Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 40 of 86
Washe gari da safe misalin ƙarfe 01:Am, dursheshe take gaban Abba ta zo gaidashi a parlour sa kamar yadda ta saba tun da can baya.
“Ya hannun naki”.
Tana sauƙe Zaid dake zamewa daga jikinta tace.
“Alhamdulillah da sauƙi sosai”.
Ummi ya kalla tare da cewa.
"A ƙara kula da hannun nan da kyau fa”.
Ummi tace.
“In sha Allah kuwa”.
Sai kuma duk suka kalli Zaid ɗin daya miƙe tsawonsa ya fuskanci kakan nasa ga mamakinsu kawai sai gashi yana tafiya ɗingis-ɗingis.
Cikin tsananin jin dadi Abba ya ware mishi hannu tare da cewa.
“A'a ikon Allah Fariyda ashe sun fara tafiya?”.
Cike da mmki take kallon yadda yake tafiyar tare da girgiza kai tace.
"Abba yanzu ya fara”.
Da sauri ya abka jikin Abba tare da fashewa da dariya ganin suma duk suna dariya.
Cikin farin ciki Ummi tace.
"Ikon Allah wato giji lahira sun dawo shekaran jiya yau ya fara tafiya.
Ta ƙare maganar tare da kallon Fariyda da duk da murmushin da take yi da ka ganta kasan tana da damu a ranta.
Miƙewa tayi tana faɗin
“Abba a huta lfy”.
“Amin ya Allah Fariyda Allah yayi miki al'barka”.
Amin ta amsa tare da fitowa.
Ummi kuwa da sauri ta kuma tsayada Zaid tare da cewa.
"Zo zo zo mana”.
Ai kuwa ya balgace baki tare da fara taku.
Cikin sauri ta rungumoshi tabi bayan Fariyda.
A parlour ta samesu zaune.
Fariyda, Goggo Dada, Hafiz, Maman Samira, sai Zaitoon dake ta wasa a tsakiyarsu tana juyi.
A tsakiyar ta ajiyeta cikin farin ciki tace.
“Zaid ya fara tafiya”.
Da sauri suka haɗa baki wurin cewa.
“Yaushe?”.
Baya ta ɗan matsa nesa dashi kaɗan tare da cewa.
“Yanzu nan bari ku gani, Zaid zo zo nan maza taho”.
Ai kuwa sai duk suka fashe da dariya.
Samira da Hafiz harda tafinsu da shewa.
Goggo Dada tace.
“Iyeh Zaid anci girma wato ala dole dai sai ka nunawa Zaitoon fikon yan mintunan dake tsakaninku kennan”.
Sai kuma duk suka fashe da sabuwar dariyar kamo Zaitoon tayi ta tsaida tare da cewa.
“Ke ƙawas kalli ɗan uwanki ya fara tafiya ya barki a baya. Maza kema taho”.
Ido ta fara raba musu, sai kuma kawai ta fara tafa yan hannayenta tana ɗan ɗigirgira ƴan sawunta ganin yadda suke ta dariya.
Ido ta maida kan Zaid da Hafiz ya juyosa gabansa tare da cewa.
“Kai dakata kada ka riga my princess tafiya”.
Ya ƙare maganar tare da fidda wayarsa ya fara yi musu video.
Sai kuma duk suka zuba wa Zaitoon ɗin ido ganin yadda ta daddaƙe ta ɗaga ƙafarta ta dama tare da yin ƙara gami da tafi ƙarfi ta ɗaga ƙafar.
Ya Salam dukkansu suka faɗa a tare.
Da sauri Salim dake gefenshi ya buɗe ƙofar sabida yadda suke jiyosu ta window dake corridor ɗin ta upstairs yake.
Kusan a tare suka shigo parlour da sallama a bakin Salim.
“Yah Salam Our Uncle zo zo ku gani Zaitoon ta fara tafiya daga ganin Zaid yanayi”.
Hafiz ya faɗa tare da matsawa gefe ta yadda su Mahmoud zasu hango yaran.
Da sauri Salim ya nufesu tare da kiransu ai kuwa hankalinsu ya dawo kansu nan suka fara tattakawa da irin ci da zuciyan masu sabbin ƙafa dan so suke su isa wurin Mahmoud ɗin, da shi kuwa ido ya zuba wa Umminsa da Goggo Dada ganin yadda suke dariya cike da farin cikin da tun kafin rasuwar Yah Amin rabon da ya gansu suna cikin happy haka.
Idonshi ya juyo kan su Hafiz Salim Samira yadda suke ta dariya parlour baki ɗaya cike da farin ciki.
