Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 119 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWAalliya:
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN WUNI LAFIYA ALLAH YA SADA MU DA ALHERIN SA AMIN
LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI YAFI.
Irin samakon da yayi ne ya ba malam mamaki matuka har ya kasa boye hakan a zuciyan shi yakewa ya jafar din ba, daya fito yana fadin.
Kai ka dauka zan sace ma matar takane kayo min wanan samakon hakan a gida ya fada yana dan dariya tare da mikawa jafar din hannu kafin ya juya wurin kanwata da ta rako ya jafar din gidan malam din yana fadin kece yar rakiya ko kika nuna mai gidana.
A cikin dan kunya ya jafar yake fadin malam an tashi lafiya ya kwanan iyali ya amsa da lafiya tare da fadin mu karasa ciki ko malam jafar ya fada yana nuna mai kofan shiga zauren nasa kai tsaye.
Bayan sun zauna suka kara gaisuwa da malam din kafin malam ya fara magana yana fadin ka kyauta da ka amsa kirana da gagawa don mu samu mukai karshen zancen ba tare da kowa yasan meke gudana ba a tsakanin ku.
Don ko yanzu an fara sake zancen a gari saidai wasu basu yarda da hakan ba gaskiya kaga ko a kai karshen abin zai fi.
Gaskiyane malam ya fada cikin dan kunya da dukar da kanshi kasa malam yaci gaba da fadin gaskiya sam baji dadin hakan daya kasance a tsakanin ku ba tun farko.
Ya sake dukar da kanshi kasa don kunya da nauyin malam din da yake ji har cikin ranshi a lokacin.
Nasan fashewan wanan zancen yanzu a gare ka babban nauyi ne da kunya ace dan musulmi ke aikata wanan sabon a doron kasa hakan .
Dan adam yakan manta da irin azaban da Allah ya tahadar mashi tun a nan duniya kafin aje ga lahira ya koma a makomar da Allah ya tanadar masa.
Duk wani jin dadi sabo da bawa zai aikata a cikin sabon shi na dan lokaci ne don yanzu duniyan rayuwan cikin sa kalilan ne.
Ka godewa Allah daya hadaka da wanan yarinyar mai zuciya irin na manya da sanin ya kamata da dogaro ga ubangiji.
Yau da ace watace ba zainab bace na tabbatar da wanan rikicin sai yafi hakan a gareku ya dan dago kai a lokacin tare da fadin gaskiyane malam.
Nasan zainab yarinyace mai karanci da kara agareni wanan yasa nake jin ba zan iya rabuwa da duk wani abinda zatai min ba na tozarci.
Baza a kai ga hakan ba da yardan Allah don yanzu haka zainab tasan abinda kai da iyayyen ka baku sani ba a zancen nan naku.
Ya dago kai da sauri ya kallo malam, malam din yace eh haka zancen yake don abinda bincike na ya nuna min mun tatauna shi da ita nan ranan .
A yadda nasan zainab da tausayi da karamci a rayuwan ta zata duba ma kan hakan sai dai da yake shi dan Adam ajizine ba a yanke mai hukunci ga abinda zuciyar shi ke nasa mai don haka ban san dalilin zainab na aikata hakan da tayi ba a yanzu.
A sanina nasan zainab tayi hakan ne bisa wani dalili nata da ba lalaine mu iyayyenta mu san hakan ba tunda har ta iya boye ma iyayyen ta sirin dake tsakanin ka da ita don har gobe basu san mai kake aikatawa yarsu ba na asha.
Ya dago kai ya kalli malam malam din yace kwarai ko wanan hujan da suka rike ninan na fada masu hakan don kawai a fitar da wani tuhuma ko zargi a tsakanin ku.
Kuma na tabbatar da zainab ba zata taba fada masu sirin nan ba don kawai kare mutuncin ka a idanun su.
Dukar da kanshi yayi yana hawaye don jin abinda malam din ya fada kafin malam din yace na kirakane nan kafin kazo da iyayyen ka a zauna ya kamata in ganka mu zauna a tsara komai a mutunce.
Malam dai bai boye mai ba duk yadda mukayi dashi ya fadawa jafar din komai har makarin daya ba zainab ta bashi sai daya fada mai.
Cikin mamaki jafar din ke tambaya malam kana ganin jifana wani yayi da wanan mumunan akidar yace kwarai kuwa.
Bakai akaso ya shafa ba mahaifinka akai wa da farko sai abin ya dawo gareka kai din anyima naka don duk inda zasu su duba kan iyalin shi farko sunan kane zai haska.
Wanan dalilin yasa suka juyo a kanka suka saki kowa da komai a cikin iyayyen ka don ganin taurarin ka sunfi na iyayyen naka haskawa nan gaba.
Allah ya kawo saukin abin ta sanadiyar zainab data dauki mataki akan ka da wuri wanda ba kowa ne zai iya tsayawa yai maka hakan ba kai tsaye.
