Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 34 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
2ï¸Â⃣7ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GARE KU YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA AMIN, , , , ,
Jin abinda hjy ke fadi yasa dole na daina kuka don ba zanso nayi sanadin mami da mahaifiyar ta arayuwana ba don na samesu cikin so da kauna iri ta da mahaifi a tsakanin su.
Ni na bar shiri sai ga tsohuwar ita tana hada kayan ta wai ita gida zata bata kara kwana gidan mami.
Hakan ya tayar da hankalin kowa a gidan don mami har kasa take tana ba hjy hakkuri hjy ko sai fada take tana fadin.
Sam bazan zauna inga wanan cin fuskan da yaran ki kewa yar mutane ba haka idan ke kin kasa da ita ni zan tafi da ita can kauyen mu in yaso shi Jafari yazo gurina ya nemi auren ta.
Kin dauko amana dadi dadi kina riko tsakani da Allah ashe rikon naki ga yar baikai ciki ba da har dan ki zaiji shawan hada iri da ita ki fito kina fadin baki yarda ba don ita din ba diyar kowa bane a kasan nan.
Gasu nan birjit a gari dan naki yaje ya zabi daidai dashi a kadarta yau Aisha ce dan tallakawa ya fito nema ashe ba zaki iya bada aurenta ba ga wanda take so ?
Don kawai yanzu kudi ya bude maki ido kowa kuna kallon shi a mutumin banza koko samun abokai yan duniya dakikayi ne yanzu ya sauya maki yanayi.
Idan ma hakan ne sai kije ki aura mashi wacce duk kike son aure mai din ita kuma wanan din zan tafi da ita gurina in sakata karatu idan ina raye wata ran sai kince ba ita bace a gidan nan.
Kuma ki sani koda danki zai mutu ne idan yazo ba zan bashi yar nan ba muddin na bar gidan nan da ita.
Inda nake ta kalla tana fadin tashi muje yar nan nasan dai ko ban san kowa a garin nan bazan kwana a waje ba yau zan samu na Allah da zasu duba tsufana su tausaya min.
Tana kokarin sungumar jakkan kayan ta daga saman gado inda yake ajiye mami tayi saurin dafe jakkar tana fadin hjy don Allah ki rufa min asiri a garin nan kada kije ko ina gwiwa biyu nakai kasa tare da daga hannaye biyu sama ina fadin.
Hjy don girman Allah kiwa mami hakkuri karki fushi da mami ba laifin ta bane laifin zuciyane.
Da yau danta bai bijiro da wanan zancen ba da mami batai fushi dani ba har gobe mami uwace a gareni mai mutunci da kima a idona.
Bazan taba mance mutuncinta a gareni ba don Allah kiyi hakkuri ni in tafi ko mami da yaran ta zasu zauna lafiya.
Hjy ba zan biki ba zan koma gidan ubana in zauna duk abinda Allah yayi min mai kyaune a rayuwata Allah ne shedata wani kalami na soyayya bai taba hadani dasu yaya ba a gidan nan wanan yana daga cikin kaddaran rayuwata.
Don Allah hjy kiyi hakkuri ki zauna a cikin gatan ki kada ki fushi da mami sabodani kada laifin hakan nima yazo ya shafeni watarana.
Ina fadin hakan na fashe da wani irin kuka mai tsanani na mike tare da nufar wardrobe inda kayana yake cikin jakka a jere ina kokarin daukan jakkar.
Takwara ina yanzun kika gama bani hakkuri akan uwarki idan nayi hakkuri ke kuma ina zaki a cikin daren nan .
Ko so kike in fasa hakkuri da uwar taku mu tafi tare kafata kafarki mubar gidan nan a yau din nan basai gobe ba.
Hjy ba Anchau zan tafi yau din ba zanyi kokari in kai kaina gidan anty safiya har kashe gari ta sakani mota in koma gida nufina ke nan muddin barina gidan mami zaisa ta samu sallama tsakanin ta daku.
Ba zaki bar gidan nan ba koda bana raye sai idan aure ya rabaku da uwarki kamar yadda aure zai rabata da yarta Indo.
Muryan mami ke fadin ke zeey mayar da kayan nan ki fice daga nan ki ban wuri da hjy kije gun su kande ko dakin Aisha ki jirani.
