Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 70 of 86

Kallonsa yake yi cike da maida dukkan hankalinsa kan tv kwanciya yayi yana ware duvet É—in ya shiga ciki, a haka bacci yayi awon gaba dashi.
Washe gari da yamma zaune suke a Office ɗin Dr Imran Patel, Zaid na kan ɗan baby bed dake office ɗin nasa, ya tuɓeshi zir, a hankali yake ɗan latsa kasan mararsa har zuwa saman kan cikinsa, ɗaya Dr dake gefensa ne yayi saurin sa hannunsa ya danne inda yagga Dr Imran Patel ɗin ya cire yatsarsan, wani irin gigitaccen ihu Zaid ɗin ya sake da karfi.
Wanda hakan yasa Mahmoud saurin miƙewa tsaye ya nufi wurinsu.
Kai Dr Imran ya jinjina cikin gamsuwa ya kuma fara bin wurin yana latsawa yadda yake dannawa haka Zaid É—in ke kuka.
Da sauri ya É—agoshi sama ya É—an cillashi kana ya manna fuskarsa kan cikin Zaid É—in iska ya É—an hura mishi tare da fara jijjigashi.
Ajiyan zuciya Mahmoud ɗin ya sauƙe ganin Zaid ɗin yayi shiru.
Da sauri ya juyoshi gaban Mahmoud É—in kana ya nuna mishi gaban Zaid É—in dake tashe.
Zagayawa yayi ya zauna tare da fara mishi bayanin tasirin ciwon ya É—aura da cewa yanzu zasu tafi dashi gwaji su É—an jirasu a anan.
yace, a a sai dai su tafi tare.
Kai Dr Imran Patel ɗin ya jinjina yana miƙewa tsaye ya ce masa su tafi.
Ita kuwa Fariyda Zaitoon dake zaune kan table É—in sa tana wasa da tarkacen yara dake kai ta É—aga zata bisu yace.
Tai haƙuri yanzu zasu dawo.
Wani side na musamman dake cikin asibitin suka nufa, duk wani gwajin da bincike duk sunyiwa Zaid a ƙalla 3 hours sukayi kafin suka shigo a tare.
Da wata nurses biye dasu a baya da leden Pharmacy É—insu a hannunta.
Gyara zama tayi da gyara riƙon wayar da takeyi tace. “Afwan Yah Mujahid zamuyi mgna anjima”. Kai ta ɗan langoɓar cikin tausasa murya tace.
"Afwan Zaid zan duba, ina gamawa zan kiraka”. Sai kuma ta ɗanyi shiru na ƴan seconds a hankali tace.
“To Yah Mujahid”. miƙewa tayi tare da kallon Mahmoud ɗin da ya juya zai fita da ledan magun gunan, Zaitoon da Dr Imran ke shafa kanta tare da mata wasa ta ɗauka kana taɓi bayansa.
Ummi da Goggo Dada zaune gaban Abba dake musu bayanin.
“Yanzu mukayi waya da Mahmoud yace, yau sunje sunga Dr kuma sunyi duk abinda ya dace, Alhamdulillah ciwon bai rigada ya gama cin lfyarsa ba, sai dai sun tabbatar da dole ayi masa aiki, dan in ba'ayi aikinba zai shafi lafiyar mazantakarsa. Sun basu magungunan da zai sha na kwana goma, kafin ayi masa aiki.”
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Allah yasa a dace”.
Amin Goggo Dada ta amsa tana kallon Hafiz da tun safe da ya tafi school bai dawoba sai yanzu.
Aunty Amina ce zaune a parlournta tare da Salim da Salma da ya kawo ta duba kayan lefen da aka haɗa, in akwai abinda take buƙatar ƙari ko sauyi a cikin kayan ya tambaya cikin kulawa bayan duk ya bubbuɗe mata komai.
Murmushi tayi cike da jin gamsuwar nagartar kayan tace.
“Komai yayi ba buƙatar ƙari ko sauyi Allah ya ƙara buɗi”. Aunty Amina tace.
