Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 139

ANCAU KADUNA STATE

Kamar yadda Asabe ta sha alwashi akan Abban mu dole sai ya kara aure hakan ne ya faru don Asabe taje nema mashi auren yar wata mata da ta dade tana zawarci batai aure ba a kauyen mu.
Tun innan mu bata san wanan zancen ba har yakai ta sani saboda bakin Asabe dake sake suratai barkatai na rashin ilimi da jahilci tare da kiyayya ga inna damu diyan ta.
Da yake Allah yayi inna mu mace ce mai hakkuri da kawar da ido ga komai koda tasan kaine ke cuta mata din.
Sai ma bata nuna tasan Asabe nayi ba a gidan don bata nuna damuwata ga abinda Asabe ke yawan fadi ba ko yaushe.
Mu kan mu bamu tsira ba gurin Asabe don tana nuna muna tsana karara kamar ba jinta muke ba mudin .
Daga zagi sai dungura dan abu kadan yanzu zata sauke muna bala,i a kanu komai mukayi bamuyi daidai ba.
Ainihi Asabece mahaifiyar data haifi mahaifin mu ta hayayyafa da dama basa tsayawa da sun dan tasa an yayesu sai zazabi ya kama su su mutu.
Sai ya kasance ga mahaifin mu ta samu ya fara tsayawa sai mace da muke kira da gwaggon birni don a birni take yanzu da mijin ta daya samu wani ubangida a can ya daukesu bayan aure ya mayar dasu a birnin.
Sai ya kasance mahaifin mu yanzu kawai a gaban ta sai yan jikoki da take dashi ta tsatson shi wanda kiyayyan fitowan mu diya mata a duniya yasa bata kaunar mu har cikin ranta.
Ni dana dan kawo wayau a cikin mu nasan halin da muke gidan na zaman Asabe da innar mu don su sauran yan uwana gorin inna bai taba tayar masu da hankali ba sai ma kawai ja baya da sukayi da al,amarin ta.
Don yawan fada da zagi da take muna a gidan duk da Abba ya dan kewayewa Asabe gefen ta ma,ana ya dan raba tsakanin mu da ita sai dai hakan bai hana Asabe fitowa zaman sa ido ga inna damu.
Wajen karfe dayan rana kasancewar yau asabar muna gida bamu zuwa boko mun dawo islamiya tun sha daya muna gida.
Ina daki ln mu na yara don shigata ke nan na gama wanke tufafin mu da suka dan taru nayi wanka ina shafa mai.
Naji muryan innar mu tana kwala min kira da yar mairo na amsa da Na,am inna daga dakin tare da saka hijjab a jikina na fito da sauri.
Ina fadin gani inna tace yi maza ki dauku abincin nan ki kaiwa umma kada yayi sanyi nace tau inna tare da dukawa na dauki kwanon samiran abincin Asabe.
Munace mata Asabe ne don dukka gari haka ake kiranta dashi in ka debe Abban mu da innar mu koshi Abba sai zuwan inna ne gidan ya canza mata suna dama da Asaben yake kiranta.
Na isa kofan Asabe ina ta sallama bata karba min ba haka yass na kunna kai dakin na aje mata abincin a gefen kofan ta kadan ko waige banyi ba na fito daga dakin.
Dawowa nayi na karasa shirina kafin mu zauna cin abinci tare da yan uwana don a tare mu hudu ake hada muna abinci don yana kawo dankon zumuci inji manya sukace.
Muna gab da gamawa sai ga Asabe tun kan ta karaso wurin mu take kwalawa inna kira cikin tashin hankali.
Gaba dayan mu hankalin mu ya koma gare ta muna duban hanyar kofanta tana zuwa take tambaya wa yakai min abinci a dakina ?
Cikin sanyi murya irin na innar mu da kusan kowan mu ya gado hakan take tambayan Asabe wani abin ne inna ?
A hasale asabe ke fadin tambaya nakeyi wa kika aika yakai min abincin don yanzu na aje dankali na fito bangani ba .
Haka yasa nasan duk wanda yakai min abinci shine ya daukan min shi dama an dade ana min sata a daki ina hakkuri banda dama in aje yan kwabbaina sai in nema in rasa.