Mami ta bani umurni da hakan da sauri na juya na bar dakin nan na barsu tare da mahaifiyar ta na nufi gurin su mama kande na zauna.
Sun dade da mami da hjy a dakin har bayan magariba san nan salma tace dani hjy tana kirana a daki.
Na mike na tafi ina addu,a a raina Allah yasa sun yake hukuncin in koma gidane gaban iyayyena zaifi min wanan zaman rashin yancin kai da banda shi a gidan mami yau har ni zainab Nazifa ta dafawa satan waya.
Hajiya ta idar da sallah har isha,i ina shiga da sallama fuskan tar a kaina tana son ta fahinci halinda nake ciki take tambayana da nayi sallah na bata amsa da nayi tun dazun hjy.
Zauna ki zuba muna abinci ta fada kai tsaye dai umurni ta bani babu daman yin mussu gareta ke nan.
Itama ba wani cika mata nayi sosai ba na dai zuba kadan kadan sai dai nawa din yafi zama kadan don nasan ba zan iya cinye wanda ma na zuba din ba.
Sai faman cakulan abincin nakeyi cikin sanyin jiki itama dai hjyn haka dai take kokari tura abincin a bakin ta can naji tace kada ki yarda in hada nawa baki karasa cinye wanan dan abincin da kika zuba ba kamar za,abawa yaron goye.
Dole na fara tura abincin da sauri ds kyat nake hadeshi gaba daya raina babu dadi a lokacin har na samu na gama kamar yadda ta umurceni dayi.
Ba zancen hira garemu sai kowa yayi shiru a dakin dan dama hjy ma takan dan jefo min magana jefi jefi.
Washegari aka tashi da shirin tafiya kamar in dora hannu akai ince wayo ni Allah don banson inyi nisa da gida kuma.
Dan dama nan na rike sunan unguwar da muke dana su anty safiya don bam manta da sunan unguwar ba har yanzu a raina.
Ina ji ina gani har aka fara fadin a fito da kayan da za a wuce dashi a mota don masu mota zasu rigamu tafiya nake gani.
Jakkunan kayan mu gaba daya an labta su a mota hakan yasa naji raina ya kara baki nasan yanzu kan zuwa ba fashi gareni.
Hjy ta aikeni dakin mami don in tuna mata zancen maganin ta da za a saya mata nan kaduna.
Ina gab da shiga dakin nake jin muryan mami na fadin saida nace kada ku sayo ticket da zeey mota zatabi ita dasu kande baku maganata ba sai da kuka sayo.
Ba laifin mu bane mami ya J yasa mu saya mata kinga ko ba zamu ce masa a a ba tunda kudin sane.
Gulman ku zai ciku daku har jafar din in dai akan wanan yarinyar ne ido na zuba dani da jafar din a gidan nan za,aga waye zai sare a karshe.
Jikina ya sake yaraf kamar kayan wanki inaji kamar in juya kada in shiga dakin a lokacin sai dai na ba zuciyata sanyi na fada dakin da sallama.
Duk suka juyo suna amsa min shigowana ya basu daman sulalewa daga dakin suka bar mami tare dani ina fada mata sakon da hjy ta aikoni.
Naji ki fada mata za a saye na daga don barin dakin sai naji ta dakatar dani ta hanyar kiran sunana.
Da sauri na koma na tsuguna a inda nake tare da dukar da kaina kasa ina sauraren abinda zata fada min a lokacin.
Mami ta dan dade tana kallona na dan wani lokaci kafin ta bude baki ta soma magana dani.
Zeey ina son ki saurareni dakyau kiji abinda zan fada maki kaina gyada ina wasa da yan yatsun hannuna dana hade a wuri daya ina saurenta.
Ba zan taba bari ki bar gidan nan ba koda hjy bata nuna hakan ba don in taimakeki ki taimakeni na raboki da iyayyen ki zuwa nan.
Saidai zanso kiyi nisa da duk wani dana bawai jafar ba kwai a a ina nufin gaba dayan su muddin kina son mu zauna lafiya dake a zaman mu.
Zancen karatu kuma da mun koma abuja zan sa a nema maki wani makaranta gwaunati ki karasa karafun naki a nan.