“Masha Allah Salman Salim, kayi dace da mace mai godiyar Allah duk da baki ga su bra and pants ba kikace ba bukatar ƙarin komai”.
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta tare da miƙewa ta fita.
Cikin dariya Amina tace.
“Haka fa Fariyda ba yadda ba'ayi da itaba ta faɗi size ɗin ta, fir taƙi ƙarshe haka dai akasa mata yassara”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Itanma taƙi faɗi sai asa matayassaran”.
Washe gari da safe wuraren tara zuwa goma, kamar kullum wanka tayi musu, ta shiryasu ta basu Chivita da taga yasa an kawo katon biyu.

Zaitoon ce ta nufi parlour, da sauri ta ƙarasa cikin saboda hangoshi zaune a dinnin table, ganinta ne yasashi miƙewa dan ya kamalla yin breakfast nashi, ɗan rage tsawonsa yayi ya buɗe mata hannu, a tare suka iso jikinsa ita da Zaid daya biyota a baya, hadesu yayi ya rungume ya miƙe tsaye dasu, yana sumbatar kumatunsu, a kan Centre table ya ajiyesu, ya jawo shi gaban kujerar da ya zauna, ledan magungunan Zaid ya jawo daga cikin drawer Centre table ɗin, buɗewa yayi ya fara bawa Zaid, fuska ya kwaɓe jin mgna a bakinsa, iska ya hura masa kan fuskarsa hakan yasa ya haɗiye mgnanin, na biyu ya kuma bashi yana ɗan tallaɓe da kanshi saida ya haɗiye, kana ya sa mishi na ukun da yaƙe kwaya ne, a ƙasan harshensa ya manna masa.
Da sauri ya kamo hannun Zaitoon dake ƙoƙarin buɗe kwalban maganin da ya rufe ɗin.
Tattare su yayi ya daure ya maidasu wurin zamansu.
Dai-dai lokacin ta fito, Dinnin table ɗin ta nufa, ganin Tray da plate a rufe ne yasata, buɗewa, sunkuyowa ta ƙarayi tana kallon sev puri dan kamar wainace, taɓawa tayi da fork ɗin da yake gefe bowl ɗin ta buɗe bisa alamu da miyar ganye yaci wainar sev puri ɗin su da ta ɗan banbanta kaɗan da tamu wainar, ɗaya bowl ɗin kuma pasta ne yaci a ciki, sai cups ɗin tea biyu na gado.
Wainar kwaya uku rak ya rage, a hankali ta guzura, zata kai baki taji yace.
“Karki yadda kici min sauran abuna”.
Da sauri ta ajiye fork ɗin tare da zama kan kujerar dinnin table ɗin, manu, ɗin Restaurant ɗin kitchen hotel ɗin dake kan table ɗin ta jawo tare da fara buɗewa dan zaɓar abinda zatace su kawo mata, tanayi tana faɗin.
"Taya zanci ragowar najasa dama can ni ba ci zanyi ba”.
Kanta ya zo ya tsaya tare da cewa.
"Me kika ce?”. Dan bai jita da kyau ba, ya dai ji Najasa da tace, ido ta ɗan ɗago ta kalleshi sai kuma tace.
"Ni dama bana cin sauran wani”.
Juyawa yayi jikin washing hand baby É—in dake wurin yana wanke marafen maganin da ya bawa Zaid tare da cewa.
"Da kikace baki da kunya ai da kin maimaita”.
Ko ƙala bata ce ba, shi kuma wurin su Zaid ya koma.
Bayan sallan isha turare take fesa musu a jikinsu bayan ta gama yi musu shirin bacci, Zaitoon dake riƙe da wayarta ta kalla tare da miƙa hannun.
“Bani waya ta nan, muje ku kwanta”. Da sauri ta ƙara rarrafawa tayi can kan gadon tana ɓoye wayar a bayanta, Zaid dake kwance a bayanta ne ya miƙa hannun ya amshi wayar, da sauri ta juyo itama ta karɓi wayar tare da zama tana mishi alamun shima ya zauna.
