Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 90 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWARAYUWA TANA FARUWA WUCE TAKE KAMAR BA AYI BA UBANGIJI ALLAH KA NUFE MU DA AIKATA ALHERI A KULLUN DA BIYAYYA TSAKKAKE A GAREKA ALLAHUMA AMIN, , , , ,
Sun gama duk wani shirin daya dace ga tafiyab su kamar yadda suka tsara abinsu gaba daya gidan zasu zo mai hutu wanan karon har yan matan mami da har yanzu suna lake da ita a gidan.
Ya jamal ne yace sai a rage yawa mami tace don me za a rage sun riga da sun sa rai ga tafiyan nan bayan hakama.
Shida ya dauki diyan talakawa zuwa can yana biya masu komai sai nasa da zamu dan je muyi sati biyu ko uku acan mu dawo zakace wai wani a rage yawa.
Barima in kira yar iskan yarinyar in sheda mata don kada muje tace zata yi muna halin su na yan talkawa da kuwa naci mutuncinta sosai wallahi.
A take ta fara kiran layina fitowa na daga class ke nan kira ya shigo min na dauko waya ganin mamine yasa na dauka da sauri na fara gaida ita.
Bata karba gaisuwa ba sai cewa da tayi ke ki bude kunnuwa ki kiji da kyau duk sanda na shirya zaki iya ganin mu gidan ku.
Zanzo inga irin iskancin da kikeyi don samun wuri a gidan shi don na kula yanzu gaba daya kuna kokarin jaye hankalin shi gareni da yan uwan shi.
Sai ke da iyayyeb ki kawai ya sani a yanzu zan zo zan sa ido na gani idan har hakan gaskiyane ba zan daga maki kafa ba wanan karon.
Zaki san ni maryam ba sa,an yin ki bane har uwayen ki dake kauye suna maki tafi har idon jafar ya rufe a kanki.
Daga inda nake ina sauraren ta na runtse idanuwana don iyayyena data sako a cikin zancen naji wasu irin hawaye sunzo min suna kokarin zuba a idona.
Da kyar na iya budan bakina na furta mami Allah ya baki Allah ya kawo ku lafiya naji ta kashe wayan.
Nabi wayan da kallo na girgiza kai tare da barin wurin na cin ma Maya a inda muke zama na zauna.
Kallon yanayi tayi taga ya sauya gaba daya take tambayana abinda ya sameni zan iya cewa ranan ne karo na farko dana fara ba Maya din labarina a takaice.
Ranan haka na dawo gida da bacin rai a tare dani ban fadawa kowa wanan zance ba haka na barshi a zuciyana ina dakon wahala.
Ba abinda yafi batawa mami rai kamar yadda akace karatuna har na kusa gamawa a yanzu don dan watanni ne ya rage muna mu karasa don haka take jin wani irin tsana tun lokacin da jamal ya fada mata hakan.
Ga karatun su baiwani ci gaba ba wanan lokacin dani a can na kusa kammala karatuna zuwa wanan lokacin na zama wata irin classic queen don daula da nake samu zakace yar wani basarake ne nidin.
Don gaba daya na tattara damuwana da tsoro na aje a wuri daya na fuskanci karatuna zuwa wanan lokacin .
Addu,a kan kullun muna kan yinsa ba fashi halimatu ma yanzu girma ya soma zo mata don haka na kara taka tsantsan tare da sa ido ga duk wani al,amarin ta.
Banda kawa kaf kasan bayan Maya duk da ba addinin mu daya ba hakan bai hanamu kawance ba don babu wanda ke tabo addinin wani a tsakanin mu.
Iya ka dai abu gudane idan lokacin ibada yayi zata rakani inyi ibadana ko ta tuna min is time for pray.
Inda nima hakan zan tuna mata da nata lokacin ibadan su idan ta shagala da karatu inda na kulla da yaya jafar yanzu.
Kawar da kai da nake ga al,amarin shi yanzu mun koma kamar wa da kanwar shi ga yawan alheri da kyautatawan da yake muna yanzu.
Don mota ko yaushe a cikin canza min shi yake da yayi yan watanni a gurina zanga ya sawo min wata an dauke wancan na farko.
