Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 139
Zaune yake saman farar kujeran roba a gurden din gidan mai dauke da dogayen itatuwan da ba wani zugun ganye suke dashi ba sai dai tarin tsayi a gasu.
Babu wani abinda yakeyi duk da sytem din shi dake gaban shi a bude ya kasa aiwatar da komai sai faman tune a ranshi.
Yakai hannu a hankali ya rufe sytem din ya dafe kan shi dashi yana ci gaba da tunanen shi ya rasa yaya zaiyi ne da wanan hukuncin da yake kokarin yakewa a ranshi.
Allah ya gani bawai yana son yarinyar da mami ke son hadasu bane zai dai amincene don farin cikin mahaifiyar shi kawai.
Don yadda mami dasu hjy suke nuna mai muhinmancin yin hakan gareshi saidai shi Allah ya gani bawai ya shiryawa aure a wanan shekarun nasa bane.
Anya kuwa idan yayi gangancin yin aure a yanzu ba zai jawa kanshi matsala bane ga hakan.
Kai ya girgiza shi kadai tare da fadin dole yai juriya da fin karfin zuciyar shi don ya samu su rabu lafiya da mahaifiyar su.
Muryan Rufaida dake fadin ki tabbatar da kin wanke kayan nan tas wallahi kada inga jirwaye a jikin su banza kawai mun zuba ke nan dake a gidan nan.
Ke gaki kin samu wuri zaki mike kafan ki kiji dadi ko to wanki har na tufafina duk ke zaki dinga wankin su a gidan nan daga wanan ranan.
Nima ga nawa Nazira ta fada shegiya munafuka mumuke zamuyi maki a gidan nan ba tare da mami ta san da hakan ba ta jefo min unders din ta a fuska.
A daidai lokacin daya karaso wurin don jin zagin da suke min din yayi yawa a lokacin.
Yana tsaye hannun shi duka biyu zube cikin aljihun wandon shi kallon kayan yayi yayi saurin kawar da idon shi ga kayan.
Ya dago yana kallona su kuma sai dan kame kame sukeyi suna fadin sannu da hutawa yaya J ke daga daga nan ki shige ciki ya fada yana kallona.
Da sauri na bar wiein kayan na koma ciki dama wurin su mama kande nake zaune suka sameni suka ban wanan sikin wankin.
Nan nabar masu kayan nasu na shige ina share hawaye babu mami a falin sai hjy dake zaune ita kadai ta kurawa tv ido tana sauraren malam daurawa dake wa,azi a tashan sunna tv.
Na zauna take fadin yar nan akwai kura kuren da mukasha tabkawa a rayuwa sosai a baya wanda sai yanzu kake jin bayanai akan abubuwan da bamu sani ba a can baya.
Jin tana magana ban bata amsa ba yasata dago kai tana fadin kinga kamar da can baya ai bamu sancewa ga lokacin da mutum ya dace yayi , , , ,
Ido ta kura mi don hawayen data ga ina sharewa a lokacin salati ta saka hankali tashe tana fadin .
Waya tabaki me akai maki yar nan ki fada min wanda ya musguna maki yanzu don nasan ranki aka bata haka.
Muryan mami ne ke fadin hjy lafiya wa aka batawa rai zeey lafiya me ya faru yanzun fa kika bar falin nan da raha da hjy .
Mami ba komai ba komai kamat yaya ta fada tana kallona tana zama saman kujera takon kafab shine yana shigowa daga kofan baya yake fadin.
Mami kiwa yaran nan iyaka da yarinyar nan abin is too much sun mayar da ita boya a gidan nan .
Mami idan baki iya masu magana su daina don Allah ki mayar da yarinyar nan gaban iyayyenta haka cin fuskan yayi yawa.
Ya kwashe komai da yaji yana fadawa mami rai bace yana gama fadi ya juya ya fita hjy ma tana masa magana bai tsaya sauraren ta ba ya fita don bai cikin dasin rai a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
2ï¸Â⃣1ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS
MAKAWA
YAR UWA FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA TARE DA IMANI A ZUKATAN MU AMIN DON ALLAH KADA KI FITAR KARKI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA KI TUNA DA AKWAI RANAN HISSABI YANA NAN TAFE.
