Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 105 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWAYA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA KASA MUNA CIKIN YANTTATUN BAYIN KA KA HANE MU DA AIKATA HARAMUN KOMAI KANKANTASHI KA BAMU IKON BAUTA MAKA BAUTA MAI TSARKI A GAREKA YA ALLAH.
YAN UWA BARKAN MU DA SHAN RUWA YA ALLAJ KA NUNA MUNA KARSHEN SA LAFIYA ALLAHUMAN AMIN, , , ,
INA MAKI TUNI DA MU GUJI SHIGA HAKKIN WANI DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA YAR UWA.
Haka na koma part dina a sabule ban tsaya bashi amsa ba sai juyawa da nayi na fita daga dakin zuciyana cike da zargin kaina ga abinda na aikata din ba tare da tunanen abinda zai je ya dawo a kaina ba.
Na dade a zaune ina wanan tunanen kafin na koma tuna abinda ya fada na nayi nasaran raba shi da giya da homosexual a yanzu wanda ban tabbatar da hakan ba duk daya fadi hakan da bakin shi.
Saidai zan iya cewa hakan don ganin yadda yake kashe lokacin a gida kuma tare damu ba ba irin zama tare da katan banzan da muka zo kasan muka samu suna baibaye dashi kamar jela.
Sun hanamu sakewa ko dogin motsi dashi a lokacin ko kaunan fitowa ba muyi mu gansu suma din hakane kiri kiri suke nuna rashin kaunan mu a fili basa boye hakan ko kadan a zuciyar su.
Yanzu ko sai ince kamar hakan ya zama tarihi a gare mu don tun dawowan mu daga Dubai ban kara ganin wanan taju din daya saka yar kara a tsakanin mu .
Na cewa dani dashi aga wanda zai karbe J din ni dai nasan ban fadawa kowa wanan zancen ba amma kuma gashi tun wanan ranan dana gansa tsaye zamu shiga ruwa har wanan ranan ban kara jin duriyan shi ba ko a gari.
Mikewa nayi na kewaya don fitsarin daya cika min mara din tsoro don a nawa wautan sai nake ganin yanzu babu yarda ko aminta a tsakani na da yaya din kan wanan zancen.
Na fito Sadiya tana shigowa dakin kin gama assigment din ke nan na fada eh na dauka kina part din ya j ne ai nazo na dauki wayan ki ne na duba tana fadin hakan ta nufi wurin da wayan ke caji a socket.
Gado ta fada tana fadin wanan gamen din nake son yau na karasa ko zan ci ina last stege din sa a yanzu ta fada tana gyara kwanciya.
Kokarin dauko kaya da zan saka na kwanciya nakeyi don haka ban tsaya nabi ta kanta ba sai dana gama na hau gadon ina fadin.
Wai ni wanan taju din yaron yaya ne ya fado min a rai yau wanan dan iskan mai baki kamar yayi wanka da kwata ?
Ni sam bai min ba wanan mutumin haka kawai nake jin tsanar sa don kallon banzan da yakewa mutane idan ya ganka da yaya J.
Ke sadiya harke yakewa hakan na zata aini kadai yakewa kallon raini haka ranan ai ban fada maki bane saida ya j yace ya fice masa a mota da suka daukoni.
Ki bari don Allah na fasa cikin mamaki wallahi anty kawai yacewa driver yaja mota ban gama shiga ba don shi yaya yana aiki a sytem a lokacin.
Mugu azzalumi wanan ma yafi mami bakin ciki da zaman mu da yaya na fada a dan hasale ni a dole an taba min kanwata .
Ranan kan taju yasha zagi a gun mu har Nabil saida muka tuno dashi mukayi masa nasa wasalin kafin na kai kwance don shirin barci .
Nan barci ya daukeni na barta tana game a wayan don haka take bata lokaci wurin buga gamen da ya fito zata shiga ta iya do rashin aikin yi da bamu dashi.
Washe gari naso na share sai dai hakan bai yuyu ba don shi da kanshi ya shigo wurin mu da zai fita ya gaisa damu a cikin sakin fuska bai nuna komai ba a ranshi.
