Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 99 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA YAR UWA MU GUJI ABINDA ZAI KAIMU GA FADAWA HAKKIN WANI, , , , ,
Kwana biyu ina faman tunane a raina na yadda zan samu daman bashi wanan abin ya sha na rasa dabara yin hakan sai tunane nake a raina.
Kai karshe dai na barzancen har na fara mantawa da wani zancen magani can a kanshi don nazo nayi tunane uwarshi ma da ta haifeshi ta barshi a haka balle ni.
Iyaka dai na samu hanyar tsirewa daga gareshi da zaran na gama karatuna shike nan na fita wanan sarkekeniyar na auren shi ai.
Na sani sarai bai daina halin nan ba don babu abinda ya fasa daga cikin halaiyar nasa shiyasa na yiwa kaina alkawarin ko a gabana yake mugayen halinsa iyaka na ido sai kuma addua ga musulmi da zanyi tsakanina dashi.
Ashe abin ba haka bane idan ance miji abin yafi da nan duk da auren namu na wasan tamola ne ba kamar sauran auren da aka sani bane da farko.
Matsalan abin banda abokin shawara a rayuwana ga zurfin ciki dake damuna ko banza balle wanan din da ban yarda kowa yaji wanan zancen a gurina ba .
Ko abu yana damuna haka zai tsaya min a rai har lokacin da Allah zai gusar min da tunanena na manta da zancen ga baki daya .
Don ina da saurin mantuwa a rayuwana ban faye rike abu a raina na tsawon lokaci ba bai fita mun a raiba.
A bangaren mami kuma mu dai dan gaisawa yanzu a kai akai akala sau uku da ko sau biyu a sati zata kirani ta tambayeni muna lafiya dai ko ?
Idan na bata amsa zata sake tambayana yaya mijin naki zainab saidai nayi murmushi bazan bata amsa ba akan komai.
Zakaji tace kiyi hakkuri insha Allahu komai zai dawo daidai insha Allahu tare da kara kwantar min da hankalina.
Saidai duk yadda na iya daure da hakkuri saida yaya ya kaini kull har ya kawo muna matsala don yanzu kan kamar kara masa iskanci akeyi don dawowan taju gidan ya kara maidashi ruwa sosai.
Don yasan na sani yanzu ba zancen boyo a tsakanin mu a fili yake abinsa don ba mai kwaba masa yake gani.
Ranan na dawo school da wuri daga makaranta don haka kawai nake jin ba dadi a jikina muna fitowa darasin farko na shigo mutana na dawo gida don in dan kwanta.
Saboda ina jin kamar barcine ke damuna ko zazzabi ke son kamani a irin hakan kawai na yanke shawara in dawo gida.
Nayi mamakin ganin falon a bude don ban tsanmanin dawowan yaya gida a wanan lokacin daya dace ace yana wurin aikin sa.
Haka na bude falon cikin karfin hali na shiga har na rufo kofan na shigo kai tsaye tsakan falon na samesu kamar wasu karnuka suna romace a tsakanin su kamar wani miji da mata ko saurayi da budurwa.
Inna lillahi na fada da karfi ina sake yar hand bag dina dana sako tarkacena a cikkn sa.
Salatin danayi ne ya dawo dasu hankalinsu suka mike lokaci daya tare da sakin junan su ga maballan rigansu duk sun balle sun shagala da hakan.
Tashin hankali iya tashin hankali na shigeshi a ranan yadda gaba daya idona ya rufe na ke fadin stupid, idiot noses mazinata fasikai ku fice min a falo kafin na tona maku asiri a nan.
Ido rufe kamar gidana suke sheke ayan su din a ciki don yadda idona ya rufe da ganin su baro baro danayi a lokacin.
Wani kallon tsana taju din yai min don yadda yaga abokin fasadin nasa yayi laushi sosai yana fadin wai meye haka me ya dawo dake gida wanan lokacin ana karatu.
Ban iya magana ba don duhun da idona ya fara yi mun a lokacin na kara fadin ku fice min nan nace kada fushin ku ya shafeni a wurin Allah.
Ke ki natsu ki san abinda kike fadi mana da irin wanan kalaman naki ya mike da kyar yana mai gyara rigansa yake wanan maganan tare da nufo inda nake tsaye.