Sutura ba,a maganan shi a wurin mu har fadila don yadda yake dan gayu dan kwalisa haka yayi kokari ya mayar damu muma da sutura tun bayan iya sakawa har yazu na iya irin kwaliyan su saidai ban yarda na kaucewa addinina ba da hakan.
Mun samu hutu muna zaune gida don bikin kirismeti da zasu yi a kasan ko mu da bamu addinin su an gyara muna gida yadda ya dace.
Amma saidai duk wanan abin baisa na daina jin tsanar shi da kyamarshi a raina ba sai dai ina kokarin ganin na nisance shi ga duk wani abinda zai kawo muna matsala ga hakan.
Falo muke zaune dukkanmu mu uku kallo mukeyi fadila da halimatu da yanzu bakina ya saba da sadiya kamar yadda kowa ke kiranta a gidan dole nima na kama kiranta da sadiya yanzu.
Sai fira suke tsakanin su da fadila yayin da hankalina ke ga karatun da nakeyi ga drinks da dan tsunken da nake zuka sai snack a gabana da nake dan hadawa ina ci.
Kofan aka turo alaman mutum ya shigo gidan a lokacin hakan baisa na dago kaina daga karatun ba sai da naji sallama muryoyin da ba zan taba mantawa dasu ba a rayuwana.
Muryan jalal da jamal ne don sune farkon shigowa gidan da sauri na dago kaina don jin muryan su da nayi mukai arba dasu na mike tsaye.
Ya jamal kune tafe na fada cikin farin cikin ganin su na nufi inda suken a lokacin aka turo kofan sai ga mutane na shigowa.
Tsaye nayi ina mamakin hakan a raina nace yanzu yaya yasan da zuwan su shine bai sanar min ba in san da hakan in shirya.
Mamice da hjy kusan na karshen shigowa gidan ganin hjy na manta da kowa don suna tsaye soror sai kallon mamaki suke min gaba dayan su a lokacin.
Sannun ku da zuwa nayi masu ina kokarin amsan jakkar hannun mami data rataya a kafadan ta kamar yadda ta nasaba amsa idan tadawo lokacin da nake gidan ta.
Fuska a daure tana yatsune fuska tace No ki barshi kawai sai banji dadin hakan da tayi min ba a gaban kowa don yan matan suna tsaye sun daskare a wuri daya sai kallon mamaki suke min.
Fadila har ta mike ta shiga kitchen ko ta hado masu abin tarbon baki ta kawo ta zube a gaban su bissimillah nayi masu wasu suka fara dauka .
Wasu kuma mamaki ya hanasu ai watar da komai suna zaune kawai sun zuba min ido tare da bin ko ina na gidan da kallo.
Na gaida mami ina masu anzo lafiya ta katseni da fadin yar mulki ashe kina gaida mutane ke nan ?
Dama tsiyan tallaka ya samu wuri ke nan sai yayi kokarin mallake komai ya dauka komai a banza akayi shi.
Haba iyami daga zuwa da wanan zaki tarbi yarki dashi ina shi arziki Allah kewa bawa shi.
Na dauka ai wanan zancen ya rigada ya wuce tun tuni a wurun ki don da rabo ya ratsa ai yanzu sun kai ga diya biyu a gidan nan rabon dai ne dake nesa ya kawo hakan.
Hjy da wanan ta daukeni uwa ai da ba hakan ba banga ranan da zan dauki zainab a matsayin sakuwana ba a zuciyata.
Maimakon inyi fushi irin da ko hawaye sai murmushi da na sake a fuskana kadan mami kiyi hakkuri ko na kira ba s dagawa yasa na daina kira yanzu.
Kowa shiru yayi yadda nake magana babu shayin komai ga hausan nawa zakace ma yare nakeyi a lokacin.
Komawa nayi saman kujera na zauna tare da harde kafafuna daya saman daya wanda bansan nayi hakan bani don sabo a yanzu.
Na dago kai a hankali na kalli inda su Aisha suke zaune dasu Rufaida nace kunzo lafiya ya hanya ?
Firgigit sukayi saida Aisha ta mike take fadin lafiya nuna muna dakin da zamu sauka don Allah ta fada tana nuna gajiya a tare da ita.
