Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 66 of 86

“No Abba ba haka bane, Abba bana son tuno rayuwar da nayi kafin wannan lokacin ne, shiyasa bana son yin mgnar da kowa, ba wai baka kai bane”.
Cikin sanyi Abba yace.
“Shiyasa ban cika son yi maka magnar ba, dan bana son fama maka ciwon zuciyarka, Amman ba komai shi Mumini da yarda da ƙaddara aka sanshi Allah kuma shi mai yafiyane, dan haka ka daina tuna baya”.
Cikin rumtse idanunsa tare da hakaito shekarun baya da sauri ya buɗe idon ya miƙewa tsaye yana motsa lips ɗinshi yana nanata.
“Astagafurllah Astagafurllah”. Jin haka ne yasa Abba sauƙe numfashi ya katse kiran.
Shi kuwa Mahmoud kai tsaye ya wuce room É—in su, key É—in É—akin da ya kamawo Fariyda ya É—auka tare da juyawa ya fita.
Ita kam Fariyda dake kan salla da ido ta bishi ganin wani irin yanayin da fuskarsa ta nuna.
Baki ta taɓe ta gyara zamanta ta fara karatun qur'an a wayarta.

Yana shiga ɗakin da shima yake gyare fes ansa komai na buƙatar a ciki.
Al'wala yayi tare da yin sallan la'asar da lokacin ta ya cika.
Sujjadar ƙarshene ya kafe goshinsa a ƙasa cike da ƙanƙan da kai ya rinƙa addu'o'i masu tarin yawa.
Koda ya idar jingina yayi da jikin gadon idonsa ya lumshe tare da motsa lips É—inshi a hankali yana istigfari.
A hankali ta gama kimtsa komai, bayan ta gama shirya yaran ta shirya cikin wani riga da wandon pallazo da suka É—ara na jiya kyau komai nasu fararene sai É—an zanen heart red collar.

Turo ƙofar ɗakin ya shigo Kanshi ya kauda gefe ya wucewa ciki, box ɗinsa ya ɗauka ya juyowa ya kalli Zaitoon dake miƙa masa hannun ɗaukar yayi ya ɗaura bisa saman trollingnsa sai kuma ya ɗauƙi Zaid ya tallabeshi a kafaɗa.
Juyawa yayi ya fita, yana kauda kai gefe jin tana cewa.
“Bazan iya fidda akwatin nan bafa”.
Bai kulata ba ya fice, da sauri tabi bayansa da hand lounge É—inta kawai.
A Reception É—in ta sameshi zaune.

Can gefenshi ta É—an zauna, tana zama taga É—an taxi É—in da ya kawosu jiya ya shigo.
Card ɗin ɗakin ta miƙa mishi jin Mahmoud nace masa ya dauko kayan nata amsa yayi ya nufi ɗakin nasu.
Jim kaÉ—an ya dawo, amsar card É—in yayi ya bawasu yasa hannun daga nan suka fita.

Ƙarfe huɗu dai-dai suna cikin Airport ɗin indara Gandhi international airport Mumbai.
Zaune suke a waiting Area.

Nigeria
Dariya mai cike da amo mara daÉ—in ji Mummunan mutumin da Mujahid ke zaune gamansa yayi tare da cewa.
“Ai aiki ya kammala komai ya tafi yadda ake so, shi dai da ita kam sai gani da ido”.
Ajiyan zuciya mai nauyi Mujahid ya sauƙe yace.
“Wata ƙil yanzu zan iya bacci, tunda naji hakan daga gare ka, kishin Fariyda da sonta yana hanani bacci, a duk sanda na tuna tana can tare da wannan yaron da surar jarumtansa kesa ni na mijima ganinsa a ingarman na miji bare mace, hankalina na tashi har nitsuwata na barin jikina in na tura surar halintan jikin Fariyda babu wani lafiyayyan ɗa na miji da zai kasance da ita a muhalli ɗaya ba tare da ya kwadaitu da kasancewa tare da ita ba, iya ƙamshin jinta in naji sai nayi wanka kafin inyi salla, ko lips ɗin inna gani ɗimaucewa nakeyi, ina sonta boka ina son kasancewa tare da ita a matsayin mata da miji na har abada”.
Cikin kaurara murya yace.
"Na gaya maka shifa yaron can baya bashi da damar kasancewa da mace har abada koda yana sonta, bare kuma baya sonta bazai taɓa kasancewa da ita a yadda kake zato ba dan yana da ƙaddarar da ta ruguza masa lafiya”.

