Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 116 of 139
Ya jafar ya kira layin nawa yafi a kirga da safe zuwa rana don hakane ya nemi layin Abban mu yake tambayana.
Abban yake fadin bata fadama zasu ziyara nan fambeguwa wurin yan uwan mahaifiyarsu ba yace ok kila ta fada min na mantane ya kashe wayan bayan sunyi sallama da Abban yace masa bari ya samo lamban da za a samemu dashi a can.
Abba ya shigo gida ranshi a bace yana wa innan mu fada kan zuwana wuri mijina bai sani ba gashi yanzu ya bugo waya yana tambayana.
Itama inna hankalin ta ya tashi nan ta buga waya sai dai wayan baya shiga hankalin inna ya tashi take tambayan sadiya ko ba service a garin tace sun baro services a can lafiya kafin su dawo.
Hankalin innan mu ya kara tashi gashi yarta di ba waya ke gareta ba balle su kira nata layin suji ko lafiya nake.
Har dare inna na kokarin kiran layina shiru babu layin hankalinta kuma yaki kwanci da hakan har sadiya ta dawo daga zari,a ta samesu a hakana itama ta gwada layin nawa bai shiga.
Sai cewa ake layin yana kashe idan sun kira sadiya dake gefe tace aiko anty mu bata kashe wayan ta haka idan dai ba wani matsala ne ya faru da wayan ba.
Har washe gari basu sameni ba haka yasa sa,adatu fita ta samo layin wata yar garin data sani ta kira akan taje gidan ta duba in lafiya nake ta fada min na kunna wayana ya jafar nason magana dani.
Basu akace wa kawar babu wata bakuwa a gidan wace suka zo duk sun wuce koda ta kira sa,adatu dare yayi lokacin don haka saidaf safe sa,adatu ta sameta take fadin abinda aka fada mata.
Sai hankalin su ya tashi sosai nan inna hankalin ta ya kawo cewa akwai matsala ta bangarena ke nan lalai wanan abin da nayi yana da alaka da zance da yaya jafar di nan hankalin ta ya kara tashi sosai.
Sai gashi ya jafar din ya kara kiran Abban sun gaisa yake tambaya ko na dawo dan layina baya shiga ana fadin layin yana rufe har lokacin.
Mamaki ya kama Abba yake fadin bata kira kaba ke nan danace su sanar mata bayan sunyi sallama ne Abban ya shigo gida ya hau inna da fada ta inda yake shiga banan yake fita ba.
Dole washe gari sa,adatu tayi asubancin zuwa fambeguwa da kanta ta duboni ko taji inda nace dasu zan tafi daga can don hankali su ya kwanta.
Saidai tana zuwa din kamar ta karo tashin hankalime gare su don ta dawo da labarin ba wanda yasan inda na tafi sai innan mu ta fashe da kuka.
Dole ba yadda za ayi aka fadawa Abban mu komai shima nan hankalin shi ya tashi ya fara fada inna cewa komai ya sameni itace don itace ta kirkiro da surfan aje gun yan uwanta ai.
Daba haka ba ai da ina gida asirin su rufe yanzun me zasu fadawa mijina cewa nayi tafiya na bata ba a san inda nake ba ko me ?
Daga shi sai inna da yan uwana ake kumbiya kumbiyan maganan a tsakanin su har karshe dai saida Asabe ta san da zancen itama hankalin ta ya tashi sosai.
Inna taje gidan malam tana kuka take zayana masa komai malam din yai murmushi tare da fadin nasan za a rina don yarku na cikin wani hali wallahi.
Sai dai kada ku damu sosai za a san abin da akayi ta dawo gida lafiya kada abin ya kai ko ina amma hankalin ta ne ya tashi sosai da mijin nata har mahaifiyar shi.
Nan dai malam di yace za ayi rokon Allah duk inda na shige na dawo gida lafiya ba tare da wani abu ya faru dani ba insha Allahu.
Abba kan ya saka inna a gaba har ya kai inna itama ta hasa ta mayar mashi da amsa a cikin zafin rai ta fadin shin malam kana ganin laifina a nan.
Kai tunda yarka tazo garin nan ka taba zama da ita ta fada ma halin da take ciki a gidan auren ta daudai da rana daya malam a gidan nan.
Abba yace owwoo yanzu kika fito mi a mutum sak watau duk abinda yar nan tayi da sanin kine Asiya boye min kawai kikeyi dama ?
Tace wallahi bada sanina bane malam don babu uwar da zata koyawa yarta mugun abu haka tabar dakin mijin ta da mutane suke hangen tana a cikin daula ne ita.
