Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 101 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FITA HAKKIN KI NA FADA MAKI YAR UWA ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMIN SA AMIN, , , ,

Ina zaune saman gado nayi zaman balance irin na goggagun mata yan duniya na wani harde kafa rabin cinyana duk a waje yake.
Na bude baki a hankali cikin wani yauki da yatsune ina fadin sannu da dawo tare da kawar da kai kamar shigowan shi ba dameni ba yadda na nuna.
Amsawa yayi da mamaki karara a fuskanshi yana kare min kallon irin shigan da nayi a lokacin don fitan da zamuyi din dashi.
Yayan mu na shirya muryan sadiya ya daki kunnuwan mu lokaci daya tana fitowa wani dan lungu dake dakin don dakin babbane an masa part part kamar kana cikin babban gida mai dakuna da yawa.
Mayar da hankalin shi yayi gareta har ta kara fitowa yake fadin Wa, Wooo wai wanan sadiyace kanwata dai dana sani ko idona ne ke mun gizo haka ?
Dan murmushin jin dadi ta sake a fuskanta ya mika mata hannu tazo gareshi yace kanwata kinyi kyau sosai wallahi .
Tace har na kai yayan mu yin kyau kuwa ya J har kin fita ya furta tare da jawota yana mata rada a kunnen ta kafin ta juyo ta kalleni a inda nake zaune bakin gado.
Idan kun gama gulman sai mu tafi na fada ina mikewa tsaye na dauko handbag dina dake gefen inda na zauna.
Ina gyara gyalen dana yafa saman hullar daya rufe min kaina da kyau ido ya kara bina dashi na turu baki ina fadin wanan kallon ai sai mutum ya kware haka.
Ina mamakin wanan kwalliyan ne haka don ban taba ganin kiyi irin sa ba duk da ruwa zamu shiga amma kika chaba ado haka dake ?
Nayi ne don daga ni sai kai sai Sadiya zamuyi tafiyan da ace wurin mutane da yawa zamu shiga bazanyi shi ba.
Hanya ya nuna min da hannu na kalli sadiya ina fadin shige mu tafi ta fara hanya na mara mata baya ya rufo dakin da makulli bayan mun fita.
Dan tafiya ne ya sadamu da wurin ina bin ko ina da kallo sai gamu bakin ruwa nidai har cikin raina dama ina son shiga ruwa koda bai kai haka yawa ba a rayuwa .
Sai gashi yau zan shiga ruwa irun wanan jiragene a wurin jere da juna muka tun kari wurin nomban da aka bashi.
Bamu sha wahala ba don jirgin yana da matakala kamar a tudu muke a wurin shiga cikin jirgin kuma a kwai komai kamar yadda muke ganin sun shiga a cikin film.
Bayan shigan mune kamar ance in daga ido sama ina dagawa na hango taju a tsaye saman bene yana kallon mu.
Dan murmushi na sake tare da daga mashi hannu alaman bye kafin na karasa shiga cikin jirgin ga baki daya a lokacin har jirgin ya soma tafiya damu ko.
A gaskiya masu kudi suna jin dadin su sosai a duniyan nan don idan ka dace da rahaman ubangiji gaskiya ka huta .
Allah yasa mu cika da imani na fada a raina kafin na kai zaune ina mayar da idona rufe ba komai ya sani haka sai tunawan da nayi da irin rayuwan da yaya yake ciki.
Ya haka kuma keda kikace jirgi kike son shiga kika rufe idanun ki yanzu kuma ?
Jin hakan da nayi yasani bude idanun nawa na sauke a kanshi yana zaune ya bude system ko har ya fara aiki a cikin sa yake wanan maganan.
Duniya nake tunane yaya na bashi amsa don nasha alwashin sakewa dashi yanzu a kan taju duk yadda zanyi sai naga na raba wanan alakan nasu koda kuwa yin hakan bazai sa yaya ya daina ba sai dai ya canza wani katon bashi ba.
Tunanen me kikeyi na duniya nace a daidai lokacin da nayi wani irin zama na yan barikin mata ina dora kafana daya saman daya.
Wanda yin hakan har ya baiyanar da rabin cinyana a waje wanda dama rigan nada tsaga har kasa idan mutum yayi irin hakan zai baiyana sosai a gani.
Duniya aljanan kafiri lahira kuma ta mai rabo duk wanan jin dadin naga iyakar shi duniya za a barshi ba a zuwa lahira dashi nagani.
Yaji maganan sosai har cikin ranshi sai dai bai kara magana ba yaci gaba da abinda yakeyi a cikin computer din shi ya kyaleni.