Saboda haka in kinyi abinda na fada maki kiji dadina idan kuma kinki to ina mai fada maki zeey zaki kwammace dama baki sanni ba a duniyan nan.
Na riga nagiwa jafar mata amma saboda ke yana kokarin ya bijire min kan umurni na don kawai ya nuna min shi dan zamani ne.
Mami kiyi hakkuri in Allah ya yarda zan kiye ni ban taba magana dashi ba kuma bazan taba ko a bayan ki mami.
Shike nan zeey zaki iya tafiya mami ta fada ba sakin fuska a tare da ita zuwa gareni a yanzu haka na mike na fita daga dakin.
Karfe biyun rana muka fito mami tana makale da yan matan ta dake mata sallama mu kuma muna guri daya dasu ya jalal da hjy sai Aisha dake daga gefen mu tsaye tana sana,an ta da waya.
Ba wanda ya kula da yai min sallama kamar yadda suke sallaman su hjy da su jalal dan dama salma dace zeey za a tafi ke nan na danyi dariyan yake ina fadin sai mun dawo anty salma tace ko sai munzo ba.
Haka motar mu ya daga kamar su jawoni su fidani daga cikin motar yadda suke watsa min harara daga sama har kasa kuma kowa ya kula da hakan.
Karfe hudu duk muna cikin gidan mami na Abuja da farko mami taso raba muna daki ni da hjy don tace naje daki daya zamu zauna dasu kande a nan.
Sai hjy tace ni kuma na zauna dawa idan kin kaita can kinsan ko a gida da yaran yayan ki nake zama ai.
Don haka barmin ita mu zauna tare kawatace ko banza tare muke kashewa mu bisa a dakin mu daga ni sai ita.
Haka yasa na koma da zama a dakina dana bari da farko kafin mu wuce kaduna don yanzun ma a nan zamu zauna da hjy din.
Mami bata da lokacin zama gida tare da mu karfe taran safe baya mata a gida don hakane nake tashi da sassafe nai mata aiyukan dana saba mata a dakin ta harta shirya ta tafi.
Kamar yadda mami ta canza min hakan nima nake canza don a gurguje zan karasa aikina kafin ta fita na bar mata dakin sai idan ta gama zata rufo dakin ta kawo makulli gurin hjyn ta ta fice.
Satin mu daya da zuwa wani yammaci muna zaune da dare a falon dukan mu ya mamud ya shigo muka shiga gaida shi da dawo yana amsa muna.
Ina zaune kusa da kafan hjy naji yana fadin mami monday fa yarki zata fara shiga school don na samo mata makaranta a nan garin.
Da bakin wa kayin wanan mami ta fada a daidai lokacin da nake murnan hakan ina kuma gode masu a raina sai naji wanan furcin nata a bazata.
Gabana ya yanke ya fadi lokaci guda naji taci gaba da fadin ko akwai wanda ya kawo min ita gidan nan ne a cikin ku da kuke nuna min gaba gadi game da yarinyar nan.
Meye gaba gadi cikin wana zancen iyami ina taimaka maki yayi kan abinda baki samu lokacin yin sa ba kuma nautin kine kiyi hakan.
Ko haka yar taki zata zauna a gida ita bata karatu ta taimaki rayuwan ta nan gaba tunda a zamanin nan kome ka zama idan ba wanan karatun baka cika cikkaken mutum ba a idon jama,a..
Hjy kikan so tarewa yaran nan fada a kan gaskiyata da zai tafi nema mata ai sai ya nemi shawarata yaji abinda na yanke a kanta.
Fada muna yanzu ai gashi zaune me kika yanke a kan yar nan a yanzu tunda an hutar dake baki ga hakan ba.
Iyami bansan yaushe hali ki ya sauya ya zama na mutanen zamanin nan wajen , , ,
Hjy ba nufina ke nan ba bandai jin dadin yadda yaran nan suke min abu gaba gadi haka kamar banda daraja a gunsu kamata yayi yazo ya fada min kafin ya samo mata din.
Sai kawai yazo yanzu yana fada min magana haka kai tsaye wai mondaya zata fara tafiya wani makarantar ma ka samo mata din.
