Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 79 of 139
Muna zaune a falon don mama tafi son taga mun hadu wuri daya tana jan mu da hira har hakan yakai mun dan saki jiki da ita tunda ma halimatu da yanzu suke daki daya da ita.
Ya shigo da sallama shi duka muka waigo muna amsa sallaman tare da gaidashi da dawowa .
Zama yayi akan daya daga cikkn kujerun falon suna dan hira da mama wanda gaisawane tare da tambayan ta idan ba matsalan komai ?
Naso na share shi amma sai naga rashin dacewan hakan a gaban mama don ko a lahira wani nacin albarkacin wani.
Na mike zuwa kitchen din gidan wanda baifi shigana daya ba tun zuwan mu gidan sai kuma yau din dana shiga.
Na fito daga kitchen din ina saye da dogon rigar atampa a jikina wanda akai mai dinkin free haka tunda na sanyo kai a falon gaba daya ya maida hankalinsa gare ni.
Ya zuba min ido yana mamakin irin girman dana kara lokaci guda har na iso gareshi bai kawar da idon saba a kaina.
Cup din da goran ruwa dana dora a tire na aje agabasa ina fadin ga ruwa yaya bai iya amsa min ba na dago na wuce ta gaban shi.
Ga ruwa nan matar ka ta ajema a gaban ka mama ta fada tana kallon shi duk da ya nuna bani yake kallo ba a lokacin .
Saidai hakan bai hanata fahintar abinda zuciyar shi ke raya masa ba a lokacin sai ji yayi mama na fadin ai haka ya mace take dama.
Gata kamar ba zainab ba dai a yanzu gaba daya ta sauya wa wanda ya santa a baya a hankali ya dauki kofin tare da wani irin yar sanyayyar ajiyan yana bude ruwan.
Falon na bari gaba daya don nasan kons zauna karshe mama zata ce inbisa ne yasa na bar falon ga baki daya na shige ciki.
Wani tunane yayi a zuciyar shi yana kai ruwan a bakin shi da sauri ya aje cup din kamar wanda ya tuna da wani abu a lokacin a ransh ya nufi hanyar part din shi da sauri ido mama ta bishi dashi tana tausaya mashi .
Mutum baida hutu a rayuwa kullun yana cikin aiki haka kamar injin ko lokacin kansa baida shi.
Wanka ya shiga ya fito ya shirya falon shi ya zauna waya yakeyi da mami sun gama ya kira ya mamud sun dan dade a wayan kafin suyi sallama.
Ya dan zauna ya mike dakina ya nufa baiyi zaton ina ciki dakin ba koda ya shiga sai gashi ya hangoni akwance saman gado nayi rub da ciki kamar ina barci.
Kamshin turaren shine ya sanar dani shine ya shigo min daki a lokaci ba halimatu ba dake yawan shigowa wurina idan ina dakin.
Sani hakan baisa na dago a yadda naken ba ina kwance naji yana fadin jiya ina maki magana don kin rainani kika wuce kika barni a tsaye ko waima me kika zauna jira a daki baki shigo da wuri ba ?
Ban iya bashi amsa ba don jin tambayan da yayi min saida ya kara fadin watau ke yanzu ki rainani ko ?
Don kawai kinga in tausayi ki ko har kike son ki wuce matsayin ki a wurina raini nason ya shiga tsakaka .
Sai lokacin na dago ina fadin ni kaina ban san kana da bako ba a part din don da ban shiga ba nayi kwanciyana a nan.
Bakon ki ko nawa ya fada a dan hasale nace kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allah.
Don dukkan mu musulmai muke haramune wani bako ya shiga dakin da yake kebabbe a wurin mu koda yarone balle wanan din da yake baligin kansa ya zauna a tsakiyan mu.
Dabi,un shi ma sam basu hallata ba yadda ya zauna kusan tsirara a gidan daba na muharamin sa ba yana yawo a hakan a tsirara dashi.
Rasa abinda zaice dani yayi yana sauraren yadda nake fada masa magana haka akan abinda shi ya kasa ganewa nake nufi ko ?
Wanan maganan ya kona masa rai sosai a cikin dakewa yake fadin kinsan ni bansan abinda ya dace ba sai ke .
Kada ki kara gigin kai dare kuma idan baki manta ba na fada maki banda saka min ido a gidana ga duk abinda kika gani.
Ban saka ido ba yaya asalima da nasan da zuwan sa na zanyi gigin shiga maku daki ba don hakan ya sabawa addinina ai.
Wani kallo yai min ya juya don a yanzu babu abinda zai fada min da zai kare kanshi ga abindana fada bayan wanan don haka fita dakin shine alherin sa.
