Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 77 of 139
Har muka tashi a gurin ya jamal dake dakin shigewan mu yana jin mu nikan ina shiga dakin ban daki na shiga na dauro alwala na fito.
Nafilan da na saba yi duk dare kafin in shiga wanka nayi kafin in dora da shafa,i da wutiri na mike na gyara jikina tsab yau da yake mun dan dauki lokaci muna fira a falon sai yasa ban samu zuwa na kwanta a makwancina da wuri ba.
Na gama tsab na jawo kofana lokacin wata zuciya tana fada min inyi kwanciyana kawai a dakina tunda dare yayi a yanzu.
Saidai na wuce kada hakan ya jawo min laifi a wurin shi kuma tunda mun aje hakan dashi tun zuwan mu garin.
Na fito na jawo kofana na rufe na nufi hanyar part din shi kai tsaye sai dai nayi mamakin ganin kofan a rufe a ranan.
Murdawa nayi don ina jin dan kida yana tashi a ciki yasa nasan baiyi barci ba a lokacin idon shi biyu wata kila yana falke yana sana,arshi ta latsan waya ko computer.
Kofan na dan duka kusan sau uku a lokaci daya naji na a bude ba don haka nayi niyar juyawa in koma dakina.
Naji ana bude kofan haka yasa ni waigo don na koma in shiga tunda ya bude part din a yanzu.
Saidai ana budewa ne idona yayi tozali da wani farin matashi a tsaye daga shi sai tawul daure a kungun shi yana rike da kofi a hannun shi da wani abu a cikin sa.
Da mamaki nake kare mai kallo a cikin wani yanayi dana kasa gane koshi waye da har ya shigo part din yaya din kuma gashi daga shi sai dan tawul a jikin shi.
Muryan yaya naji daga bayan shi dake fitowa daga cikin daki yana fadin who is there ?
Cikin tambayawa sai saurayin ya jaye daga kofan don yaya din ya hangoni shima dai yana daure da towel kamar daurayin na farko.
Wani irin faduwa gabana yayi lokaci guda nake kallon shi da mamakin ganin haka karara a fuskana.
Yanayin fuskan shine ya canza lokaci guda munayin arba da shi a wurin yake fadin ke mekikeyi har yanzu baki kwanta ba.
Saida nayi mai wani kallo na raini na sauke akan cup din dake hannun shi na juya ba tare da na bashi amsa ba na koma dakina na rufo da makulli.
Saman gado na fada lokaci guda wanan karon ban iya yin kuka ba sai tambayan kaina nake me nagani me sukeyi haka a ciki ?
Ta yaya shi yaya zai yarda ya kawo wani bako a part din da muke kwana a tare har zai yarda wani bako yazo haka ya kwana a ciki harda tubewa haka dashi.
Anya waiko yaya yasan addini kuwa yasan abinda shari,a ya tanada kuwa yau aiko matsayin kanwarsa nake bazai kawo wani kato a part din shi ba yasan ina cikin part din kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWABan fito daga dakin ba sai dana kwatanci fitan shi a gidan don wanan abin na daren jiyan daya tsaya min a raina.
Ina mamaki duk dakunan dake wanan gidan ya jafar ya rasa inda zai sauke bakon shi sai part din shi alhalin yasan bashi kadai bane a part din nima a nan nake kwana.
Anya kuwa ya jafar yasan addini kuwa sosai ai ko ba matar shi nake ba zaman kanwarshi nakeyi a gurin shi balle wanan kasan mutane da nazo ta dalilin shi.
Ya kamata ace ya tsare min mutumcina da kimana na ya mace a gurin kowa balle kuma ina zaman matarshi ta sunna a yanzu.
Idona kodai kodai sai dan fuskana daya kara yin fau ya wani zuke saboda kwana a kusan rayen da naye a daren jiyan .
Nayi mamakin ganin ya jamal a gida shi da yake fita tun safe zuwa duban hjy a asibiti sai gashi yau na ganshi a gida tare dasu mama a falo zaune.
Gaba dayan su ido suka zuba min har na karaso inda suke zaune ban zauna ba saida naje gaban mama na tsugunna na gaida ita da kwana.
Kafi in juyo wurin ya jamal shima na gaida shi ta amsa tana fadin yanzun ko maman ku ta bugo waya tana tambayan ki nace baki tashi ba tukun.
