Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 139
ANCAU
Tunda safe na samu masu kitso don haka na zauna muna kitson ga innan mu tana aikin girkin gida don yau Abba yayo cefane ana dafawa aci duka gida.
Ditin mota mukaji a kofan gidan mu sai dai bamu dauki hakan wani abu ba don ba wanda zaizo gidan mu da mota ai.
Haka yasa muke zaton ko makwabtan mu motar tazo yin wani abu sai can mukaji sallaman mata na shigowa gidan namu lokaci guda.
Amsa masu sallama mukayi dani da matan da nakewa kitso sai inna ta dago dan ganin masu shigowa gidan lokacin.
Tarbon su tayi tana fadin wa nake gani yau kamarsu hjy safiya garin namu ?
Ba kama bane mune dai din kike gani don kasancewar su kamar tobasai tunda tana auren yaya a garsu.
Dakinta ta kaisu don Asabe bata gidan lokacin ba laifi don dakin inna duk da yawan mu koda yaushe tsab yake don tsabtan ina yara basu hanata gyaran daki da tsakar gida har din muka koyi hakan.
Don ko a kauye akwai masu hali irin na yan birni da zaka samu a talauci amma komai nasu yana tsab.
Tabarma ta shimfida masu saman sumintin dakin dake sheki sai dan kamshin turaren wutan dake tashi ba wani mai kamshi ba amma duk da hakan ba laifi dai dakin don ba zakace dakin mai yara bane.
Ruwa ta kawo masu a kofin silver tana fadin ga dai ruwan namu babu sanyi don har yanzu yayan naku baija wuta ba gidan nan.
Ikon Allah duk wutan nan daya kewaye garin nan ba a ja maku wuta ba har yanzu inna dai bata ce komai ba kada zancen yayi nisa a hakan.
Safiya ta dauka ta dan kurba kadan ta mikawa anty Sa, a kaita girgiza alaman ba zata sha ba ta aje kofin a gefen ta.
Lokacin na sakewa matar kai nazo don in gaidasu da zuwa a dakin innar mu din .
Saida nakai har kasa na fara gaida su da zuwa anty safiya na fadin wai kada dai ince wanan ce nan wa take da sunama don mantawa da sunana da tayi a ranta.
Inna tace ki dai tuna don kinsan niba fada maki zanyi ba dai ta fada tana mikewa don barin dakin.
A hankali nace Abu sunana gwaggo tace naji dayan da ake kira da anty sa, a tace min haba wani irin Abu kuma keda kanki kike batawa kanki suna haka?
Zainab din ne kike kira da Abu wai kamar sunan wani abu can daban wanan ai suna tsofine nagani.
Nidai na fita ina dan murmushi don jin may suke fada a gatin nan kan wa zai tsaya kirana da wani zainab can.
Nakai kofa naji tana tambayana ina yan uwan ki suke nake fadin suna makaranta na fita daga dakin kai tsaye na koma inda nake kitso .
Yaro inna ta nema ta tura a kira mata Asabe datace zata shiga makwabta tana jin lokacin da take fadawa Lantana hakan.
Ba, a jima ba sai ga Asabe da dan saurin ta ta shigo tana fadin bakin daga birni su waye umma yayan kine su safiya inna tace.
Sai lokacin na tuna dasu da suna yawan zuwa gidan muna kanana amma daga baya suka daina zuwa ban san dalilin hakan ba garesu.
Suna ina Asabe ta tambaya inna ta nuna mata dakinta sai ta dan tabe baki ta nufi dakin inna din .
Muryan lantana ne ya dakatar da ita shiga dakin lokacin lantana na fadin umma kin dawo ashe ?
Na dawo yar nan yanzu yaro ya sameni wai nayi baki daga birni sai lantana tace au baki akayi ashe mu dake gidan ma bakin ciki ya hana a sanar damu.
Dago kai nayi na kalli lantana da take maganan don nasan da innan mu take wanan maganan haka.
Asabe ta shiga basu dade ba suka fito zuwa sashen ta tare da bakin sai lokacin lantana ta tafi gaida su.
Don a nata nufin bazata shiga dakin innan mu ta gaida bakin da zuwa ba don innan mu bata kai mata can ba .
Inna tana gama abinci ta zuba masu a kwano mai kyau ta dauka takai masu ta dawo ta debi ruwa ta sake kai masu a can.
Abba ya shigo gidan yana fadin yanzu ake fadamin anga munyi baki a gidan yasa na garzayo in ga su waye suka zo.
Can ya samesu a aurin Asabe suka zauna sun dan dade a tare kafin su fito suce zasu tafi sai da suka sake shiga dakin innan mu sukai mata alheri kafin su fito su tafi din.
Bayan kwana biyu naji lantana na fadin duk kyau da bokon wasu ga aikatau zasu kare rayuwan su karshe ma su kare ga auren maigadin gida.
Dagani har innan mu kallon juna mukayi lokaci guda don ba wanda ya fahinci may zancen ta ke nufi a lokacin.
Share ta kowa yayi abu kadan yan kwanajkin nan zata ce kyau wasu ya kare ga banza tunda zasu tafiyin bauta a gidan wasu.
Banga wanda ya isa ya tura min dana yawon bauta ba a gidan kamar banda kowa a duniya har dai ranan da dare muna zaune muna hira a dakin inna gaba dayan mu inna ke fadin.
