Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 124 of 139

Yan uwa ina mika sakon ta,aziyana a gun yan uwan da sukai rashi a cikin satin nan ubangiji Allah ya gafartawa musulmi yakai hasken rahama a kabarin su amin ya gafartawa duk wani musulmi daya kwanta daman shi Allahuma amin.

ZAINAB IDRIS MAKAWAJUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMI UBANGIJI ALLAH YA SADA MU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN RANAN ALLAHUMA AMIN.
YAR UWA LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA VIKIN SALAMA DON KARUWAN KANKI DA KANKI YAR UWA, , ,

Kamar yadda maya tayi min alkawarin kirana karfe takwas na dare ina daki zaune saman sallaya ta kira layina din.
Na dauka muka gaisa take fadin yanzu haka tana gidan kakarta don yadda tajini a dazun bata ji dadin haka ba.
Da yake video call mukeyi da ita ta nuna min fuskan kakar nata a screen din wayan ta tsohuwar take murmushi ba yaren su nake ji ba don haka na daga mata hannu alaman gaisuwa a gareta .
Bayan mun gaisa din takewa maya yare mayan ta kalloni tana fadin wai me ye damuwana a yanzu ido na dan lumshe kafin na sauke ajiyan zuciya na fara ba maya din bayani ita kuma tanawa tsohuwar kamar yadda nake fada mata.
Daga ta bata fuska sai ta dan kada kai tsohuwar keyi don jin bayanin da nakewa maya din.
Saida na gama ta fara magana tana dan tafiya a duduke zuwa wurin da take aje maganin ta ta dauko ta juya tanawa maya magana.
Maganin naga maya ta amsa a hannun ta tana nuno min tare da fadin wai ki duba irin wanan maganin ta baki irin sa kwanaki.
Shi zaki dauko kiyi amfani dashi a yanzu ta bude maganin tare da nuna min shi sosai a screen din wayan ta nace nagane.
Ta sake fadin zaki jika mai a ruwa har sau uku daga nan ki bar bashi sai tsohuwar ta katse ta da bayanin da takeyi din ta fara magana tana nuna mata wani farin garin magani dake hannunta.
Nan dai sukayi min bayanin komai na yadda zanyi amfani da magugunan data bani a kwanaki da na tafi masu sallama zamu dawo Nigeria.
Don ni na barsu kenan a nufina bazan sake komawa kasan chaina din ba kuma a yadda na yanke a zuciyana.
Bayan mun gama wayan ne dasu ba nufi wardrobe dina ina binciken inda na aje maganin da tsohuwar ta bani din.
Suna ajiye kamar yadda na ajesu daya bayan daya na duba ko wani na dauko na dawo bakin gado na zauna ina kallon maganin.
Can kasan zuciyana nace Allah kaga nufi a kan hakan banyi don na raina ma yin ka ba ya Allah ka gafarceni akan hakan idan na saba maka .
Kasa wanan karon iyakar wahalance ga hakan kasa mu dace da nasarorin ka ya Allah na fada ina shafa hannuna a fuskana.
Tashi nayi daga inda nake zaune din na nufi inda wasu cup suke ajiye na dauko tare da goran ruwa na zauna a inda na tashi din.
Ruwan na fara zubawa a kofin na daga tare da karanta fatiha kafa bakwai a cikin sa don ance kome ke damun ka fatiha na maganin sa da yardan ubangiji.
Na kawo garin farin maganin na dan zuba a cikin sa kadan na fara karkadawa kafin in daga in kai bakina da bissimillah.
Na gama duk yadda ta fada min din inyi bayan na kamallah na koma na kwanta saman gadona ina mayar da numfashina a hankali.
Ina nan kwance ido a rufe naji an turo kofan dakin an shigo na bude idona a hankali sadiyace ta shigo tana fadin anty kin kwantane da wuri haka yau.
