ta dawo da baya dan yau kuma mutane a kunne har yana ɗauke ido wani irin ƙyalli kawai yake yi, wani kyakkyawan mirror console table ne mai kyau a gefe, sai kuma ɗaya gefen wani babban durowane mai marfin transparent glass ido ta zuba a kai ganin jerin takalma ne a ƙalla zasu kai ƙafa 37 zuwa 40 ko wanne da layinsu gaba ɗaya sheƙi da ƙyalli sukeyi.
Da sauri ta bar wurin a fili tace.
"Mai girman kan tsiya da almabazzaranci ga takalma kamar na sayarwa da yake bai san zafin nema ba, sai kashewa ko ni mace takalma na basu wuce 23 ba, da 16 bags”.
Tsaki taja tare da buɗe ƙofar parlour ta fita tana buɗe ƙofar hanci dan shaƙar ƙamshi a kuntace tace. “Daga gani ya kusa dawowane ake yi masa wannan hidimar ba dole yayi faɗin raiba yana ganin ana masa abu kamar sarki sai wani nanna akayi dashi ana wani ji dashi masifa kamar barkono zafin rai kamar wuta”.
A haka ta shigo Parlour Ummi ta samu a kitchen É—in ita da Maman Samira.
“Yauwa yar al'barka zo ke kiyi aikin nan, kaina ke ciwo da zanyi da kaina”.
Tana ɗan rusunawa ta gaidata tare da amsar kifin da take miƙo mata guda biyune ma dai-dai ta basuyi ƙatti har can ba.
Ummu tace.
“Gasawa zakiyi sai ki ɗan haɗa chips yaji albasa kisa duk abinda ya dace, sai kiyi irin indomie nan da kika yiwa Abbanku jiya da dare dan yayi daɗi Abba yana ta yabawa”. Kai take gyaɗawa cikin girmamawa da jin gamsuwa dasu a matsayin iyaye tace. “Allah sauwaƙa Ummi kinsha maganin ko?”. Kai ta gyaɗa mata cikin jin dadin kulawarta garesu.
tare da kallon Samira tace.
“Ki soya mana doya kiyi mana da pepper soup ɗin jan nama”.
Fariyda tace. “ UmmieJeki kwanta ki huta”. Cikin farin ciki da dace da surka ta gari tace.
“Allah yayi miki al'barka Fariyda na”. Da Amin ta amsa tare da fara haɗawa kifin duk abin buƙatar gashin.
Sai kuma ta tafasa indomie leda uku.
Ta satseni tare da rufeshi ta maida gefe, ƙwai ta fasa guda biyar, tare da ɗauko kifi gongoni ta juye a ciki, da ɗan guntun diddigin nama ta watsa kana tasa ɗan jajjagen taruhu da albasa da ɗan maggi a leda ta ƙulleshi sannan ta sashi kan ruwan zafin data ɗaura tare da maida marfin ta rufe, jan nama ta ɗan ɗiba mai ɗan yawa ta yankashi ƙanana ƙana, tare da yi musu kekkyawan gashin tukuya mai ɗan kaurin romo.
Green pepper da carrot da albasa ta ɗan yayyanka mai ɗan dama, kwan da taga ya dahu ta sauƙe tare da yayyankawa ƙanana, sauran jajjagen ta ɗauka ta juye cikin ɗan man da tasa a tukunyar wanda tasa albasa mai ɗan yawa a ciki.
Lokacin ɗaya kitchen ɗin ya ɗauƙi ƙamshi, bayan ya soyu ne tasa ruwa ɗan kaɗan sannan ta ɗauko indomie nan ta juye a ciki batare da kwan da ta dafan da jan nama duk ta haɗa a ciki ta watsa su carrot da duk kayan ɗanɗanon, da sauri ta rufe tukunyar jin kifin nan yana baza ƙamshi na musamman.
Zaro shi tayi ta ajiye tare da É—an buÉ—ewa.
“Kai Masha Allah yayi kyau ga ƙamshi ga kuma daɗi”. Maman Samira ta faɗa tana kallon yadda kifin yayi lugun ya kwanta albasa da sauran kayan ƙawan suka rufeshi.
