Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 20 of 86
Da sauri Abba ya fara kutsawa sakaninsu jin muryar Aminullah ɗin can ƙasa cikin rauni yake ta maimaita.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun. Dr zan mutu ku kira min Abbana da ɗan uwana.
Ahmad ka kira min Æ´an uwana, Ahmad ina Abbana ina Mahmoud?â€.
Sai kuma ya ƙare maganar murya can ƙasa tare da fara fizgar numfashi.
Da sauri Abba ya isa kansa da sauri ya runtse idanunsa cikin tsananin bugawar zuciya da tashin hankalin da yasa jikinsa fara wani irin karkarawa ganin yadda gaba É—aya kamannin Aminullah É—in ya sauya.
Gaba ɗaya ya karairaye hatta haƙarƙarinsa suna a karye ga kansa dake zubda jini wanda shine Doctors ɗin ke ta fafutukan tsaidawa amman abin yaci tura.
A hankali murya can ƙasa yace.
“Alhamdulillah Abba ina Ummi na ina Mahmoud, Abba Fariyda Abba ku yafe minâ€.
Sai kuma yayi shiru tare da lumshe idanunsa da sukayi fari fat.
Numfashi ya fara fizga da ƙarfi.
Ganin haka ne yasa Ahmad yin sauri ya nufi waye.
A jikin ginin ya kife kansa tare da fara wani irin tsuma.
Ummi kuwa da sauri ta isa bakin tab É—in dake wurin
Al'wala tayi tare da zare É—an kwalinta ta shimfiÉ—a a barandar wurin.
Salla ta kabbarta duk da tsananin rawan da jikinta keyi.
Goggo Dada kuwa da sauri ta isa gaban Bappa Lawan da yanzu ya iso kenan.
A can cikin kuwa da sauri Abba ya ƙara yin ƙasa da kanshi har yana manna kunnensa kan lips ɗin Aminullah ɗin saboda yadda muryarsa tayi ƙasa ainun gashi ta cika da raunin kareyar numfashi.
Kai ya rinƙa jinjinawa yana mai maimaita innalillahi wa innalillahi rajiun, yana jin kalaman da ɗan nashi yake faɗa mishi kalaman da suke sa yakejin tamkar ana zare ƙasusuwan jikinsa.
Can kuma sai yaji muryar ta ƙara yin ƙasa da sauri ya ɗago kansa ya kalli yadda yake yi.
Doctors É—in Kuma cikin zafin nama suka dawo dai-dai kan kirjinsa.
A hankali ya sake hannun Abban nasu yana faÉ—in.
“Abba ina Mahmoooouudâ€.
Dai-dai lokacin Bappa Lawan da Ahmad suka shigo ciki.
Ganin sune yasa Abba yin sauri ya fita ya bar É—akin.
Shin kuwa Bappa Lawan da sauri ya riƙo hannunsa yana faɗin.
“La ilaha'illaha Muhammadurrasurillah S.A.Wâ€.
A hankali murya can ƙasa yace.
Sallalahu alaihi Wasallamaâ€.
Cikin dakiya da karfin zuciyar maza Bappa Lawan yaci gaba dayi masa kalmar shahada tun yanayi har yayi shiru sai idonsa dake buÉ—e.
A can wajen kuwa da sauri Ummi tayi sallama ganin yadda Mahmoud ya shigo asibitin cikin wani irin driving na fitar hayyaci.
Ganin Abba ya nufotane yasa tayi saurin isa inda yake tsaye gefen Goggo Dada dake kuka tana faÉ—in.
“Yah ya Aminullah É—in?â€.
Yana mai kauda kai daga kallon Ummi da tausayinta ya kamashi yace. “Ba komai, ai akwai Allah kuma, ya fimu son Aminullah.
Asma'u kiyi masa addu'a ki yafe masaâ€.
Dai-dai lokacin Mahmoud É—in ya iso wurinsu jin kalaman da Abba keyine ya sashi harbawa a guje ya nufi ciki.
Yana shiga Ahmad yayi saurin tareshi.
Da ƙarfi ya ture Ahmad ɗin. Ya kutsa tsakanin likitoci da suke ta ƙoƙarin ceto numfashinsa dake yanke wa.
Da sauri ya sunkuya kanshi tare da riƙo hannunsa ɗaya da hannunsa na hagu.
Hannunsa na dama kuma ya É—aura kan goshinsa.
Ido cikin ido suka kalli juna.
Murmushi mai tafe da hawaye Aminullah ɗin yayi tare da ƙara damƙe hannun Mahmoud ɗin dake cikin nasa a lokaci guda kuma ya lumshe idanunsa a hankali, hawaye dake ciki suka gangaro gefen fuskarsa.