Na fara ja da dan baya kadan bai daina nufo inda nake ja da baya din ba naci karo da wani abu a bayana na fadi kafin in kai kasa na some don tsoro a wurin.
Da sauri ya karaso ya tareni na fada a jikin shi sai lokacin yaga ai a some nake ma ashe ya fara kiran sunana da karfi yana jijigani ban farfado ba.
Yasa ya juya inda taju din yake cikin daka tsawa dauko min ruwan sanyi a fridge mana da sauri baka ganin ta somane.
Haka taju din ya nufi kitchen da sauri ya dauko goran ruwan da har ya fara kankara ya kawo mashi bai tsaya kulawa ba kawai ya watsa min a jikina .
Na sauke wani ajiyan zuciya tare da dan bude idona kafin na mayar na rufe na kara sakewa lokaci guda kuma.
Ya subbanallah ya fada tare da dan jijigani yana kiran sunana a hankali kuma a rude ka barta zata farfado ai tunda ta falka taju ya fada.
Shout,up ya fada da karfi duk waya jawo hakan yanzu saida na fada ma ka bari zan dawo don jaraba ka manne min saida hakan ya faru.
Na fada ma yarinyar nan yar gargajiyace da rikon addini kayi duk wani taka tsatsan dasu don komai yanzu a cikin tako nakeyin shi don su.
Taju din yace I am sorry boss ban san zata dawo yanzu bane ni kuma ina son jinka a jikina wanan lokacin.
Yace yasa kayi min karyan baka da lafiya na bar aikina zuwa gida yanzu ga abinda ka jawo min yanzu wanan abu baka san iya inda zai tsaya ba .
Duk zancen da sukeyi ina jin su don na fara farfadowa lokacin zancen su yana shiga kunnena bandai bude idona kawai bane don ban son ganin su sam a rayuwa na.
Ji kawai nayi ya cicibene zuwa sama bai ajeni ba sai saman gadona ya shifideni ya juya wurin AC ya kunna tare da sake volume din AC din.
Ya dawo inda nakw yana dan murza min goshi tare da kiran sunana a hankali da zainab kina jina don Allah ki kwantar da hankalin ki mana ki natsu.
Don Allah ka fita yaya bana son ganin ka a rayuwana kai din shedan ya gama ma fitsari a zuciyar ka bama iya kanka ba.
Yaya a gidan ka ?
Gidan da iyalin ka suke zaune anan kake shimfida fasadi irin wanan kamar kai din ba musulmi ba haihuwan musulmai ?
Enough zainab ya isheki kin dai san koni waye don haka ki kyaleni yadda kika ganni a haka na fada maki.
Wayo ni Allah na na shiga ukku na lalace a rayuwana.
Ni zainab naga ta kaina ya Allah na tuba ka yafe min da wanan jerabawan dakake jarabbata na dashi idan laifi nayi ma ka jefoni a wanan rayuwan.
Tsuki yayi ya mike bai tsaya ba ya rufo kofan da karfi ya fice na kara kurma ihu kamar an tsikareni kuma na mike tsaye ina saukowa daga saman gadon.
Dan jakkana na dauko na nufi kofan fita nima da sauri sai dai ina zuwa bakin get din security din kofan ya rufo kofan da sauri yana min wani yare da ban sani ba.
Duk yadda naso fita daga gidan sun hana hakan dolw na koma cikin gidan rai bace ina hawaye.
Tashin hankali ranan na shige shi ga tunane kala kala da nakeyi a zuciyana sai can Sadiya ta fado min a rai don lokacin dawowan ta da yayi har ya wuce yasa na kara mikewa tsaye na nufi hanyar waje .
Ban kai ga fita daga falon ba sai ga sadiya din ta fito daga dakin tana fadin .
Yau yayan mu kin barni ina jiran ki saida ya jafar ya turo aka dauko ni a makaranta ya din yace driver ya fada min kina gida baki da lafiya wai .
Hannu na warewa sadiyan tare da fadin yar kanwata zo gareni don Allah ki rungumeni ko zanji dadi a rayuwana kada in mutu.
Da sauri ta karaso ta rugumeni din tare da fadin yayan mu meke damun ki baki da lafiyane ko wani abu ya sameki.
Saidana runtse idona ina jin dadin dumin ta a jikina kafin ince da ita ya jafar daine yake son kasheni Sadiya.