Tsawon wani lokaci wurin yana shiru jirgin sai tafiya yake damu a cikin ruwa hannu na mika na dauki dayan cup din dake saman table din dake tsakiyan mu ina tsiyayya ruwan enabi na fara kurbawa a hankali.
Yana sane da sabon halin dana tsiro dashi don yasan ba haka nake ba da rashin kunya sai dai yana bina yaga iya guduna kawai.
Daga inda nake zaune na kara daukan kofi na tsiyaya drinks din na mike a hankali zuwa gefen da yake zaune na zauna gab dashi ina mika mai abin sha.
Dan juyowa yayi ta miko min bakin shi da zuman wai in bashi don shi wanan ba komai bane a gareshi.
Don ko Aisha da take kanwarsa watarana ina gani itace ke basa a baki yana sha tun ina zagin su har na saba da ganin hakan na daina.
Tunawa da hakan da nayi banyi sanyi a gwiwa ba na mika masa ya kurba a hakan har ya shaye cup din.
Na aje na dan jiginu da jikin shi tare da daukan jaridan dake saman table din wanda aka aje don mu na fara karantawa.
Matane sexy girls gasu nan iri iri ko wace da irin nata shigan ciki computer ya rufe tare da fadin ki tashi mu leka waje kuga ruwa.
Don ita sadiya tana nata aikin kallo a cikin wayan ya dauke mata hankalin ta garemu tana jin hakan tayi saurin dago kanta tana son jin amsan da zan bashi.
Batare da yin magana ba na mike zaune shima mikewa yayi muka fita sosai muke jin dadin wanan fitan namu don sai da gari yai duhu muka dawo masaukin mu a cikin an,nashuwa.
Tun fitan shi dakin ko washe gari bamu kara jin duriyan shi ba saida yamma ya shigo muna ruwan saman da akeyi a garin ya dan dukeshi.
Don ni a lokacin har zuciyana ya fara wasi wasin din ko dai taju shima ya nuna fushin shi kan fitan mune yasa bai shigo dakin namu ba yau ya fita .
Tunda taju din da ire iren su sune kishiyoyina a yanzu wurin shi yasa na fara wanan tunanen haka sai gashi ya shigo dakin da yamma.
Gaidashi din dai mukayi yake tambayan sadiya ko zamu koma ruwa ne yau din ma Sadiya mu kwana a cikin ruwan.
Da sauri tace a,a yaya j bazan koma ba jiya ma banyi barci da dadi ba wallahi don da zaran na rufe idona ruwan nake gani saina bude.
Matsoraciya yace yana juyawa ya fita dakin yakan shigo da dare kafin mu kwanta sai gashi bai shigo dakin ba ranan.
Hakama washe gari bai lekomu ba sai wajajen karfe biyu aji wayan dakin na ringing na dauka.
Muryan shine a cikin wani irin yanayi yake fadin zainab sun kawo maku breakfast ki hado min ruwan zafi ?
Nace eh yace ok black tea kawai zaki hada min ki kawo min yau ban fita ba bana jin dadin jikina ne kadan.
Subbahanallahi nace hope dai da sauki yace ciwon kaine kawai ke damuna har nakai wurin kayan breakfast din sai wani tunane yazo min a rai.
Da sauri na koma na dauko wanan maganin ba tare da nabari sadiya ta kula da abinda nakeyi ba na nufi wurin da zan hada mai tea din da jakkata.
Na hada kamar yadda maya tayi min bayani na dauka na kai mai dakin da shine farkon shigana tun zuwan mu Dubai din duk da bamu da nisa dashi.
Yana kwance saman mamakeken gadon dakin jikin shi saye da dogon wando ash colour sai farar singlet daya saka a saman jiki ya kife cikin saman gadon yana kwance na shigo dakin.
A hankali na taka zuwa bakin gadon saida na kai zaune nake fadin ga ruwan tea din nan yaya na gado maka gaba sai faman faduwa yakeyi kamar nayi laifi za a kamani.
Dan dagowa yayi sai ya koma kwance yana tsuki kafin kuma ya dago da karfi ya tashi gaba daya yana fadin a daidai lokacin da nake mashi sannu, da jiki yace.
Ina ganin ruwan daya dan dukeni ne jiya yaja min ciwon kai dama jikina bai shiri da dukan ruwa ko kadan.
Kasha magani yace nasha don dashi nazo ban faye yarda da magani su nan ba shiyasa nake tafiya dashi duk inda zani.
Ya shiga ban daki ina ganin baki ta wanko ya fito har lokacin ina zaune a wurin dana zauna din ya dauki ruwan shayin yana kurbawa daga tsaye.
Dan kai na dago na saci kallon shi na dukar da kai shiru muke bayan ya gama kurban ruwan tea din ya aje cup .