Idonsa ya lumshe cike da gamsuwar tabbas yaran nan sune cikon farin ciki da walwalar gidan gashi daga dawowarsu har murmushi da dariyar su Ummi ya dawo.
Miƙewa tsaye tayi tare da amsa kiran da Aunty Saddiqa tayi mata, ɗakin Goggo Dada ta wuce.
Tana shiga ne taji duk sun kuma dariya harda tafi Hafiz na faɗin.
“Yesss my princess har ta wuce shi ma”.
Juyowa tana kallon Salim da suka wuce shi suka nufi Mahmoud ɗin da sauri yayi ƙasa tare da ware musu hannunsa ai kuwa a tare suka abka jikinsa.
“Ƙiuya sukeyi ne?” Salim ya tambaya yana shafa kan Zaitoon da Mahmoud ɗin ya miƙe tsawonsa dasu.
Hafiz yace.
“Ai ko mamansu basa kulata in Uncle Mahmoud yana nan”.
Wani irin kallon tsana tabi fuskar Mahmoud ɗin tare da shiga bedroom ɗin tana mgnar zuci.
“Mugu mai fuskar shanu, kowa na dariya da farin ciki amman shi ba alamar murmushi ma tare dashi bare dariya.”
Da sauri ta kalli wayar tata jin Aunty Saddiqa na cewa.
“Hmmm Mijin naki kike faɗawa haka Fariyda dan bakya tsoron Allah ya ƙonaki”.
Da sauri tace.
“Ai wlh in dai Allah bai ƙonashi shiba, in sha Allah ni kam zan tsira, in ban kirashi muguba dame zan kirasa”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“To ke bakya yafiya ne, da mantuwa ba dai hannun ya warkeba”.
Kai ta jinjina ido cike da ƙwalla tace.
“Ai har abadan bazan yafe masa ba Aunty Saddiqa.
A gaban iyayenafa ya matse min hannun ya murɗa ya targaɗani dan kawai yaga an kaini wurinsa a banza kamar mara gata a duniya. In Banda mugu mai baƙar zuciya wa zaiyi haka, ai ko mutuwa tana kunyar idon iyaye”.
Cikin sanyi tace.
“Kiyi haƙuri Fariyda komai da kika gani na rayuwa mugaddari ne min inɗinllah, baki san me Allah ya ɓoye tsaka ninku ba”.
Cikin sauri tace.
“Ba komai sai rabuwa, dan wlh ni dai har gaban abadan bazan taɓa zama dashi ba, gwara in tabbata ba aure da in zauna dashi.”
A can parlour kuwa shafa kansu yake yi tare da kissing goshinsu cikin tsananin farin ciki, sai dai da fara'a ba yawane da ita a fuskarsaba murmushi.
Sai su yaran da suke ta zagayeshi suna dariya.
Washe gari da safe. Jidda ce durƙushe gaban Mamanta kuka takeyi da magiyar da tasa jikin Mama yin sanyi da fara kitsima yadda zata cika burin ƴar tata.
“Dan Allah Mama da tsarkin Alqur'ani ki gayawa Baba wlh ina son Yah Mahmoud, kinga tun da nake faɗa miki da kin gaya masa da yanzu ba'a aura masa wannan mayyar yarinyar nan ba, kika ƙi faɗi na roƙeki yanzu dai ki gayawa Baba wlh naji na gani ko a ta biyu zanje gidansa, ni ina sonsa kuma zan riƙe su Zaid tsakani da Allah, ita da bata sonshi ma”.
Kanta Mama ta shafa tare da cewa.
“Ba komai Jidda yi haƙuri in sha Allah sai kin samu biyar buƙatar burinki na auren Mahmoud...
Murmushin da yasata zubda ƙwallan farin ciki tayi tare da rungume mahaifiyar tata.
Yau sati biyu kenan cib da dawowar Fariyda gidan Alhamdulillah kuma sosai tafiyar su Zaid ya fara nuna yaran sun sake sosai har wata ƙiba sukayi wuni sukeyi zagaye parlour zuwa dinnin area side Abba har kitchen zuwa sukeyi, farin ciki kuma ya samu damar dawowa zuƙatan Ummi, Goggo Dada, Abba, Hafiz, Samira, Maman Samira ita kanta Fariyda jinta take sakayau kaso 80/100 ma damuwarta ya gushe, gani tayi kamar zaman Aminullah take yi kamar tafiya yayi, tunda ko mgna bata taɓa haɗata da Mahmoud ba wani zubinma sai tayi kwana biyar bata ganshi ba su Ummi kuwa suna matuƙar kula da ita da yaranta har ita kanta ta fara maida ƴar ƙibarta, shi kuwa Mahmoud har ranshi ma ya mance da batun auren wata Fariyda.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.