Sadiya take her to my room na fada sadiya ta mike da sauri tana fadin muje ita da kanta taja logued din ta zuwa dakin nawa.
Na juya wurin fadila nace a gyarawa mami dayan dakin part din can sai dayan na sauran sisters hjy zata zauna a dakin ta.
Nuriya kan ido ta zuba min mamaki ya hanata sauke numfashi ga yaran ta da alaman basu ganeni ba ma su.
Haka na fada ma Fadilan komai yadda zata kai kowa masaukin shi har nuriya da yaranta da mijinta.
Wai ina shi jafar din yaje ya mamud ke tambaya mami ta amsa da fadin nima shi nake son in tambaya ai yanzu.
Yana ciki na bata amsa kai tsaye shine baki fada mai zuwan mu ba muka kallo juna da fadila a daidai lokacin da mami din ta mike tana fada.
Wai zan rabata da danta da yan uwan shi dama burina ke nan inga kowa bai mameshi ba nasa ni dai har yanzu murmushi kawai nakewa fadan nata .
Duk da raina yana baci a yanzu yadda take kokarin tozartani a gaban yayan nata dake zaune.
Da ace mami tasan nima maraba nake nema da dan nata da bata tsaya bata baki ba haka don ni a yanzu godiya zan mata idan har ta rabani da danta.
Haba mami ya mamud ya fada baki sani ba ko tana da dalilin yin hakan amma yaya zainab zata hanaki ganin danki kuma ?
Kai mamud wai meyasa baku son ana zancen yarinyar nan ne haka wai ?
Yanzu har sai mun tabayeshi zata fada mai munzo koda a ce bamu bane muka zo gidannan
Ina part din nasa yake ta tambaya mami yana ciki baya son ana shiga mai part na fada maki ya jamal ke magana tare da nuna mata saman inda dakin shi yake.
A fusace mami ta nufi can din tayi sa,a kofan na bude ta tura ta shiga tana fada yadda ta samesu da yadda ya ganta a bazata ne yasa kowan su shiga rudani.
Shi dama a irin wanan lokacin da ake zaman gida yake samun lokacin sheke ayan shi yadda ranshi ke so a gidan.
Da baya baya mami ta fito daga falon a daidai lokacin na iso wurin don gudun abinda zai biyo baya a lokacin.
Ji tayi na rike ta ta baya nayi part dina da ita ba tare da kowa yasan meya ke faruwa a lokacin ba mami na biye dani har zuwa bakin gado na zaunar da ita kamar mutum mutumi.
A daidai lokacin Aisha ta fito daga wanka yanayin data ganmu ciki yasa taja ta tsaya daga kofan bayin tana kallon mu da mamaki.
Don yanzu ta barmu a falon mu fada gamu kuma tare a cikin wani yanayi ina ganin ta nace mami don Allah ki natsu kada hankalin saura ya tashi zan mamaki bayani daga baya .
Na mike tare da fita daga dakin da sauri na nufi part din nasa ina shiga yana zaune daga shi tawul a jikin shi daure a kugun shi.
Jin shigowana yasa ya dago kai gareni yana kallona nima kallon shi nakeyi tare da fadin kasan zasu yau yaya ka tsaya aikata wana fasadin ?
Kamar ya nasan zasu zo bake kika gaiyato su suzo dama ba ni na fada da mamaki a daidai lokacin da dayan katon gardin ya fito daga dakin da sauri yana gyara aninin rigan jikin shi.
Yana son fita daga dakin da hannu na nuna mashi ya koma ciki ya tsaya yana kallona da mamaki na juyo wurin ya jafar din ina fadin kowa na gidan nan yanzu don har ya mamud da Family shi suna tare.
What , ya fada da dan karfi nace sosai kuwa zan fita zan fada masu baka gida don mami ma yanzu haka tana dakina a cikin wani hali.
Shiru yayi har na gama bayani da zanyi na juya don barin wurin naji ya ambaci sunana a sanyaye da zainab .
Jin hakan yasa na tsaya cak may yasa kika bari mami tashigo part din nan ya tambaya yana dago kai.
