Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 86
Tana shiga parlour yana biye da ita a baya.
Inda ta zauna ya durƙusa gefenta yana fuskantar mahaifin nasu da ƙanwarsa Goggo Dada
“Barka da safiya Abba”.
Ya faɗa cikin murya dake bayyana yana cikin damuwa.
“Ka tashi lfy Abbana?”.
Abba ya tambaya yana nazartar yanayinsa tare da gyara riƙon Zaid dake hannunsa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya gaida Goggo Dada ta amsa cikin kulawa.
Aminullah kuwa Zaitoon dake yiwa Mahmoud ɗin dariya ya miƙa mishi.
Amsarta yayi tare da rungumeta a jikinsa kana ya kalli yayan nasa dake faɗin.
“Yaya Mahmoud ina kwana”.
Kai ya ɗan sunkuyar tare da cewa.
“lfy”. Sai kuma ya kalli Ummi dake haɗa musu tea.
“Ummi ina kwana”.
Kai ta kauda tare da miƙa Abba da Goggo Dada cup ɗin tea da kuma bread ɗin alkama, juyawa ta kuma miƙawa Aminullah da normal bread ɗin,
amsa yayi tare da yin godiya,
Sai kuma ya gyara zama tare da fara shan tea ɗin.
A karo na uku ya kuma cewa.
“Ummi ina kwana”.
Ya ƙare maganar yana shaƙar ƙamshin turaren jikin Zaitoon dake maƙalewa a wuyansa.
Gyaran muryan da Abba yayi ne yasa duk suka maida kallonsu kansa cikin nagartacciyar murya yace.
“Koma menene Abbana yayi ya cancanci a yafe masa a amshi gaisuwarsa”.
Da sauri Goggo Dada tace. “Gsky dai kam dan Allah yana son masu yafiya”.
Cikin cikakkiyar biyayyar nagartattun mata ga maza su ta kalli Mahmoud ɗin tare da cewa. “Lfy”.
Sai kuma taci gaba da shan tea ɗin nata.
Shi kuwa Abba ido ya zuba mata ganin ta matsa shi kuwa Mahmoud ya ƙara matsowa inda take.
“Infa baka daina binaba zan watsa maka ruwa tea ɗin nan a fuskarka”.
Da sauri Abba yace.
“A gaban nawa? Wai ma me yayi ne da wannan fushi da hukuncin haka bana son haka Asma'u”.
Tana maiyin ƙasa da kanta tace.
“Kasan abinda yayi kuwa”.
Da sauri Aminullah yace.
“Please Ummi dan Allah kiyi haƙuri kada ki gayawa Abba kawai ki yafe masa tun jiyafa da safe yake ta binki akan abinda tsokanarsa akayi”.
Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Me yayi?”.
Tana ƙara matsawa tace.
“Raina Aminullah yayi har yake nunashi da yatsa”.
Numfashi mai sanyi Aminullah ya sauƙe jin ta sakaya mgnar domin yasan zuciyar Mahmoud gadon ta Abba yayi in ya fusata abin ba daɗi bare ace yaji Mahmoud ya zagi iyayen Fariyda ya kuma ce zai dake ta.”
"To ku yafe masa kuyi masa uzuri tunda da alamun Aminullah yayi tsokana ne tunda baison a faɗa min”.
Cikin kulawa Goggo Dada tace.
“Gskya dai kam anɗan tsokaneshi ne”
Cikin sanyi Aminullah yace.
“Ni kam Abba na yafe masa tun a lokacin ma”.
Kai ya jinjina kana ya zubawa Ummi ido jira yake yaji me zata ce.
“Na yafe maka Allah ya shirye ka yayi maka al'barka ya sassauta maka wanna zuciyar ya baka ikon iya buɗe baki ka bawa mutane haƙuri”.
Amin Abba da Yah Amin suka amsa, shi kuwa Mahmoud nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe sabida samun yafiya da al'barka mahaifiyarsa cikin sanyi murya yace.
“Nagode Ummi Abba Allah ya ƙara nisan kwana da lfy”.
Amin suka amsa a tare.
“To a haɗa masa shayin shima”.
Cewar Abba kai Ummi ta jinjina kana ta haɗa masa shayin.
Bayan sun gama shan shayin ne Abba ya gyara zama tare da fara yi musu nasiha da jan kunne akan zaman lfy da ƙaunar junansu ya ƙare da cewa.
“Inama zuriyar tamu take da yawan da zamu ce zamuyi faɗa da juna.
Kuna ganin kamar rabon yaya uku uku Allah ya ƙaddara mana a zuriyar.
Kunga dai mu uku rak iyayenmu suka haifa ni da Goggo Dada sai bappa Lawan ɗinku,
Kunga ni ma ɗin ukun Allah ya barmi itama Goggo Dada ukun ta samu gashi daya nema ya rayun mata Sulaiman, shima Lawan ɗin ukun gareshi gashi Amina ma ukun rak ta haifa, ga Ahmad ma ukun ya haifa.
A haka ina mukaga yawan da zamu yi faɗa da juna har muyi gaba ko riƙo.
Dan Allah ko bayan raina ku riƙe juna ku zama tsintsiya ma ɗaurinki ɗaya”.
Cikin sanyin murya Mahmoud ya ɗan motsa lips ɗinshi a hankali yace.
“Hakama wani kam bazai samu ko ɗaya bama.
Amman Alhamdulillah hakama mun godewa Allah, Allah yasa Yah Amin ya haifa mana da yawa”.
Da sauri Goggo Dada ta miƙe tabbar parlour dan ta san kanta da saurin hawaye.
Aminullah kuwa cikin sanyin murya yace.
