Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 68 of 139
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5ï¸Â⃣7ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA BAZAN GAJI DA TUNATAR DAKE KAN HAKKIN WANI BA WANAN LITTAFIN NA KUDINE DON GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA.
Yar uwa kada kiga namatsa da magana don tunatar dake sauke nauyin haki nake fadan wanan kalman a kullun don akwai ranan tambayan hakki ga kowan mu.
Kamar yadda fadila tayi alkawari hakan ne ya kasance don tun safe yati muna sallama kan zata duba haifiyarta da yara.
Sako ta bari a fada mai idan har ya neme ta bata gidan a fada mashi ta tafi duba mahaiyar nata bayan tafiyan ta sai gidan ya koma muna shiru.
Don hakane ba fito ba tunda ni kadaine a gidan kwanciya nayi daga nan barci mai nauyi ya daukeni har tsawon wani lokaci ina kwance.
Ashe shima ya fita zuwa asibiti duban hjy tun safiyan har lokacin daya dawo gidan baiji motsin kowa ba sai yan aiki dake aiyukan su a kitchen da wajen gidan.
Hakane ya bashi mamaki don rashin jin duriyan kowa daga cikin mu ba yasa shi zuwa dakina direct daya fito daga part din shi.
Kofan yake ta bugawa har sau uku ba a bude ba yasa kai tsaye ya turo kofan ya shigo dakin nawa.
Akwance ya hango saman godon nayi ruf da ciki ina sharan barcina hankali kwance sai hannuna dana danne da zai iya min ciwo idan na falka daga barci.
Sai gashina dake daure dan kwalin dana daure ya koma gefe daya da barcin da yai nisa a lokacin ban ma sanda hakan ba.
A hankali ya tako zuwa inda nake yana tafe yana kare ma fuskana kallo mai kama da barcin ma a wahalce nakeyin sa a lokacin.
Da dukawa yayi a hankali yana kokarin dan dagani tare da ciro hannun dana danne saboda dadin barci tare da sauke idon shi a kan fuskana kurruciyana da yake gani ko yaushe ya kara fito mashi fili a idon shi.
Yanayinb Numfashi da naji ya surku min duk da a cikin barci nake lokaci hakan bai hanani sanin bakon yanayi ya surkumin ba a lokacin.
Da sauri ba bude idona a daidai lokacin daya kura min idon shi a kaina shine tsaye a kaina saidai ina ganin hakan kamar duk nauyin barcine mafalki nake a lokacin.
Don haka na mayar da kaina saman hannun shi din da yake kokarin gyara min kwanciyan tare da juyawa a yadda nake kwance din.
Bai san lokacin daya dan saki murmushi a fuskanshi ba don wautan kurciyan daya ga nayi a lokacin har da Ac dakin ya rage min yadda yaga na koma takure na kwanta kamar sanyin yana damuna lokacin.
Saidaya fita daga dakin karan rufe kofan yasani bude idanuna da sauri tare da kallo kofan shigowa dakin.
Ya riga ya fita a lokacin sai kamshin turen shi daya bar min a dakin lokacin yake tashi ta haka na gane cewa ya shigo dakin a lokacin ba mafalki akeyi ba ashe.
Da sauri na zabura na bude idona tare da mayar da hankalina gun agogon bangon dake manne a bangon dakin.
Mika nayi kafin in koma in lafe ina runtse idona a hankali tare da tunanen meya kawo shi dakina a wanan lokacin.
Ganin anyi azahar har ana neman uku da wani abu yasa na mike zuwa ban daki da sauri na dauro alwala don sallah a zahar.
Ban fita ba bayan na idar don sanin da nayi yana gidan a lokacin ya hanani fita duk da na fara jin yunwa a cikina amma haka na daure na lake a dakin ban fito ba.
Banyi tsamani akwai wanda yasan tare da halimatu zamu tafi ba don koni sai a wanan shigowan na san da zancen tafiyan ta a bakin shi.
Ya shigo yana fadin yau ina wanan mai aikin naki ta shiga dago kai nayi na dan saci kallon shi tare da fadi ina wuni yaya.