Sai dai wani halin da ban san dalilin shi ba a yanzu da yaya yake tsiro min dashi shine yawan son taba min jiki isan muna tare.
Zai kama hannuna ko yayi hugging dina kamar yadda dabi,un yan kasan yake ko kuma ina zaune zai dan lakatar min kumatuna da hannun shi.
Da farko ina daukan hakan ga dan shakuwan dake tsakanin mune a yanzu yasa yake yawan min hakan.
Sai dai yanzu dalilin wanan maganan daya fada a daren jiyan yasa na fara zargin hakan da wani abu na daban da yake ji a hakan.
Don dacan ko kallo ban isa a wurin shi ba balle yayi gigin taba wani part na jikina da nake daukan hakan da kyama ko tsanan mata da yakeyi ne ya jawo hakan da yake nuna min.
A yanzu ma dalilin wanan tunanen shine bai fita daga falon ba saida ya dan rungumeni na sai ya dawo in kula da kaina don sadiya a nan ta barshi ta tafi don tunda na gama nawa karatun ya hutar dani da fitan safe saidai driver ya kaita ya kuma dauko ta idan ta tashi daga school din.
Haka ya fita ya barni da wanan tunanen tare da kamshin turaren shi a jikina wanda yakan dafe min a jiki kamar nice na shafa zan wuni ina jin kamshin a tare dani yana saukar min da wani irin feeling a jikina.
Na dade kwance a katon falon gidan wanda yaji kayan alatu iri iri na zamani sai babu ne kawai babu garemu a gidan.
Can nayi mika na gyara kwamciyana ina lumshe idanuna tare da wani tunane kafin na sake dan murmushi a fuskana don tunawa da zancen fadila da nayi a lokacin.
Da take fadin ke din fa mace ce da ko wani na miji zai kyala ido a kanki ya kasa kawar da idanun shi a kanki .
Balle mijin kin nan da yake yaro mai yayi da zamani ga kudi ga ilimi ga kyau ga tsare gida dole ko wace mace zata so ta mallakeshi idan ta samu wanan daman a wurin shi don haka ki kara kama jiki ki kwato mutuncin kina ya mace a wurin mijin nan naki.
Wanan sayi da tayi basar da kanki da kuke yi ba zai kaiku ko ina ba nan gaba zaku dawo kuna ganin laifin junane a tsakanin ku ga banza.
Wanda kema kina da laifin a wurun hubbasa hakan gareku a yanzu koda yana kyamar mata a rayuwan shi ke ki daure ga hakan ki bishi a yadda yake har komai ya daidaita a tsakanin ku nan gaba.
Haba fadila ina hakan zai yuyu ga mutumin da bakinsa ya fada bai san dadin dake ga ya mace ba da wasu mazan suke fadi.
Ta yaya zan iya mu,amula da mutumin da yake kallon mace kamar namiji a wurin shi bai dauki fadan ma,aikin Allah da wani muhinmanci ba ?
Mutumin da ya zabi ya butulcewa ubangijin shi ta munanan hanyoyin da Allah ya fadi irin azaban daya tanadarwa masu irin wanan halaiyan tun a nan duniya kuma ya karanta yasan da hakan.
Amma ya take sani saboda rudin duniya kawai da abokai sai naji wani irin tsana da kyamar shi yana sauk mn a zuciyana.
Hawaye ne ya gangaro min daga idona zuwa fuskana nake kokarin sharewa don takaici da jin zafin halaiyar yaya din a yanzu wanda nasan ba ko wace mace ne zata gane hakan ba don irin daulan da muke ciki a gidan kullun sai macen da irin haka ya sama na kaddaran rayuwa.
Abin akwai ciwo akwai takaici don koda nayi rantsuwa yafi dubu ba kowane zai yarda cewa bai taba aikata haka dani ba duk tsawon dadewan mu dashi na zaman aure da nakeyi a gidan shi.
Mutane ba zasu taba yardan cewa wani abu maka mancin wasan aure bai taba shiga tsakanina da yaya ba tunda ina zaune a gidan shi har tsawon wanan lokacin.