Yanzu duk mu manta da wana
n mafita shine abin nema a gareka ya zama dole gareka ka tsaya kasha magani sosai ka dawo mutum kamar kowa.
Tare da kuma neman tsari don kasan mai neman naka na gidan kune ba fasa jifan ka zasu yi ba tunda sun dauki niyar hakan a zuciyar su sai sunga bayan iyalin ku kaf.
Sun dauki lokaci suna tataunawa da malam din kan matsalan nasa da kuma irin matakin da zai dauka don zaman mu ya dore dashi nan gaba.
Nan dai yayiwa malam sallama tare da ajemai alheri amma malam din yaki amsa ko daya daga cikin abinda ya bashi din.
Karshe jafar din yace ai masa sadaka dashi a inda ya dace da niyar Allah ya rabashi da abinda ke damun sa a rayuwan shi.
Nan dai ya kama hanyar airport bai ko leka gidan mami din ba don gaba daya yaji gidan nasu da yan uwan shi sun fita ranshi a lokaci daya.
Sai tunane yake ko mai yaiwa wani da zai masa wanan karen aikin hakan na zancen abokan sa kuma zai yi kokari ya nisanta kanshi dasu in Allah ya yarda.
Ya iso Abuja a gajiye don gaba daya wani irin zazzabine ya rufe shi lokaci guda jan jin wanan maganan da yayi daga bakin malam din mai nauyi haka da kunya.
Dakin shi ya shige ya kwanta ya rufe kanshi kwanan shi biyu bai leko waje ba ya mamud yana zuwa neman shi ace yana ciki bai fito ba .
Ga kuma wayoyin shi duk a rufe lokacin hakan ya tayar da hankalin mamud din zuwa na karshe da yayine ya dawo gida hankali tashi ya samu mami data dau zafi dasu baki daya kan zancen dan uwan nasa don sun mara masa baya kan maganan yana fadawa mami din.
Itama hankalinta ne ya tashi sosai ta mike ba bata lokaci zuwa gidan jafar din da yaranta gaba daya suka tafi hankalinsu a tashi dukan su.
Sunyi dukan kofan da kyar ya taso ya iya budan kofan a lokacin har mami taba da shawaran a balla kofan aga halinda yake ciki a cikin dakin.
Sai gashi ya bude masu da kyar duk ya rame ya fita hayacin sa yayi wani irin baki lokaci guda mami na shiga tana gani yadda dan nata ya koma ta hau fada tana fadin.
Wanan yarinyar ta zama min masifa a rayuwa yanzu a kan wan yar kake kokarin halaka kanka jafar da sauri ya mamud din yace haba mami ba lokacin wanan zancen bane ai .
A samu a ceto rayuwan sa tukun kafin a fadi wani maganan da za, aimai yanzu don yadda ya koma din nan ya kamata yaga likita gaskiya.
No ku barshi ba sai naga likita ba ai na samu sauki sosai ya fada yana gyara zama saman kujeran da ya hau din.
Mami da sai binshi da wani irin kallo takeyi tana mamakin wai jafar ne ke son halaka kan shi akan mace haka ?
Tambayan da jafar din ya jefo matane yasa kowa ya kadu a falon don cewa yayi mami ko zaki tuna ina karami gidan da mukaje akan ban abinci naci har ya zama min matsala a lokacin ?
Abinci a kasan nan ko a can US din ta tambaye shi yace a nan dai mami don ance nayi ciwo sosai a lokacin kan cin wanan abincin da nayi ?
Wanan kuma wani zance ke nan yaushe mami zata iya tuna hakan abinda ya dade dayi ba yanzu ba .
No ni zan tuna jafar ya fada don har ni nayi ciwo a lokacin ai gidan uncle musane mana mahaifin Rufaida daddy yaje damu ranan anty ta bamu abincin daddy bai ci ba yace mu muci tun a gidan mukai ta amai.
Kwarai kuwa ta fada ainayi fada da daddy ku a lokacin kan hakan tunda ba sabawa da irin abincin nan kukayi ba da yasa kukuci.
Ido jafar din ya lumshe na dan lokaci kamar yana tunane kafin ya bude su ya sauke ga yan uwan nasa a daidai lokacin mami ta jefo masa wani tambaya da cewa .
Mai ya faru kake tambaya yanzu babu komai ya bata amsa yana kawar da kanshi gefe daya kowa falon yai shiru yana nasa tunanen a zuciyar shi.
Ita kanta mami abinda ya farune a wanan lokacin yake dawo mata a rai gaban tane ya fadi ta kura dan nata ido a lokacin ne likitan da suka kira don ya duba shi ya shigo dakin.
Bayan yan aune aune yake fadin ya kamata ka huta don jinin ka gab yake da ya hau a wanan lokacin ya kamata ka fitar komai a ranka yanzu don samawa kanka lafiya.
Dan murmushi ya sakewa likitan ba tare daya furta masa komai ba yans gyara kwanciyar da yayi a lokacin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.