Saida ya da bata fuska kadan nasan halin malam baushe ne yaki jini maikom in bashi amsa sai kuma na dauko mai wani topic yanzu na gaisuwa.
Bayan ya amsa min tare da maimaita tambayan shi garen ta tafi gaida mahaifiyan ta tace a fada ma kara daure fuskan shi yayi kamar hakan baimai dadi ba.
Kada ku dauki kaya mai yawa don tafiya ya fada yana daidai fita daga kofan dakin nawa daya shigo jin haka yasa nake masa kallon mamaki ta hanyar binshi da idanu.
Ko baki gane abinda na fada bane cewa nayi kada ku dauki kaya mai yawa daya wuce kala biyu ko ukku .
Nida wa kenan na tambaya batare da na shirya tambayan shi a lokacin ba saiji kawai nayi bakina ya subuce min lokaci guda ina tambayan shi.
Dake da sadiya mana ko a nan dama zaki barta kike nufi ya jefo min tambaya kamar a hasale yana kokarin juyawa ya fita daga dakin.
Nan ya barni zaune mamaki da imani ya cika min ciki don ban taba zaton haka ba daga gareshi sai tunane nake ni kadai a dakin .
Wai shin dama haka rayuwan shi yake kodai nine yakewa hakan yanzu don ina matsayin matar shi amma kuma naji ko anty fadila takan yaba kokarin shi sosai garesu kaf masu aiki a gidan.
Sai lokaci na tuno da ita don haka na mike ina zaton ta dawo zuwa wanan lokacin sai bayan magariba ta dawo gidan.
Inda ta leko dakina ta samu ina sallah a lokacin ta wuce zuwa dakinta ban fito ba saida na gama duk ibadan dana sabayi kafin in fito zuwa dakin nata.
Na shiga da sallama tana waya sai ido datayi min nuni dashi in zauna na nufi bakin gadonta na zauna tare da bin dakin da kallo.
Zainab kingani sai wanan lokacin na samu dawowa ko da sauri na juyo inda take tare da dan nisawa nadan sauke a fili na mayar da hankali gareta ina fadin sannu da dawo ya su mama yaran ?
Ban samu ganinsu ba don na fada maki inda zantafi ai tun jiya dan dama mama na bita wurinta na karbi sako tare da fada mata zancen tafiyan ki.
Dan murmushi nayi cikin jin kunyan abinda ta fada taci gaba da fadin tayi murna kwarai dajin haka tana maki fatan Allah yasa ki zauna can daga wanan tafiyan kusa da mijin ki kada ya dawo dake nan kuma.
Nan ma dai kaina sada kasa don nasan abune mai wuya zamana a can tare dashi tunda ba hakan ya tsaraba a tunane na.
Kai yau nasha wahala zainab sosai wurin zuwa wanan kauyen can kauyen Narasawa ne naje don shi can yake zaune yana bada magani.
Da sauri na dago kai don jin abindata fada ina mamaki kuma a raina da irin halinta na kula yanzu a kaina tayi wanan tafiyan tun safe har dare haka ?
Kinsan nasan zaman da kikeyi a gidan nan dole hankalina ya daga dan ganin zai tafi dake can inda babu kowa da zai saka maku ido tsakani ki dashi.
Duk da dai ba tsanmani da zai iya cutar dake ba ko wani abu makamancin hakan tunda naga yana da dama sosai gaskiya saidai riga kafi ance yafi magani.
Hannu ta mika tana jawo handbag dinta data fita dashi zuwa unguwa da safe tare da dauko wani dan kwalba karami tana fadin wanan yace in baki da zaran na iso dashi zaki shanyeshi gaba dayane lokaci guda saura sai ki shafa a fuskan ki amma sai kinyi bissimillah zaki kafa baki ki shanye shi.
Miko min tayi na karba hannu na rawa tace yanzu zaki shashi dan haka kiyi bissimillah kisha yanzu don nasan halinki da rashin daukan abu da muhinmaci zainab.