Kai ta dago tana zare jikinta daga nawa tana fadi a razane zai kasheki yayan mu me kikai masa nace nima ban sani ba Sadiya ya daice zai kasheni yau a garin nan.
Daga haka naja hannunta zuwa saman kujera wayan dake hannuna na fara neman lamban mami ina kiranta.
Kira biyu saiga mami ta daga wayan murya a raunane nake fadin mami na shiga uku yau a garin nan wallahi.
A rude mami ke fadin meya faru zainab ina jafar din yake ko wani abu ya sameshi take tambaya a rude.
Mami ba abinda ya sameshi kawai dai na kamshine yana abinda ba daidai shine yai min dukan tsiya ya ce zai kasheni ba zai barni da raiba tunda na saka mai ido da yawa.
Innalillahi shi jafar din baibar wanan dabi,an bane zainab ko kwayance ta fara tabashi yanzu har yake furta hakan ?
Sai kawai naji ta fashe da kuka nima kukan nakeyi na daukan hankali ina tausayawa kaina kan wanan rayuwan dana samu kaina a ciki.
Yayan mu mu gudu mana idan yaya a zama mugu kada ya dawo ya kashe ki din a gidan nan sadiya ta fada a tsorace don taji wayan mu da mami din.
Ni kuma na fadi hakan ne don labarin da Maya ta bani daya taba faruwa da wata inda take cewa zasu iya kashe mutum idan ya faye saka masu ido basu da yadda zasuyi dashi .
Sai kawai su kashe mutum su huta kuma ba ai masu komai idan an kwana biyu kigansu a gari suna yawon su.
Do suna da daurin gindi sosai a wurin manyan gwaunati da sauran jami,ai don haka ba ai masu komai ko an kamasu.
Jin hakan yasa nake tsoron hakan don nasan shima yaya din dole yana da wanan halin data fada min don bai rasa daurin gindi yadda naga yana shanawa a kasan son ransa.
Wanan dalilin yasa na fadawa mahaifiyar nasa haka don riga kafi a yadda na ganesa yau din kafin ya fita don zai iya aikata min komai tunda na gansa din yau ido da ido.
Sai gashi a rude ya dawo gidan tun kan ya hawo sama yake kwala min kira ina zaune sama ina jin yadda yake kwala min kiran a gigice muna tare da sadiya a dakina na tashi na rufe kofan da sauri a tsorace.
Don nasan sunyi waya da mami ke nan akan wayan da mukayi da ita dazun kan wanan zancen yasa ya dawo a hasale yake min wanan kiran na tashin hankali.
Muna jin lokacin da yakw dukan kofan a haukace muka rike junan mu a dakin a tsorace kamar zai shigo muna dakin ne, bayan a rufe dakin yake.
Har ya gaji da haukan sa ya tafi kilama dama a buge yake zo ya sauke haushi a kaina waya sanar mashi mudai muna ciki lokacin.
Haka muka kwana tsorace rai kuma bace damu don ko sadiya da take karama a tsorace ta kwana makake dani ranan.
Tunda safe na sake kiran manmi duk da nasan a lokacin sauran darene a can Nigeria ina kuka na tayar mata da hankali akan ta saka baki ya turo mu zuwa gida don na gama zama dashi ni.
Mami hankali tashe ta tayar da ya mamud tana fada mai abindake faruwa a waya duk da ban fito fili na fada masu gaskiyan maganan ba amma hankalinta yayi matukar tashi a lokacin.
Wanan wayan ne ya tayarwa kowa hankali tunda safe sai kiran shi akeyi aka daga mai hankali don mami ta fada mai har in ya yarda ya turoni nageria a haka asirin su ya gama tonuwa ke nan a kasan nan.
Tayi rantsuwa duk abinda ya sameni wallahi sai tayi sanadin da za a kashe shi shima kafin ya bata mata sunan zuria a duniya.
Yabi wayan da kallon mamaki bayan sun gama waya da mami yana mamakin yadda a shekaru na iya jefashi cikin wanan rikicin haka.
Don kalaman mami sunyi tsauri sosai a gareshi hankalin shi ya tashi sosai gashi ranan ya kori taju bai kwana dashi a dakin ba.
Don yana ganin duk shine ya jawo mashi wanan fitinan daya faru yana zaman shi a office din shi tajun ya daga mai hankali.