Allah na tuba ka yafe min idan har zamana da yaya laifine a wurin ka na fada ina mikewa zaune don kwanciyan ba zai min ba a lokacin.
Allah ya gani idan da a yanzu ne yadda nake din nan na kara wayau ba zan zauna da yaya koda na wata daya bane a gidan shi yana wanan halaiyar na Allah waddai da tsinuwa a wurin Allah.
Tambayan kaina nayi ni yanzu yaya zanyi da rayuwana don nasan komai boyo dole mutanen Nigeria su san wanan magana wata rana.
Kukane tazo min sosai lokaci guda ina fadin ya Allah ka yafe min in har zama cikin wanan gida mai zunubi laifine a gare mu baki daya.
Kuka nayi sosai har yanayi na ya canza ga baki alaman na wuni ina kuka ya baiyana a gareni wanda hakan ya saukar min da zazzabi.
Inda Allah ya taimakeni sadiya ce ta rigashi dawowa gidan shigowan ta yasa na dan tashi ta hada min tea ina zaune ina sha dukunkune sai gashi ya shigo dakin .
Da alama ko part din shi bai shiga ba a lokacin ganin yadda ya sameni ne yasa yasan babu lafiya a tare dani ga kuma muryana daya dan sauya a lokacin.
Lafiya meya sameki pretty na ganki a haka nace zazzabine kuma nasha magani ya sauka min a cikin wani yanayi ina kawar da kai nake wanan maganan dashi.
Takowa ya karasa yi har zuwa inda nake zaune yakai hannun shi zuwa jikina yana dan tabawa babu zafi jikin naki ya fada.
Ina runtse ido don tabanin da yayi din sadiya ce ta bashi amsa da fadin jikin yayi sanyi yanzu data dan sha tea din nan amma a kwance rijib na sameta dana shigo.
Ina zuwa ya fada yana ficewa dakin sai da ya dauki yan dakiku sai gashi ya shigo dakin wanan lokacin ya sauya kayan jikin shi zuwa wasu yadi masu taushi na kasan chaina.
Irin wanan kayan sukan mashi kyau sosai idan ya saka saidai bai damu da saka irin su ba shi ko su din farare ne kal dasu da wani dan less a kasan rigan da sai mutum ya duba sosai zai gane hakan.
Idan ya saka kayan musulunci yakan burgeni har bai isata kallo a ranan sai gashi yau din daya saka ko kadan bai burgeni ba sai ma kawar da kai da nakeyi daga kallon shi din tunda yai sallama ya shigo dakin.
Tashi muje asibiti ya fada yana shigowa dakin na kawar da kai ina fadin naji sauki ba sai naje asibiti ba .
No ban yarda da wanan ba tashi maza muje kiga likita nasan bakya ciwo a wasan dadi don hakan muje a dubaki.
Ban so ba ba kuma yadda zanyi dashi dole na mike hijjab na dauko yau na saka muka fita yana biye dani a baya yaiwa sadiya sai mun dawo.
Mun danyi tafiya kadan yake fadin meya sakaki kuka har kika jawa kanki ciwo haka lokaci guda ?
Kamar yadda bai kalleni ba nima hakan ban kallo shi ba sai bin motan danayi na kara narkewa a hankali ina lumshe idona.
Tambayan ki nakeyi zainab ya fada wanan karon yana dan kallona nima kallo shi nayi ina fadin kawai dai haka kukan yazo min.
Maganan tafiya Nigeria ke nan ya sakaki kuka haka ko har kina kokarin jawa kanki ciwo a yanzu ?
Shiru nayi kawai ba amsa don bansan abinda zan fada ba ya sakani kukan don ta dalilin shine hakan ya faru har nayi kuka.
Bai kara magana ba sai ma gudun daya karawa motan sai gamu wani asibitin dabana gwaunati ba nan dai yaga likita sai gashi an shiga dani ciki an dan min tambayoyi kamar mayu suma din sun gane hakan ya faru ne ta sanadiyar kukan da nayi yaja min hakan.
Likitan bai dauka ni matar aure bace koshi ya fada mai nidin sister shi ce oho har yake fadin ko dai nayi kuka akan saurayina ne ?