Banda hujjan da zan dakatar da mami zuwa part din danta idan baka manta ba kuma kayi mi warning na daina shigo ma part din ka matukar bakai ka nemeni ba.
Don haka babu yadda zanyi in shigo ma don kai da kanka kayi warning dina akan ha, , , , ,
Koma su waye kice dasu gani saukowa kada kice masu komai tunda mami ta riga data ganni ko yanzun zanyi wanka in sauko.
Ban tsaya jiran abinda zai karasa fadi ba nasa kai na fice a dakin cike da takaicin shi a raina lokaci guda.
Dakina na koma don kowa na masaukin da aka bashi suna sauke gajiya ina shiga dakin na samu Aisha tsaye a kan mami data kasa magana tun fitana dakin.
Tsugunne nakai gefen gadon tare da dukar da kaina hawaye na zuba min a idanuwa tana kwance bata ko motsa a yadda take ba.
Jin sheshekan kukan nawa yayi yawa Aisha da take a rude take fadin mami wani abu ya farune da na shigo daki halan ?
Shiru ba amsa daga gurina har mami din da idonta kawai ta tsurawa kofan shigowa bata ko kfttasu don gaba daya ta fice cikin hayacin ta a lokacin.
Aisha dan fita ki bamu daki mami ta fada ba tare data iya dago kai ga yar nata ba Aishan ta fita tana dan waige da sauri.
Sai bayan fitan Aishan daga dakin muryan mami yazo min a kunnena tace zainab na amsa da na,am mami.
Wani irin rayuwa kukeyi gidan nan da mijin ki ne don yanzu na sameshi dana shiga a cikin wani hali.
Alama ya nuna kin san komai a kan hakan don yadda kika taroni daga baya zuwa dakin nan ya nuna min kin san abinda idona ya ganan min ke nan ?
Kai na dago cikin hawaye na dan kalleta sai kuka ya rinjayeni ganin hakan itama mami ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Jin ana nocking din kofan yasa nayi saurin share hawayena na mike zuwa budan kofan hjy ce tare da ya mamud .
May ke faruwane da zuwan mu mami ya mamud ya fada a lokacin mami ta kara karfin kukan da takeyi din gwanin ban tausayi.
Kai kai haba mami wanan ai saiki dagawa mutane hankali mu dauka wani abu mumunane ya same ki daga zuwan mu ko kin samu wani sakone mara dadi daga gida ?
Haba dai wani sako iyami zata samu har ya daga mata hankali haka tana wanan irin kukan haka yanzu ?
Hajiya take fadin hakan tare da juyowa inda nake gurfane nima kukan nakeyi sosai a lokacin .
Wanan abin naku akwai daure kai wallahi ko dai wani abune ya samu shi jafarin bamu sani ba sai yanzu da zuwan mu zamu samu labari ?
Cikin karfin hali nace da ita lafiya yake hjy dama dai magana ce muka danyi da mami ya saka ta kuka don Allah kuce ta yafe muna zan bar yaya jafar din idan haka shine zai sa mu samu jituwa da mami dagani har yayan.
Jin abindana fada mami ta rage kukan da takeyi tana fadin zainab ni dama baki min komai ba zainab don dai rashin biyayyan da kukaki min ne ai tun farko nake wanan haukan daku.
Mami kiyi hakkuri ki yafe min ki roka min ya jafar ya sakeni in koma gida zaifi muna sauki.
Shout up zainab a kul na kara jin wanan zancen a bakin ki zan saba maki rai a wurin nan abinda ya riga ya wuce ya wuce ko ya mamud ya fada
Yau zainab da bakin ki zainab kike fadin hakan duk hakkurin da kikayi da wanan auren ai yanzu kun zama daya kike furta ya sakeki ?
Zata ce hakan dole hjy don jafar mutumin banza ne a yanzu na fahinci dalilin shi na zaben zainab dayayi a matsayin matan auren shi.
Wanda dacan hankalina bai kawo min haka ba sai yanzu dana fahinci waye jafar din don rayuwan jafar baida kyau hjy.
Jafar ya fita daban a cikin yayana da al,umman musulmai baki daya hjy zan iya fadin yau nayi dana sanin haihuwan jafar da cikina wallahi.