Don na fara wuce tunanen sa a yadda ya daukeni da farko ashe kallon mai saman ruwa yake min don na wuce nasa tunanen ke nan shi yana min daukan karamar yarinya sharr ashe abin ba haka yake ba.
Lalai iyayyen arewa na bawa yayansu tarbiyan sanin kai tun suna kana zasu fara fahintar addinin su.
ZAINAB IDRIS MAKAWAYau ya kasance jumma,a tun safe danayi wanka na saka wani dogon riga silk mai taushi bakin a jikina rigan baida kwaliya ko ina a jikin shi.
Falo na fito don ingaida mama da kwana anan din na samesu zaune wanan karon harda ya jamal suna zaune.
Mun gaisa na zauna da kur,ani a hannuna ina jiran karfe tara ya buga indanyi karatu don mun saba da hakan koda nake gidan mami ina karatu duk ranan jumma,a da alhamis a wanan lokaci.
A hankali na bude dama da alwala na nafito na fara karatu a hankali jin suratul kafi nake ja yasa halimatu dake gefena karbewa tana bina a cikin daga murya sosai ta yadda duk wanda ke gidan zai iya jiyo muryan mu.
A kasa nake zaune sai itama ta zamo ta dawo kasan a kusa dani ta zauna munayi a tare har yakai matan dake kitchen din gidan da mamakin mu suka fito suna leken mu daga kofan.
A daidai wanan lokacin ya fito part dinshi a hankali yake takowa jikin shi yana saye da farar suith kal sai yar jakar da yake fita da ita rike a hannun shi.
Da mamaki yake karasowa inda muke jin yadda muke karatun mu hankali kwance kuma cikin rashin damuwa da kowa muke karatun mu.
Take yaji jikin shi yai sanyi lokaci guda sai faman tunane yake a zuciyanshi tare da fadin yaran nan haka suke da ilimin addini ashe ?
Idan ko hakane akwai aiki a gabana don dole watarana zata fahinci wani abu daga gareni wanda iliminta zai iya haska mata hakan.
A hankali har ya sauko ya kai zaune saman kujera hankalin shi yana gurin mu yana jin karatun yana taba mashi zuciya kafin ya juyo yana fadin antashi lafiya mama ?
Kafito mama ta fada tana dan gyara gyalen jikinta data yafa a jikinta tare da gyara zaman ta sai halimatu ta dago tana gaidashi ya amsa tare da fadin yau karatu ake munane a gidan nan haka ?
Ta danyi dariya tana noke kai mama ke fadin ai gara suyi don karatu a gida yana saukar da rahaman ubangiji ga kowa dake gidan.
Sadiya ai akwai kokari ko karatun bokon nan haka takan dameni dashi a daki wani lokaci har ta isheni.
Ya kara kallon halimatu din yana dan murmushi sai a lokacin ya jamal da hankalin shi kega waya ya dan dago kai yana gaidashi.
Ya amsa kafin ya mike ya nufi wurin cin abinci don ya karya ba tare da kara furta wa dan uwan nasa wata kalma ba daga gaisuwa da sukayi kawai inda shima ya jamal din ya mayar da hankali ga abinda yakeyi.
Ina kai aya na mike a hankali na nufi dining din na sameshi zaune yana waya da wanda naji ya kira da philis.
Abincin na soma budewa har lokacin ban bude bakina munyi wani magana ba dashi sai kokari zuba mai abincin da nakeyi a plate.
Ina gamawa na juya don in koma in karasa abinda nakeyi na jiyo muryan shi yana fadin zanan zainab.
Cak naja na tsaya a wuri daya kafin in juyo inda yake ina fuskantar shi don jin abinda zai fada min a lokacin.
Kujera ya nuna min da hannu saida na kalli kujeran duk da na gane me yake nufi da yin hakan na dan gusa zuwa wurin kujeran na zauna.
Kin karyane ya tambayeni kai na girgiza mai alaman a, a da sauri yace sai zuwa yaushe zaki karya din ?
Sha biyu na bashi amsa a takaice ina kokarin tashi naji ya kara fadin ke baki gudun yunwa yaja maki ciwone, ki debi abinci gayanan gaban ki kici ya fada cikin daure fuskan shi gareni.
Ba musu na jawo plate zuwa gabana na fara diban abincin na zuba kadan duk yana kallona na mayar da warmer din na rufe naji yace wanan ne abincin da zakici din ?