Nikan wanan zancen bautan da amaryan baban ke fadi na rasa gane inda maganan ta ya dosa da fadin haka ko yaushe .
Wanan inna ai ita ko ba dalili kirkiro magana take ta yabawa mutane don kawai ayi fitina tunda bata son a zauna lafiya ita na fada.
To dan wataga za,a tura yin bauta da take fadin haka inna karma magananta ya dameki don Allah saratu ta fada tana jan tsuki.
Shiru mukayi kowa na nazari a cikin ranshi kan zancen don innan mu tafimu fahintan da akwai wani abinda zai faru da diyan ta don haka kawai bai saka lantana tayi ta gorin haka a tsakar gida.
Aiko ranan da safe baba yai kiran mu nida innan mu yana lungun Asabe muka tafi don amsa kiran Abba din.
A zaune muka same su a dakin kowa yai shiru saidai yanayin su ya nuna kowa na cikin bacin rai a lokacin.
Wuri muka samu muka zauna nikan ina daga kofan dakin don ban shiga ba a lokacin inna tace gamu malam.
Zuwan lantana yasa yayi shiru ya kasa maganan da zaiyi sai Asabe take fadin kayi magana ka tsaya kana wani kimbiya kumbiya kamar kana tsoron matar taka da yarka.
Ke yahanasu bawani abu bane yake son fada maku ke da yarki sai zancen tafiyan yar ki birni da nace a turrata aikatau.
Koba komai zai dan samu abinda zai rage saya mata kayan daki a nan tunda kunki bari ya aje komai gashi sun cika muna gida zagada zagada dasu.
Aikatau kuma umma ina ta fada da mamaki karara a fuskan ta sai naji asabe tacd eh aikatau ko yar taki tafi karfin yin sikatau din ne.
Ina ko tafi umma wanda yake nema ya samu duk wata za,a lalo mashi yaji dumus ai yafi zaman wanan kitson da takeyi kullun tana tara muna munafukai a gida lantana ta fada daga inda take.
Koba zaki bari ta tafi bane Asabe ta fada a hasale tana duban inda inna take zaune.
Abba yayi karfin halin fadin a barta suyi shawara da yarta umma don kinga daga sama sukaji wanan maganan yanzu.
Shawaran me zasuyi wanda yafi wanda na fada yanzu a gaban ta kuma ko kuma sai abinda tace zamubi tunda itace ta ajemu bamu ba.
Ai shike nan tunda kace haka dama ni kai nakejiwa nake tausaya maka tunda hakan ne kawai zatayi ma a matsayinta na ya mace ta taimakawa rayuwan ku na dan lokaci.
Umma ai Allah daya bamu su yasan yadda zai iya mana dasu basai mun kaisu inda bamu san kowa ba don neman abin duniya.
To mara kunya akan yar fadin ki kike kokarin musayan magana dani to kiji ki karaji zuwa birni babu fashi ga Abu.
Idan ta samo kudin bakuso ku bani wani ya hana ki haifota a namiji halan birni daine kamar taje tagama yanzu haka na fada babu fashi ga zancena kuma.
Inyaso idan ta tafi ta shiga duniya karewan rashin sanin kowa inds zata ke nan aikatau daine sai ta tafi.
Wani kuka ne na fashe dashi lokaci guda don jin hukuncin da asabe ta yanke min yau a gidan mu.
Ta hanani karatu don wani manufanta yanzu kuma zata turani birni yin aikatau do kawai a musgunawa innan mu.
Daki inna ta sameni ina rusa kuka itama kukan ta shigo dashi a dakin muka taru muka rasa wanda zai ba wani hakkuri a cikin mu lokaci guda.
Sai nice nayi karfin halin fadin inna kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zan tafi yin aikatau ba a birni.
Yar mairo me nayiwa umma take min haka a raguwana ko yaushe take kokarin sai taga bakin cikina a rayuwan ta.
Ita ya mace ba diya bace da za ai alfahari da ita cikkn zuria da wasu basu gane hakan.
Ban taba bakin ciki da nadaman samun ku a diya matan da kukazo min ba don ban san kyautan da Allah yai min ba don haka bazan butulcewa Allah na ba.
Amma umma kulun magana ya tashi a gidan maganan ta daya ne shine na cika masu gida da diya mata bafa san yadda zatayi da diya matan da nake haifo masu ba.
Innan mu kiyi shiru ki barsu nasan munafuncine aka kula a turani yin bauta a gidan wasu.
Koda Allah ya nufa zan tafi inna nayi maki alkawarin kula da kaina a duk inda na samu kaina din.
Balld ba zaki tafi ba yar mairo muddin nina haifeki ba zaki tafi wanan bautan da umma ke nufin kije ba don kawai ta musgunawa rayuwan mu a gidan nan.
Innan mu don Allah kada kice zakiyi wani abinda auren ki zai tamu gun Abba tunda shima ya nuna baison hakan a gaban mu amma asabe tace sai na tafi.
Kiyi hakkuri ki bini da addua a duk inda zasu kaini ya zama kariya a gareni ko yaushe.
Sai naji ta kara rushewa da wani kukan nima kukan na fara lokaci guds mun dauki lokaci a haka a dakin.
Ranan da wanan bakin cikin gaba dayan mu muka kwana tare da tunanen ina za,a turani shine abinda ke damuna a raina .
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.