Wa,iyazu billahi mami don Allah ki bar fadin haka ko mai yai maki haka mai zafi kiyi hakkuri ki tausa zuciyar ki akan shi.
Idan kaga na yafewa jafar har mun shirya dashi ya daina wanan halin banzan da yakeyi a rayuwan shine zamuyi zaman da uwar shi.
Don haka yau ba sai gobe ba gaba dayan ku ku shirya mu bar masa gidan shi don banga amfanin zaman mu a gidan mai fasadi irin jafar ba.
Wa iyazu billahi iyami dan naki kike aiban tawa haka da bakin ki har kina kiranshi da mai fasadi wani irin aikin asha yake aikatawa mai muni haka.
Please mami don't tell her abinda idon ki ya gane maki don hjy bata da karfin zuciyar daukan wanan maganan a yanzu na fada da turanci.
Gaskiyane ya mamud ya fada shima a cikin harshen turanci sai hjy tace nasan dai ba zai wuce akidan nasara ba da yake yawan dauka kuma ko yaushe mukai waya ina masa huduba da hakan.
Jafar din ne ya turo kofa ya shigo da alama ya danji wani abu daga cikin zancen namu a dakin don kofan a rufe yake lokacin.
Yayi wankan shi fes ba zaka taba cewa shine ba mai mumunan halaiyan nan idon shi akan mahaifiyar su dake darzan kuka saman gadona.
Kafin ya mayar da kallon shi wurin hjy dake tsaye a kan yarta ni kuma ina rusunne a gefe ina hawaye.
Hannun ya mikawa ya jafar yana fadin so you surprise me zuwa haka babu sanarwa duka family baki daya.
Cikin dan basarwa ya mamud di yace dokan mami ne hakan ta hana kowa ya sanar daku zuwan mu saidai ku ganmu kwatsam.
Nayi dana sanin wanan zuwan yafi dubu dana san abinda kake aikatawa a kasan nan da ban taba taka kafana zuwa gidan ka jafar .
Dan murmushi yayi irin na masu karfin hali tare da fadinn haba mami me yai zafi haka kuma da bazaki zo gidana ba .
Ai ko baki zo don ni ba zakizo don yar ki nan ki ganta kiga inda take zaune tunda kin huce damu.
Shidai na gani sai dai kuma kai ja,iri da zuwan uwar taka ka bata mata rai haka me kayi haka da zafi har ka fice mata a raine lokaci guda ?
Dan murmushi kawai ya sake tare da kallon mamud yana fadin ina madam da yaran su ke ko har dasune tafiyan .
Kowa na nan ya mamud ya fada tare da fadin muje daga waje don mami ta huta ya soma tafiya yana fadin hakan.
Shi kuma ya mara mai baya muryan mamine ya dakatar dasu din da wani irin tsawa take fadin mamud na fada ma kafita ka samo inda zamu sauka gobe zamu bar kasan nan da yardan Allah.
Lokaci daya suka juyo gareta da mamaki suna kallon ta hjy ce ta katse su da fadin kekan tir iyami da wanan halin naki na rikau.
Don kawai danki ya bata maki rai zaki fadi haka gareshi idan kinyi hakan ma kanki kika bawa kunya ai.
Kada ki manta wanan tafiyan ba iya diyan ki kawai kikayi shi ba don haka ki shiga hankalin ki tun kan duniya ta saki a baki.
Ki fada muna laifin yaron nan kuki fitowa fili ku fada daga ke har matar tasa sai kwanaye kwanayen da kuke muna a yanzu.
Wanan maganan da hjy tayi yasa jikin mami sanyi amma kuma sai ta sake wani sabon kuka mai tayar da hankalin mutum .
Ya mamud din ne yajashi suka fice daga dakin suka sauko kasa nan ma babu kowa duk suna dakunan da aka saukesu suna mayar da fadi a game dani da kuma irin gidan da muke zaune.
Inda Aisha ke basu labarin ai basu ga kallo ba sai idan sun shiga dakina da nake zaune a ciki a nan zasu sha mamaki wai duk zee ce da wanan daulan haka.
Har suna hada baki wurin fadin ki bari don Allah nan ma din kadan ke nan ashe muka gani bisa ga nata din
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.