Sit wurin yayi gaba É—aya Doctors É—in suka tashi daga sunkuyen da suke a kanshi.
Tare da zubawa kekkyawar fuskarsa idanu.
Bappa Lawan kuma da sauri yasa hannunsa ya rufe bakinsa.
Shi kuwa Mahmoud ido ya zazzaro tamkar zautacce.
Sai kuma ya kalli hannunsa da yaji Yah Amin É—in nasa ya sake.
Cikin wata iriyar murya mafi ƙololiwar rauni da kiɗima ya fara magna.
“Yah Amin! Yah Amin! Open your eyes, open ka gannin fa Mahmoud É—inka ne, buÉ—e idonka Yah Amin zan kaika duk inda nasan zaka samu lfy, Yah Amin kayi min magna manaâ€.
Wannan kalaman ne suka sa Doctors ɗin ma zubda ƙwalla.
Ahmad kuwa wani irin kukane mai ƙarfi ya kwabce masa tare da nufar waje a gigice.
Jingina yayi jikin gini yana wani irin kuka tare da bubbuga kansa jikin gini.
Da sauri Abba ya kamo hannunsa tare da cewa.
"Aminullahi na ya tafi koâ€
Ina Ahmad ya kasa cewa komai sai, Kai ya ringa bubbugawa jikin gini.
Ganin hakane yasa Ummi zamewa da sauri Goggo Dada ta tarota tare da zaunar da ita bisa kujerar dake bayansu.
Barrister ne yayi saurin kusa kai ciki dan jiyo muryar Mahmoud daya shaƙe wuyan likitan da yace masa yayi haƙuri da Aminullah ya rasu.
“Kaine mai rayawa da kashewa da zaka cemin Yah Amin ɗina ya mutu.
Baka iya aikinka bakoâ€.
Da sauri Bappa Lawan ya kamo shi.
Amman ina ya kasa banbare hannun Mahmoud a jikin wuyan Doctor.
Saida Barrister da sauran Doctors É—in suka taimaka.
Kana suka tura gadon gawar sukayi gefe dashi.
Da sauri ya yunƙura zai kamo gadon cikin sauri Abbansu da ya shigo ya fizgo hannunshi ya jawosa jikinsa ya rungume shi gam-gam a ƙirjinsa cikin muryar dake cike da imani da tawakkali ya fara maimaita innalillahi wa innalillahi rajiun.
Yanayi haka su Ahmad suka kama.
Cikin rawan jiki shima Mahmoud ya fara bin bakinsu suna ta maimaitawa.
Can Abba ya kuma fara maimaita.
“Allahumma gafirlahu qara hamhuâ€.
Wani irin saddaƙarwa jini da jiki da brain ɗin Mahmoud sukayi a lokaci ɗaya sai kawai yaji duk tunaninsa ya tsaya kawai dai ya tsinci bakinsa da maimaita.
“Allahumma gafirlahu warahamhu".
Yi yake cikin motsa lips É—inshi a hankali dan jikinsa daya sake.
Haka yasa bashi da sauran gardama.
A haka Abba ya jashi suka fito.
Amotarsa ya sashi tare da kallon Ahmad da yake ta kuka tamkar ransa zai fita Sai kuma ya kalli Ummi dake riƙe da cikinta tana wani irin kuka mai cike da rauni da fidda kalaman yafiya.
A mota ya sata ita da Goggo Dada dake rusa kuka tana faÉ—awa É—anta Sulaiman abinda ke faruwa.
A hankali ya kalli Barrister maƙoncinsa yace.
“Barrister ko zaka bisu ku tafi tare saboda shima Ahmad naga ba hayyaci tare dashiâ€.
Kai Barrister ya jinjina kana ya zauna gaba gefen driver yayinda Ahmad ya zauna gefen mai zaman banza.
Mahmoud dasu Goggo Dada suna baya daga nan yaja mota ya nufi gida.
Su Abba da Bapp Lawan kuwa da wani ɗan maƙocinsu da abokinsa wanda abokin Hafiz ne suka tsaya.
A gama komai a basu gawar.
A can gida kuwa a inda suka bar Farida har yanzu anan take tsaye ba yadda Maman Samira da Samira basu yi ba akan ta zauna Amman ina ta kasa zaman.
Jikinta kuwa har yanzu rawa yake yi.
Ta kuma kasa koda furta ko ƙalane a zahiri sai dai a cikin zuciyarta take ta ambaton Allah.
Hon ɗin da akayi ne yasa ta ƙara zazzaro idonta tamkar zata mannasu jikin gate ɗin.
Su Samira ma miƙewa tsaye sukayi tare da zubawa babansu da yake buɗe gate ido.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.