Dan dariya mai kama da yake na sake a fuskana tare da kokarin bude dan kwalban data miko min ba tare da tunanen komai ba danjin bissimillah datace inyi kafin insha nasan koda na cutarwa ne Allah zai tsareni don bissimillah danayi kadin insha din.
Duk da inada yakinnin tsakani da Allah take taimaka min dinndon naga alama hakan sau tari da yawa a gurinta.
Saida na zuke dan ruwan dake cikin kwalba a gabanta kafin tace makaru ne sosai kingan shinan yana da amfani sosai a jikin mutum.
Sai wanan kuma wanka zakiyi dashi sau uku kinga yau ke nan zaki fara gobe da safe kuma kiyi sai da yamma kuma shike nan kin gama dashi.
Sai wanan gaskiya shi amfani dashi kamar zai maki wuya nake gani zainab don yace zaki shafa ne ta yadda zai iya shakan shi sosai a jikin ki.
Ni kuma naga yaushe har zai shaki wanan din idan kin shafa saidai kawai mu gwada sa,an mu akai kinga kamar yadda zaku shiga jirgin nan har in wuri daya zaku zauna dashi hakan zaiyi tasiri gareshi ko ya kika gani ?
Banda abin fada don haka na kada mata kai kawai da na amince da hakan tunda banda zabi bayan wanan tunda don ni take wanan kokarin haka.
Miko min tayi na karba ina fadin nagode anty tace babu godiya a tsakani mu zainab don nima kin mun kokari sosai shiyasa dole nataimake ki ai zainab.
Kinga aikin nan wallahi ba don ke ba da yanzu na rashi ga baki daya to sai Allah ya taimakeni ke din yarinyace mai dubaiya sosai wallahi.
Don ba karamin rufamin asiri wanan aikin yai min ba wallahi don har mutane suna ganin yanzu na samu wani babban aikine don rufin asirin da suke ganin mu a ciki ni da iyayyena a yanzu.
Saidai ina jiwa karki tafi ki manta dani zainab don kin san mu mata zumuntan mu sai idan muna tarene yafi karfi sosai haka ke faruwa tsakanin mata da yawa wani lokaci idan ana wuri daya anfi zumunta mai karfi.
Saidai saukin abin tunda muna nan tare da halimatun ki zaki dinga tunawa dani don rabuwan mu a yanzu gaskiya zan shiga wani matsala nake gani.
Duk da naji wani iri a raina saidai ya zama dole in fada mata tare da halimatu din zamu tafi yace duk da ban san yadda mami zata dauki tafiya da halimatu din ba idan taji hakan.
A sanyaye nace anty ai dazun ya shigo yana fadin tare da halimatu din zamu tafi can wai bai yarda a barta na ba .
Yanayin fuskantane ya sauya lokaci guda kafin tace min dama nayi tunanen hakan tuntuni don da wuya ku bar halimatu a nan tare damu bakinan.
Shike nan nasan sallamata zaiyi idan zaku tafi don aikina ya kare ke nan a gidan nan dama dan kunake zaune a nan.
Tausayi maganan ta ya bani a kasan zuciyana ban san lokacin danace da ita ba koda ya kama ki bimu can din anty ba zaki iya hakan ba.
Zainab ke nan yanzu har kina tunanen zai aminta da ku tafi dani can idan ma shi ya yarda da hakan idan kin roka min iyayyena nakejiwa da hakan.
Yanzu dai tashi kije kada mu makara kiyi wanka da wanan ruwan maganin kamar yadda malam din yace ban fada maki ba yace ki dage da addu,a da sadaka.
Saidai abune mai wahala a can ki samu wanda zaki bawa sadaka kamar nan hakan yasa nayi tunane idan kina da hali saiki bar dan wani abu anan wanda za a rika bayar maki da sadaka lokaci lokaci.
Ko ba a hannuna ba zaki iyabawa innan ki tana maki wanan sadakan don yana da kyau mutum ya dinga sadaka lokaci lokaci.