Saidai mu iyayyen mun kayi sakaci wani lokaci har abu ya girma ba tare da mun maida hankalin da halin da yaro ke ciki ba sai abu ya lalace.
Shike nan Asiya kin sai komai dai da yarinyar nan tayi ke nan to wallahi bari kuji baku isa ku kunyatani ba a idon jama,a.
Duk inda taje koma wani iya shege take ji dashi a zuciyar ta zata dawo nan ta sameni sai ta koma gidan mijin ta bata mai dani mutumin banza a garin nan ta tona min asiri ko watau kunga Allah ya rufa min asiri ta tsatson ku ?
Kaiya kaiyya ina ta fada har sau biyu kafin tace shine matsalan malam bahaushe wallahi kaji na fada ma yarinya tana cikin matsala watau kai ko a jikin ka malam don kawai dan abim duniyan da kake samu daga wanan mutumin ko ?
Ya rufe maka ido ba zaka dawo da hankalin ka wuri daya ka natsu kaji ko meye matsalan yar taka ba da miji nata kadai kawai burin ka ta dawo ta koma koma meye ta karata can dashi ko ?
To ban yarda yata ta halaka a haka ba don kawai kana kwasayin abin duniya kai yanzu idanuwan ka sun rufe ba zaka nemawa yarka manufa ba.
Nan Abba shima ya taso kamar zai daki inna a ranan kan wanan maganan har yana fadin idan ta kuskura ta kashe aure na da ya jafar a bakin auren su ke nan itama.
Ran inna ya baci matuka tana mayar mashi da martani har yakai saida su sa,adatu suka ja inna zuwa daki sannan Abban ya fita .
A waje ya hadu da lantana dake labe tana saurare ta rasa gane zancen da akeyi da farko amma ta dan tsuntsunci wasu daga cikin maganan inda ta fahinci akwai matsala ke nan ga aurena dama tana neman sanadin da zata katse duka jin dadin daulan data hangomu a cikin sa ni da innan mu da kowa a dakin mu da wanan bakin cikin take kwana take tashi dashi a kullun.
Abban mu yana fita gidan malam ya nufa don ya kai karan inna a can ya sa ai masa iso a wurin malam din nan ya samu wuri a waje ya tsaya yana cika yana batsewa har malam din ya fito ya sameshi a wurin.
Bayan sun gaisa ne ya koro magana ya fadawa malam din komai saida malam din ya gama jin Abba ya nisa tare da fadin.
Bello ka ban mamaki matuka duk da matar ka ta baka haske a cikin zancen auren yarka zuciya ya hana ka gane hakan ?
Malam wani matsala take kira wa yarinyan nam fisabililah duk wanda yaga yar nan yasan tana a cikin daula ai.
Malam ya katse shi da fadin kaiya amma bakai tunane ba bello a nan ka yanzu barin fito maka baro baro ka sani yar ka na cikin matsalan aure a rayuwa ta a gidan mijin ta don haka ka daina wanan kumfan bakin da kake yi a yanzu.
Kamata yayi ka natsu a sama ma yarinya mafita ga rayuwan ta ayi abinda zai kawo zaman lafiya garesu da kwanciyan hankali .
Don babu auren da za ayi tsaon wata daya ko biyu zuwa uku ace babu wani abinda ya taba shiga tsakanin mata da miji irin na aureta a tsakanin har wanan lokacin.
Bale yarka dake neman shekara shidda yanzu a gidan mijin ta ya kake ganin wanan abin zai kasance komai hakkurin yar ka kuwa ?
Jikin Abban mu yayi sanyi wani zufa ya fara keto mai lokaci guda ya kara gyara zama yana cire hulan kanshi.
Kafin ya nisa yana fadin yanzun malam kana ganin hakan yana yuyuwa a tsakanin su kadafa yarinyar nan taiwa mutumin nan sheri kuma kan hakan ?
Malam yace malam Bello ke nan ka godewa Allah daya baka ya kamar wanan yar mai hakkuri da sanin ya kamata do sauran zancen ba zai fadu ba.
Abba yace wa iyazu billahi ban samu zama da ita ba gaskiya malam ban san da wanan zancen ba sam wallahi.
Ya dan dade suna tautanawa da Abban kafin suyi sallama da juna ya nufo gida gwiwan da sanyi sai tunane yake a ransa.
Yana hanya bai karasa gida ba kiran ya j din ya shigo mai haka ya bar wayan har kiran ya katse don ko ya dauka baisan amsan da zai bashi ba a lokacin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.