Zan tashi yanzu na bata amsa ina mikewa tare da fadin kin ci abincine tace min bata ciba muje yanzu muci na fada a daidai lokacin dana sauko saman gadon.
Mun zauna falon ke nan ya shigo fuska a daure nice na fara mashi sannu da zuwa wanda hakan ya bashi mamaki don ya dauka a yadda muka rabu da rana ina cike dashi a ranan.
Haka yasa yaje gidan mami ya zauna abinsa ya yini a can bai dawo ba sai wanan lokacin daya shigo gidan.
Duk da hakan bai tsaya a falon ba ya nufi part din shi kai tsaye bayan ya dan tsaya yana amsawa sadiya gaisuwa tare da tambayan ta tana lafiya ?
Baifi yan mintuna a tsakani ba na mike tsam ina fadin sadiya ina zuwa na nufi part din nasa nima.
Na sameshi tsaye a tsakar dakin yana cire rigan jikin shi na karaso inda yake ina fadin yau ina ka shiga har wanan lokacin ?
Ina gidan mami ya bani amsa kai tsaye a yadda yake amsa min din naji ba dadi gaskiya saidai na hade hakan a raina na kara takowa har inda yake ina fadin .
Suna lafiya ya yaran ya mamud basu zo badai gidan nan har na tambaye shi don rasa na fadi a lokacin .
Kema kinsan uwarsu ba zata bari suzo gidan nan ba din har yanzu fushi takeyi dani bata zuwa ko naje gidan.
Ikon Allah me yai zafi haka a tsakanin ku ta dauki fushi dakai haka hummm kawai yace yana kokarin wuceni ya shiga bayi.
Ya kai kofan bayin duk a cikin daurewa nake fadin mu jirakane ka fito muci abinci na tambayeshi don karfin hali don kawai in nuna mai yanzu ba haka zancen yake ba a guna.
Naci abinci gidan mami a koshe nake ya fada yana shigewa bayin kai tsaye nabi bayan shi da kallo.
Kafin ajiyan zuciya ina mai jin zafi a raina tare da tunane nabar dakin nasa watau mu mata a zalunce mu kuma mu koma bi da biyayya garesu Allah sarki diya mace ubangiji Allah kaiwa mata rahama albarkacin Annabi Mohammadu sallalahu alaihin wasallam.
Falo na dawo na zauna a dinning muka fara cin abincin da aka shirya na dare don mu a gida.
Mun gama hira muka danyi kafin kowan mu ya mike zuwa part di shi har lokacin banga ya leko mu ba .
Haka yasa na gane cewa bazai fito di ba ke nan yake nufi ina shiga daki na fada bandaki nayi wanka na fito na shirya tsam kafin in saka rigan barci na dauki abinda kakan maya tace min in shafa bukata kawai ko bai shafa bashi yaji kakshin shi dab a hancin shi dai kawai ko hakan ya wadatar.
Sosai na mulke jikina da maganin nabi da dan turare a sama saboda kar kamshin maganin ya tashi sosai.
Na dan dade a zaune ina tunanen hanyar da zabibsakon ya isa a hancin shi duk da nasan abune mawuyaci yin hakan garemu a yanzu.
Can dai na daure na mike na dauki hijab din sallah na na dora saman jikina kamar yadda na saba yi idan zan shiga part din.
Bakina tab da addua kamar kullun na nufi part din nasa kofan yana bude har lokacin na shiga jna rufo kofan a hankali nasaka key narufo kofan.
Kwance na hango shi rigingine ya na saye da jallabiya a jikin shi ya dora hannu a fuskan shi kafaduwab shi suna a harde yana dan kada su a hankali.
Duk da nasan ba barci yakeyi ba a lokacin hakan bai hanani tafiya a hankali ba motsi ba na karaso har baki gadon da yake kwance din sama.
hankali nakai zaune saman gadon har lokacin ina kan adduan da nakeyi a lokacin na gama na tofa tare da shafawa a jikina nayi bissimillah na hau gadon da kyau tare da dan jawo jikina zuw inda yake kwance duk da ban taba masa hakan ba sai wanan ranan.