Ganin hakan na mike na dauki cup din na fita dashi da zan fita nace Allah ya sauwa yake fadin ai barci zanyi na dan lokaci ko zan tashi inji saukin shi.
Nakoma daki da fargaba a ciki zuciya do dai kam na kada na bashi ya kuma sha saura in jiran hukuncin ubangijin mu yanzu kam a kan wanan lamarin.
A cikin wanan tunanen ne har barci ya daukeni ban sani ba barci sosai na samu nayi a lokacin a can cikin barci nake jin wayan dakin yana ringing alaman kira yana shigo min lokacin .
Da kyar na iya bude idanuwana da sukai nauyi saboda barcin na mike da kyat din kuma na jawo kan wayan dake gefen gadon.
Muryan yayane baya fita da ji yana cikin tsananin ciwo a lokacin yana fadin zainab kizo kada in mutu .
Gabana ya bada ras ras lokaci guda da sauri na sauko saman gadon ban tsaya jiran komai ba na nufi hanyar fita waje zuwa dakin nasa.
Ina shiga yana wani irin nishi da kakari kamar zai mutu ya dafe cikin shi da hannun shi daya yana mulmula a kasa.
Da sauri na karasa inda yake kwance saman ties din yana wanan gurjin kamar karimin yaro.
Gaba sai faduwa yakeyi don tsoro don ni su maya basu fada min zaiyi wanan wahalan ba haka.
Tsugunne nakai saman kamshi ina dan kiran sunan shi da yaya yaya me ya sameka haka ina fadi a rude tare da kai hannuna saman jiki shi ina taba shi.
Bai iya dago kai ba ba kuma magana sai kokarin nuna min cikin shi da yakeyi da hannun shi na kara rudewa sosai.
Magana yake son yi ya kasa haka yasa na mike a rude ina kuka zan fita daga dakin naji ya rike min hannu na a cikin nasa.
Na dawo inda yake din yana son kara yin magana yai wani irin yunkuri sai ga amai yazo mai lokaci guda wani irin bakin amai da ban taba ganin irin saba a duniya.
Amai yayi sosai a wurin na kara rudewa kamar rayuwan shi zai dauke a lokacin duk ya fita cikin yanayin sa lokaci guda har halittan shi ya dan sauyawa ganina.
Nishi yakeyi sama sama can ya samu magana yazo mai da karfi yana fadin dauko wayana ki kira a kaini asibiti don Allah kada in mutu.
Da sauri na mike na nufi wurin gadon dakin ina neman wayan nashi a karkashin filo naga wayan na dauko ina tambayan shi wani nomba zan kira.
Mai 00 karshe ya fadi yana mayar da kanshi a kasa da alama sayin yake so sosai a lokacin ya ban tausayi matuka.
Kamar jira suke a kirasa baifi minti biyu ba sai gasu dakin da gagawan su suka daukemu zuwa asibitin.
Likitoci sunyi aune aune a kan aman da yake yi din basu gane dalilin aman ba, yan magunguna suka bashi tare da karin ruwa muka dawo masaukin mu dashi.
Duk ya zabge lokaci daya yayi wani irin rama mara ma,ana a jikin shi ko don ban taba ganin wani a irin wanan halin bane oho ?
Aman bawai ya tsaya bane ga baki daya don yana yinsa lokaci lokaci idan ya taso mai da kyat mukaga safe ranan dashi don a dakin nasa na kwana.
Washegari ya dan tashi da dama amma duk jikin shi ya sake bai ko iya tafiya sai da kyat da bin bango yake iya zuwa ban daki ya kewaya.
Har na gane yana tsunguni ranan ya dawo ya kwanta ina zaune na zuba mai ido cikin tashin hankali da tsoron abinda zai biyo bayan hakan a kanshi.
Wayan shi dake gefe yayi kuka na dan kalleshi idon shi a rufe baida niyar budewa balle ya dauka.
Har kiran ya katse wani ya kara shigowa sai nakai hannu na dauka sunan mami na gani da sauri nayi recieve kada ya kare katsewa irin na dazun.
Jafar lafiya banji ka kira ba tun jiya ta fada mami bashi bane gashi kwance baida lafiya tun jiya din na bata amsa .
A rude tace meya sameshi kuma zainab injin dai ba abin bane ya fara bashi matsala har muryan ta yana sarkewa a lokacin don rudewa.
Mami daga ciwon kaine sai ya koma amai da tsugunni a yau din jiya dai aman yakeyi kawai.
Yanzu kuna ina ne wai ta tambaya, nace muna nan Dubai munzo hutu ne last week kunje asibiti ko nace jiyan munje sun bashi magani muka dawo.