Ki biya ki karanta a cikin salama yar uwa kan dari uku kada a tsayar dake ranan da kowa tashi ke fitar dashi sai abinda ka shuka.
Yau tun safe Lantana da haibaici ta tashi a gidan don kawai Abban mu ya kwana a dakin innar mu kuma taga Abba ya fito ban daki da asuban farko.
Saboda ta hana idon ta barci duk ranan da Abba ya shiga wurin innan mu haka take kwana leken tagar dakin ta don ganin halin da suke ciki.
Wanan dalili ke sa Abba ko zai shiga dakin sai yaji wa,azi da nasiha abokan shi ko wani na kusa dashi akan yadda yake wofintar da innan mu har yan waje suka gane hakan.
Hakan ba abin mamaki bane sanin ko wacece uwar lantana a garin dan zaman kanta takeyi tana sana,ar tuwo tuwo.
Haka kuma take mu,amula da maza bata boye halinta har mutanen gari suka ki auren yarta data taso shine Asabe kakar mu taje ta kwasowa Abban mu ita.
Don kswai a lokacin suna dan dasawa da mahaifiyar ta har suka hada wanan alakan cewa idan Abban mu yana son lantana yazo ya nemeta da aure ko za,a dace ta haifa mai diya maza a gidan.
Bayan auren yanzu kuma ya fita a tsakanin su suka koma kamar annabi da kafiri tun bayan dataga ta haifi namiji din duk da dan ba lafiyayye bane yazo.
Innan mu tana bakin murhu tana hura wuta ta fito ta zauna a kofan dakin ta tana fadi a fakace.
Yau kuma su oo me aka samu da farar safiyan nan ake wanan duke a gaban murhu ko anyo aikene daga bariki za a sha dadi haka ?
Inna dai yi tayi kamar bata jita ba taci gaba da fadin muna nan dai idan tayi wari maji ai .
Gashi dama ko a gida a shedesu da dan hannu balle anje birni anga banza aita wawurowa ana kawowa gida.
Hakan bai mata ba ta sake fadin wasu dai sunji takaici ya ko auren fari babu har ta shiga duniya yawon banza .
Har azo anawa mutane feleke a gari a saka a canza duk da kayan zina to ai haka ba mamaki tunda tsohuwa ma ta tsufa bata san ta tsufa ba ka jaraba kullun ana makale da naji ana abu daya diya tayi da kaitai a birni uwa tayi nan da tsoho.
Allah sarki dadin abun dai da tsohon sunna tsohuwar ke makale ba mazan wasu take ci ba a titi kamar macijiyar da bata ramin kanta.
Sai dai anyi rami tayi shige ko tabi darnin makwabta ana dannan ta ana sukawa akanta saman titi da tsufanta diyata dana makwabta suna kallo.
Innalillahi aikuwa dama inna takan tara mata na kwanaki kafin ta gaji ta bata amsa koshi sai idan taji ta tabo zancen diyan tane zata samu mai zafi daya ta fada mata taja bakinta tayi shiru ta barta tana haushi.
Wani lokacin har makwabta sai sun shigo rabon ta akan tayi hakkuri ta daina idan kuma sun gaji sai tayi tayi sai ta gaji zata kyale don kanta.
Wani lokaci kuma har uwarta takan tako gidan tazo taya ta fadan suyi harsu kare babu mai tankasu.
Yau din ma da taga haka jin amsan da inna ta bata ta yafa gyalenta ta fita zuwa fadawa uwarta abinda ke faruwa harda karya da gaskiya ta kwasa ta fadamata.
Sai gasu tare sun dawo ita haushi uwarta haushi Allah ya taimaka inna ta gama girka dan taliyan hausa da take dafawa yara su karya dashi din Abba yace kuntu billahi baida ko kwandala a hannun shi da zasu karya.
Amma yana fita ya shiga dakin lantana data haushi da masifan ai ta ganshi ya shiga ban daki daga yau sai ka koma ka mannewa tsohuwar matar ka tunda duk kokarin da nake maka baka gani kai.
Halin maza sai su nan Abba ya dan fara kame kame yana rarashinta har yakai ya dauko dan kudin daya kwana dashi hannun shi ya mika mata su gaba daya don kawai ya samu ya shawo kanta kada ta gujeshi kamar yadda ta fada din.