Kai kawai na gyada don ban son maganan komai dashi a yadda nake jin kaina don na gama fahintar yana da rauni a bangaren addinin mu sosai
Tunda har zai iya nuna tashin damuwa kan abinda ya aikata min na kawo wani kato a dakin da nake a cikin sa nayi magana ya nuna hakan ba komai bane a gurin shi.
Ko yanzu ma shiyasa na koma ga Allah don yayi min mafita gareshi dama wa yanda yake mu,amula dasu baki daya ko ranan haka maza suka shigo muna gidan kai tsaye bai nuna wani damuwa akan hakan ba .
Gashi kuma shidin ashe mashayine na kwarai ban sani ba wanda nake zaton ko yan uwanshi da iyayyensa ma basu sanda hakan ba dan dama dama ya jamal da shima a lokacin yace ya fara sanin halinsa ke nan.
Wata kilama yana da wasu halin na boye da ban sani ba tunda ina jin yadda anty fadila take yawan fada a kanshi ko yaushe.
Inko hakane ni wace irin wawiyace da ban fahinci mai take kokarin nuna min ba a lokacin to ta yaya zan sanda hakan tunda bata fito fili ta fada min gaskiyan maganan ba kai tsaye.
Da babu abinda zai kaini biyo shi kai ko gidan shima ba zan zauna ba don abin kunyane a kauyen mu aji wai mashayi nake aure ni Abu.
Bansan sanda na girgiza kaina ba na furta bani ba zama da mashayi a rayuwana sai naji yace me kike fada ?
Sai lokacin na tuno a gaban shi nake na dago ido na kalleshi ya dago kai ya tsareni da idon shi sun kada sunyi ja a lokaci guda yana son tantance sanadin maganana na zuciya da har ya fito fili.
Why zainab kike son ki ja matsala a tsakanin mu har mutane sunyi muna dariya musanman mami idan taji wani abu yana wakana a tsakanin mu haka sai suyi muna dariya ita da abokanta damasu mara mata baya.
Nasan kinyi hakuri sosai da kika iya boye wanan zancen a zuciyar ki kin nuna min ke din mace ce jaruma a cikin mata duk da karancin shekarun ki kuwa .
Don haka ki daure ki min addua Allah ya rabani da wanan halin don kece mutun ta farko da nake bukatan adduan ta bayan mami, don ni kaina bansan lokacin da nayi zurfi ga wanan dabian ba a rayuwana.
Idan ka hangomu zaune wurin dining din zaka dauka wani hiran mata da miji mukeyi a tsakanin mu a lokacin.
Don har mama dake kallon mu daga inda take zaune don shi ya jamal tuni yabar falon ya fice daga gidan tun zaman mu a wurin.
Cikin mamaki na dago kai ina mashi kallon mamaki don jin ya ambaci waini matarshi ce a yau a karo na farko zamana dashi.
Nace am not your wife dan dama dama ka kirani da sister ka zaifi sauki garemu hakan .
Cikin daga hannu kada mama ta fahinci make faruwa a tsakanin mu yace dani to to naji dama aike kanwatace tunda ke din yar mamice.
Yana fadin haka ya mike don gudun kada asirin shi ya tonu a gaban mama da halimatu dake can zaune dan nisa damu.
Nan ya wuce ya barni zaune na tasa abinci a gaba ina kallo naji mama na fadin har zaka fita ke nan yau dai ka saka zainab karyawa da wuri haka.
Bata son cin abinci bansan meyasa hakan ba ta saba zama da rashin karyawa da wuri tun a gida.
Tun daga wanan ranan ya saka min ido kan karyawa da safe na dai gane yana neman wani hanya na dan shakuwane a tsakanina dashi don haka na kara shan nin jikina dashi.
Allah da ikon sa sai ga hjy an sallamota gida taji sauki sosai kamar ba ita bace akazo kasan da ita a tallabe.
Dawowan hjy gidan ya kara muna sakewa da an,nashuwa ko yaushe muna kusa da ita tana kara jan mu a jiki tare da bamu dariya da barkwanci kamar yadda muka saba a baya da ita a gidan mami kafin mu bar gidan.
Saidai tsakanin ya jafar da ya jamal har yanzu babu jittuwa a tsakanin su suna dai gaisawa sama sama a tsakanin su.
Tun hjy bata farga da har yanzu babu shiri a tsakanin su ba har yakai yanzu ta soma fahintar suna nan a yadda suke sai ta soma zargin akwai wani abu dake faruwa mai girma a tsakansu.
Babban abinda yafi damunta shine ni kaina ta fahinci irin zaman da mukeyi dashi na wasa da hankalin mutane gashi idan ta fambayeni sai ince mata lafiya muke zaune dashi.