Barin fadawa mamud ko zai iya tasowa yau yazo idan zai samu jirgi a lokacin naji ya dan yi magana na juyo gareshi yana fadin
Kice ta barshi zamu koma chaina ne inje asibiti can likitana ya ganni a can din ba sai yazo ba.
Na fadawa mami din abinda yace nan ta fara fada hankali tashe nayi shiru ina saurarenta tana fadin zai dauki ciwo tundaga Dubai har zuwa chaina nan babu likitocine da zasu dubashi ?
Nikan karshe wayan na kara mashi a kunnen shi yana jin fadan da mami din takeyi a wayan yace a karshe mami na riga nayi booking ko zai gani da zaran mun isa can din.
Yau zamu koma insha Allah anyi booking din jirgin tafiyan mu a yau din don likitan shi yasan matsalana.
Ba zainab din waya muyi magana ta fada ya miko min wayan tace zainab don Allah idan kun isa kinga abin bai tsaya ba ki kira mu ki fada muna halin da ake ciki .
Murya na rawa nace tau mami insha Allahu ki kula dashi sosai don Allah zainab nasan halin jafar da gardama kada ki daka ta nasa don Allah.
Ni yanzu idan mami tana min magana sai abin ya dinga ban mamaki balle yanzu da har mami din taji wai muna dubai da danta bansha zagi da sheri ba.
Wai har da danka min kula da dan nata a hannuna tana wani hadani da Allah can bayan ta gama min cin fuska a baya.
Don darajana da kima baikai na wace zata shiga cikin wanan daulan ba na danta iya abinda mami ke nufi dani ke nan ba wani abu ba.
Amma yanzu data ga dan nata yana da mugun tabo masu yawa da kyama a rayuwan shi shine take kokarin nuna min cewa tana sona a cikin ahalin ta a yanzu.
Idona na runtse wasu hawaye masu dumi suna zobo min meta fada maki daya sakaki kuka a yanzu muryan shine cikin sanyin murya yake min wanan tambayan.
Ban iya bashi amsa ba sai mikewa da nayi don barin dakin da sauri kada ki fita ki barni haka a cikin wanan halin da nake ya fada.
Ja nayi na tsaya wuri daya ban kara gusawa ba daga inda nake tsaye din yaci gaba da fadin banji ta fada maki wani abinda zai sakaki kuka haka har ki fushi ki fita ba ki barni ni kadai ina cikin wanan halin.
Don koma ta fada maki bazan yarda da hakan ba kema kin sani don haka ki dawo ki zauna har na dan kara jin karfin jikin nawa.
Zan je na fara shiri ne na bashi amsa ba tare dana juyo inda yake ba nake magana ina kokarin fita duk da ya hanani ina son kebewa inda zanyi kuka ma,ishina ba wanda zai hanani a yanzu.
Bina yayi da kallo har na bace mai da gani kafin ya sauke ajiyan zuciya yana runtse ido cikin takaici don shidai ya rasa meyasa ni kuka a cikin wanan maganan kuma ?
Ban iya zama dakin ba don halin dana barshi a ciki koda na koma na samu ya fito ban daki ya zauna a kofan don bai iya karasowa cikin dakin da kafafun shi a lokacin.
Nan kan hankalina ya tashi sosai don sai dana kamashi ya koma saman gado ya kwanta na shiga fadi a raina shike nan nine zanyi ajalin yaya ke nan ashe ?
Kofa aka buga don shigowa na mike na bude kofan wasu mutum biyu ne na sama a wurin tsaye suke tambayana shi na nuna masu ciki da hannu suka shiga.
Ashe likitane da wani abokin shi suka shigo basu fita ba saida aka daura mai ruwa da sauran magani sai gashi ya samu karfi har sallah naga yayi a tsaye bayan fitan su.
A lokacin hankalina ya fara dan kwantawa don ganin ya soma samun lafiya a jikin shi yanzu dama ni tsorona shine kada ya halaka a sanadiyar maganin da na zuba mai wani abu yazo ya same shi kuma.
Karfe takwas na dare muka bar cikin hotel din mun dan jira kafin jirgin ya tashi zuwa tara na dare muka bar kasan zuwa chaina.
Muna isa asibiti aka wuce dashi daga can duk gwaji likitan yace shi baiga courses din ciwon nasa ba sai dai idan wani abu yasha na daban da ya jawo mashi hakan.
Sai dai nan din sun kwatar dashi na kwana biyu kafin su sallamoshi ya dawo gida ya karasa jinya a gida kuma yana shan magani.
Bashi dake jinyar ba koni na rame sosai don ciwon nasa ya daga mi hankali amma yanzu da naga ya dawo normal na fara sake jikina nima.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.