Kaina nakai saman kirjin na dora lokaci guda yayi wani irin zabura yana fadin kanki daya kuwa zainab ?
Sau nawa nake fada maki idan har bukatan hakan ya taso min da kaina zan nemeki da hakan.
Ikon Allah na fada a raina kafin a fili ince dashi ban kwanta a nan don wani feeling ko wani abuba na kwantane kawai don in dan samu sauki a zuciyana a wurin dan uwana don kawai naji dumin wani ajikina.
Ba tare da yai magana ba ya kai hannun shi da zuman bambareni a jikin shi na kara lafewa kamar da gaske a jikin nasa.
Da karfi ya fincikoni zuwa gefeb shi ya juya yana wani irin mayar da numfashin sa da dan sauri kafin can inga ya mike zuwa ban dakin.
Shiru shiru bai fito ba sai zuwa can ya fito da alaman ruwa a jikin shi yayi wanka ke nan a lokacin don kawai na dan taba shi din ya watsa ma jikin shi ruwa a lokacin.
A hankali na mayar da idona na lumshi jin bai hawo gadon ba a lokacin yasa na bude idona yana tsaye gaban mirrow yana faman goge jikin shi.
Tabdi jam ashe abin bana wasa bane na fada a raina ina kara gyara kwanciya har barci ya daukeni ban sani ba lokacin.
Kodana falko a cikin dare na hangoshi can saman kujera kwance kuma har lokacin baiyi barci ba idanun shi biyu da waya a hannu shi.
Tashi nayi zuwa bandaki na dauro alwala kamar yadda na saba yi a kullun don Nafilan dare.
Sai zuwa can ya shiga ban dakin nan ma dai irin abinda yake ji yaji a ban dakin ga kanshi yayi wani irin daure mashi lokaci guda haka dai yaja kafan har ya fito.
Yau ba mafalkin asalima tsorone kawai daya ziyarci zuciyar shi haka kawai yake jin kamar tsoro yake ji saidai baisan na meye ba a lokacin.
Saida yai sallah raka,a hudu ya dan samu saukin abinda yake ji a zuciyar shi muna wurin har akai kiran sallah asuba .
Nayi sallah kamar kullun nabar dakin zuwa dakina sai dai abin mamaki ba kamar yadda ya saba tashi a cikin kuzarin shi ya tashi ba a yau.
Gashi nan so wick dashi bai son magana da kowa a ranan karshe ma ya kwanta yana barcin rana abinda bai taba yi ba ke nan a sanina dashi .
Koda kuwa baida lafiya baya barci da rana saidai ya rufe idon shi kawai na dan lokaci ya bude .
Allah ka tsare muna rayuwan mu daga fadawa a cikin halaka saboda duniya ko neman wani abu makamancin hakan.
Duk da irin halin da nakw ganin shi baisa na fasa shafa wanab magani ba insha kuma a nasa bangaren kuma sam ya rasa gane lafiyan jikin shi sam.
Shidai yasan cewa lafiyan shi kalau baya jin ciwon jikin shi tako ina amma kuma yawan kasala da damuwa ya hanashi sukuni ko kadan.
Ban dada ba ban kara ba a yadda aka ban lokaci da zanyi amfani da magani in bari daga nan kuma aka sake dorani kan wani da zan fara.
Nikan garin ceton wani naga ta kaina yar uwa sai dai abinda zance yanzu gaskiya kamar yadda malam ya fada min ne naga sauki sosai ga harkokin ya jafar a yanzu.
Ranan ya shigo da rana yake fadin in shirya zamu Samunaka mu duba hjy bata jin dadin jikin ta su mami sun tafi mu zuwa yamma jirgin mu zai tashi.
A rude na dago ina fadin subbahanallahi har ciwon yayi serious hakane sosai yace ance sosai ne ciwon suna can dai sun tafi su dubo.