Mami inda yaran nan suke zuwa a nan na sama mata itama sai su dinga zuwa tare duk da ita a secondary section zata zauna.
What har nawa za a dinga kashewa a kanta ke nan ina kosu yaran nan kana min korafin yayi yawa da farko saidana haneka.
Mami indai zatayi kararun ai karuwan kowa ne nan gaba don haka kiyi hakkuri nayi kuskure ya fada yana dukkar da kanshi kasa alaman ban hakkuri a gareta.
Allah ya kyau hjy ta fada tare da dafani tana fadin yar nan nayi maki murna ubangiji yasa a shiga da kafan dama nace.
Yaya na gode Allah ya karawa arziki albarka yace ba komai ki dai dage da karatu sunce idan sun gwada ki kinyi nasara zasu iya barin ki inda kike a can kaduna.
Allah yasa hjy ta fada tana tattara takardun dake gaban ta alaman zata bar falon ke nan nayi saurin mikewa ina karban kayan daga hannun ta.
Sai naji tana fadin wa zai dinga sauke su a school din kai ko driver zai kaiku ya amsa da fadin.
Dama ai nike saukesu kafin in shiga office yanzun ma nidin dai ne zan dinga sauke su idan zan fita .
Ka nema masu driver daga yanzu da zai dinga sauke su kai ka wuce office din ka kaji abindana fada ta juya wurin hjy tana fadin hjy zan shiga in karasa aiki a daki.
Ni dai na aje kayan na fito daga dakin don babu wani abinda zan mata a lokacin don haka na dawo falon na samu hjy da yaya mamud suna hira Aisha ta shige dakinta ko lokacin.
Har kasa nakai na kara mai godiya yacs Jafar ne ya saka in sama maki nan don haka shi zaki godewa idan ya dawo.
Sai ki mai da hankali ki samu abinda kikaje mema banda wasa ko wani hali na banza don Allah.
Nagode yaya na kara fada kaina yana kasa nake fadin hakan don gabana na faduwa tun lkkacin daya ambaci sunan ya Jafar din.
Suna ta hiran su da hjy ni kuma ina faman tunanen gargadin hjy a raina a wani bangare kuma ina Allah Allah in ga na fara zuwa makaranta ranan monday din.
Rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya hausa suka fada don yau gani a class tare da diya manyan mutane don an gwadani na ketare da kyat don su ba wani gata da zaka nuna masu su yarda su kaika gaba saidai idan kokarin kane ya kaika.
Na mayar da hankalina sosai ga karatuna banyi kawa ko aboki ba kamar yadda naga wasu sunayi a school din koda yaushe ni kadai zaka sama a class din ina bitar takarduna da akai mana darasi.
Ranan kwatsan mun dawo daga school tun a haraban gidan idona yayi tozali da bodyguard din shi suna tsatsaye waje suna mazurai da idanu don motan mu daya danno kai gidan.
Gabana ya shiga faduwa haka na daure na shiga cikin part din mu da sanda nayi arziki babu kowa a falon sai tv dake aiki a falon shi kadai babu mai kallo.
Da sauri na shige dakin mu inda na samu hjy zaune ta idar da sallah la,asar a gurin tana zaune.
A gurguje na tube uniform din jikina na fada bandaki ban fito ba saidana shirya a cikin wani dogon riga duk kayan da Aisha ta ban ne nake sakawa a jikinao.
Na fito na o da sallah nacewa hjy zan leka kitchen in fito daga can na zauna abina ina taya su mama kande aiki har muka karasa na dawo don yin sallah lokacin har mami ta dawo tana dakin ta .
Tunda na tun karo wuein kamshin turaren shi ya daki hancina na tsaya na dan saurara ko yana dakin in koma kitchen in zauna har ya fita.
Naji banji wani hayaniya a dakin ba na shiga hjy ne zaune ita kade tana ganina take fadin wai ina kika shiga haka daga barin je in dawo naji shiru sai yanzu.
Har yaron nan ya dawo daga balaguron da yayi yana tambayan ki bai dade da fita daga dakin nan ba.
Wa ke nan na tambaya kamar ban fahince ta ba tace wanan bayahuden mana jafari ai ya dawo tun dazun da ranan nan wai wata kasa yaje kallon ball kawai don barnan kudi.
