Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 54 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

4️⃣5️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

FATAN ALHERI GAREKU HAR ABADA YAN UWA MUSULMAI ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA ALLAHUMA AMIN, , , , , ,

LITTAFIN NAN NA KUDI NA YAR UWA IDAN BAKI BIYA BA KADA KI SHIGA HAKKIN WANI DON ALLAH , , ,

Zan iyacewa gaba dayan mu dakin mun shafa da zancen zuwa wani bako da yafada a jiyan do bamu dauki abinda muhinmanci ba a rayuwan mu.
Sai gashi kawai an kwadawa Abban mu sallama da sassafe ya fita zuwa waje ya dan jima sai gashi ya shigo yana kwalla min kira kamar a kidimance shima yake a lokacin.
Da sauri na dago daga saman raggan katifan da nake kwance na sa,adatu data barmi in kwanta don ina bakuwa a cikin mu.
Abba ina kwana nake kokarin fadi yayi da Abba ya dakatar dani da fadin yar sani wasu mutanene suka zo min da wani zancen yanzu a waje wai maigidan ki ya turosu daga birni zasu duba fili a nan kusa ko wani wuri za aiwasu aiyiuka ko ?
Da sauri na dago kai na dan saci kallon Abba din dake tsaye ya kura min ido don jin karin bayani daga bakina a lokacin.
Kai na girgiza tare da fadin Abba ban san da wanan zancen ba gaskiya na fada dan azauna lafiya kada Abba yayi zargin wani abu innan mu ta hada a lokacin.
Ko wani zargi yazo ya shiga wanda hakan zai iya jawowa innan mu wani matsala a rayuwan ta tunda ba zanso hakan ya faru ba.
Baki da labarin hakan Abba ya fada a cikin mamaki tare da kara kallon yanayin da nake tsaye kafin yace ikon Allah .
Ya juya ya tafi ya barni a wurin runsunne kafin in tsinkayi muryan lantana daga sashinta tana kwalawa Abban mu kira da dan karfi kamar tana bashi umurni.
Abba dake a rude a lokacin bai samu amsa kiran nata ba sai fita da yayi zuwa waje ya nufi gidan dan uwansa a nan cikin unguwan namu.
Hakan baiwa Lantana ba naga ta yafa zani ta bi bayan Abban sai dai ganin bakin datayi a wajen gidan namu wanda wata kila ta firgitane da ganin fuskokin su a lokacin.
Sai gata ta juyo da sauri ta dawo cikin gidan dama da daura gaba kawai ta dan yafa wani ragga a kanta tana rike da danta a hannu jalo jalo, ta fita daga gidan .
Ba kunya ta nufi sashen Asabe don gulma innan mu sai aikinta takeyi ba tare data mayar da hankali ga abinda ke faruwa a gidan ba lokacin.
Bamu san meta fadawa Asabe ba mundai ji Asabe na fadin subbahanallahi da safen nan haka baki a cikj bakin kaya idan dai ba wani yai masa cune ba aka turo akama min shi.
Umma lafiya inna ta fada a daidai lokacin da Asaben ta fito a rude daga wajenta lantana na binta a baya.
Ina fa lafiya yanzun nake jin mugun labari a bakin yar nan wai wasu baki da bakin kaya sunzo sun tasa dan nan a gaba zasu tafi dashi.
Anya kuwa umma haka zancen nan yake yanzu fa ya fita nan naga ya kira yar sani yana tambayan ta wani magana kafin ya fita.
Koma dai menene barin leka wajen in gananwa idona abinda ke faruwa dashi din haka tunda safen nan.
Bayan fitan Asaben itama sai gata taja ta tsaya don irin mutanen da suke wajen gasu Abban mu a gefe daya tare da wasu yan unguwa suna magana a tsanake.
Haka asaben ta fita tana ratsa mutane a dan gigice tana tambayan abinda ke faruwa ba wanda ya koma ta kanta karshe ma suka kwasa suka shiga mota zuwa gidan maigari.
Nan suka bar asabe tare da wasu yan tsirarun mutane a wurin yan gulman da basu gane komai ba ala dole ko sai sun gano hakan suji kwam.
Sai kusan sha dayan rana mudai tun muna saka rai da dawowa Abba har muka koma daki don mu karya masu wanka kuma suka shiga yin wanka don ka,idar innan mu ce tasa ruwan wanka kowa yayi wanka kafin rana ya dago.