Chips É—in ma yayi dai-dai misali.
Da sauri ta ɗauko wormas ta shirya komai kana ta taya Maman Samira ƙarasa sauran aikin.

Ƙarfe takwas dai-dai suka gaba komai, ta shirya na Abba Goggo Dada data shigo yi musu sannu da aiki ta wuce dasu, da nata ita da Ummi, maman Samira ma ta wuce da nasu, ita kuma ta shirya wannan a dinnin table kamar yadda Goggo Dada tace mata tanayi tana tunanin to ba waye.
A cikin gidan kuwa tuni Samira ta gama gyara É—akunan da parlour komai yayi fes.
A parlour ta zauna da plate É—in guntun indomie da ya rage sai É—an chips É—in sai tea.
Anan tayi breakfast bayan ta gama ne ta miƙe ta koma kitchen da plate ɗin inda ta samu Samira ta wanke komai da sukayi amfani dashi.
Tukunya number 3 ta daura da ruwan a fili tace.
“Rice and Stew kawai zan mana da rana”. Sai kuma ta juya da sauri tabuɗe fridge tare da ciro tukunya number 2 wacce ke cike da miyan stew ɗin da yaji naman kaza, ɗuma miyar tayi kana ta ajiye gefe tana shirin wanke shinkafa Maman Samira ta shigo.
“Fariyda Ngd da taimakon aiki, jeki huta bari in ƙarasa”. Miƙa mata robar tayi tare da juyawa ta fita tana faɗin.
“Wata ƙil ma su Zaid sun farka”.
A parlour ta samu Ummi da Goggo Dada.
Gefen Ummi ta zauna tare da cewa.
“Ummi ya jikin”.
Ummi Tace. “Alhamdulillah da nayi bacci ya sake”.
Fariyda tace.
“Ga can abincin na gama yana kan dinnin”.
Kai ta ɗago da nufin yin magana sai kuma duk suka kalli ƙofar shiga.
A hankali yake tafiya riƙe da hannun Zaid da Zaitoon gefen hagu da damansa.
Yau jallabiya ce a jikinsa ba 3 quarter da sune mafi akasari kayan zaman gidansaba suma irin masu faÉ—in nan.
Goggo Dada tace.
"An ga juna kenan uba da yayansa”.
Cikinsa ya É—an shafa tare da cewa.
"Goggo Dada Yunwa”.
Dinnin ta nuna masa tace.
"An gama komai kai kaɗai ake jira kaci”.
Dannin area É—in ya ya nufa yana faÉ—in.
"Ummi sannu da aiki”.
Kai Ummi ta gyaÉ—a masa tana kallon Maman Samira dake cewa.
“Ah ah Mahmoud sauƙar yaushe?”.
Ummi ne tace.
“Ƙarfe biyu su sauƙo dole yasa Salim ɗaukosa kuwa kamar abin masifa”.
Yana ajiye su Zaid kan table É—in yace.
"Uhmmm Ummi to zama zanyi inyi gadin Airport ne”.
Ita dai tunda ya shigo da ta kauda kanta bata kuma ko kallon ta inda yake ba, watoma shi Ummi tasa tayiwa girki.
Shi kuwa Mahmoud ido ya zuba wa indomie, sai kuma ya kalli gashin kifin cikin nazari, maida marafen yayi ya rufe tare da juyowa ya kalli Ummi yace. “Ummi ba kece kikayi girkin nan ba”. Da sauri Goggo Dada tace.
“Nice nayi maka da kaina”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Goggo Dada wannan ba girkinki bane”. Cikin tsuƙe fuska Ummi tace.
“To koma waye yayi ai kai dai cine naka sai ka zauna kaci.”
Yana kallon su Zaid da suka maƙaleshi yana dauƙesu yace.
“Ni bazanci ba ya isheni”.
Da sauri Ummi tace saboda me.
Yana yamutsa fuska yace.
“Kawai bazancin girkin shirme jogogolen banen ba..............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.