Ashema kina falke ban sani ba na tashi tun dazun mama bandai fito bane kawai ina ciki ina fitar da kayan wankina.
Wurin halimatu na juya ina fadin halimatu lafiya kuwa don yanayin ta danaga ya canza lokaci guda.
Ta dan nisa tare da fasin yayan mu ina kwana ashe ba barci kikeyi ba ma ?
Lafiya kalau take don yanzu take muna zuba a nan tana bamu labarin karatun ta ana dariya kece ma dai yanayin ki ya nuna kamar dai baki da lafiya yau.
Lafiya ta kalau mama na bata amsa ina mikewa tsaye sai naji halimatu na fadin yayan mu ina wanan rigan da nazo dashi sabo shi nake son in saka yau jumma,a.
Yana daki mana ki duba na bata amsa ina zama sai take fadin ban ganshi bane tunda mukazo kuma naga kin dauko min shi.
Na dauko mana yana daki ki duba kafin in gama magana mamata mike tana fadin barin kdan kewaya na fito yanzu da wanan rigiman na sadiya don ni kadai ke kiranta da halimatu kamar yadda muka saba tun a gida.
Barin mama wurin yayi daidai da barin halimatu don haka aka barni dagani sai ya jamal zaune a wurin.
Sai dan shiru ya biyo bayan hakan can na dago kai na dan kalleshi nace ya jiya ya jafar ya ban mamaki a gidan nan.
Banso na fada ma wanan maganan ba amma ya zama dole in fada mashi a yanzu don shi kanshi yaya yasan haramun ne sauke bako haka balagage a part din shi kuma yasan ina a cikkn part din.
Wani kallon mamaki ya jamal ke min hakan ya hanani ci gaba da maganan da nake son fada a lokacin.
Kai naga ya girgiza yana fadin nasan ba zaki so hakan ba idan kin gani don ke ba jahilan addini bace zainab don nasan kinsan kanki duk da kina yarinya karama.
Da sannu zaki fahinci abinda ni na kasa fada maki daga cikin halayai shi saidai ke wani mataki kika dauka da kikaga hakan ?
Na bude baki da zuman magana naji halimatu na fadin nifa ban gani ba yayan mu sai kuma muryan mama tana fadin kijeki duba mata tunda yau fitina take ji kan riga kamar karamar yarinya dake tana hararan ta.
Mikewa bayi don bin umurnin mama din muka jera zuwa ciki da halimatu din muna shiga dakin take fadin nafa ga rigan yayan mu.
Dama ina sin ki tasone in fada maki abinda mami ta fada a kanki da ta kira wayan wai cewa tayi dake wai kece yar mulki dan tallaka bai iya samun wuri ba za a ce har yanzu kina kwance kina barci.
Inji mami din ta fadi hakan don Allah daga yau kome mami ta fada a kaina kada ya kara damun ki kuma ki bar fada min don in banji ba banji bane kin gane ko ?
Ta gyada min kai alaman eh nace ai sai ki dauki rigan ki saka a jiki kada su fahinci abunda kikazo fada min ke nan yanzu a daki.
Tace ai ya jamal ya ce mata mulkin me kikeyi bayan ke ake cuta a kullun don dantane ai mai mulki sai tayi dariya tana fadin yai min daidai ai ba dai taji dadi a gidan nan ba wallahi tunda tace ita yar naci ce da kwadai zataga wullakanci saita raina kanta wallahi.
Niko basu san ina jin komai ba don ina tsaye daga kofan shiga part din mu nake jin komai.
Ido na tsura mata ina mata wani irin kallo kafin ince watau halimatu bakya ji ko saidai da kika fada min komai yanzu.
Ai na bari tunda kince in bar fada maki wanan din ne kadai na fada tana wani turo baki a gaba tare da daukan kayan dake gabata data fitar ta saka ta fice a dakin.
Zaune ta barni ina faman tunane sai yaushe mami zata daina hattarana kan dan ta ne dan da ba wani dadin zama dashi nake ji ba a tare dashi.
A hankali na mayar ds idona na runtse wuri daya don yanzu na daina wanan ruwan hawayen da nakeyi saidai yawan tunane kawai da shiga halin damuwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.