Ya na fadin haka ya juya ya fita daga dakin nan ya barni ina jimame akan tsohuwar har wani lokaci kafin in mike in fara shirin tafiya .
Bayan sallah la,asar ya shigo yana fadin ba zamu tafi din ba mami tace mu dakata zasu zo da ita nan Abuja yau din nan.
Sai naji hankalina ya kara tashi sosai ba abinda nakeji sai rashi zuwa ganin ta da banyi ba gani har kaduna amma ban samu leka wurinta ba har na dawo.
Tunda ya fita bai dawo ba ranan har dare sosai haka yasa nasan yana can wurin su hjyn ke nan a lokacin nasan sun iso da ita Abujan kenan tunda yakai wanan lokacin haka a waje.
Har na gama komai na shiriya zuwa dakin shi na kwanta ni kadai a dakin ina addu,in dana iya a bakina.
Barci ne ya daukeni na dan lokaci sai gashi ina mafalkin wasu mutane masu bakaken kaya duk jikin su sun saka hulunan kayan saman kawunan su.
Wanda duk yazo ya wuni a inda nake tsaye ina kallon su din cikin mamakin me ya kawo ni nan kuma su din su waye ?
Fuskan dayan abokain shi philis na gani na gane a lokacin ya daga hannu kamar yana warning dina Allah ya taimakeni na furta Au,zubikalamati min sheri min halak .Lah illa ha in,llah anta subahanaka inni kuntun minal zalumin ya wani yanka ihu duk sauran suka kallo mu sai na juya da sauri nabar wurin.
A daidai lokacin kuma na falka daga barcin sai wani irin zufa dake fita a jikina don wahala na mike zaune a firgice ina bin dakin da kallo a tsorace.
A daidai lokacin kuma kiran wayan jafar din ya shigo wayata saida na dan zabura don tsoron da nake ciki a lokacin.
Na kai hannu da kyar na dauki wayan yana fadin kina inane haka nace dakin ka na kwanta ki koma dakin ki yanzu har in dawo ya fada a cikin comand ya kashe wayan.
Wayan nabi da kallo tare da kallon lokaci karfe biyu na dare da wasu yan mintina a lokacin.
Na mike da sauri zuwa dakina banko rufo kofan dakin da kyau ba wurin sauri don ba karamin tsorata nayi ba a lokacin gaskiya.
Ban kwanta ba na shiga ban daki na dauro alwala na tayar da sallah na dade zaune ina karatun kur,ani naji dawowan shi gidan uku da darabi koda ya shigo.
Dakina ya fara shigowa tun daga kofa yake jin kira,a na har ya karaso tsakiyan dakin inda nake zaune yana fadin.
Mesaya kikaje dakina ke kadai a wanan lokacin na dan dago kai na kalleshi na mayar naci gaba da abinda nakeyi shima ya juya ya fice a dakin da saurin shi.
Kafin asuba wani irin zazzabi mai karfi ya rufeni lokaci daya haka nayi sallah a dadafe na koma saman gado na kwanta.
Rufe nake ina nishi da kyar sadiyace ta shigo ta sameni a wanan halin hankalinta ya tashi sosai ta juya da sauri zuwa part din shi ta fada mai halinda nake ciki.
Tare suka dawo dashi yana tambayan ya nake ji nace zazzabine kawai nakeji a lokacin ya fita sai gashi da magani ya kawo min nasha yana zaune har ya dan fada min.
Sai lokacin nake tambayan shi jikim haji yace taji sauki daya barsu jiya da dare yanzu zai koma yaga jikin nata kuma.
Wani asibiti take na tambaya a cikin karfin hali ya fada min tare da fadin kada kice zaki a wanan halin ki bari sai kinji sauki ya fita.
Bayan fitan shi zazzabin ya taso min sosai na ce sadiya ta ban ruwa na karanta fatiha a ciki nasha sai barci ya dan daukeni a lokacin.