A wanan lokacin ne Abban mu ya dawo gidan ko yanzu shigowan ujula yayi yana kokarin fita daga gidan Asabe ta dakatar dashi.
Abban ya dawo tare da dan mata bayani a takaice tare da fada mata cewa umma ba komai bane sai alheri haihuwace ke kokarin nuna dadin ta a gidan nan yau.
Do yaron nan mijin Abu ne ya turo a sai fili a kusa damu nan za, ai masa wani aiki a wurin wanda bansan me za,a gina maiba amma dai aiko maiye dai karuwa mune ai.
Hakane inji asabe ta fada tana gyada kai alaman gamsuwa da maganan shi tana fadi ikon Allah .
Akan ya mace ne wanan baiwan ya sauka a gidan nan haka duniya kabar mutum a inda ka gansa don baka san baiwan da Allah yai mar ba.
Ranan dai mutanen basu bar wurin ba saida suka tabbatar da an fara aiki yadda suke so sukayiwa kowa sallama suka bar garin da yamma lis.
Injiniyan sa zaiyi aiki da ma,aikatan shi aka bari bayan sun samu masauki inda zasu zauna ko washe gari haka suka tashi da aiki wanda hakan ya jawowa mutanen unguwar mu ciniki a wurin su da safen .
A kwana biyu da fara aikin kwantsan saiga shi a garin yazo dagashi sai wani abokinshi saikuma security dinshi da yazo dasu inda kallo ya dawo garesu.
Zatinshi, izzashi da wayewa da kamala uwa uba ilimi da isa ya kara hakashi idon duk wanda ya ganshi a lokacin .
Duk wanda aka fadawa wai shine mijina bai yarda don sam ansan shi din ya wuce ajin aurena saidai idan an masa dole a kaina sai ya aureni da wata manufa dai.
Zancen zuwan shi yabi gari lokaci daya duk wanda yasan da hakan saida ya tofa albarkacin bakin shi kan zancen auren kowa da irin abinda yake fada kinsan kauye da samun magana.
A ranan bayan ya gama ganawa da iyayyena tare da zaga aikin ginan da akeyi babu kama hannun yaro don kudi na shan kashi sosai ga aiki ga kayan aiki sai shigo dashi ake tun ranan da aka fara aikin.
Ganin zuwa matar malam illiya yasani shan jinin jikina sosai don abinda malam din ya fada min ranan da naje gidan shi din.
Ba wani bata lokaci muka hada tafiya inda halima ta nace saita bini nan dai aka kwasa sai karshe aka yarda mu tafi tare idan matar malam zata dawo su dawo tare.
Ba takura ga zaman mu don motar mu daya ni matar malam da kanwata motar daya sai scurity din dake gaban motar a zaune tare damu.
Munbar kauye da zance a bayan mu tafiyan dan lokaci ya kaimu kaduna na dauka ba zamu tafi gidan mami ba kamar zuwan mu.
Sai gashi mun sauka a gidan inda muka samu Nazifa da anty salma kawai a gidan Rufaida bata nan sunce bata faye zama gidan ba yanzu sosai.
Sunyi matukar mamakin ganin mu a lokacin saidai sa yake a tare muke dashi daga mu harshi babu fuskan yun wani zance a lokacin .
Na dauka zama kwana kaduna sai baya munyi sallah munci abincine anty salma ta shigo tana fadin wai ya J yace mu fito zamu tafi.
Ba a cikin wani sakewa muke ba dukkan mu har anty salman da take min kallon mamaki a fakaice ta kasa ko dan sakewa damu Nazifa kan tun ganin farko da mukai mata a falon ban sake sakata a idona ba har wanan lokacin.
Rufaida dasu Ruby sun zo gidan gulma sun samu mun wuce don ko mami dake Abuja har labarin zuwan mu gidan ya isar mata a lokacin.
Sai ashar ta kundumawa dan nata damu tare da fadin a fada mai maza mu bar mata gida kafin ranshi ya kaiga baci.
Ba wanda zai iya fada mai sakon har muka bar gidan don dama da abinsa zaiyi a kadunan yasa muka tsaya a nan.
Karfe takwas na dare muna a cikin wani rantsetsen gida da ban san ko a ina wanan gidan yake ba haka mudai namu idone kawai.
Alhamdullahi komai a kwai a gidan babu ne kawai babu ga gidan da girma duk da darene bai hana mu gane hakan ba.