Da sauri na furta Allah ya tsareni da daukan abin wani nina kai abinci kuma ko kallon dakin ki banyi ba na fito.
Ke rufa min baki kwadayayya satan naku har yakai haka ban sani ba dole in kira mai gyara ya saka min kuba a kofana don watarana kada kuyi min wanda yafi wanan.
Wani irin bakin cikine ya rufe ni a lokaci daya ina jin idona kamar zai rufemin a wurin don satan dankalin da Asabe ta laka min.
Da ba don nasan itace ta haifi mahaifin mu da naja mata Allah ya isa a gurin duk da hakkurin inna saida tayi magana wanan karon.
Haba umma a gabana yarinyar nan ta shiga takai maki abinci ta fito kuma ban ganta da komai ba a hannun ta.
Ai dada goyon bayan ta zakiyi ta fara mugun abu tun a gida idan yayi karfi sai ta zauna maki a gida ai don babu mai kwasan barauniya yakai gidan shi.
Abbane yayi sallama ya shigo ganin mu cirko cirko a tsaye bai hannashi fadin yanzu dankaline har yai yawa haka a gidan aka barwa Akuyan umma tana ci haka?
Gaba dayan mu kallon Asabe mukayi don jin abinda baba ya fada nan kuma ta fara kame kame tana fadin .
Hannu na dora akai na fasa wani uban ihu ina fadin Asabe mai nayi maki kika dafa min sata a gaban kowa.
Ashe akuyan kice ta daukar maki dankalin ki kazo kina fadin nice na satar maki harda kudi nake shiga dakin ki in sata.
Abba ya daka min tsawa tare da fadin ke ke meye haka kike fada da sauri kanwata Fatima dake bi mun take fadin Abba yanzu fa Asabe ta gama fadin wai Abuce ta sace mata dankalin ta a daki daga kawai takai mata abincin ta da innarmu taba takai mata.
A wani irin yanayi na bacin rai da mamaki lokaci guda Abba ya juyo yana fadin sata kuma umma ?
Ina yaran ne jinin kine umma koda itace ta daukar maki ai ba zaki kira hakan da sunan sata ba.
Ta daka mashi tsawa tana fadin yi min shiru wanda baisan abinda yakeyi ba.
Yau aka fara sata min abu a gidan nan bana magana don gudun irin haka in magana ku karyatani a gaban diyan ka da matan ka.
Waya sani ko itace ma ta dauko din ganin za,a ganeta ta jefawa Akuyan nawa.
Allah ya sauwaka Abba yace ya nufi hanyar dakin su bai shiga ba ya duka ya dauki buta zuwa ban daki.
Asabe ma ta juya zuwa sashenta tana fada inda take shiga ba nan take fita ba wai Abba da innar mun suna lalatamu da gurbatacen tarbiyan da suke bamu.
Inna kan daki ta shige tana kuka hankan yasa dole na tsayar da nawa hawayen don komai ya wuce a ran inna.
Tun faruwan wanan abin na ja baya da lamarin Asabe ba ruwa na da tsabganta iya kana da ita gaisuwa ban yarda in shiga ko lungunta.
Muna kallo idan jikokin ta na birni sukazo yadda take ji dasu take nuna kamar su kadaine ta haifi uwarsu sam mu bamu isa mu rabe ta ba.
Shi yasa ake fadin kakanni sun fison jika na wurin diya mace don ni na tabbatar da wanan maganan gun kakantamu.
Sannu sannu har lokacin Auren data nema wa Abban mu ya karaso buki ya tashi sosai Asabe ita tayi uwa tai makarbiya don Abba yace shi baida zarahin kara aure a yanzu.
Ta saka aka tayar damu daga dakin da muke kwana munaji muna gani aka gyarashi tsab wace kullun take kukan bata da kudi sai gata ta fitar da kudi don kawai taga ta kuntatawa innar mu rai .
Sai fadi take Allah dai ya kawo amaryan Abba tazo ta haifa masu magaji a gidan ko suma zasu shiga fagen zurian dake tun kaho da diya maza a gari.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.