Mafalki marasa kyau na dinga yi a wahalce dai nayi barci sosai a lokacin koda na tashi na dan samu sauki har nayi wanka.
Na fito na shirya don zuwa duba hjy don tana raina a lokacin sosai mu uku muka tafi da sadiya da fadila zuwa duban ta sai abinci da kayan marmari da muka saye a hanya don mu kai mata.
Kusan kowa na asibitin a lokacin don bayan sallah la,asarne lokacin mun shiga mun gaisa dasu tana kwance an daura mata ruwa ana kara mata.
Mama Ramatu ke fadin dazun mijin ki ke fada muna baki da lafiya ai nace naji sauki ne na taso gashi a lokacin wani zazzabi nakeji da sanyi a jikina.
Mami dake gefe zaune tace ya dai fadane kawai don ya kareta wani zazzabi kika gani a nan don Allah.
Kai haba yayan mu kika sani ko alherine ya samemu ake wanan zazzabin yanzu haka ai wasu haka suke laulayin cikin su dama.
Dakin yai shiru ba wanda yai magana a lokacin mamice ta sake fadin ai bata da niyar baku jika ta zauna suna jin dadi idan suka hadu da fushina watarana maganin su zanyi ai.
Da yafi mami tunda ita bata iya haihuwa ai hara a kawo wace zata haihu muna Aisha ta fada fadila ta karba da fadin Allah ne bai kawo ba hjy komai dan lokacine ai.
Wanan kina min shishigi da yawa mami ta fada abin mamaki a lokacin hjy akaji muryanta tana fadin iyami ko bayan raina kikasa jafari sakin yarinyar nan ban yafe maki ba.
Dakin yayi tsit ana sauraren hjy kafin Aisha tace dama na fada maku ai ji wanan tsohuwar da kowa ya rude a kanta tun jiya batayi magana ba yanzu take fadin haka.
Sai aka kwashe da dariya hjyn da take kwance take fadi cikin karfin hali zo nan kiji kawata inji dumin ki kusa dani tana kokarin mika hannun da ake mata karin ruwa dashi gareni.
Kai hjy da zainab sai Allah a tsakanin ku Na,ima ta fada tana fadin to mu din da baki damu da jin dumin mu ba sai mu tafi tunda zuwan mu baida amfani a wurin ki.
Ni dai na taka zuwa bakin gadon na riko hannun tsohuwar ta rike gam tana fadin zauna a nan kinji ko suna so ko basu so kin shigo cikin mu ke nan.
Muna zaune a haka sunawa junan su sheri suke fadin albarkacin bakin su kan hjy mazan suka shigo ya jafar yana ganin mu a dakin yake fadin.
Zainab kin iya tasowa ne yanzu naje gida bakwacen ake fada min kunzo asibiti ya mamud ne ke min sannu da jiki yana gaida ni har su jamal din kasa nayi su lokaci guda akaga na sunkuya kawai dama ni kadai nasan yadda nake ji a lokacin karfin haline kawai nakeyi a hakan.
Tsale daya ya jafar yayi ya kai gareni ya rungumoni na some a lokacin ban sab inda nake ba kuma sai hankalin su ya fara tashi.
Da sun dauka pretending nakeyi a lokacin har mami tana jan tsuki jamal ya fita da sauri ya kira likita yazo dashi dakin likitan ya duba yake fadin dama bata da lafiya ne haka har jinin jikin ta yana batun konewa duka.
Lokaci daya mami ta mike tsaye cikin furgicin jin abinda likita ya fada a game dani yana kiran nurse da sauri yana fadin a shirya daki a kaini ciki nan hankalin kowa ya tashi kuma.
Mami da kanta ta rikeni har dakin da aka kwantar dani duk bansan wainar da ake toyawa ba a lokacin sadiya kan kuka ta saka masu tana ihu ganin halin da nake ciki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.