Shiru nayi don ban san me zan fada ba sai kuma hakan yaiwa hjy zafi take fadin anya yar nan kinko damu da yaron nan kamar yadda ya damu dake.
Don shi da zuwan shi ke ya fara tambayana na fada mai kindan fita sai gashi shiru shiru baki leko ba dakin nan sai yanzu daya fita.
Ko uwar taku tayi nasara a kanki ne tun yanzu nace hjy dan Allah ki daina zancen shi dani kada mami taji ta riga da tayi min kashedi a kanshi tun a kaduna hjy.
Ita iyami din hjy ta fada nace hjy kada kiyi mata magana ko dan karatun nan da yanzu nakeyi kada in rasa sa,ata ta wanan dalilin.
Wai maryama kanta daya kuwa gaba daya yarinyar nan ta rikice min lokaci guda na kasa gane inda ta dosa kan zancen nan.
Haka mukai ta shan bambam dashi ban yarda mun hadu ko sau daya ba a gidan tundaya dawo garin.
Ran ba makaranta ina zaune inawa kaina kitso muna hira da hjy ya fado dakin namu daga sallaman shi ya kutso kai ciki.
Ba daman in gudu in shige koda bathroom ns don ya riga daya ganni ko dole na daure na gaida shi tare damai an dawo lafiya.
Shima yadda ya amsa min naji dadin hakan don ba yabo ba fallasa gareni sai na mike zan bar masu dakin don dai kawai in kaucewa warning din mami gareni.
Ki zauna fita zanyi na leko hjy ya fada daga inda yake tsaye yana magana da hjy gashi ya kara haske sosao yayi wani kyau dashi bakin gashin kanshi yayi lub kwace a kanshi sai sheki yakeyi ga wani saje daya bari a fuska tasa wanda bai saba bari shi a fuska ba.
Yana gama magana ya sa kai ya fita ya bar dakin gabana sai faduwa yakeyi min don abinda idona ya gane min din duk da ban kalleshi sosai ba ma ke nan.
Tun daga wanan rana ban yarda mun kara haduwa dashi ba a gidan don ina ganin shima bai faye zama a gidan ba sosai sai jefi jefi.
Ranan zan fito daki ke nan don hjy na falo mami tafita gurin aiki bata dawo ba ina ganin shi na ruga da gudu na koma daki a zatona ko bai ganni ba ne.
Saida ya dan dade a zaune kafin ya mike ya nufi dakin namu hjy dai tana zaune tana kallon shi tare da tausayi mu a ranta.
Ya tsaya daga bakin kofa dakin bai karasa shigowa dakin ba sai hannun daman shi dayayi amfani dashi wurin rike labulen dakin dashi.
Wa kike gudu haka ya fada a cikin muryan nan nasa mai fida sauti mai dadin saurara kunnuwa suka jiyo min hakan.
A razane na juyo ina kallon shi yana tsaye a kofan yadda yake a wurin wani irin tsoro da damuwane suka ziyarci zuciya sosai take jikina ya fara kyarna ta yadda har ya fahinci hakan.
Hannun ya sauke daya tokare kofa dashi yana gyara suit din dayake sagale a hannun nasa karya fadi.
Takowa naga ya fara yi zuwa inda nake haka yasa gana ya tsananta da faduwa sosai a haka ya iso inda nake rakube ga bango ginan dakin.
Wani abu naji yana taso min wanda yasa na duntse idona a hankali kafin ya kara tako ya cin min a gurin.
Jin kamshin turaren jikin shi gab dani yasa na bude idona na dube shi kadan babu sauran tako a tsakanin mu ko daya a yadda muke tsaye a dakin.
Kokarin ja nayi baya sai dai babu inda zan daga don gaba daya ya tare wurin ya tokare hannayen shi a ginan dakin.
Shiru ya ratsa dakin ba wanda yai magana a cikkn mu kamar babu kowa a dakin lokacin.
Inan tsakiyan hannayen shi har lokacin idanuwa na a rutse kamar naga dodo a gabana.
Ga ba hanyar da zanbi in gudu daga wajen don ya hana hakan gareni ya kankame ko wane gefe da zan iya guduwa mashi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.