Shine bayan fitan shi inna ta fito tana hura wuta ta ja inna da wanan masifan har yakai inna ta mayat mata da martanin da yai mata zafi shine uwarta ta shigo da masifa.
Tana fadin sai tayi karan innan mu don kazafi wai inna tayi mata a cewan ta jin fitinan yayi yawa yasa Asabe fitowa don da farko batayi niyar fitowa ba.
Ji datayi tace zata kai karan inna ga hukuma yasa ta fito tana fadin ke mai tuwo baki tunanen me yarki itama ta fada mata .
Har ta bata wanan amsa itama don haka kawai ba zata fada mata ba ai don kawai an mayar da haulatu mai hakuri a gidan tana kawar da kai ga abinda yarki jeyi mata ko yaushe.
To tsohuwar banza kin fito ki shigar matane ko me yanzy haulatun ce mutum a wurun ki tunda yarta na can birni tana bin maza tana zuwa maku nan da abin duniya yanzu sun koma abin son ki kuma ?
Jin haka da innan mu tayi ta bude labulen kofan ta tana fadin saukin abindai kafin ta fara aikatau wasu sun tafi butnin sunyi har saudiya yin dandin kasa mai tsarki basu dawo da komai ba kasan nan sai tsaraban shegu.
Idan kuma suna da uba yau a fito muna da uban su mu gani don haka kafin yata taje birni bin maza tsohuwar banza ta fara zuwa ta dawo muna garin nan da tsaraban annoba.
Yau zaki san kin tabani garin nan yau zan nuna maki ko wacece ni a garin nan inna tace idan kin tashi kisa a rufeni dan makullin ya bace iyaka ke nan.
Lokacin har yara da mata da muke makwabtaka dasu sun cika gidan suna kallo da saurare.
In dai barikin ne ai iyawace don karshe sai an koro yar taki da ciki kowa ya gani a garin nan lantana ta fada cikin jin kunya da nauyin yaran dake ihu bayan fitar uwarta don halin su ya ishe mutanen unguwa dama.
Har wurin aikin Abban mu lantana da uwarta suka sameshi suna fadin sai sunyi karan innar mu don tayi masu kazafi da cin mutuncin da ba a taba masu shiba yau.
Abba ya shiga ba mahaifiyar lantana hakkuri yana fadin ta barshi da inna dama halin innan mu yakai mashi ko ina a gidan.
Haka dai Abba ya samu ya lalaba su suka bar gidan bai dade ba shima a waje sai gashi ya shigo yana kwalawa inna dake bandaki kira .
Bata amsa ba saida ta fito ta bayan shi take fadin gata ai tana sauraren shi.
Ke don baki da mutunci yanzu har kika iya bude baki kika zagi uwar lantana a gaban ta karya suka fada wayasan inda yar taki take a birni dama.
Allah sarki hakane dama ai na sani kaima yaran ba damuwan ka sukayi ba ai tunda tun lokacin daka mikata wurin yar uwarka har yau baka taba bin bayanta kaga inda take zaune ba don an hanaka zuwa gani don a samu abun fada min.
To bari kaji malam idan ku dakai da uwar matan naka bakuyi karana ba yau ni zanyi naka a garin nan duk inda kakai min ya sai ka fito min da ita don wanan abin ya isheni.
Ni ga Allah na dogara nasan irin tarbiyan dana ba diyana don bata gaji shashanci ba a gurina balle taje tayi shashanci a birni.
Yanasu yau ke da bakin kike fadin zakiyi karana kan yar cikina a mata ya baci inna tace kwarai kuwa bello ta fadi sunan Abba ba sakaye kamar yadda take kiranshi da malam.
Mamaki ya kara kashe abba jin abindata fada sunan shi gatsau haka babu sakaye data sabayi mai don gabadaya ta birkice masu a gidan.
Wani kalon kalo suka watsawa juna kafin Abba ya kuta yana fita daga gidan inda lanta taji haushi cikin daga murya take fadin tunda har kika zageni dani da iyayyena ke kuwa sai yar taki tayo abin kunya birni an korota ta dawo maki maga ta tsiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.