Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 86
Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.
Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.
Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA
Ita kuwa Fariyda cikin ƙara tsanar Mahmoud ɗin ta miƙe ta nufi part ɗin su Ummin.
A parlour ta same ta, tuni ta gama aikin breakfast ɗin Mahmoud ɗin ta shirya masa a kan table ɗin dake tsakiyar parlour ta kimtsa komai gwanin kyau.
“Yauwa Fariyda kin taso Aminullah ko”.
Tana mai faɗaɗa murmushinta tace.
“Eh Ummi yana zuwa”.
Cikin son matar ɗan nata tace.
“Madalla Allah yayi miki al'barka. Bari in je in duba Mahmoud kuma in tasosa, dan yau zamuje gidan Bappanku”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Nima zanje gida Baba Malam ya dawo Umrah jiya”.
Tana gyara mayafinta tace.
“Eh haka dai Abbanku yace min.
In kije ki gaidasa sai munzo. Amman Aminullah ne zai kaiki ko”.
Kai ta gyaɗa mata alamar eh ta ɗaura da cewa.
“Ai Baba Malam ya ƙwace key ɗin motana ya maidawa Yah Amin wai baya son inja mota”.
Kai Ummi ta jinjina tace.
“Ai nima ina tsoron kija mota, kinyi ƙanƙanta Fariyda kuma hannunki bai gama faɗawa ba, ki bari sai kin ƙara girma”.
Tana kallon Ummi cikin kwaɓe fuska tace.
“Ummi to sai yaushe zan girma?”. Murmushin mai sauti Ummin tayi tare da cewa. “Da saura kaɗan sai randa kika daina kuka in su Zaid na kuka”.
Daga nan ta fita tana murmushi ganin ƙuriciya da yarinta a fili a wurin Fariyda ita kuwa ala dole ta girma.
Bayan sun gama yin breakfast ne.
Ita da Aminullah suka nufi ƙofar ruwa gidansu Fariyda kenan.
Mahmoud kuwa da Ummi tudun Yola suka nufa gidan Bappa Lawan.
Zaune yake gaban ƙanin mahaifin nasu da kuma Ƙanwar mahaifin nasu Goggo Dada wacce suka bi bakin Aminullah duk suke kiranta Goggo Dada har yayunta da matansu.
Kanshi ta shafa cikin so da ƙaunar ɗan ɗan uwan nata tace.
Ai shekaran jiya da Abba yazo mu tafi, Lawan ne ya hana yace, in ina nan zaka fi zuwa da wuri”.
Kai ya ɗago yana kallon ƙanin mahaifin nasu da ya amshi zancen da cewa.
“Sam Mahmoud baya son zumunci, dan Aminullahi ya fishi son mutane, sai ayi kusan wata biyu uku baizo ba, sai in naje can yaita kame-kame Mamudu shi zumci ladansa nada yawa da falala mai tarin yawa kayi zumci domin ladanci na kai mutum cikin inuwar aljanna”.
Yana mai gyaɗa kai murya cike da gamsuwa da nasihar ƙanin mahaifin nasa yace.
“In sha Allah Baba zan ƙara”.
Murmushi dattijon yayi tare da cewa.
“Allah yayi muku al'barka”.
Amin suka amsa da sauri.
Murmushi Mama tayi tare da kallon Bappa Lawan dake cewa.
“A'a Jidda baki kawowa yayanki komai ba”.
Murmushi wacce aka kira da Jidda tayi tare da ɗan kallon gefen Mahmoud ɗin sai kuma tayi saurin kauda kanta ganin yadda ya kuma ƙara tsuƙe fuska.
Mama kuwa Ummi dake shan fura da nonon da akayi mata damun Yolawane ta kalla tare da cewa.
“Hmmm Alaji kenan kamar dai ka manta waye Mahmoud, mutumin da tun yana yaro baya cin abincin gidanan”.
Da sauri ya ɗan kalli Bappa Lawan jin yace.
“Wai Mahmoud har yanzu baka bar wannar ba hagor dabi'artaka ba?”.
Kai ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Afwan Baba yanzu nayi breakfast kafin mu fito shiyasa”.
Murmushi Mama tayi tare da cewa.
“Hmmm kai dai kam ai ko yunwa zata naɗema hanjine nasan ba ci zaka yi ba”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Eh to yau dai kam a ƙoshen yake, nasan da ko apple kam zai ɗan ci in yana jin yunwar to amman da zamu fito ne ya karya kin sanshi kuma shi da cin wani abun sai kuma gobe sai dai ko ta ko Custard shima sai dare”.
Salim dake gefenshi ne ya ɗan mari ƙeyarsa tare da cewa.
“Mama kin ganshi nan fa har yau bai taɓa cin abincin matar Yah Amin ba, wai a jogolgolene”.
Haram Salim ɗin yayi sai kuma suka kalli Goggo Dada dake cewa.
“Ai lamarin Mahmoud sai shi, in ba Umminsa ce tayi girki koni ko Amina ba bai ie bazai ciba, mutumin da ko spoons and fork ɗinsa da plate nasa a keɓe suke baya taɓa amfani dana wani, ko cup ɗin tea ɗinsa bai amfani dana kowa, inko wani yayi amfani dashi ya haƙura dashi kenan.
Aminullah ne kaɗai ke taɓa masa Abu ya iya sake amfani dashi, shima tunda yayi Aure in yaci abinci da spoon nashi baya kuma taɓashi sai yace mishi wai jeka na baka shi”.
Dariya sukayi baki ɗayansu shi kuwa.
Kai ya ɗan sosa tare da kallon.
Yah Ahmad wanda yake Sa'an Yah Amin ne.
“Hmmm Abu kamar al'ajanu”.
Da sauri Goggo Dada tace.
“Kuma wlh ko baya nan in dai an taɓa mai abinsa in ya dawo sai ya gane”.
Sai kuma duk suka kalli shi jin yadda ya ɗan ja gajeren tsaki.
Kai ya ɗan juyo ya kalli Salim tare da cewa.
“Muje ko”.
Da sauri Salim yace.
“Ina?”.
Yana miƙewa tsaye tare da ƙara tsuƙe fuska dan ganin kallon maitar da Jidda keyi masa yace.
“Ban saniba”.
Daga nan ya nufi waje, hakan ne yasa Salim binsa a baya...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.