“In sha Allah ma ni shida zan samar mana Mahmoud yanzu su Zaid nakane in na sake samun na uku nakane ko suna ma da nake suke Amfani tun yanzu, ni kuma in sha Allah zamu kuma samun wasu uku koma shida ko tara ma, mu haifi dozin”.
Cikin sanyi yace.
“Ai dama kaine baka samuba Yah Amin ni kam ko yanzu na mutu gasu Zaid Allah ya bani”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Bazama ka mutuba in sha sai ka bawa yaranka tarbiyya wata rana Zaid ya maka abinda kai min jiya kaji ya akeji”.
Kanshi Abba ya shafa jin yana faɗin ban mutu bama ai bazaku samu faɗin zuriya ta wurinaba Unmi”.
A hankali Abba ya fara shafa kansa tare dasa mishi albarka dayi mishi kalamai masu taushi.
Hakama Ummi tuni ta mance da fushin da take yi dashi.
Ta miƙe tare da cewa.
“Bari inje in haɗa ma breakfast Abban Abba me kakeso”.
Yana ɗan miƙewa tsaye yace.
“No Ummi inada abinda zanci ki huta, kin manta Maman Hafiz ta hutar dake na kwana biyu”.
Ya ƙare maganar yana fita ya haura sama, kai tsaye bedroom nasa ya wuce.
Ranar
Laraba misalin ƙarfe 8:12 pm kusan a tare suka shigo Aminullah na gaba yana riƙe da hannun Mahmoud ɗin na biye dashi a baya.
Tun da abun nan ya faru bata kuma ganinsa ba sai yanzu.
Wani irin kallon dake bayyana tsananin tsana ya watsa mata da ita da parlour nasu gaba ɗaya.
Raban da ya shigo part ɗinsu tun bayan aurensu da wata ɗaya rak da ta fara gaya mishi mgnar dashi ya fara assasa gaba a tsakaninsu.
Ko da akayi mata CS aka cire su Zaid ma ko kallo bata ishesa ba, yaran kawai yasa aka kawo mishi parlour Ummi daga nan a hannunsa suke wuni sai da akayi suna da ya tafi Dubai bai dawoba har taje wankan gida ta dawo.
Sama ya wuce dashi.
Ita kuwa Fariyda fuska ta tsuke tare da wucewa ɗakinta bayan ta maida ƙofar corridorn data buɗe musu suka haura saman.
bakin gadonsa ya ajiyesa tare da zamewa ya zauna a ƙasa kan carpert sai kuma ya ja bid side drawer dake gefenshi.
Wasu files ya fita kusan guda goma.
Sai kuma ya juyo masa da laptop ɗinsa dake kan gadon da alamun tun yamma aiki yake yi.
Woyoyinsa ya miƙa masa cikin sanyi yace.
“Buɗe wayar nan”.
Ya ƙare maganar yana miƙa masa Samsung Galaxy da suke dukkan harkar social media dashi.
“Me pin ɗin”.
“1996”.
Da sauri ya ɗan kallesa fahimtar shekar haihuwarsa ya saka a matsayin number sirrin.
Dannawa yayi tare da buɗewa.
Kana ya miƙo mishi iPhone 16 ɗinsa itama shine dai code ɗin budeshi.
Laptop nashima shine sai harafin MBZ da ya saka.
“Me MBZ?”.
Yana bubbuɗe files ɗin gabansa yace.
“Mahmoud Baban Zaid da Zaitoon”.
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi tare da cewa.
Na ukun in namijine Zayyat za'a saka masa”.
Numfashi mai sanyi Aminullah ya fesar ganin Murmushin ƙanin nasa sai kuma ya ɗaura da cewa.
“Duk yadda kake so haka za'ayi.
Yanzu dai so nake in nuna maka komai, dan zan bar maka aikin kafin in dawo”.
Daga nan ya fara nuna mishi komai na harkar business nasu dake a waya.
Sai kuma ya jawo Files duk ya fara yi masa bayani a kan ko wanne da kuma aikinsa.
A ƙalla awa biyu yana masa bayanai cikin sauƙe numfashi yace.
“Kai Yah Amin I salute you hsky aikin nan ba sauƙi”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ai bari ma mu dawo nan. Kalli jerin jadawalin kayan da Gombe, Zamfara, Logos, Kaduna, Taraba, da Borno.
Yanzu sarin nan da zamu tafi ƙarfin buƙatar nasune.
Sosai Mall ɗinmu suka ɗanyi ƙasa ba kaya.
More Especially kayan shimfinɗin gado da carperts labulaye da sallayu da kuma abayoyi da riguna da wandon sun nan.
Sai takalmansu dan ana son kayansu sosai.
Daga can ma za wuce Egypt don akwai sabbin abayoyin da masu sarinmu na online suke buƙata”.
Numfashi mai ɗan tsawo ya fesar tare da cewa.
“Ni wannan lissafin duk na menene”.
Yana ƙara nuna mishi dukkan shige da fice da dukkan motsin dake duk cikin kasuwancin nasu yace.
“Hmmm to in ban gaya makaba ta yaya zaka san matakin takawa”.
Kai ya ɗan jujjuya dan wuyansa da yayi tsami cikin komawa baya ya kwanta kan gadon yayan nasa tare da cewa.
“Ai bazan taɓa iya abinda ka iyaba Yah Amin, kuma ma ai wannan aikin kane”.
Ya ƙare maganar tare da lumshe idanunsa.
Shi kuwa Aminullah miƙa ya ɗanyi tare da haɗa files ɗin da duk ya gama mai bayanin komai ya maida ma'adanarsu sannan ya juyo gareshi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.