Numfashi ta sauƙe jin alamun kasala na rufeta dan yau tun safe data tashi bata kumayin bacci ba, wuni tayi a bedroom ɗin waya dasu Aunty Saddiqa da Salma dake bata labarin kaya lefen Salma.
Juyawa tayi ta shiga bathroom.
Bayan ta fitone ta murje jikinta da mai da turarukanta masu sanyin ƙamshi.
Tanayi tana kallon Zaid dake riƙe da waya, dan tuni Zaitoon tayi bacci.
Wata tattausar riga da wando na bacci Pink collar ta zura a jikinta bayan tasa pant kaÉ—ai.
Ƙirjinta ta kalla ta mirror ɗin ganin yadda suke tsaye cur sun cika pam dan tun a jirgi bata kuma bawa su Zaid ba kuma suma basu nemaba gefen gefen ƙirjinta ta kalla da suke ɗan bayyane dan rigar mai ɗan siririn hannune, juyowa tayi tana mai gyara gashin kanta da take lissafin yau kwana takwas kenan da gyara shi, dan yau kwanakinsu biyar cib a Ahmedabad Alhamdulillah yaye dai ya tabbata ta faɗa a zuciyarta.
Da sauri ta juyo ganin Zaid ya miƙe tsaye da wayar a hannunsa yana miƙa mata, kan ta ƙarasa wurin kuwa ya cilla wayar ƙasa.
Cikin sauri ta É—auki wayar sai kuma ta juyo ta kalleshi cikin takaici ta buga mishi tsawa tare da kai mishi mari a fuska tana faÉ—in.
"Wannan ɗin ma ka fasa min ita hankalinka ya kwanta k”. Bata kai ƙarshen mgnar ba, tayi shiru tare da tsaiwa tana kallonsa sabida yadda ya saki wani irin firgitaccen kuka tare da callara sautinsa da ƙarfi.
Da sauri ta juyo bayanta jin ya turo ƙofar ya shigo yana faɗin.
“Me ya sameshi”. Shiru tayi cike da takaicin sangarcin Zaid ɗin tsawa ya kumayi mata yana jijjigashi yace.
"Me ya sameshi”. A kufule tace, wayata ya fasa minfa wai dan na mishi”. Katse ta yayi da cewa. “Akan wannan banzar wayar ne zaki dakeshi a banza, ke ko tausayinsa bakya ji yaron da lfya ma bata ishesa ba dan baki da imani sai ki dakesa”.
Ya ƙare maganar yanayi mata wani irin kallon takaici tare da juyawa ya bar ɗakin.
Akan kirjinsa ya kwantar dashi tare da ja musu duvet ɗin ya rufeshi har kanshi shi kuwa iya ƙirjinsa.
A haka suka kwana har sai da Asuba daya tashi ƙarfe huɗu saura ne, ya miƙe rungume dashi.
Kamar kullum a hankali ya tura ƙofar ya shiga, bakin gadon ya nufa a hankali ya kwantar dashi kusa da Zaitoon ɗin bisa gadonsu.
Miƙa yayi ys shige bathroom.
Sautin rufe ƙofar ne yasa Fariyda da fitsari ya tada ita ɗan juyowa.
Numfashi mai nauyi ta sauƙe tare da maida kai ta kwanta tana matse cibiyoyinta, juyawa tayi daga gefen hagun zuwa dama duk jikinta na cikin duvet sai iya kanta ke waje.
A hankali ya fito daga bathroom É—in sanye da bathrobe kayan bacci da ya cire ya jefa cikin Wordrobe kana ya juyo a hankali da alamun baya son taji motsinsa ne bare tasan ya shigo.
Juyowar da yayine yasata saurin rumtse idonta da ƙarfi tare da jan nannauyan numfashi sai kuma tayi saurin yaye duvet ɗin ta ture gefe ya miƙe tsaye da sauri dan jin fitsarin na............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.