Irin su cultizen su club ko Iliminaties, dai da sauran su ai zubur mami ta dago tana fadin what, what, mami ta kara fada tana gyara zama jalal yace yes of course mami don yanzu ai kinsan duniya saida wanan kuma muddin sunan har zaiyi fice ka kaiga wani matsayi nan gaba.
Kirji ta dafa tare da fadin innalilllahi wa inna,alaihim rajin sai ra hada da mikewa tsaye a daidai lokacin kuma shi ya mamud ya shigo falon tare sa jamal.
Jalal ke fadin mami nifa bawai nace hakan bane naga kin daga hankalin ki sosai kwatance kawai nayi maki ai da hakan ya fadi a cikin damuwa.
Mami kan ta shiga wani hali a lokacin don bata masan me take fadi a gaban diyan nata ba a lokacin.
Mamud naci amanan mahaifin ku nayi sake da zamani ya cuceni ta fada tana komawa zaune yarfan saman kujera a cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali.
Jalal ya mamud ya kalla tare da fadin kai wai meke faruwane hakane naga mami a wanan yanayin ?
Ina fa daki kwance yazu ta kira ina zuwa take tambayana wai irin su culties din da turai da saura Asian countries ke sashi nake mata bayani shine na ganta a hakan ?
Da sauri ya juya inda mami take zaune yake fadin haba mami hakan ai ba kyau ki fara zargin dan cikin ki da kanki har duniya ta zarga mai hakan akan shi.
Mamud idan har jafar ya kasance a cikin irin wanan kungiya bazan taba yafe mashi ba a rayuwana ku sani.
Haba mami ki bar wanan magana don Allah ko akan dan wani ne balle naki yana illiminaties zai dinga sallah jamal ya fada .
Da sauri ta mayar da kallonta gun jamal din tana fadin Allah yasa hakan ne jamal na shiga uku da wanan yaron abinda ban taba zato da tsamani ba a cikin zuriata yana kokarin faruwa dani haka.
Jin sam batun na mami yai yawa yasa ya mamud dagowa da sauri a cikin bacin rai yana fadin kai jalal take her to her room kai jamal zo muje ya fada tare da fara tafiya.
Jamal din ya mara mai baya nan suka bar mami da Jalal yana kokarin lalashin mami din don ta daga su shiga part din ta su kaucewa idon yan aikin gidan a falo.
Ranan dai haka suka kwana a cikin tashin hankali a don kosu hankalin su a tashe yake kan wanan zancen sabanin mu dake gidan nasa tsundum ciki zaune sai damuwa da kewan gida kawai a lokacin ne a ramun babu wani tunanen komai a tare damu.
Kusan zance zuwa da matar malam.yai min dadi don sai ta zame min kamar hjy data tafi ga kuma halima da ba abinda ya dame ta a rai sai faman zuba surutu da tambayayoyi da takeyi hankali kwamce tana ci da sha duk ko da dare ne muka shigo gidan bai hanata bude ciki ta dura abinci ba.
Duk da munga shigan shi gidan a lokacin hakan baisa ya kwana nan tare damu ba gidan mami ya wuce ya kwana a can kamar yadda ya saba kwana din .
Da safe dan uwan shine ya tayar dashi daga barci ta hanyar buga mai kofa ya fito da mamaki yake kallon ya mamud din dake tsaye a kofa ciki damuwa.
Lafiya dan uwa ya fada bai bashi amsa ba tasa kai zuwa ciki dakin kai tsaye ya bishi a baya daga inda ya barshi tsaye a kofa .
Zama sukayi suna fuskantar juna na dan lokaci kafin mamud di yace kai abubuwa fa suna son baci a bangaren mami don yanzu kokarin zarga wani zance takeyi.
Daga baya ke nan ya fada yana mikewa tsaye don ni yau zan bar kasan nan da dare zan koma baki aikina ba zan dawo ba sai yarinyar nan ta gama zana exam din ta zanzo in tafi da ita.
Ya zakayi da mami mamud ya fada yana kallon dan uwan nasa yace cikin ko in kula akan mefa ?
Komai ma kana ganin zancen nan data dauko zata barka ka koma idan kuma har ka tafi kabar yarinyar nan baka gudun wani abu ya biyo baya .
Wani abin me zai biyo baya matace fa ba zaman kowa takeyi agarin nan ba yanzu sai zamana don haka duk wani mataki daya kamata na dauka akan hakan na riga dana dauka a yanzu ko.