Don haka tasha alwashin tambayana don jin irin zaman da mukeyi a tsakanin kafin shi ta tunkareshi tasan ba zata fahinci komai a bakin shi.
Ranan ya jamal zai fita da mama data matsa ya kaita wani shago daya bata labari nima nace zan bisu zuwa shagon muyi kallo.
Saida muka shirya hjy tace na zauna gida ba zamu barta a gida ita kadai ba badan naso na zauna din don naso fitan tunda a gaban yaya mukai maganan fitan har nace nima zan bisu y yarda.
Bayan fitan sune tasa na debo fruit muna na debo a cikin bowl biyu na shigo dashi falon hjy kan tana shan nata saidai ni na saka nawa a gaba sai wasa da spoon din hannuna nakeyi ina faman tunane.
Hjy ta aje cibin dake hannun ta ta tsura min idanu na dan wani lokaci sai ta lura ban ma san tana kallona ba a lokacin.
Abu lafiya kike kuwa shiru ban dago kai ba ta kara fadin Abu nace meke damuwan ki haka kike wanan tunane haka ?
Abu fa ta fada a karo na uku tana tafa hannayen ta idon ta a kaina firgigit na dawo a cikin hankakina ina dago kai tare da duban inda hjy take zaune.
Ni take kallo a cikin mamaki baiyane karara a fuskan ta kafin tace dani me kike tunane haka yar nan kinga mu kadai ne a gidan nan yanzu.
Ki saki jiki ki fada min abinda ke damun ki a rai ki dauka ni din mai baki shawaran da zai fitar dake daga hakin damuwan da kikene .
Ko yanzu kin daina daukana a matsayin kawarki jafari ya kwace min ke kin daina yayina sai shi kadai ?
Da sauri nace a, a hjy har gobe kina nan a matsayinki na kakata a zuciyana yanayin fuskana kawai ta kalla ta fahinci akwai wani abinda ke faruwa a tsakani mu da yayan.
Duk sai nabi na tsargu da irin kallon da take min a lokacin don haka sai na dukar da kaina kasa ina ci gaba da wasa da cibin dake hannuna.
Zainabu hjy ta sake kiran suna na dago kai a hankali ina amsawa da na,am tare dan kallon ta tace .
Kinga ki fada min meye damuwan ki da mijin ki kada ki boye min komai ki daukeni tankar nice na haifi mahaifiyar ki ko mahaifin ki.
Na dan gyada kai a hankali alaman gamsuwa a gareta kan abinda ta fada taci gaba da fadin tun zuwan mu ina kule da yanayin yadda kuke zaune dashi.
Nayi shiru na tsayin lokaci kaina na a duke a kasa ina dan guntun tunane anya zan iya fada mata matsalan mu kuwa ko banza fa itace ta haifi mahaifiyar shi.
Kuma ta nuna tafi son shi a cikin jikokin ta kaf idan na fada mata a wani yanayi tsohuwar zata shiga don jin jikan nata ashe mashayine na gaske.
Don haka na yanke shawaran fada mata wani abin na daban na dan dago kaina tare da fadin hjy bana cikin matsalan komai dashi
Ta dan tsura min ido na tsawon lokaci kafin tace kin tabbatar da hakan zainabu na gyada mata kai kawai sai naga tayi murmushi kadan a fuskanta kafin tace dani.
Amma ni ga dan nawa fahintar sai naga kamar har yanzu babu wani mu,amulan aure dake wakana a tsakanin ku illa kawai gaisuwa da dan kulawa a gaban mu koba haka bane zainabu ?
Da sauri na dago kai na kalleta sai kuma na dukar da idona saiga hawaye yana zubo min daga idanuwana lokaci guda.
Ai kinga irin ta zainabu ina son ki sani ni mace ce yar uwan ki kuma manya sunce kowa ya rigaka kwana yana rigaka tashi.
Hjy babu komai da dawani matsala ai zan sanar dake kawai dai ni karatu nake son inci gaba dashi yasa nake tunane na tsunci kaina da fadin haka a gareta.
Hjy ta kalleni ta girgiza kai tare da fadin to shike nan amma kada ki dawo da baya kina dakin sanin kin fada min gaskiyan da bakiyi ba.
Koda yake dai mai daki shiyasan inda ruwa ke masa yoyo ai idan kinfi bukatan ki tafi a hakan dake dashi aiga fili ga mai doki sai mu zuba ido mu gani zainabu.
Ban yarda abinda kika fada ba a yanzu domin ni nasan kin boye min ne kawai don kina daukana ta bangaren jafari nake.
Amma ni nasan da akwai abinda kike boye min a zuciyar ki namiki tambayan amsan daya ce ki bani sai baki ban ban ba kina kawo min wani zancen karatu.