Mun dauki lokaci tana dan kara min haske kan abubuwa da dama sai nake jin wani iri a raina kamar nace na fasa badon hjy kakarshi ba babu inda zanje gaskiya.
Nayi kamar yadda tace dani kan maganin yayin da tafiyan mu ya kan kama don sai shirin tafiya sukeyi gadan gadan mu namu idone kawai lokacin.
Karfe uku jirginmu zai tashi zuwa kasan ghana sai ya biya can ya cika fasija kafin mu dauki hanyan tafiya kasan da zamu din.
Ranan kan na shiga damuwa sosai kafin tafiyan mu don yadda zamu rabu da anty fadila wanda ban sani ba ko mun rabu ke nan har abada kamar yadda ta fada min dasafe.
Zama nayi na dafe habana da hannayena duka biyu har hawaye na zubo min a lokacin ban sanda hakan ba.
Kai wanan kuka naki yai min yawa wallahi kada mubi hanya dake kina min wanan kukan a dauka sato ki nayi haka.
Anty fadilace nake tunane yaya ya zamu barta a nan yanzu mu tafi gashi aikin nan dashi ta dogara kuma yanzu, , , ,
Kukane ya kubuce min daga hakan na kasa fadan abinda zan fadi a lokacin don kukan daya rinjayeni a lokacin na rabuwa da matar data nuna min kauna bayan uwata da mami ke nan.
Wani irin kallon banza ya watsa min tare da fadin kinsantane ko ta dalilin wa kika santa ke wai wace irin yarinyace da bata da tunane.
Wani irin sani kake son in mata bayan wanan danayi mata mun saba da ita a gidan nan ta dauke mu kamar yan uwanta na jini tana zama damu tsakani da Allah yanzu kuma ace za a rabamu da ita.
Baiyi magana ba illa fitan da yayi daga dakin ranshi a bace nan ya barni na ci gaba da kukana ba wanda yasan inayi har sai lokacin da tafiyan mu ya gabato mai aiki ya shigo yana fadin ance mu fito da kaysn da za a tafi dashi.
Duk da yahana mu tafiya da kaya mai yawa hakan bai hanani daukan kayan da muke so ba kuma baiyi magana kan hakan ba.
Kuka sosai mukayi lokacin rabuwan mu da anty fadila din kamar ba gobe a ranmu yana ciji mota zaune yana kallon abinda mukeyi din uffan baice damu ba don haushin da muka bashi a lokacin muma yaya ya iya damu ina batun dauko mashi wata yayi ya damu mata duka can.
A airport din mun samu mami dasu hjy a can suna jiran mu sai bayan mun fito daga mota lokacin mami ta bamu baya tana magana da wani da nake zaton dan uwansune .
Muka iso inda suke tsaye gaidasu mama Ramatu nayi har kasa kafin in juya wurin mami din in gaida ita ta amsa a cikin wani irin yanayi ba yabo ba fallasa gareni haka na mike jiki ba karfi na koma gefe daya na tsaya halimatu tana biye dani duk inda nasa kafana.
Bayan mami ta gama magana da mutumin ta juyo tana fadin ita wanan fa ina rakiya tayo maku dai ko ?
Ban bata amsa ba don yadda take magana akwai rashin mutunci a idanunta gareni ya mamud ne suka karaso shida iyalinshi yake fadin.
A,a mai masaukin hjy ashe har kun karaso kuma hjy dai tace sai da kece zata yarda ta je a dubata don bata zuwa gidan gwauro ta zauna ba mata a gidan.
Dariya akasa mata tana fadi da kyar kunga laifinane kan hakan muryan mami ke fadin wai wanan da kuka zo da ita fa tana kallon halimatu din.
Kila da ita zasu tafi mana mami Nuriya matar ya mamud ta fada tana wani yamutse fuskanta ita kamar me kyamar mu.
Dama abinda nakewa gudu ke nan gashi ko ya fara faruwa a mayar da gida kanar kasuwa kowa yazo cin banza ya tafi.