Da mamaki yake kallon wayar Yah Amin É—in nasa dake hannunsa ido ya zuba wa number dake kiran wayar ganin number nan India ce.
Meda wayar yayi cikin aljuhun suit ɗin jikinsa ya miƙe ya nufi gate 3 jin ana shaida musu, passengers ɗin Ahmedabad subi nan.
A hankali ta miƙe tare da cewa Raihana da suke waya.
"Yanzu zamu tafi, sai mun sauƙa zan kira ki haɗani da Mamy”.
Kai ta É—an jinjina tace mata.
"Ina su Zaitoon ne ban gansu ba”.
Tana tsuke fuska tace.
“Gasu can wurinshi”. Murmushi Raihana tana faɗin.
"Ina son ganinsu”.
Kai ta É—an jinjina alamun tunani sai kuma tace.
"Ok bari inje wurinsu”.
Daga nan ta nufi inda yake tsaye saboda ɗan cunƙoson mutane kaɗan.
Da sauri ta ɗago Zaitoon ɗin data miƙo mata hannu alamun ta ɗagata.
Murmushi tayi lokacin da taga Raihana É—an hannunta ta É—aga tare da gwaranci.
Sa'ad ne tsaye a parlour kiran wayar yake tayi ba ƙauƙautawa, numfashi mai cike da zaƙuwar samu da rashin da yayi ne, na jin wayar na shiga kuma ba'a ɗagawa ne, yasa yaci gaba da kira cike da zaƙuwa, sai kuma yayi saurin zama jin kiran ya katse Mommy ya kira, bugu ɗaya ana biyu ta ɗauka, cikin sanyi da sauri yace.
"Mommy ina bukatar addu'arki, yau layin yana shiga, amman ba'a picking call ɗin nawa, Mommy ki sani a addu'a Allah yasa a ɗaga.”
Cikin jin dadi tace.
"In sha Allah kuwa Sa'ad zanyi maka, addu'a kuma zata ɗaga, yanzu ka bari sai bayan one hour sai ka kuma kira in sha Allah zata ɗaga”.
Cikin zaƙuwa da zafin so da ƙauna yace.
“Mommy zan iya kuwa?”.
Tana gyara zamanta tace.
“Yess Sa'ad zaka iya, yanzu ka katse kiran kayi karatun Alqur'ani ka roƙi Allah in har al'khairi ne Allah yasa yau ɗin nan ko gobe a amsa kiranka”.
Cikin gamsuwa yace.
"To Mommy amman dai a yau ba sai gobe ba, kar ki kai addu'a har gobe”.
Murmushi tayi tare da cewa.
"in sha Allah in dai ita al'khairi ce a gare ka a yau ɗin nan zuwa gobe za'a amsa kirana”.
Cikin sauri yace.
"Allah yasa haka”.
Amin tace tare da katse kiran.

Indara Gandhi international airport Mumbai.
A hankali take tafiya cikin takun dake nuna gogewarta da tsananin buÉ—ewar idonta fiye da baya, wasu irin masiyatan kayane da sukayi masifar matse dukkan suran jikinta, wani irin gashin ne maroon color baje a kafaÉ—unta.
Da sauri ta juyo gefen gate 3 ɗin daga can gate 2 da take tsaye, cikin wani irin sauri ta ɗanyi ƙasa da glass ɗin idonta.
Da sauri ta fito daga wurin tare da nufo inda suke tsaye.
Ta gefen Fariyda ta wuce har tana É—an tureta dan so take ta tabbatar shi É—in ne.
Wani irin tsalle tayi da ɗan ihu mai tafe da tsananin farin ciki mara misaltuwa tayi tare da faɗawa jikinsa tayi masa buƙatacciyar runguma mai cike da farin ciki.
Cikin mamaki Fariyda ta É—an ja da baya ta zuba musu ido.
Shi kuwa Mahmoud idonsa ya rumtse da masifan ƙarfi ba tare da ya rungumeta ba.
Sakeshi ta ɗanyi sai kuma ta ɗan kalli fuskarsa, cikin bege ta ƙara ware hannunta ta kuma rungumeshi da ƙarfi gami da faɗin.
“Papi i miss you so much.”
Sai kuma ta manna mishi kiss a kuncinsa tare da cusa hancinta a wuyansa, wani irin tsuma jikinta ya fara tamkar wacce ake watsawa dusan kankara.
Shi kuwa Mahmoud tunda ya rumtse idanunsa bai kuma buÉ—esu ba, sai yanzu da yaji ta manna lips É—in kan nashi.
Kanshi ya janye tare da watsa mata rikitattun idanunsa da suke fidda ruwan tashin hankali a ranshi ya kira sunanta da bazai manceba
“Idaya”.
Cikin sauri ta ƙara matsowa da nufin ƙara rungumarsa, sai kuma ta ɗan ja da baya tana kallon Zaid dake riƙe da hannunsa yana gwarancin faɗin.
“Appiy”.
Ido ta kuma maidawa kan Mahmoud ɗin tana karewa tsananin kamanninsu kallo sai ta kuma kalli Fariyda da ta zuba mata ido cikin fuskar nuna ƙyamarta dan uban gashin data kima a kanta.
Zaitoon ta kuma kalla cikin sanyi ta kalli Mahmoud ɗin da ya ɗago Zaid ya rungume sai kuma ya kalli Zaitoon dake miƙo masa hannu tana zamewa daga jikin Fariyda.
Amsarta yayi ya itama ya saɓata a kafaɗa tare da ratsawa gefe zai wuce.
Da sauri ta kuma shan gabansa ido cike da zafin begenshi da tuno mata ni'imar kasancewa tare dashi tace.
"Yaranka ne?”. Kai ya gyada mata tare da wucewa.
Da sauri ta kuma riƙo hannunsa tace.
“Papi Yaushe kayi aure? Dama ka samu lfy ne? Papi meyasa baka nemeni ba? Bayan kasan kai kaɗai ke iya samar min nitsuwar da nake buƙata a tare da namiji”.
Rumtse idanunsa yayi da ƙarfi tare da watsa mata rinannun idanun nasa da sukasa tayi saurin sake masa hannun.
Wani irin kallo mai wuyar fassarawa yayi mata kana ya ratsawa gefenta ya wuce, yana motsa lips É—inshi a hankali.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.