Yaja min zazzabi da ciwon kai na dan lokaci don jikina bai nuna wani abu yana shirin samuna ba da har kaina zai min ciwo.
Magani da sauran tarkace suka bani muka fito don ba zancen allura don wanan ciwon kawai da suka gani a lokacin baikai ai mun allura ba.
Bai dauki hanyar gida ba sai ya nufi wani wuri da suke sayar da kayan kwalama na sayin yayi leda biyu ya dawo muka dawo gida har lokacin bai kara min maganan komai ba saida zan fita cikin motan yake fadin.
Ki tabbatar da kin sha maganin nan yanzu don kada ciwon ya zama maki babba a jiki nan gaba.
Falo na zauna don sadiya tana falon shima da ya shigo nan ya zube ledojin dake hannun shi ya nufi kitchen da kanshi ya dauko min goran ruwa mara sanyi ya kawo min tare da fadin.
Karbi nan ya duka ya bude ledan maganin ya balla min ya miko na karba nasha don dole badan naso ba.
Na koma na kwanta saman kujeran yake fadin sadiya bude ledan nan ki dauka kusha ta taso da sauri tana budewa abinda ta gani a cikin ledan yasata murna tana fadin wai yaya ashe a kwai wanan a kasan nan ?
Ranan naga wanan taju din dashi yana sha mugu ya shanye bai bani ba kina son shine ashe ya fada yana dago grif fruit din ya balla tare da fadin ki wanko mana sai musha.
Amma Taju baya kasan nan ne yanzu na fada ba tare dana kallo shi ba yi yayi kamar baiji abinda na fada ba a lokacin sai da sadiya ta dawo ta aje fruit din ya kara tsunka ya kai a bakin shi ya tauna yake fadin kefa ba zaki sha bane kin tsaya kina tambayan wanda bai shafe ki ba ?
Ya shafe ni tunda yana tare dakai a gidan nan kaga ya shafeni idan akwai kara ai .
Ba mamaki tunda ke dashi kun dauki junan ku da kishi har kunawa juna barazana a kaina ko ?
Ni din na fada da mamaki yace karya zan maki bakuyi hakan bane dashi a dubai na nuna maki hakan a wayan ki ?
Sai yanzu ma na gaskanta abinda ya tunzuraki har kika zuba min maganin da kike ganin zai hanani wani halaka dasu a yanzu.
Idan ma na zuba kanshi ai ba laifi nayi ba tunda kaima ka fada yanzu da bakin ka cewa shi din kishiyatace a wurin ka kaga ko zanyi komai a kan ya barka har abada idan zan samu daman yin hakan ai ba laifi bane.
Zaki ba kanki wahala a kan hakan don kowa da kalar rayuwan shi abinda wani ke so bashi wani ke so ba ai.
Koda ace Allah ya halasta hakan akan mutum zai ki bin umurnin Allah na fada ba tare da na dago ba saidai zancen ya saka sadiya a cikin tamtama don bata san dalilin da yasa muke wanan maganan ba.
Dama nasan meya sakaki wanan damuwan har kikai kukan daya ja maki ciwon kai kina son ki bawa kanki wahala akan hakan.
Yaya ka daina ba kanka wahala da tunanen zan iya zubama abinda zai cutar dakai don ban san kowa ba a kasan nan da zan shiga na samo wani abu.
Nasan wanan shine kuma abinda ke daure min kai har yanzu kan hakan zuciyana ta kasa gaskanta min gaskiyan wanan zargin da nake yi.
Zargin yayan mu kakeyi yaya sadiya ta fada a cikin mamaki ba zarginta nakeyi ba sadiya idan ma tayi hakan tayi nasara kan abinda ta aikata din.
Ya mike tare da daukan ledan shi fuskanshi a daure ya nufi part din shi na dade ban dago ba bayan tafiyan shi sai sadiya take fadin akan me yake maki wanan zargin yaya ?
Gashi kinji ya fada wai nice silar barin Taju gidan nan wanda bansan kan abinda yake magana ba ?