Haba haba mami hakan baida kyau wallahi kema ai gidan ki a cike yake da yan uwa dan ta dau, , ,
Ya jamal bai karasa maganan shi ba mami ta katseshi da fadin jamal ni kake kokarin yiwa wa,azi akan abindana sani kome ?
Ba wa,azi bane mami ya fada yana juyawa don barin wurin ranshi a bace don dashi zamuyi tafiyan ashe .
Wai me ke faruwane kuma ya jafar ne daya iso wurin yake tambaya shiru kowa yayi har mami din dai nuriya ce take fadin mami ke magana kan wanan yarinyar tana nuna halimatu din wai da ita zaku tafine ?
Eh tare zamu a ina zamu barta tunda tare da yar uwanta take zaune dama ni nace a bamu ita don kada zainab din ta zauna ita kadai dama.
Amma ai baka fada min da ita zaku tafiba ko ta fada a dan hasale shima cewa yayi but mami wanan ai issue din family dinane OK.
Zatayi magana hjy tace kai iyami ki bar wanan zancen tunda kinji abinda ya fada daga nan aka fara kiran masu tafiya har aka kawo kanmu.
Duk da na taba shiga jirgi daga kaduna zuwa abuja sai naga wanan din kamar daban ne shi saboda checking din da yai yawa sosai.
Kujeran mu daya dashi su hjy da mama Ramatu suna bayan mu sai na jamal da halimatu a can baya.
Tunda muka zauna tunane ne a gabana shiko system din shi ya bude yana wani aiki a ciki har jirgin ya daga damu na runtse idanuwana a hankali ina tunanen iyayyena da a waya kawai nayi sallama dasu.
Ba wani dadewa ake sanarwa mun iso kasan ghana za a dauki sauran fasinja anan muci gaba da tafiya tun wanan lokacin naga ya lumshe idanuwan shi a hankali.
Jirgin bai dade a nan ba ya daga bayab fasijan sun shiga mukaci gaba da tafiya har lokacin yana a cikin wani irin yanayi da ban kawo komai a raina ba a lokacun kan hakan da yayi din.
Barci ne ya daukeni har ban sani ba na dan kwanto saman jikin shi bai tayar dani ba ya barni a hakan yadda nake don na samu barci sosai a lokacin.
Bumu isa ba sai washegari mun dai dan fita a wani kasa sai lokacin na yaba da karfin halinshi dana gani na zyaa Nugeria a hakan din nabina gaji ga hjy da ake bata taimako don kada ta galabata don jikin da take ji.
Mun isa lafiya kuma mun samu taro a wurin su don har mota uku suka zo taron mu wanan baiban mamaki ba ga dan sanin da nayi koshi waye din .
Kallo kan bani kadai ba harsu hjy da mama Ramatu da jalal da suka saba shiga kasashen duniya saida suka kalli abubuwan mamakin da muke gani a kasan kamar ba duniyan mu daya dasu ba.
Bayan tafiya mai nisa daga airport din muka shiga wani unguwa mai yawan gine ginen zamani sosai na kasan wani katafaren gida aka shiga damu.
Tun abin yana babu mamaki har muka gaji da kallo muka zubawa sarautan Allah ido zuwa lokacin hjy ta gama gajiya sosai don tafiya mai nisa da mukayi.
A cikjn gidan ma munsha kallo don kamar gaba daya yan aikin gidan mazane duk suna saye da uniform a jikin su iri daya.
Wani katafaren falo aka shiga damu sai nake ganin abin kamar a mafalki wallahi ba ido bude nake ba.
A falon ne naga wasu mata biyu yan kasan sun fito suna muna sannu da zuwa tare da kawo muna ruwa da drink's suka aje a gaban mu.
Ban yarda nayi nisa da halimatu ba duk da wuri daya muke zaune dasu mama Ramatu har hjy dake kukan kafanta yana damunta sosai shi kuma bai shigo ba har lokacin.
Muna kanta muna faman mata sannu da jiki sai gashi sun shigo tare da ya jamal da sauri sukayo kanta tare da tambayan meke faruwa da ita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.