Saida ya mamud din ya dan kurawa kanin nasa ido na dan lokaci kafin ya ware hannayen shi yana fadin shike nan har idan ka shiryawa hakan ai ba matsala.
A shirye nake ga duk wani barazanan da mami zata iya kawo min kan wanan matsala ya kare da fadin OK ga dan uwan nasa sai ya gyada mai kai alaman gamsuwa.
Bayan fitan dan uwan daga part din shi ya dade zaune a wurin yana dan tunane a ranshi kafin ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa jikin shi tare da shiryawa kafin ya fito.
Kai tsaye part din mami ya nufa daga nan dakin yana rufe yasan tana gida don babu inda take fita idan ba wani dalili ba a irin wanan ranan ta jumma,a.
Da sallama a bakin shi ya turu kofan tare da dan rike hannun kofan kafin ya sake turawq ya shigo cikin dakin gaba daya.
Tana zaune a cikin shirin ta na doguwan riga leshi sai mayafin kayan dake saman jikinta da alama dai shirin fita take a lokacin itama duk da baranan fitan ta bane yau.
Tunda mami ta hango dan nata taji gabanta ya fadi don kwarjin sa sai kara fita fili taga yana mata tunda zancen auren nan nasa ya taso .
Wanda take gani a yanzu zancen sa ta fara zargi nasane ya fara baiyana mata hakan gareshi don wani asirttacen baiwa nasa da yanzu ta kara hangowa gareshi.
A hankali ya kai zaune a gefenta yana kamo hannunta tare da fadin mami antashi lafiya ya gida ya aiki ba tare dajin shakkar komai ba.
Cikin basarwa mami din ta jaye hannun ta tana fadi kalau nake tunda yanzu kana ganin kakai ba zaka iya bin umurnina ba koka fada min idan zakai abu.
Jiya me ya kaika kaduna ba tare dana san zaka shiga ba sai kawai wai inji kana min gida da wanan shegiyar yarinyar kauyen.
Yasa na ce ace kabar min gida tun kan na bata ma rai daga kai har ita sai in saba maku ba wani aiki bane gareni hakan.
Mami ai ba wanda ya fada min sakon ki sai yanzu nake jin hakan garwki but iam sorry hakan ba zai sake faruwa ba insha Allah.
A hankali ta lumshe ido cikin jin wani irin yanauin amsan daya bata din a cikin rashi damuwa da furcinta garshi ke nan.
Yau kaduna zan tafi ta bashi amsa tana mikewa daga inda take zaune lafiya dai mami zaki tafi kadunan ya tambaya cikin son jin amsan da zata bashi.
Eh akwai abinda zai kaini mai muhinmanci can yau din idan na gama da wuri yau din zan dawo garin nan.
Tana magana a cikin wani irin yanayi dake nuna akwai abu a zuciyar ta sake damun ta a lokacin shidai shiru yayi bai tankata ba a lokacin yana zaune a inda ta barshi.
Saiga jalal ya shigo dakin kallo daya yaiwa yayan nasa ya kawar da kai a cikin tsarguwa mami take fadin dauki jakkar can fita min dashi gurin mota kafin in fito.
Ok mami ya fada ya nufi jakkan ya dauka Allah Allah yake ya bar dakin a lokacin don a tsarge yake kada yai laifi a wurin yayan nasa kuma don ya dauka mami ta fada mai komai zai zargeshi.
Bayan fitan dan uwan da kaya shima ya mike yana fadin mami Allah ya tsare hanya ya dawo daku lafiya sai dai yau da yamman nan na nake son in, , , , ,
Jafar wani kungiya ka shiga da ban taba sanin kana a cikin wani hali ba sai daga bayan nan nasan da hakan tare dakai ba.
Mami kungiya kuma name ya fada yana kallon ta a ciki mamaki karara a fuskan shi don jin abinda ta fada mai din game dashi.
Wani cultu kakeyi jafar don jikina ya bani wani abu a game dakai ba dadewan nan ba.
Mami ya fada a cikin mamaki tare da fadin cult kuma ai da ina cikin wani cult din daba haka ba da yanzu na wuce sanin kowa a kasan nan ni wanan baya gaba ko kadan ya fada yana hade rai ya nufi hanyar fita daga dakin ta bishi da kallo kawai da nazari a zuciyar ta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.