Gara daya bar gidan nan wallahi don ni wanan mutumin bai mun ba sam ya faye fadin rai da jin haushin mutane wallahi.
Duk da dare ne a lokacin bai hana ni shiga part din yaya ba a lokacin nayi mamakin ganin kofan a bude bai rufe ba.
Har na wuce falon banji motsin shi ba kamar mai sanda nake tafiya zuwa bed room din shi sai kamshi ke tashi ta ko ina a part din.
Kasa na hango shi zaune saman ties din dakin ya aje kwalba da cup a gaban shi sai kankara daga gefen shi da alama kamar sallah ya idar ya zauna a wurin.
Da sauri na juya zan bar dakin naji muryan shi yana fadin karaso mana ki shigo ina kuma zaki bayan kin shigo ?
Kamar zan tafi sai kuma na juyo na karaso inda yake zaune din kallo daya nayi mai na kawar da idon ina fadin.
Nazo muyi magana akan wanan zancen da kake fada min ko yaushe saidai kuma gashi ko a yanzu din hakan na nuna baka bar komai ba da kake yi a baya.
Ya dago kai yana fadin da kikaga me a yanzu ina kin ban maganine din na daina sha da sha,awan maza yan uwana da Allah ya doro min ?
Allah bai doro maka hakan ba kai ka biyewa shedan ya dora ma wanan halin don da abin kwarai ne da sauran yan uwan ka sunyi hakan.
Na gane akwai raini mai yawa yanzu tsakanina dake zainab zaki iya fada min maganan da duk yazo maki a baki ba tare da kinji shakkar fada min hakan ba.
Daga inda nake tsaye na kalleshi nake fadin ba zan taba son na kasance cikin irin matan nan ba a rayuwana saida yin hakan ya zama min dole a yanzu don sanin kokai waye a gareni.
Nafi kowa kusanci gareka yanzu a duniyan nan kasancewa ta wace muke kwana muke tashi a rufi guda ma,ana a gida daya .
Murmushi naga yadan yi kamar yadda yakeyi idan baison magana yanzu yaya sallah ka idar amma ka tasa giya a gaban ka kana sha fa ?
Zainab wai me kika daukeni ne halan ina don na daina shan giya kika ban maganin da ki kaki amsa hakan cewa don shi kika ban har yanzu.
To don me kuma zaki dawo kina zargin har yanzu ina shan giya a rayuwana giya a yanzu ko sunan sa bana son ji a rayuwana.
Yasa a kullun nake maki korafi kan abinda na kasa bari don kaina sai gashi ke kinyi nasaran rabani da wanan dabi,an a cikin sauki.
Kina zaton yawan tambayan da nake maki kamar da wani manufa nake maki hakan No ina tambayan kine don nasan ainihin inda kika samu wanan makarin a cikin sauki.
Yadda yake min magana a lokacin zaka fahinci akwai abubuwa a zuciyar shi da suke damun shi don ba yadda nazo muyi maganan kan irin yadda ya sani a gaba da wanan zancen har hakan yake damuna ba sosai.
Wanan idan ba giyar bace meye yaya kana ikirari a kullan yanzu ka daina sha ka daina sha kamar ruwa yadda ka saba kwankwada ko me ke nan haka ke nufi yanzu ?
Ya dago idanun shi da suka sauya kalla don abinda nake fadi yace ko zan boyewa kowa halin da nake ciki ba zan taba boye maki ba ke don nasan kona boye zaki san gaskiya.
Ya dago kwalban yana fadin karbi ki duba idan giya nake sha don zuciyar ki ya huta zargina kullun.
Wani iri naji kunyane ko tausayi ban sani ba yana fadin ni yanzu kunyar kaina nake ji a wurin kowa idan baki sani ba ma yau ki sani giya dai kan na daina shan sa har abada ta dalilin ki zainab.YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA UBANGIJI ALLAH KA YANTA MU CIKIN YANTATTUN WANAN WATAN MAI ALBARKA AMIN YA ALLAHU.
ALLAH KA KARFAFA MUNA ZUKATUN MU MU ZAMO MASU KASKANTAR DA KAI A GARE KA AMIN YA ALLAHU, , , , ,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.