Yayin da shi kuma tajun ya kwana yana neman mafitan hanyan da zai ga ya raba tsakanina da jafar din gaba daya don tun haduwan mu da jafar din gaba daya komai ya jagule masa ba yadda abubuwa suke tafiya masu ba a baya.
Don yanzu jafar din ya canza kamar bashi bane mai yawan sha,awa a kansa a baya yanzu bai faye damuwa da hakan ba sai yaga dama tunda har yana iya koran sa a yanzu.
Shiyasa ya zama mai dole ya dauki mataki a kan zainab din da yakewa kallon karaman yarinya da farko sai fashi yarinya nason rabashi da farin cikin ga baki daya.
Matakin daya yanke a ransa shine yayi min silent kill ba tare da wani ya gane hakan ba har jafar amma ta yaya zaiyi hakan ba, a fahince shi ba.
Don idan ba raba yarinyar nan yayi da duniyan ga baki daya ba wanan karin kan yasan ba zai taba samun kan jafar din ba kuma.
Da ire iren wanan mafarkin ya kwana a ranshi har safe bai kai ga mafita ba yana falkawa wayan shi ya jawo yana neman layin jafar din saidai wayan yawan busy yayi yawa a ranan.
Shiko jafar daya gaji da tunane mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da dauro alwala yazo ya tayar da sallah kafin ya fara samun natsuwa na zuwa mashi lokaci guda.
Saida ya shrya tsaf kafin ya fito part din namu ya nufa kai tsaye ya samu dakin har lokacin yana rufe bamu bude ba.
Mami ya kira itace ta sakamu mu bude kofan ya shigo don sadiyace ta bude mai kofan ta rabe a gefe a tsorace har ya shigo dakin yana mata kallon mamaki.
Kafin ya dago ya kalli inda nake zaune rakube saman sallaya a wurin danayi sallah har lokacin ban daga ba ina zaune.
Sadiya ya kara kallo yana fadin jeki kiyi wanka ki shirya na saukeki school tace to a tsorace ta fice daki da sauri zuwa abinda ya umurce ta yi din tana waigena a tsorace.
Sai take ganin kafin ta dawo dakin ya gama halakani ga kuma tsoro da biyyaya yasa ta barni dashi a dakin ta fita.
A hankali ya tako zuwa inda nake a dakin ya zo gab dani ya tsunguna a gabana ya kura min ido na dan lokaci.
Kafin ya furta a hankali zainab a zatona ke yar uwatace da zata iya rufa min asiri a duk irin halin da muka tsunci kan mu a cikin sa.
Sai gashi ke din ce a yanzu ke neman hadani fada da mahaifiyata da yan uwana har kina ikirarin zan kashe ki in rabaki da rayuwan ki.
Ban kawo ki kasan nan don na tozarta ki ba cin zarafin ki sai kawai don wani bukatana na daban wanda a baya na zata zaki iya daurewa da irin rayuwana.
Ashe abin ba haka bane ke a wurin ki tunane bai barni na gane irin ra,ayin ki na rikau da kike dashi ba a lokacin.
Ban taba zaton hakan ba a wurun ki don na dauka ke din ma a dan uwa na jini kike dauka na kamar yadda yasa na zaboki kan tayin mami na aure a kaina.
Nayi zaton idan na biyo ta wanan hanyar komai zaizo min da sauki a rayuwana ashe abin ba haka yake ba kece ma zaki min fiye da abinda na guda a gurin wata.
Don ke din na kula abin duniya gaba daya baya gaban ki kin nausa a wata duniyan na daban.
Ban iya cutar da wani ba zainab balle na fara a kanki a yanzu don haka ina rokom ki da kibar kiran mahaifiyana akan rikicin mu don Allah.
Banda ra,ayin rabuwa dake ko nan gaba balle wanan yasa na mayar dake Nigeria kamar yadda kike so nayi maku.
Idan zaki kwantar da hankalinki wuri daya saura kiris ki karasa karatun ki idan naga hankalin ki ya kwanta na kaiki gida kiga iyayyen ki idan kuma haka zamuci gaba da zama zaki tabbata a kasan nan baki je gida ba din zuwan ki a haka illa ne garemu baki daya.
Da sauri na dago kai ido tab da hawaye don ban so ma ganin sa na kalleshi ina son yi magana kuka ya rinjayi zuciyana har bakina bai iya buduwa a lokacin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.