Karatu kan ai dole kiyishi zainabu tunda kina auren wanda boka ya huda ko jiyan nan naji yana magana akan karatun ki har nace ya barki a nan basai kin koma gida kinyi a can ba nan kusa dashi zaifi mai saukin yawan sintirin da zaiyi idan kina can Nageria din.
Da sauri na dago kai a karo na barkatai na sauke kan hjyn don jin abinda ta fada na wai in zauna nan tare da yaya a kasan mutane inda bansan kowa ba.
Eh hakan nace kuma ya amince da hakan don haka idan zamu koma ba tare dake zamu tafi ba a nan zamu barki keda kanwarki.
Amma hjy da baki fada masa haka ba don shi kanshi yayan zaifi bukatan zamana a can gida da nan din ya dai amsa makine don baya iya mussata maki zancen ki gareshi .
Eh hakan yana da kyau tunda harkin fahinci hakan keda kanki sabanin ke da yanzu kika fara daukana a wani matsayi na daban.
Zainabu nasan ki nasan halinki don haka ban yarda da abinda kika fada ba a yanzu.
Domin ke kullun yar ba komai ne saidai duk wanda yasan ki ya dubeki a yanzu yasan da akwai matsala a tare dake zainabu.
Na dauka nice mutum ta farko da ko ban tambayeki ba zaki iya budan bkin ki ki fada min halinda kike ciki da mijin ki a gidan shi.
Tunda ninayi tsaye har wanan auren naku ya kullun a tsakanin ku saboda ni nasan halinki da nasa da kyau don ke yarinyace da bata gama mallakan hankalinta ba har yanzu.
Hawaye naji sun taru min a idanuna lokaci guda ina tausayawa kaina halin kuncin da nake ciki a wanan lokacin da abin zai fadu tabbas hjy kece ta farkon da zan fara fadawa wanan maganan a yanzu.
Amma a fili nace da sauri na mayar da hawayen nawa ban yarda sun digo a gabanta ba sainace hjy addu, a kawai zaki tayamu dashi a yanzu nan gaba idan bai daina ba zan fada maki insha Allahu.
Bayan ta dan tsura min ido tace to shike nan Allah yai maki albarka kin nuna min kedin mace ce ta gari mai rikon amnan mijinta ako wani hali ta tsunci kanta zata iya rike mai sirin sa a rayuwa.
Madalla dake zainabu insha Allahu hakkuri ki ba zai tabe a banza ba kici gaba da hakkuri da addua kuma kada ki yarda ki saka damuwa a ranki kinji.
Har muka bar wurin hjy tana min kallon tausayi don nasan tana da magana a zuciyar ta saidai ban bada daman hakan ba a lokacin.
To me zan fada mata ince ga yadda jikan ta yake ai saidai tajishi a bakin wani na sani ko in fada ta sake ribcewa ciwon dayafi wanda ta taso a yanzu.
Dakina na shiga cike da tunane na dan watsa ruwa tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah azahar sai uku da rabi su mama suka dawo da sayyaya mai yawa tare dasu.
Ban fito ba don tunanen da nakeyi kan zancen mu da hjy ba abinda ya tsaya min a rai sai zancen karatuna da zanyi a nan .
Shike nan yanzu babu zancen komawa gida a garemu ke nan sai tsawon wani lokaci anya kuwa zan iya daurewa in zauna da wanan mashayin haka?
Idan na zauna a nan dagani sai shi ta yaya zan iya shawo kansa babu kowa nasa a kusa dashi irin ya jamal da zai saka mai ido kan abinda yakeyi tunda ni ba zaiji magana na ba.
Ya zama dole ke nan a gareni in kara jajircewa akan yadda zaman mu zai kasance a yanzu bayan tafiyan su hjy da mama.
Zan kuma kara sa mai ido inyi iya kokarina wurun rabashi da wanan halin da yardan ubangijin mu sai dai babban matsalana a yanzu shine rashin layin waya da banda shi a tare dani.
Don ina son muyi siri da malam mijin mai zube sai kuma matsalan anty fadila da nake son ya dawo da ita kusa dani don da taimakon ta zan iya samun nasaran abinda na dosa a yanzu.
A takw dabara ya fado min a rai nace da hjy ya kamata na hada wurin shawo kan shi ya yarda fadila ta dawo nan mu zauna tare da ita .
Ko abunuwa zasu zo min da sauki yadda nakeso don tafini sanin ta kan duniya ko naso yin abu bazan iya ba don hankalina baikai na hakan ba a yanzu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.